Furar Danko Book 2 Page 1

  𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣




*_UK (LONDON)_*


........Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko'a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara'a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya....

          Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya...

       *_Aliyu Mika'il Idris Mawashi_* kenan da ke amsa sunan _Smart Mawashi_ a duniyar ƙwallon ƙafa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa ƙasar ta UK a London yay signing a club ɗin Queen City. Du da kasancewar ƙaramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba'ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama'a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaɓar da tafi kowace gaɓa muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha'awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin ɗaukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damƙa mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun ƙaddara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama ɗaya da ga cikin ƴan ƙwallo a wata ƙasa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma'u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo ɗaukar ɗaya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya ɗauki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da ɗibar kunun gyaɗar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga ƙofar falon a buɗe da littafin da ya gani ɗazu a saman gadon Lulu yashe a ƙofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faɗi. Amma sai ya dake cikin ƙarfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa yana faɗa mata taje ɗakin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi ɗakin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. Ɗan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruɗe tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwa”. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leƙa babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe ɗinta an ɗiba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a ɗauka”. Wani irin duka ƙirjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi ɗakin da sauri shima. Kamar yanda Maryam ɗin ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya ƙara masa ganin duk wani abu mai amfani a ɗakin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da ƙarfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya ƙarasa ya ɗauka. *_Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa'azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko'a hanya nai maka tazara irin ta sama da ƙasa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne._* jiyay jiri na nan ɗibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo ɗakin. Hankalinta ya tashi da ganin yanda Yayan nasu ya birkice cikin ƙanƙanin lokaci. Kansa tai tana ƙwala masa kira amma sai ya ɗaga mata hannu da ƴar tsawa-tsawa yace ta fita ta bashi waje. Ta tsorata dan haka ta fita da sauri. Kamar an saita batafi minti ɗaya da fita falo cikin ɗaurewar kai ba sai ga kiran Ahmad ya shigo mata. Da sauri ta ɗaya ta kai kunneta. Ko gaisawar kirki bata tsaya sunyi ba ta shiga faɗa masa abinda ke faruwa. Gaban Ahmad ya shiga faɗuwa shima da ga can, cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a gidan. Tambayar duniya Smart yaƙi cemasa komai har sai da ya nuna fusata sanan a taƙaice ya ce masa, “Tabar gidan”. Duk da abin ya daki zuciyar Ahmad ɗin. Sai ya shiga kwantar masa da hankali akan yana zuwa ya tabbatar bazata wuce gida ta tafi ba. Wayar Uncle Yousuf yay kira, da ƙyar ya samu ta shiga. Bayan ya gaishesa bai wani tsaya kwana-kwana ba ya sanar masa halin da ake ciki. Hakan ya ɗan ɗimauta Uncle Yousuf ɗin shima amma sai ya yanke kiran yace yana zuwa. Gidansa ya fara kira Aunty Saliha dake tsaye itama cikin tashin hankali ta ɗaga wayar da sauri. Dan dama nemansa take tun ɗazun ta gagara samunsa. Kafin ma yay mata tasa tambayar ita ta jeho masa abinda ke bakinta. “Abban Ra'is wlhy akwai matsala babba. Yanzu nan Khadijah tai kirana akan na shirya naje gidan Mawaddat babu lafiya na lallasheta da kwantar mata da hankali, banyi ƙasa a gwiwa ba nai shiri dan na shiga tashin hankalin bayanin Khadijahn. Sai dai muna kan hanya sai ga text massege ɗin ta ya shigo wai karmu nemeta, dan tayi nesa damu, na faɗa maka a kira Aliyu ya bata sakinta ta arziƙi inba haka ba zata sashi ya bada ta wuya. Duk da saƙon ya bani mamaki nacema driver yay sauri mu tafi gidan nata. lokacin da muke shiga street ɗin mun haɗu da wata baƙar mota mai tinted glass suka wuce muka wuce. Mun samu gidan buɗe da wani makwafcinsu tsaye a bakin gate ɗin, driver na ƙoƙarin shiga ya dakatar da mu cewar aiko baijin gidan nan da kowa. Dan yanzu yaga wata mata ta rirriƙo matar gidan tana kuka sun shiga mota sannan a loda akwatina a Hilux ma, shima ganin sun bar gidan buɗe ne ya sashi fahimtar babu lafiya, shine fa naketa nemanka ka kira Aliyu koka turo min Number sa amma na kasa smaunka”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” Uncle Yousuf ya shiga maimaitawa. Nan ɗin ma baice komai ba ya yanke kiran. Mommy ya kira, itama bai tsaya sun gaisa da ƙyau ba ya jeho mata tambayar ko Lulu taje gidan. Da mamaki tace bata zo ba gaskiya, kuma batajin zatazo ɗin, dan yau tanada Shari'a. Jin haka Uncle Yousuf ya ɗan samu nutsuwa ya yanke kiran. Ahmad yay kira yace su maza court dan tana can zai turo Aunty Saliha yanzu su riƙeta. Da sauri Ahmad ya miƙe, shima Smart sai ya miƙe. Har Maryam basu bariba suka kulle gidan. Sai dai me koda suka isa can ɗin ma babu Lulu, an kuma basu tabbacin bata zo ba. Sosai yanzu kuma hankalinsu ya fara tashi, dan kowa yasan duk rintsi fa Lulu akaran kanta bazatai sakaci da aikinta ba, musamman idan akai la'akari da yanda take matuƙar son al'amarin. Sai dai yanda aka ɗibi kaya yayin barinta gidan na hargitsa ma kowa lissafi. Gidan ƴan uwa da duk aka san zata iya nufa aka fara bubbuga waya, gidan Alhaji Garko ne farko, amma sai cikin tashin hankali Dada tace batazo ba, ba cikin Kano ba har wajen Kano amma dai amsa ɗaya ce Lulu fa bataje ba. Tun kowa na ɗaukar al'amarin wasa harya fara shan hankali, zuwa yamma dole aka shigar da report police station. ALLAH sarki Smart, yini guda baici komai ba sai ruwa, dolene a kallo ɗaya ya baka tausayi, sai da Coach ya tsaresa bayan sallar magrib yasha shayi, yana gamawa kuma sai amai, sai zazzaɓi mai zafi. Dole ranar Ahmad da Abdull na gidansu sai anan suka kwana, dan suma dai tuni sun san mike faruwa Ammah duk kawaicinta a ranar sai da ta taka gidan Smart da ga ita har Abbah. Umma kam wani shegen daɗi takeji, dan a ganin ta in har wani abu ya samu Lulu iyayenta sai sun ɗaure Smart na tsawon rayuwa.

         Al'amarin kamar wasa tuni ƙaramar magana ta zama babba, dan kwana ɗai-ɗai har uku babu labarin Lulu Daddy da Uncle Yousuf tuni sun wancalakar da ayyukan gabansu sun dawo Nigeria. Hakama su twins duk suna Kano. Smart yay wata irin zabgewa, bawan ALLAHn ko murmushi baka gani a fuskarsa, ya duƙufa kawai gayama UBANGIJI, dama Abba ya kai islamiyya da masallatai a taya addu'a, hakama ƴan sanda nata faman kai kawo da bincike. A cikon kwana na biyar ne fa Addu'a bata faɗuwa ƙasa a banza sai ga binciken ƴan sanda ya fara maida akalarsa kan Dada, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai dalilin ganin sanda aka fita da Lulu da maƙwaftansu yayi, dan ƴan sanda basu barshi ya hutaba shima. Yana ganin Dada yace ma ƴan sanda “A'a to ai wannan Maman ce na gani da yarinyar a waccan ranar, tare da wani saurayi haka mai ɗan kammani da su”. A take kowa ya dubi Dada da duk ta daburce, sai kuma ta hau borin kunya. Ran kowa a wajen sai da ya ɓaci idan ka cire Alh. Sulaiman da Tajuddeen da suka san komai. Smart kam wani irin kallo yakema Dada kawai, ji yake yau da ace bata da alaƙa da Lulu wlhy duk da tsufanta sai ya koyama matarnan hankali, dan sai ta tabbatar da ainahin Aliyu Hydar. Daddy ma dai da duk ya zabge a tsaye harda ciwo akan ɓatan Lulun a wani irin rikice yake kallon Dada da Alh. Sulaiman a karo na farko, shikam dama ya zargi Alh. Sulaiman, sai dai Uncle Yousuf ya kwaɓesa akan hakan. ALLAH sarki Uncle Yousuf sarkin dattako, da ya fahimci faɗan na cikin gidane sai ya sallami ƴan sandan kawai, da ƙyar suka tafi dan sun ce dolene Dada ta fuskanci shari'a. To abinka da manyan mutane, a take akai kiran cp ya basu umarnin tafiya. Bayan wucewarsu ne fa gida ya hargitse, dan Dada tace bazata taɓa faɗar ina Lulu take ba sai Smart ya saketa. Karan farko da tun faruwar al'amarin ya saki wani shegen murmushi mai ƙona zuciya a baɗini mai kuma hasala abokin gaba a zahiri........✍️



     _Alhamdullah barkanmu da sake dawowa a book 2. Yanda muka fara a Sa'a ALLAH yasa mu kammala da nasarori. Ina godiya da jirana da kukayi tare da fatan alkairi 😘😘👏._




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: Furar Danko Book 2 Page 1
Furar Danko Book 2 Page 1
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh10gCMwsmegQ6oYejiPEQarW3LAl_A2QAyegFLDtelLNSYvS24s3xthLpMJ1eOA_-9yRda0ux5qBQBzXI1ZW0qtsbjUOZB33uXuUuHDJz5aBjtzm8aCxptfT0q8D7MQ_KgszrD8K5BHpOEW0hE1-hmSHTHoEWNbHBafTddAl4bXiktjgda02vzONDj1jjw/s320/img_1697305001307.webp
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh10gCMwsmegQ6oYejiPEQarW3LAl_A2QAyegFLDtelLNSYvS24s3xthLpMJ1eOA_-9yRda0ux5qBQBzXI1ZW0qtsbjUOZB33uXuUuHDJz5aBjtzm8aCxptfT0q8D7MQ_KgszrD8K5BHpOEW0hE1-hmSHTHoEWNbHBafTddAl4bXiktjgda02vzONDj1jjw/s72-c/img_1697305001307.webp
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-book-2-page-2.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-book-2-page-2.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content