.......An kai ruwa rana kafin asamu na farfad'o, ina farfad'owa kuma sukamin allurar barci domin nasamu Hutu.
.......An kai ruwa rana kafin asamu na farfad'o, ina farfad'owa kuma sukamin allurar barci domin nasamu Hutu.
Sai a lokacin hankalin iyayena yad'an kwanta.
Baba k'arami da yagama birkicewa akan shifa bazai yardaba, saiya maka iyayen Haidar a kotu. wannan wane irin tozarcine haka? sunzo sun kar6i kayansu, anbasu batareda anduba wulak'ancin dasukayiba, shine kuma dan rashin mutunci shi Haidar d'in zai jamusu 'yarsu ta salwanta, to shifa bazai aminceba.
Hak'uri Dady da Abbanmu suketa bashi suna tausarsa akan yayi hak'uri, su d'auki hakan matsayin k'addara kawai, indai mijine ALLAH zai bani wani ai. k'ilama shid'in ba alkairi baneba agareni dama.
Innarmu dai tun tana kukan zuci harya fara fitowa fili, mama Rabi'a nata tausarta.
'Yan gidanmu babu Wanda ya biyomu sai maman fauziyya, har innaro k'in zuwa tayi.
Ban farfad'oba sai gabanin magriba, lokacin su Abba na shirin tafiya masallaci, na bud'e idona ahankali, da innarmu na fara tozali, sai mama Rabi'a da maman Fauziyya a gefenta, Munubiya na gefen gadon danake kwance rik'e da hannuna ta kifa kanta ajikina alamar barci ya saceta ahaka.
Nan komai yashiga dawomin sabo a zuciya, fashewa nai da kuka mai tsuma rai, cikin dasashiyar murya nace “shikenan innarmu, shima na rasashi, Haidar yatafi, yakuma ce har abada bazai ta6a dawowa gareniba, mi muka musu suka za6i mana wannan sharrin dabazai ta6a barin rayuwarmu ba? yarigada yazame mana tabo a tarihinmu, ya ALLAH ka gaggauta saka mana akan duk mai hannu akan buga jaridarnan, wlhy Haidar ban aikataba, sharri sukaimin, dan ALLAH karka barni, ina sonka wlhy, sosai nake sonka, dan ALLAH mama Rabi'a kuce masa sharrine, ban aikataba, Munubiya dan ALLAH karkubar haidar yatafi, ina sonsa wlhy.......�.
Kuka Munubiya takeyi sosai, dan tunda na fara magana ta farka, dama barcin nata bawani nisa yayiba. Innarmu kam tashi tayi tafita tana share hawaye, maman Fauziyya na rik'e dani tana lallashi. Mama Rabi'a ma kuka takeyi saboda ganin 'Yar uwarta Na kuka.
A haka su Abba suka shigo suka samemu inata wannan sambatu, da rok'on akiramin Haidar, dan wani masifar sonsa nakeji a lokacin, fiyema da son Dana masa muna tare.
Duk saida nabama su Abba tausayi, Dady ya zauna akujera tareda rik'e hannuna.
“Munaya ya isa haka kinji, kiyi hak'uri, ki yarda da k'addara, dama can ALLAH ya rubuta shid'in ba mijinki baneba, insha ALLAHU mijinki nanan zuwa soon. Ubangiji nason bayinsa masu hak'uri, wata rana komai zai zama labari tamkar ba'ayiba kinji�.
Ahankali na fara sassauta kukan danakeyi, ina sauraren lallashin Dady, sai ajiyar zuciya danakanyi lokaci-lokaci.
Bayan doctor yazo ya dubani yace abani abinci nasha magani, sunaso nakuma samun isashen barci danna samu na kuma hutawa. Saboda jinina yahau gaskiya.
Hankalin su baba k'arami yakuma tashi, ace 'Yar k'aramar yarinya dani amma da hawan jini, (ALLAH yay gaggawar sakamin akan duk mai hannu akan wannan tushen matsalar).
Da k'yar aka samu nasha shayi, nasha magani barci yakuma kwasheni.
Sai kusan 10pm su Abba suka tafi gida, akabar Mama Rabi'a da Munubiya zasu kwana dani.
***°••�***°•••�***°••�***
Yana shirin fita asibitin sai ga Momma tadawo gida, tun yana sakkowa daga benen ya hangota zaune afalo itada jakadiya, da alama magana sukeyi.
Takun takalmansa da k'amshin turarensa yasasu juyowa suka kalleshi gaba d'aya, ya k'araso cikin falon cikeda takunsa na asalin jinin sarauta cikakke. Kujerar gefen Momma ya zauna yana fad'in “Momma yaushe kika shigone?�.
Idonta akan d'an nata tana nazartar yanayinsa tace, “ban dad'e da shigowa ba, nama zata barci kakeyi ai? danJakadiya tacemin tuni kana gida�.
Guntun tsaki yayi yana lumshe ido, tare da kuma jingina kansa jikin kujerar, ahaka yace, “wlhy kuwa Momma, nad'an tsaya wani aikine aciki�.
Idanu ta tsira masa domin hango damuwa k'arara a fuskarsa. “Muh'd mike faruwane? mike damunka?�.
Idanunsa da har yanzu suke da sauran ja ya bud'e, yasaki murmushin gefen baki, “babu komai Momma, mikika ganine?�.
“bakaso dai nasani kawai Muh'd�.
Yad'an narke face alamar shagwa6a, “please Momma ki yarda dani mana�.
Girgiza kai kawai tayi tana murmushi, “to na yarda dakai. yanzu sai ina?�.
“dama zanje hospital ne, dan inaga zanje Goa gobe idan ALLAH ya kaimu, maybe kuma na kwanama�.
“ok. ALLAH ya kaimu to, dama muna magane da jakadiya akan akawo wasu sabbin bayin, kaga aikin yanama su Samha yawa a gidannan Muh'd, gakuma makaranta, idan suka fita kaima ka fita sai gidan yay shiru, gashi mukuma muna Asibiti�.
6ata fuska yayi yana gyara zamansa, “Amma kuma Momma bakwa tunanin a kuma samun matsalar datafi ta baya? kiduba kiga dad'ewar da mukayi da wad'ancan, amma hakan bai hanasu munafuntar muba�.
“Humm Muh'd kenan, wancan karonma bawai dabararmu bace ta tsaremu, muyi hak'uri akawo koda guda 20ne, maza 10 mata 10�.
“kai Momma, amma har 20 ma?, ina laifin 5 kawai, idan sukayi yawa gidanan hayaniya zaiyi yawane�.
“wane irin 5 kuma Muh'd?, yanzu badan laluraba data kawomu nan ta ajiyeba konan da can ka isa matsawa batareda bayi ko dogaraiba, sha'anin gidan sarauta sai hak'uri, wlhy tunda aka kwashe bayinan gidan saiyayi wani iri, tamkar bana masu sarauta ba, yanzu haka kullum k'orafin Mimi kenan adawo da bayin gidanan�.
“momma kenan saboda Aunty Mimi za'a maidosu?�.
“kusan haka to, saboda ita saboda buk'atunmu muma ko�.
“shikenan, sai a dawo damasu min hidima idan naje ko?�.
“a'a baza'ayi hakaba, idan an kwasosu kaikuma idan kaje kuma fa? wad'ancan munriga da mun yardaba da amarsu, idan mun maidosu nan kafin mu samu masu amanarsu zamusha wahala,, amma idan nan aka kawo mana wasun zamu saka ido sosai akan su yanzu ai?�.
Kai kawai ya gyad'a mata batare da yace uffanba. saikuma zuwa can yace “inaga nima next week zanje Nigeria �.
“Nigeria kuma Muh'd? mizakayi?�.
“murmushin gefen baki yayi yana kallonta, kwantar da hankalinki Momma, 3days kawai zanyi na dawo, wani d'an aikine zai kaini, ko masarauta bazasu San najeba ma Dan ba a can zan saukaba�.
“Amma Muh'd baka kudin abinda zaije ya dawo? kuma kana ganin zaka iya Shiga Nigeria kafito batareda kowa yasani a masarautarku ba?�.
“kimin addu'a Momma, insha ALLAHU lafiya lau d'anki zanje ya dawo kinji, kuma zanyi taka tsantsan d'in yanda bazasu San najeba insha ALLAHU�.
Murmushi Momma tayi, tace “to shikenan, ALLAH yabada nasara akan abinda za'aje, yakuma tsare mana kai. amma nikam Muh'd yamagar yarinyar nan da aka muku 6atancinnan tare?�.
“ban saniba Momma, dan ni ba saninta nayiba fa�.
“amma dai gaskiya ba a k'yautaba, yarinyarnan dukda anazargin da had'in kanta yakamata anemi iyayenta ai, amma ba ayi burus da lamarinta ba, kuma wannan aikin Kaine yakamata kayishi tunkan kabaro k'asar alokacin�.
“Nima nayi tunanin hakan daga baya Momma, amma wlhy a time d'in hankalinane yatashi sosai, sai dai karki damu, a wannan karon zansa amin bincike akanta�.
“hakan yafi kam gaskiya, bara na kimtsa saimu wuce k'ila kafin mu tafi su Sauban sun dawo. antafi d'akko Khaleel kuwa?�.
“ai da sauran time Momma, kuma nifa yanzu nace aringa kawoshi a school bos, dan kinga mu ba kullum Muke gidaba, ga khumar har yanzu bai dawoba, inaga jikin mahaifiyar tasa yayi tsanani shima�.
“kama tunamin wlhy Muh'd, yakamata koda kaida Sauban ne kuje Ku dubata, wannan shine adalci da zakama Wanda yake k'ark'ashinka idan wani Abu yasamu rayuwarsa�.
“Hakane wlhy Momma, zamuje insha ALLAH, miye ma sunan k'auyen nasune?�.
“nikam nad'an manta, amma bari zan tanbayi jakadiya kota rik'e�.
“ok tom shikenan�.
Tunda Momma ta shige saiya maida Kansa ya kwantar jikin kujerar, yacigaba da tunaninsa datum d'azun yake cin zuciyarsa da ruhinsa. baya buk'atar shawara da kowa akan wannan maganar gsky. to amma koya fad'ama Harun?. kai a'a, inma fad'arne Muftahu yakamata ya sani, tunda shine ya d'ora akan aikin, kuma shi kad'ai yasan komai akan yaran, to amma ba komai ne Na sirrinsa Muftahu ya saniba ai. (zuciyarsa tace, to ai wannan baikai girman sauran sirrikanka ba, kuma abune daza'ayi Na k'ank'anin lokaci yawuce, tunda ka yanke shekara d'aya ne ko biyu), iska ya furzo daga bakinsa yad'an dafe kansa dayakejin yana Neman fara masa ciwo.....
★★★★�
Washe gari natashi da d'an sauk'i, sai dai har yanzu hawayen sun kasa barin fuskata nida 'yar uwata Munubiya. mama rabi'a ce keta lallashinmu da mana nasiha, ahaka su Ayusher sukazo kawo mana break fast itada Feena, ya Marwan ya kawosu.
Daga gidanmu kam ko ruwan zafi babu Wanda yakawo har kusan 10, sai kuma ga Fauziyya itada Jameela k'anwarta, sukace inji mamansu, tace ayi hak'uri Mubarak ne shima babu lafiya.
Mukace mun gode ya jikin Mubarak d'in?.
Fauziyya tace, “da sauk'i, tare suke da maman tasu, sunacan zasuga likita�.
Anan su Fauziyya suka zauna ana hira dayake weekend ne babu school, kusan hirar duk akan abinda haidar yayine shida iyayensa, dagani har munubiya bamu saka musu baki, ni hirarma k'onamin zuciya takeyi.
Yaa marwan dake zaune a gefe yanata latsa waya tamkar baya jinmu yamik'e, kallon Munubiya yayi yace “zo mana�.
Saida yafita sannan ta mik'e tabi bayansa, su Ayusher suka sanya dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.
Nidai bance komaiba, saibin 'Yar uwata da kallon tausayin zama da wannan mai shegen miskilancin nayi. zama da irinsu yaa marwan sai mai hak'uri wlhy.
A ranar da daddare aka sallameni muka koma gida, sai dai 'yan gidanmu maman Fauziyya ce kawai tazo, amma ko innaro batazoba. sai bayan an sallamemu su Dady sukaji babu Wanda tazo dubani. kuma Maman fauziyya Ce kawai me kai mana abinci, dukda ba ranar aikinta bane haka take dafa mana su fauziyya sukai.
Aiko ranar sunga tsantsar bala'i, dan su Abba birkice musu sukayi suduka ukun, har Dady da ake gani mai hak'uri. ita kanta innaro saida tasha jinin jikinta ga 'ya'yan nata.
Nacigaba da samun kulawa wajen innarmu da 'Yar uwata Munubiya, duk hanyar dazasubi Dan samamin farin ciki ita sukebi, burinsu kawai suga Na manta komai, hakama iyayena maza, sai yazama kowa tausayina yakeyi acikinsu, yayunmu mazama babu laifi, suna nunamin kulawa dai-dai gwargwado.
Ahaka nafara rage wasu damuwoyin.
Satina d'aya kenan da dawowa daga asibiti, duk na k'ara ramewa Na fige, hakama Munubiya, saika d'auka tare muka kwanta ciwon.
Ahaka muka tak'ark'ara muka koma makaranta, ayanzu kam maganar gsky bana fahimtar karatu, saboda damuwace tsatstsage da zuciyata, nasanma nida aure kuma har abada, kowa yafito haka za'a sokeshi ya janye, ita dai 'Yar uwata Munubiya ALLAH ya taimaketa na gidane yace yana sonta, itama nasan da yanzu an soki lamarin, musamman daba banbancemu jama'a sukeyiba. Nagodema ALLAH da abinnan bai shafi rayuwar Munubiya taba sarkin hak'uri, tabbas danafi haka shiga tashin hankali, bansan yanda zan musalta muku k'aunar danakema 'Yar uwataba, ina sonta fiyeda zaton mai tunani, wlhy zan iya fansar da raina awajen kare nata, kamar yanda nasan itama zata iya yin hakan agareni.
Yau ta kasance juma'a, dagani har Munubiya bamuje makarantaba, saboda tatashi da ciwonkai, tun muna primary idan d'aya bai da lafiya d'ayan bazaije school ba, komin zare idon ko dukanmu da za'ai kuwa, wannan abinne yazame mana jiki har girmanmu gashinan.
Bayan nagama gyaran 6angarenmu innarmu tace Na shirya naje nakaima wata k'awarta sak'o.
Badan nasoba Na kar6i sak'onnan natafi, saboda banajin dad'in tafiya nikad'ai arayuwata, tunda nataso nayi wayo ko ina zamuje sai nida Munubiya ne, mawuyacine kiga d'ayanmu tafita batare da d'ayaba.
Tafiya nake tamkar zan fasa kuka, gani nake kowa nikad'ai yake kallo, sanye nake da jallabiya bak'a datasha adon honey color d'in duwatsu, Na nad'a Veil ruwan zuma shima, haka ma takalmana masu d'an tudu ruwan Zuma, sai lady's bag d'ina, ahankali nake tafiyar cikeda takuruwa, ahaka nazo bakin titi domin samin abin hawa.
Banfi tsayuwar 15minutes ba saiga taxi, ganin babu kowa a taxi d'ina kamar karna shiga, amma sainayi addu'a kawai nashiga, gudun karnazo nayi sakin Na hannu kamun na guje.
Munyi nisa da tafiya naga mai taxi d'inan yak'i d'aukar kowa, gashi anata tsaidashi, kumani bance masa drop na d'aukaba gaba d'aya.
Cikin dakiyar zuciya nace “bawan ALLAH miyasa bazaka tsaya ka d'auki mutaneba? bayan kuma gashinan anata tsaidaka�.
Ta madubi ya kalleni yana murmushi, sorry hajiya, kekad'ai aka bani izinin d'auka ai�.
Da mamaki nace “kamar ya?�.
Dariya yad'anyi sannan yace “karki damu da wannan, ina muka dosa yanzun dai?�.
Yawu mai kauri na had'iye da k'yar sannan na fad'a masa inda zamuje.
Har k'ofar gidan ya ajiyeni, nabashi kud'i kuma yak'i kar6a, haryaja motar yabar wajen ina binsa da kallon mamaki, na sauke ajiyar zuciya nidai ina hamdala ga ALLAH dayasa na sauka lafiya.
A fili nace “k'ilama aljanine�. saikuma nace “wayyo ALLAH ya tsareni da hawa motar aljanu�.
Da wannan tunanin nashiga gidan, tun a soro nake kwad'a sallama.
Daga ciki najiyo ana amsamin, tace shigo mana baiwar ALLAH.
Shiga nayi inda ake amsamin sallamar, dattijuwar macece da zasuyi sa'anni da innarmu, ba yaune karon farko dana fara zuwa gidanba, tun muna k'anana muke zuwa yawon da innarmu ko idan munzo suna ko biki, (inna lami k'awar innarmu ce, a anguwarmu take, tun zuwansu innarmu gidansu innaro suka k'ulla k'awance da inna lami d'iyar makwaftan su innaro. harkuma yanzu akwai zuminci mai k'arfi a tsakaninsu).
“a'a a'a lalale marhabin da d'iyata, Munubiya ce ko munaya?�.
Fuskata d'auke da murmuahi nace “inna munaya ce, munu.... tana gida bata jin dad'i�.
“Ayya ALLAH ya sauwak'a yabata lafiya, ya Ai'shar dasu Aryaan?�.
“lafiya lau take, tacema na gaisheku. ga wannan tace na kawo miki�.
“to madallah, ina amsawa. ngd sosai kuwa�.
Murmushi nayi kawai bance komaiba, sai zuwa can nace “Ameera batanan? naji gidan shiru�.
“wlhy Ameera tafita d'azunnan gidan Mariya, amma nasan duk inda take tana hanyar gida yanzu�.
“ALLAH sarki, to a gaida min ita idan tadawo ni bara na tafi�.
“haba dai Munaya, daga zuwa kice zaki tafi?, Dan ALLAH ki zauna yanzu zakiga Ameeran tadawo aii. bara kiga nasa miki ko kallone kisamu abokin hira�.
Badan nasoba na zauna har ameera ta dawo, sosai tayi murna da ganina, dayake munsan juna, school d'aya mukayi a secondary, kuma ajinmu d'aya, nan muka zauna mukasha hirarmu, har ta soya mana wainar fulawa mukaci muka k'oshi abinmu.
Ban bar gidanba sai bayan an sakko masallaci, har titi ta rakoni, da k'yar muka samu taxi kasancewar anguwar tasu tad'an shiga lungu abin hawan yana wahala.
Saida muka hau titi na fad'ama driver inda zamuje.
'Yar dariya yayi yana fad'in “aina sani hajiya�.
Cikin fad'uwar gaba nad'ago na kalleshi, Dan naji kamar muryar driver n d'azun, ido na zazzaro waje da dafe k'irji dan ganin shine kuwa.
Na ware baki zan maka ihu ya jehomin farin Handkerchief a fuska. luuuu nayi da baya na kwanta a kujerar, tun ina ganinsa dishi-dishi har na daina gaba d'aya................âœðŸ?
Tofa jama'a ana wata ga wata wanene yasa a kwamushe Munaya🙆ðŸ»ðŸ˜?.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmuðŸ‘ðŸ»ðŸ˜_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙ðŸ»_*
👉ðŸ»1âƒ?5âƒ?
COMMENTS