AUREN MU Complete Hausa Novel

  [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️ COPY BY ZAINAB BUTALAWA             1-5 Official

 

[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

COPY BY ZAINAB BUTALAWA

            1-5

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne
UMMU LATEEPHA
     Biye yake da ita a baya tana gaba Yana fada itama tana Masifa tare da furta bar maka gidanka zanyi,ya furta ki bar gidan Mana sai me nima haka nake so ki tafi dama kin isheni,ae naji tafiya zanyi suka shiga bedroom suna masifa,cikin akwatinanta ta dakko daya ta bude sannan ta bude ma'adanar kayanta ta Fara fito da kayanta,Hannu yasa tare da fisge wani leshi yace wannan ai ba kayanki bane Rannan na siya Miki da kika zo gidan nan dama ba a kawoki da kayan kirki ba,au haka kace yes wannan tsohuwar atamfar taki ce ya furta tare da fito Mata da ita,ta sake dakko wata shadda yace ajiyeta maidata ai baki zo da ita ba idan kin tuna last year na dinka Miki ita,ajiyewa tayi ta zabo Wanda tazo dasu kala biyu, fannin takalma tazo ta dauki wani white flat yace maza ajiye shi ni na siya Miki,tace na manta au Kaine fa ka siya,na tuna Miki yau to yace, amma Farooq baka da kirki amma ba komai,Farooq yace ae naji,cikin fushi ta jawo akwatinta ta fito Yana cewa itama akwatin mutunci na miki amma wlh da sai dai ki zuba kayanki a Leda,Aisha tace ni ka daina matsowa kusa dani bana bukatar taimakonka,yace wayyo yarinya Allah ya kiyaye na taimakeki rakaki zanyi Sabo da na kulle gidana Kuma karki sake kice Zaki dawo gidana daga yau,Aisha tace me Zan dawo nayi a wannan banzan gidan naka.

    A Palo ta tsaya tana karewa palon kallo tana son gidan bata son barin gidan yace malama ki tafi ke nake jira tana kallon gidan tace karka taba min jaka karma kace zaka taimakeni kace zaka daukar min jaka bana so karka soma bana so,cikin masifa shima yace Allah ya kiyaye na daukar miki jaka ki daina kallar min gida ki Kara gaba,Ina kaga gidan wannan gidan nasan komai yayanka ne ya siya maka Ina kaga kudin gina gida,ae naji jeki bana son ganinki,Aisha sabo da maita sai kallon gidan takeyi karshe cikin fushi da azama ta fisgi akwatinta zata fita sai suka ji ana Kwankwasa palonsu,juna suka kalla sai Suka ji muryar Babar Farooq tana cewa ko ba kowa ne? Farooq da sauri yace gani nan Muna nan,da sauri ya dauki akwatin Aisha yace maza koma ciki Umma ce,da gudu ta dauki akwatinta ta koma bedroom,Shi Kuma kofar ya bude Mata cike da ladabi ya furta Sannu da zuwa Umma,da fara'a tace yawwa Farooq Ina matar taka ne naji gidan shuru? Farooq yace tana nan aiki ma ta gama yanzu ai Yar Albarka ce akwaita da kwazo,Umma tace Kai Kam kayi dace ba irin Dan uwanka ba gashi Kuna zamanku lfy, Aisha ya kwalawa Kira ta fito harda saka katon Hijab har kasa ta gaida da Umma tace bari na kawo Miki ruwa,a'a barshi ma tafiya zanyi dan Allah ku zauna lafiya duk da nasan Kuna kokari ba a Jin kanku Kuna zamanku lafiya kowa ya sheda,Farooq yace to Mene amfanin mace da miji su dinga fada ai babu amfani,Aisha ma tace shi yasa Muka fahimci juna mu ko fada bama yi bama cacar baki,

    Shima Farooq yace yanzu Umma ai ba a yayin fada mu bamu San ma ma'aurata suna fada ba sai dai muji labari a makwafta,Umma tace ai ni haka nake so Allah ya Kara zaunar daku lfy ta mike suna cewa ameen ta tafi,tana tafiya Suka gallawa juna harara,Farooq yace dalla daina kallona mutuniyar banza marar tarbiyya,Aisha tace tafiya zanyi gidan Ubana dama,Farooq yace ba inda Zaki je baki Isa ba na fasa barinki ki tafi kudi na biya na aureki,gidanku son abin duniyarku ya baci,tunda na fara neman aurenki ake rokata kudi,sannan Sadakin da akace na biya wajen aurenki iyayenki ai da tsada Suka sa min, ko ke lokacin da na fada Miki sai da kika tsorata,sannan ai caka min akayi cewa Kika yi ke virgin ce da nazo na shige ki wuuufff na wuce ciki ba abinda ya tareni sai kace rijiya haka na fada cikin ki,harda cewa virgin ce amma a haka na hakura na zauna dake sabo da haka ba inda Zaki je kina nan gidan,Aisha kuka ta saki tace wlh Farooq Allah sai ya saka min sharrin daka min ni zaka cewa ba virgin ba Allah Yana ganinka ta fashe da kuka me tsuma zuciya,Tsaki yaja ya koma Palo yace ba inda Zaki je Ina gidan Nan banza shashasha.

        kwan....gwan...gwan taji ana uban buga Mata kofa,lemo ne a hannun na ina Sha uban kida na tashi,kofa na bude kyakyawan Matashin ne ya dauki wanka cikin kana Nan kaya farin Jean da riga sky cike da bala'i yace dalla malama kin cika Mana gida da kida ko ke kadai ce a gidan nan, da masifa nima kyakyawar budurwa dani nace ai kudin haya na biya Kai fa nasan sirrin komai baka biya kudin haya ba sai uban daukan wanka baka da sisi,Jin na fara tona Masa asiri yasan bai biya sisi ba yayi mukus ya juya gwiwarsa tayi sanyi ihu na Masa wooo yaji kunya ba uwar da ya sani Sai wanka shi a dole gaye na ja tsaki tare da komawa ciki,shi kuwa dakinsa ya koma ya Fara shiri Yana kallon Kansa a mudubi yace gaskiya na hadu zanyi cizo,ya dauki lokaci me tsawon gaske Yana kallon Kansa kafin ya fito Yana taku dai dai.

   Lokacin nazo fita a motata ja me kyau ko kallona baiyi ba ya tako ya wuceni a bakin gate Yana Shirin barin gidan,glass na sauke a hankali cikin nutsuwa na furta dan Allah Affan taimaka ka bude min gate,kallona yayi shekeke da bala'i yace kin ga nifa ba sa'anki bane,Kawai Dan kin mallaki wannan banzar motar kina tunanin ke wata ishashiya ce me kike da shi wannan har mota ce Yana magana Yana dukan motar da hannunsa,stop insulting my car,mota hadaddiya zaka dinga zagi,Tsaki yaja yace kinci sa'a Ina da appointment fita zanyi da kin gane kurenki ya juya yaci gaba da tafiya da gadara,haka ka iya kullum kace kana da Appointment  kuma har Yanzu bama gani a kasa kullum jiya iyau na furta ina Jan tsaki na Bude motata na fito tare da bude gate na fita Office

    Affan gidan Abokinsa ya wuce Direct Mustapha Yana aiki a ministry of Environment,Shi kuwa Affan baya aikin komai sai dai buga buga idan ya samu ya siyi kayan daukan wanka kudin gidan haya ma a Estate din ya kasa biya duk lokaci in yazo sai anyi fada da shi,suna Palon Mustapha me kyau a zaune Mustapha yace me ya kawoka gidana ne nasan sai da dalili,Yace zuwa nayi ka ranta min dubu biyar bani da kudin abinci komai na kayan abinci na ya Kare, Mustapha yace dama na sani to gaskiya bani da kudi, Affan yace please ka taimaka min Kai fa abokina ne na gaske common 5k nasan baza ka rasa ba, Mustapha ba a son ransa ba yace ya zanyi da Kai kazo a abokina bai kamata nayi baboki irinka ba amma ya zanyi Zan baka 3k Amma ka tattabar ka biyani na gaji bashin da nake binka yayi yawa,Affan Yana murna yace karka damu muna tare fa sai lokacin Mustapha ya saki ransa suka ci gaba da labarin duniya.

     Affan gida yazo da Niyyar shiga sai ga wani Mallam yasha babbar riga da rawani ya tsaida Affan yace Saurayi Innalillahi wa Innailayhirraju'un, masifa ta tunkaro ka,Mallam yaga Affan Kalar Naira ya dau wanka Kalar me kudi yace kana da makiya Alhaji wasu suna nan zasu sace maka mota,Affan ya bude baki yasan karya yake shi da baida mota,yace sannan makiyanka Yan uwanka ne sun Kai sunanka za a maka asiri kwana nan zaka rasa milliyoyin kudi a cikin dukiyarka,Affan ya sheke da dariya a ransa Shi da bai da ko sisi yanzu ma bashin dubu uku ya samo da kyar,a fili gigicewa yayi yace yanzu Mallam ya zanyi kenan? Me ya kamata ayi? Mallam farin ciki ya kamashi ya samu gara zai cuce shi,yace dubu dari zaka kawo ayi aiki me zafi a kansu,Farooq yace an gama bani Address din gidan naka yanzu banda kudi a hannuna,Nan take Mallam jiki na rawa yace ya bada address Affan ya wuce gida,Yana cikin palonsa dake estate din kowa bangarensa Palo da 2 Bedroom ne a hadadden Estate a haka ma Sai me kudi ko ma'aikata ke Kama gida a ciki da gate dinsu da komai kowa da part dinsa,Yana ta kora lemo da bread babu kayan abinci.

    Raudat ce tayi parking motarta ta iske Hajiya Mairo a compound kusa da part dinta turaruka ta Bata kyauta masu kyau,Mairo tana ta murna mugun shiri sukeyi da Raudat har abinci ma idan Mairo taga dama a part din Raudat take ci itama Raudat tana ci a wajen Mairo duk gidan tasu tazo daya suna morar juna,Raudat tace landlady wancan Kuwa ya biya kudin haya? baki Hajiya Mairo ta tabe tace yo mutumin banza Ina zai iya kullum sai wanka bako sisi na gaji da halinsa a gidan nan nawa kwana nan Zan kore shi,Raudat kasa kasa tace mene amfaninsa face kora ko dubu Hamsim bazai iya hadawa ba bare dubu dari biyu,Suna haka sai ga Affan ya fito ya dau uban wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai Yana takama ko kallonsu baiyi ba ya fice suka bishi da kallo cike da mamakin yanda yake da mugun gadara baida aiki sai wanka kullum cikin kamshi amma babu ko kobo.

    Wani kanti yaje inda suke siyayya kusa da gidansu Suka tafa da me kantin yace a wannan wanka haka Affan Ina zaka je ne? Affan yace tafiya zanyi Ina so zanje Abuja ne akwai wani business da nake ya zuba karya yace gashi ma kaga Atm dina yaki aiki,me kanti sabo da yasan Affan Yana Masa ciniki Yana ganinsa cikin kyakyawar shiga ya zaci me kudi ne yace gaskiya kana tafiye tafiye Oga ko yaushe a Hanya, Affan  yace ya za ayi Harkar Business ai in kana Business ba zama yanzu ma bank Zan koma Ina so zanyi siyayya kudi yaki fita dan Allah zan karbi kaya idan na dawo daga tafiya sai na kawo ma kudin, nan take me shago yace ba damuwa komai normal ebi abinda kake so,Affan ya kwashi manyan manyan madarar gari su gwagwanin Milo kayan tea sosai ya hada sannan ya kwashi su tumatir din gongoni,shinkafa yasa ya auna Masa kwano biyar,wake,taliya, macaroni komai ya har su Mai da kwai sai da ya hada akayi Total aka rubuta a list din Yan bashi ya fita,Yana kaiwa gida ya zauna ya shirya girki me rai da lafiya yaci ya koshi sannan ya fito sai gidan Mallam Wanda ya karbi Address.

      Affan ba kudin mota a kafa ya dinga tafiya sai da yaci bakar wahala kafin ya Isa gidan Mallam Yana zuwa yaga gidan Mallam hadden gaske sama da kasa,bai Sha wahala ba aka kaishi har part din Mallam,Mallam Yana zaune shi da wani Yana fada Masa karya dan ya karbe Masa kudi,Bayan ya sallameshi Suka gaisa da Affan, Affan yace Mallam ka firgita ni shi yasa nazo da wuri kaganni sauri nakeyi zanyi tafiya yanzu ba kudi a hannuna Kuma tafiyar wani kudade Zan karbo shi yasa nazo yanzu ka bani dubu Hamsim kafin na dawo sai na baka dubu dari biyu ma kaci harda riba,Mallam Yana Jin Haka ya haukace zai samu kudi ba bata lokaci ya irgo kudi dubu Hamsim ya bawa Affan ,yayi godiya tare da cewa sai ya dawo ya fice,Yana fita yazo ya biya me shago kudin kayan abincinsa tas harda samun canji ya shiga harkarsa.

     Mallam Shuru Shuru Babu Affan ba labarinsa bai San Kuma inda zai ganshi ba,Affan yaci wanka cikin wani yadi me kyau Yana taku dai dai sai ga Raudat ta taso daga aiki ta tsaya kusa da shi tare da sauke glass tace Affan shigo na rage ma hanya Naga Kamar gida zaka je,cike da rashin mutunci yace ke kin Isa ki taimakeni,akan wannan banzar motar taki har kin Isa ki rage min Hanya ya juya da Niyyar tafiya Katsam sai yaga Mallam shi da wani suna ta magana juyawa yayi da sauri ya bude motar Raudat ya Shiga gaba taja mota suka tafi Babu Wanda ya kula wani,sai da Suka Yi nisa tace da kace baza ka shiga ba me yasa ka canja? Cikin bala'i yace to sabo da na Shiga motarki shine Zaki Raina min hankali motar ki din banza motarki din wofi,Parking Raudat tayi tace amma baka San mutunci ba fitar min a mota,Tsaki yaja ya Bude kofa ya fice tare da furta banzar mota bayan ma ba da kudin halak Kika siya ba maza ne Suka siya Miki Karuwar banza da kudin karauwanci Kika mallaki mota tunaninki bamu sani ba Alhaji Sanata ko dan majalisa ya siya Miki ya daki motar da kafa yaci gaba da tafiya cikin gadara,Raudat ce ta leko ta window tace mutumin da ya kasa biyan kudin gida talaka da Kai baza ka taba iya siyen mota irin tawa ba Never, wace zata kulaka a haka Kai a dole kyakyawa kana daukan wanka ba abinka ka iya sai siyen Kaya kana nan kayan ma duk na gwanjo ne ta fisgi mota taja gaba,yace stupid girl Wai ita me mota Allah ya kiyaye na shiga motar haram.

     Raudat yau da takaicin Affan ta dawo tana zuwa bayan taci abinci ta fito ta faki Ido kowa ta taka tsani tayi disconnecting wutar gidan Affan ta danna switch dinsa ta sakko ta koma gidanta,Yana dawowa ya kunna ko Ina duf babu wuta ya rasa dalili gashi gudun Landlady yake tana ganinsa zata ce ya biya ta kudin haya,shima Fitowa yayi Raudat tana ganinsa ta window tana ta kyalkyala dariya Yana dubawa yasan itace sai ya kunna nasa ya kashe nata wutar itama sai gata ta fito da masifa Affan kana neman masifa abinda kakeyi ka takura min a gidan nan Zan dauki mataki a kanka, Affan yace amma ke banza ce wawiya Naga alama so kike nace Ina sonki to wannan bazai Yi tasiri ba,nafi karfinki kije ki samu dai dai dake, me zanci da Kai me zaka iya siyawa matarka kudin gida ma ka kasa biya me zaka iya,Hajiya Mairo me gidan itace ta shigo da dalleliyar motarta ta fito tace Wai ku meke damunku ne baku da aiki sai fada a gidan nan me ya hada ku? Affan ya bude baki zaiyi magana Hajiya Mairo tace rufe min baki Kai har kana da yanci a gidan nan kudin haya ma ka kasa biya,kana da bakin magana rufe Mana baki,ai Kuwa sai yayi mukus baida bakin magana,Raudat ta kyalkyale da dariya sanye take cikin Arabian gown me kyau tana kamshi tace ka biya kudin gida? Ko kudin gida ka kasa biya ai Kai ba Dan gida bane ihu ta Masa wooooo ko kudin gida ya kasa biya get out, Affan sadaf Sadaf ya koma cikin part dinsa bai da sisi baida inda zai samu kuma.

      Kuka tafashe da shi tace wlh Shehu Allah sai ya tambayeka yaranka shida amma ka kasa ciyar damu kullum sai Yar sana'a ta nake cinyewa,Tsaki Shehu ya buga yace ai yaranki ne ke Kika haife su yanzu Dan kin basu kudinki shine matsala,amma Shehu kasan ni ke daukan nauyin kaina da yarana kana da kudin ba Babu ba baza ka iya ba,gasara nake siyarwa itace sa'a ta amma Watarana har da rana Koko muke sha ga yarka Nusaiba har ta girma ta Zama budurwa ko yaushe Yarinyar nan kamar almajira haka take yarinya kyakyawa amma kamar almajira Shehu kaji tsoron Allah,Nusaiba ce ta shigo cikin jemammun Kaya da katon botikin kosai a kanta tayi sallama tace Mama na manta da yajin kosan,Yajin Nusaiba ta dauka ta tafi tallanta wurin tasha inda mutane ke taruwa,Nusaiba tana ta ciniki tana irga kosai a Leda ga duk Wanda ya siya,ta mike tsaye tana mikawa wani drivern babbar mota,wani bugagge yazo ta Bayan Nusaiba ya taba mata duwawu,Nusaiba tace Ina Wasa da Kai,Ni Yar iska ce? Ka taba ganin Ina wasan banza? Ni ba irin yan Iskan Yan talla bace neman halak na fito,zaka taba min duwuwu tayi fatali da ledar kosanta bundle sabo da masifar Nusaiba ta shatile Masa kafafu ya zube a kasa ta dinga dukansa ta rufe shi da Naushi a Fuska sai da ta farfasa Masa baki mutane ana ta bata hakuri,wani yace kiyi hakuri Nusaiba sabon zuwa ne bai sanki ba,Nusaiba cike da masifa tace ba ruwana ni tunda kaga haka dama ba mutumin kirki bane yazo ya taba min duwawu ta ja tsaki tare da tara Yara Almajirai ta raba musu kosan sadaka ranta ya baci haka ta koma gida

    Tunda Mamanta taga ta shigo ranta a bace tasan wani ya tsokaneta,Shehu Abbanta Yana zaune Yana shan shayi a gaban yaransa kanana su Kuma yaran kokon da babarsu ta dama na siyarwa shi suke Sha,Shehu ne ya kalleta yace to jarababbiya masifaffiya uban me aka miki marar kunya kullum baki da aiki sai fada da mutane,kiyi fada da mace,kiyi da Namiji,kiyi da Yara gaba Daya zubar min da mutunci kike yi a layin nan,Nusaiba tana  kumbura da tashin hankali tace Kai ka sani Abba, Mama kema kin sani bana fada sai da dalili Abba ai dole nayi fada kosan ma na bada Sadaka,Abba yace uwarki Kika yiwa asara ba abinda ya dameni abinda nake so na ji Mene dalilinki na dukan wani? Nusaiba tace duwawu ya taba min duwawun da ba a tabawa sai da sadaki abina me kyau ko uban waye ba sai na illata shi ba,Abba Yana ji shima ransa ya baci Yana son yarsa bai so a lalata masa ita Shuru yayi yace kina da gaskiya,Mama tace kinyi dai dai ya zaci irin yaran nan ne yan talla lalatattu amma laifin mahaifinku ne da ya dauki nauyinku ai da haka bata faru ba

    Itama Nusaiba Koko ta zuba tasha Amma ubansu a gabansu yake Shan shayi me kauri Kuma uwarsu zai sa ta dafa shayin ya siyo Madara da komai ya hada abinsa da kauri ya Sha a gabansu suna kallo yaran kanana Nusaiba ce Kawai Babba,Babar Shehu ce tazo daga kauye da Leda katuwa ta mikawa Mama tace gashi kanzo ne da nake shanyawa na taho muku da shi kwa rage zafi,ta Mika Mata Sabulun wanki da Omo da yawa sai masara kwano uku da gero kwano biyu,ga wake kwano daya,barkono har da kuli tace nasan halin Shehu ga wannan kwa rage zafi ba yawa,Mama tana ta godiya,su Nusaiba sai Murna sukeyi Watarana sai su kwana Basu ci komai ba lokacin Nusaiba ta ebi Kanzon ta musu dafadukansa suka ci Suka koshi shi kuwa Shehu dama a waje yake cin lafiyayyen abinci yaransa da matarsa ko oho.


AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

        6-10

Official

By
AsmaBaffa


page naku ne
      Zuwa dare dukkan matan a daki daya suke kwana da iyayensu sabo da rarashin zuciya irin ta Shehu, dukkan yaran basu bacci ba sabo da Babu abincin da zasu ci Shehu suna saman gado shi da Mama su Kuma su Nusaiba suna kasa a kwance saman tabarma, mazan Kuwa suna kitchen a gefe daya suke kwana gefe daya Kuma kwanika da tukwanen abinci, washe gari da rana babu abinda su Nusaiba zasu dafa har ta lallaba kannenta suka tafi Islamiyya wacce dama ita kadai suke zuwa gwara ma kannen Yan primary suna zuwa ta gomnati ita kuwa rabonta da makarantar boko tun mda ta Gama primary,Bayan sun dawo babu abincin da zata ci Ameer Wanda ke binta yace wlh Aunty Nusaiba yunwa muke ji Babu komai da dare,Mama tana jinsu suna zancen ta kalli yaran nata cike da tausayawa tace bani da komai a gidan Nan sai masara sai dari da hamsim,kanwarsu me bin Ameer wato Ihsan tace mu Kai Nika Mana Aunty sai ki Mana tuwo ko ba Dadi sai muci haka tunda mama wake da geron sana'arta take gyarawa

    Mama tace wannan shawarar tayi ta zaro dari da hamsim tare da mikawa Yasmin ta karba ta siyo waken Miya na hamsim,manjan hamsin sai Maggi dama da daddawa sai wani ragowar tattasai guda uku suka Yi miyar kuka tuwon masara,Suna cin tuwon Mama tana furta Allah ya baki miji me kudi Nusaiba wanda zai kaini paris,Nusaiba tace gwara da kika ce Paris irin su Dubai inda tourist ke cika gari,me za ayi da London Mama baki ta tabe tace tsoron ai London bata Yi ba kasar leburori ce Kuma ko kin samu me kudi karki sake ki taimakawa Shehu ya Gama zaluntar mu,dama wa zai bawa Abba ko sisi cewar ameer suna ta labarinsu,Ihsan tace Ina ruwan Abba Kuma ma ai uba ubane ko me yayi ai taimako Zakayi sai Allah ya buda miki,Nusaiba tace hmm tunda muka taso cikin kuntatawar Abba muke,to ba sai muyi hakuri ba cewar Ihsan,duk abinda ya faru akwai dalili shi yasa idan Kika ji Mata ko Yaya suna abu wasu dole akwai dalili, Siyama ce ta shigo tare da kwada sallama,Nusaiba tace shegiya Charity ce,Ziyama wacce aka fi sani da Charity tafawa sukayi da Nasaiba, Nusaiba ta Fara tsokanarta Charity,itama Siyama tace begin at home, Charity we dey begin at home,Dariya sukayi,Siyama ta kalli Nusaiba tare da furta Wai kayan nan basa isarku ne kullum Hijab da su Atamfa,Nusaiba tace kalleki wa zai kalleki yace Yar musulma ce Kuma bahaushiya kin wani saka Riga da wando ga pcap Kuma wasu tsofaffin da ace ma sababbi ne da sauki,Charity ta kalli kanta tare da furta baza ki gane bs Nusaiba,ya yau me kuka dafa? Mu fa gidanmu yau ko gafzar ma Babu ga jarin Ummi ya karye,Nusaba ta kalli babbar kawarta Charity tace muma yau zero sai kokon safe,Miko min kokon na samu na rage,Mama ce ta zubowa Charity koko ta banka tana cika cikinta tace shike nan sai tsula fitsari Sallama tayiwa Nusaiba tace gidan kanwar Ummi Zan biya duk da bata taimako dole na Kai Mata ziyara ko banza na cika tumbi na...

    Nusaiba tace ah tsayani mu tafi yau ko bata Nan sai mun leka makwafta mun cika cikinmu,tafawa sukayi Charity tace Kuma gashi 1:30 ko waye yanzu sun sauke abinci suka fita Wanda kawai cewa suka Yi Mama zasu je karbo bashin da suke bi...

    Suna fita a kafa suka dinga tafiya har zuwa GRA dake cikin Kano,Ba kowa a layin sai manyan motoci dake shige da fice a unguwar suka shiga gidan kanwar maman su Charity suna zuwa me gadi yace sun tafi Umrah,Nusaiba ta kalli Charity suka ce bad luck, Charity tace Kinga mu shiga gidan ko uban waye a haka har mu samu abincin ci inda za a sauke mu da abinci...

    Fitowa sukayi suka samu wani katafaren gida hadadden gida na gaske Suka kwankwasa,Me gadi ya leko yace Kai Yan uwan Alhaji ne daga Kauye? da Sauri Charity tace ae,megadi ya Bude musu kofa suka shiga ciki,motocine hadaddu gasu nan anyi parking nasu iri iri,suna ta kallo suna faman zare Ido har suka hadu da wata me aiki tace bayin Allah lafiya? Nusaiba tace wajen masu gidan Muka Zo kice Yan uwansu ne daga Kauye,Me aiki tace to tare da Shiga ciki ta Kira Wayar bedroom din Ogan nata tace Sir kayi baki Yan uwanka ne daga Kauye,Tsaki yaja tare da furta maybe yan uwan Mum ne nasan itace me alaka dasu,yanzu Mum ta koma Turkey nayi nayi ta dawo taki and now tana jajibo min yan kauyensu,anyway ki kawo su palona a Basu abinci da komai bazan iya ganinsu yau ba sai gobe sannan ki fadawa gageman Kar ya Bude musu kofa su fita sabo da zasu iya bacewa a city su jawo min matsala kamar yanda last year wasu Dangin Mum na kauye suka jawo min,Kar a barsu su fita sannan na gaji ki fadawa megadi Kar ya sake barin kowa ya shigo daga yanzu,cikin Sauri me aiki ta amsa da an gama Sir ta fice.

    Yanda Oga yace haka me aiki ta isar da sako sannan ta dawo ta shuryawa su Charity abinci ya sha nama ko Ina ga lemuka da ruwa me sanyi,Nusaiba da Charity sai Murna sukeyi, Charity tace gaskiya masu gidan nan sun iya karrama baki ji girki dan Allah muci  mu koshi mu ware gida,Loma Daya Charity tayi ta kalli Nusaiba tace gyara min pcap dita ta kalli gabas girkin ya hadu, Nusaiba ma tana ci tace wayyoo dadi lallai da ace Hamisu zai dinga bani irin wannan to Zan iya aurensa, Charity ta kyalkyale da dariya tace ni Kinga akan girkin nan Ban ki na bawa Basiru kirjina sau goma ya taba ba Suka kyalkyale da dariya gaba Daya sun cika gidan da hayaniya kamar gidansu, sai da suka koshi harda hutawa suna Shan ac karshe Suka fito zasu tafi Megadi ya Hana yace Oga yace ba shiga ba fita

     Tunda Farooq yayi Sallar asuba bacci yaka kasancewar Yau Sunday ba aiki har 11am Aisha ta shigo bedroom Duke da tire ta zuba gayu kyau Kam ta zuba shi,shayi ne da yamballs sai bread ta Fara tashin Farooq Honey... Honey wake up ya kamata ka karya,Farooq ya farka cike da mamaki domin yasan halin Aisha bata Masa soyayya sai da dalili dukkansu babu na zaba a cikinsu,Aisha tace tashi ka karya Baby ba sai kaje Dining kayi wahala ba,Mamaki ya Kama Farooq sai ya tuna da wani abu yace Kinga ma Ina so na fada Miki kudin jiya da dubu dari Uku Wanda na bayar bashi nace da abokin nawa na fasa karba ma ya barsu sabo da irin mutuncin da muke bai kamata na karba ba Yana magana ya dauki Bread zai Fara ci kenan Aisha cikin bala'i da masifa tafisge Bread din tare da dauke tire din tace dalla bani ance Kai kadai ya kamata ka karya a saman gado ni wato na mutu bana so na karya ne a Kan gadon tsaki ta ja ta fice tana cewa wani ya bar Masa kudin wato ni bazan ci kwandala ba lusari,baki bude ta bar Farooq Yana mamaki duk da yasan halin Aisha....

    Bayan satikai Farooq yayi parking Yar motarsa  gidansa na me rufin asiri,Aisha ya iske a Palo tana kallo sanye cikin Riga da wando masu kyau yace fito muje kiga abin mamaki,Aisha ta kalli Farooq yasha shadda tace karka bata min lokaci fa muje na gani,tana Fitowa taga wata sabuwar mota me kyau ba laifi,key ya Mika Mata yace surprise taki ce,Ai Aisha haukacewa tayi tana ihu da tsalle ta rungumeshi tana zuba godiya,Yace maza Zo muyi hoto so nake muyi maganin makiya a layin nan,dama bashi na karbo ta na wata biyu idan muka bawa makiya mamaki a layin nan sai na maida musu abarsu mota ce me tsada ta milliyan biyu shi yasa na karbo Miki aronta zuwa Yan watanni ya Kika ce dole makiya su Sha mamaki,Takaici ya Kama Aisha sai data Gama muryarta ashe ta aro ce kudi ya bayar ya karbo aronta na wata biyu,ranta ya baci haka ta tsaya Suka din pics a jikin motar aro suka dinga posting a WhatsApp da Facebook etc, mutanensu masu bibiyarsu ana ta congrats sun faso gari

   Affan kayansa ya fito da su Yana wanki a jikin pampom katon Compound dinsu kaya akw uku amma tunda safe yake faman aikin wanke su sabo da du fito kal Kal,har Raudat taje aiki ta dawo Affan Yana wanke kayan Nan,har itama ta fito da nata tazo inda yake ta fara wanke nata bata San ta hado bra ba a ciki Affan ne ya tambayeta yace duk wannan karyar da kike da 36 kike sawa? Dama ba komai a kirjin? Kina nufin a haka Kika Yi Kasuwa harda samun Sugar Daddy har ya iya siya Miki mota,Tsaki Raudat ta ja tace idan bashi kake  so a baka kayi magana har bashi muna bawa talakawa irin ku,me kake so a ciki ka taba sai a baka bashi,Affa yaji kunya Sabo da bai taba kula mace ba ko da wasa yace ba ruwana Ni ba Dan Iska bane
Kiyu hakuri yau bana Jin Dadi

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

         16-20

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne
NAJIDA ALIYU BICCA


       Bayan sun gama wanka suka yi Nusaiba kwanciya tayi sabo da gajiya Charity ce ta fito Palo ta iske Oga Aslam ya fito sanye cikin Jallabiya Yana hutawa gaida shi tayi Yana zamansa na takama ya kalleta kadan yace kin iya girki?zabura Charity tayi ta nuna kanta tace girki Ni? Ah kasan Kuwa yanda na iya girki? bari kaji Oga sanda Ina cikin mahaifar babata ka gane lokacin da Ina cikin Mahaifa da na samu damar Fitowa Zan shigo wannan duniyar lokacin Babata tana tuka tuwo na taho Zan fado duniya Saura kadan na fada cikin tukunyar tuwo Allah ya kiyaye ta tare ni ban fada ba kaga Kuwa wanne kalar abinci ne bazan iya ba,Allah ya min basira farko ma fa da tuni Yar kwallon kafa ce Ni,lokacin da Kanu yayi tashen cin ball ba shi ya kamata yaci wannan ball din ba lokacin Atalanta cup nice ya kamata,ana wani zancen Ronaldo wani Messi dan ba a Sanni bane na iya ball amma makiya sun hana naci gaba,Ina da makiya da yawa shi yasa,Aslam Yana ta dariya a ransa,yace to me Kika iya dafawa a ciki? Na iya Alala,tuwo,danwake ga sarkin Dadi shinkafa da Miya duk na iya,Yace hmm duk ni bana cinsu me yasa kike sa kananan Kaya kina Yar musulma bahaushiya?

   Sabo da na nuna musu Ni ba sa'ar Mata bace mace ce ni me kamar maza kwari ne Babu,Ni Yar jam'iyar what man can do Woman can do better ce,to Kuma kina da saurayi? Charity tsaiwarta ta gyara ta Fara zuba Murmushi tace haba Ina da shi har da Ridwan a cikinsu yaudararsu Kawai nakeyi Ina cin kudinsu,Rannan Ridwan din ma yazo daga karbar kudin ankonsa shike nan ya rungumeni zo kaga kiss hmm kamar maye ni kuwa na ci masa mutunci nace babarsa me tsatsar hakora,Aslam dai Jin labari Kawai yake ratata tun a nan yace Charity bata kirki bace, Nusaiba ce ta fito ta dakawa Charity tsawa tace Charity kiji tsoron Allah Ridwan din baki taba sauraronsa ba yaushe ma a masifarki Zaki Bari ya Miki kiss Naga rannan Abdulhadi daga yace ki rungume shi  Kika fasa Masa Kai da dutse, Enough kuje kuyi girki cewar Aslam,komai na Kitchen din kasa amfani sukayi da shi sai siyo musu abinci yayi,washe Gari suka dinga kuka tafiya zasu Yi yace to ba damuwa yasa Driver yace ya kaisu Tasha Kuma ya tabbatar sun Shiga mota,ya mikawa driver kudin motarsu sannan ya Basu dubu ashirin ashirin kowacce,da sauri Nusaiba suka Shiga motar,suna tafiya aka zo saitin layinsu Nusaiba tace nan zamu sauka,a sauke mu a nan,driver yace ai oga yace dolene a saku a motar Taraba Kar a samu matsala su Charity suna ji suna gani aka wuce layinsu har zuwa tasha aka sasu a mota tare da biyan kudin,sai da suka tabbatar driver ya tafi suka fito daga mota suka ce sunyi mantuwa ko tsayawa karbar kudin motar Basu Yi ba Suka Shiga Napep zuwa wani gidan amarya kawarsu ce Suka bata ajiyar kudinsu sannan Suka tafi layinsu

   Kafin su karasa gida lungun da ba mutane suka tsaya Suka sallami me Napep suka shafawa jikinsu toka har gashinsu hular Charity ta cire ta wullata cikin wani gida itama Nusaiba ta jefa dankwalinta gashi sun samo toka wajen masu girki a tasha sun shafe jikinsu tare da shafa bakin gawayi a hannayensu da kafafun su cikin katuwar bolar dake layinsu suka Shiga tare da tsugunawa a ciki kamar birarrika,kowa ya wuce ana cewa Allah sarki ga wasu can mahaukata kalli Yan Mata dasu Allah ya Basu lafiya,ana ta musu addua har Yamma likis sai ga Ameer kanin Nusaiba zai wuce suka ki magana har ya wuce sai da ya wuce Charity a hankali ta daga hannu Ameer gamu nan karya muke,Nusaiba ce ta bige Mata baki suka Yi Shuru,har Yan unguwa suka gaji aka nemo Yan sanda da me unguwar layin aka je inda su Charity suke dukun dukun suna soshe soshen karya,me unguwa yace a fara bincike ko a Nan akwai Wanda ya sansu,Shehu yazo wajen Yaga yarsa Nusaiba da kawarta Siyama,Shehu yace Wannan ai Yata ce data bace da kawarta Yar gidan Dauda,mutane aka dauki Salati

    Shehu yace Wanda Suka sace su ko me ya faru oho Nusaiba da Charity sunki magana ba uhmm Babu Uhmmm Uhmm Dan Kar ma a musu fada a gida,Yan Sanda Suka ce sai dai Wanda Suka sace su ne Suka musu tsafin da baza suyi magana da wuri ba,Shehu yace tunda Sun fito Alhmdllh kaga aikin Addua ko sun sace su amma Addua tayi tasiri sun kasa yanka su ko tsafi da su Addua kenan ai ba karamin kudi na kashe ba Sadaka masallatai Masallatai cewar Shehu yaja Hannun Nusaiba suka tafi gida Charity ta faki idon Shehu ta radawa Nusaiba Kar muyi magana sai gobe,Mama harda ihu sabo da murnar ganin yarta karshe ta fashe da kukan farinciki tana oh ashe Zan sake ganinki Nusaibata,Shehu yace basa magana yanzu amma kafin mutane su Fara shigowa suyi wanka Bari naje na Kira Dauda ya fita cikin Sauri,Su Ihsan Suka dinga ihu suna fada a unguwar anga su Nusaiba a bola aka tsince su.

    Mama ruwan wanka ta hadawa ko wacce Suka shiga kowacce ta wanke toka da bakin gawayin da Suka shafawa kansu sai gasu fes ba alamar wahala a jikinsu duk sunyi wani kiba ma fatarsu ta murje amma sunki magana juyin duniya sunki magana a Haka Shehu ya siyo musu shinkafa da wake da Miya Wai sun Sha wahala hannun Yan mafiya bari a basu me dadi,suna Fara ci Anty tazo tare da Dauda Suka zauna a tsakar gida Nusaiba da Charity suna ciki suna cin abinci,ganin ba kowa kasa kasa Charity tace ba dadi abincin na Saba dana gidan Oga,Nusaiba tace ji kazar da aka sa Mana jiya a cikin shinkafa,Charity tace habawa ai sai lemon shekaran jiya ga sanyi ga dadi yanzu shike nan mun dawo cin gafza Kuma ga wanka da ruwan botiki can a shower Muka saba,ta kalli gidan su Nusaiba tace Kai Kan uba kalli gidanku dama haka yake duk dirty painti ma ba a Gane wanne kala ne,dariya sukayi yanda baza aji ba Nusaiba tace Nima sai yanzu na kula gashi mun dawo kwanciyar Kai da kafa gobe da sassafe sai tallan kosai,Charity tace idan Muna so mu huta da talla gobe zuwa jibi Kar mu sake muyi magana hauka muke cewar Nusaiba Suka sake Yin Shuru abinsu.

   Juyin duniya sunki magana haka bayan sunci abinci Dauda da Aunty Suka tafi gida da Charity,washe gari ma basuyi magana ba a Rana ta uku Charity sai ta Fara magana tace Aunty daga nan bata sake magana ba,Aunty tace Dauda yarka ta Fara magana Alhmdllh wlh yanzu tace Aunty ta Kira sunana,Dauda yazo kusa da Charity yace Siyama me Kika ce kinyi magana dazu Nima Kira sunana ba sai kince Baba ba ko Dauda Kika Kira ba matsala ai duk cikin lalura ne, Charity a ranta tace dama haka nake so wlh sai na more sunanka tace Dauda,Dauda ya kyalkyale da dariya Alhmdllh Nima ta Fadi sunana asiri ya fara sakinta, Charity ta sake cewa Dauda Iliyasu,Dauda ya sake shekewa da dariya yace haka ake kirana da a makaranta, Charity Kuwa a ranta dadi take ji dama ta gaji da kiransa Baba,yace Fadi sunan Auntynki Fadi muji, Charity tace Hajara Musa Aunty tace to hankalinta ya fara dawowa jikinta,daga Nan Charity ta Fara magana sai me ma'ana wacce ta Zama dole sai tayi magana a Haka a haka ta dawo normal itama Nusaiba haka ba Wanda ya Musu fada ko Daya da aka tambaye su ma Suka ce wani ne ya fesa musu wani Abu a Fuska Basu sake sanin inda suke ba sai a daji Suka tsinci kansu,Nusaiba tace yan Yankan Kai Suka ce a dawo da wannan matan sunfi karfin mu matan manya ne shike nan daga nan basu sake ganinsu ba sai a bolar unguwarsu,Mama tace Addua ce tayi maganin tsafinsu, Haka aka dinga zuwa tayasu murna har suka dawo bakin tallan su.

    Raudat ce ta dawo daga Office ta fito da ledar kayan makulashenta Affan ya fito zai tafi Neman kudi ko zai samu,Tsaki ta Masa tace kullum mutum sai fita kullum amma kudin haya ya kasa biya,kallonta yayi yace you are very lucky yanzu fita zanyi Ina da aikin yi da yau sai kin gane kurenki ya juya ya tafi abinsa,Yana fita wani kamfani yaje hadadde ya tambaya Oga yazo Kuwa? Manager yace bai Zo ba yayi tafiya jiya yace Dubu dari biyar zaka bani ka fada Masa,Manager jiki na rawa ya bawa Affan dubu dari Uku ya tafi,Affan kudin haya ya biya ya siyo kayan abinci da sababbin Kaya kala kala kanana da shaddoji da yadika harda takalma,Sai ganin Affan suke Yi Yana shiga ya fita cikin Kaya masu kyau,Raudat tace Amma Dan fashi ne Kai ba a sani ba da alama sana'a tayi kyau an kwaci kudin wani,Affan yace ke da kike karuwanci budurwa me zaman kanta kowa ya ji labari ai yasan karuwanci kikeyi motar ma mun San waye ya siya Sugar Daddy ne ya Gama tabeki Ina tausayawa Wanda zai aureki Yana nan zai ta wahala akanki sai ya aura yaji ya Sha wata mahaukaciyar corner kinji kunya,baza ki iya hakura da talaucinku ba,Raudat taji cin mutuncin yayi yawa ta fashe da kuka yace ai baki ga komai ba ma Sai an Miki dukan tsiya an zagi iyayenki a bariki sannan Zaki San kin Shiga duniya am warning you ki koma gida yafi Miki mutunci,ga inda larabawa ya kamata su sakawa suna Shari,ai ke titin maza ce kowa bi yake abi ta Shari sittin a fito ta Shari Mansir ko mai kin bayar a waje,Raudat tace kaima ai kwarto ne,gidan wa Kika ji na taba haurawa? Allah ya Isa ta furta tare da shigewa part dinta ya dinga dariya yace ki fito muyi mana matsoraciya yaja Tsaki ya shige bangarensa shima.

    Aisha matsawa tayi sai Farooq ya saketa sabo da haihuwa,Farooq yace wlh Indai akan laifin da nake Miki ne na daina Aisha na tuba bazan sake bata Miki rai ba yanzu zamu zauna lafiya Ina sonki dan Allah kiyi Hakuri, Aisha tace ba akan fada bane ko wanne ma'aurata Haka suke fada kullum Kawai ka sakeni haihuwa nake so na gaji da Zama da Kai, Farooq ya dafe Kai yace Aisha bakya tausayina? tace Kawai ka sakeni,kuka wiwi yakeyi ya buga ya raya taki yarda yaje ya sanar da iyayensa sunce tunda ta bukata ai ya halatta haihuwa take so ya barta ta tafi,Maman Aisha Kuwa har gida ta aikawa Iyayen Farooq Kan su sa a sakar Mata yarta haihuwa suke so,dole Farooq ya rubuta saki daya ya bawa Aisha tana kuka shima Yana kuka domin itama bata son barin gidan tana son mijinta amma son haihuwa ya rufe Mata Ido Haka ta hada kayanta Yana kallo tayi tafiyarta.

    Bayan wata daya Oga Aslam in Banda tunanin Nusaiba ba abinda yakeyi ya tambayi Mum dinsa ko Zata Gane su Sam Bata gane ba har can Taraba yaje ya zaga danginsa amma baiga ko masu Kama da su Nusaiba ba,ya shiga damuwa ba abinda yake tunawa sai Nusaiba amma bai gansu ba,yau ya fita gidan Abokinsa Yana driving yazo dai dai layin su Nusaiba sai ga Nusaiba ta dawo daga wani shago ta siyo garin kwaki,a gigice yayi parking a saitin Nusaiba tare da sauke Glass yace Hey,Nusaiba ta ganshi tabbas shine karyarsu ta Kare jikinta ya hau rawa Kar Kar, yace Kinga get in the car let's talk,shiga muyi magana,Nusaiba bata da zabi haka ta Bude gaban mota ta Shige tuni ta Fara kuka asirinsu ya tonu,kafin ma yayi magana tace dan Allah ka yafe Mana wlh dama ba Yan uwanku bane yunwa ce ta kaimu,dama haka mukeyi duk randa bamu Dora tukunya ba sai mu samu unguwa me kyau mu dinga shiga gidan mutane Watarana ma Yan polio muke cewa sai a bamu abinci mu ci mu koshi mu tafi wannan karon shine Muka fada gidanka ka kulle mu,Aslam yace oh my God da tun farko Kun fada min ai bazan sa a kulle ku ba Kun min karya kunwa kanku ya kuka Yi da iyayenku?Nusaiba ta bashi labari yayi dariya sosai a nan ta nuna Masa gidansu da gidan su Charity sannan ya tafi Yana ta farin ciki.

    Tun daga ranar yake zuwa gidan su Nusaiba Mama sai Murna takeyi Allah yasa ya auri Nusaibanta,gidansu ya samu aka sake Gina musu dakuna guda biyu ya Zama suna da dakuna Uku ya budewa Mama katon shago a layin Danta Ameer Yana Zama a ciki duk kannen Nusaiba ya canja musu school Mama ta koma bata da matsala suna babbar Sana'a idan Ameer ya tafi makaranta Mama ke Zama a shagon idan ya dawo sai ya karbeta,Har Nusaiba ta daina talla ya maidata school Allah Allah suke Aslam yace Yana son Nusaiba, Charity dai tana tallanta duk tasan taimakon da yayiwa su Nusaiba itama ya bawa Dauda kudi ya ja jari,Nusaiba an samu suturu masu tsada wanka take dauka sosai ta Zama Yar gayu yanzu sai ji da Kai takeyi ana haka Aslam ya sanar da Mum dinsa ya samu matar Aure, tace a satin Nan zata Zo Nigeria,Aslam yau driver ya kawo shi ya Sha wanka na daban Yana zuba kamshi cikin wani shadajjen yadi milk,Nusaiba ta fito suna tsaye a jikin motarsa yace kin San me yake tafe dani Kuwa Nusaiba,tace Ina jinka Allah Allah take ya furta,yace tunda na ganki naji Ina sonki a Raina Kuma Ina so na aureki da gaske nakeyi,Nusaiba tana ji tace ka turo manya ko gobe ma ba damuwa,mamaki yayi amma yaji dadi yace Inshaallah gobe Mum zata Zo idan tayi bincike Zan turo Manya ki fadawa Abba yayi nasa binciken,Nusaiba tace kyale Abba Indai Mama ta yarda ba matsala ba sai anyi bincike ba,ka Sanni na sanka mene a ciki,Aslam Yana ta mamaki dai haka,shi kuwa Shehu ana fada Masa ya shiga bincike Kuma ya samu Aslam mutumin kirki ne Dan manya Dan asali.

    Mum tana zuwa washe gari taje gidan su Nusaiba Kuma ta yaba da hankalinsu ba a dauki lokaci ba aka kawo kudin aure sannan aka saka rana wata Daya kacal,Mama harka ta bude itama kullum Shar zaka ganta da yaranta Shehu ya samu jari Babba sai harkarsa take dama baya iya ciyarwa, Charity tuni an Fara shirye shirye Charity gidansu na bulon siminti ko Ina a sumulmule su dan fi su Nusaiba danshi danshi,Nusaiba tana tashi fitar da anko ko shawarar Charity bata nema ba ta fito da leshi Dan dubu goma Sha biyar, Charity tace Haba Nusaiba kamar kin manta inda Muka taso ya rayuwarmu take kaf kawayenmu talakawa ne Yan talla ko ni da nake babbar kawarki a Ina Zan samo wannan kudin haka,Nusaiba ta yatsina fuska tace ke karki damu zansa my Love ya dinka Miki haka na fitar da anko biki ne na masu kudi wacce taga zata iya tayi wacce baza ta iya ba fine dama Mum dinsa Bata Jin dadi ba wata Dinner za ayi ba,dalla share zancen nan na baki labari nasan fa ana daura aure zamu tafi honey moon irin su Paris da Dubai ya Kika ce,Charity ta kalli Nusaiba tace tsakani da Allah Nusaiba kin canja kina bani mamaki Wai kudin Aslam Zaki aura ko kuwa aure zakiyi tsakani da Allah na fa kasa gane miki,Nusaiba tace Kinga nifa bana son irin wannan ke ana neman harkar ci gaba kina shirme yanzu kudi ake aure ki tashi ki nemi naki kema idan saurayi bai shirya kashe kudi ba yaje ya huta yaci gaba da Adana gwaurantakarsa Ni da uwata Alhmdllh yanzu mun samu daula,Siyama ta tsaya kawai tana kallon Nusaiba da mamaki.

    Nusaiba tana komawa gida ta bawa Mama labarin Kawarta Siyama,Mama tace Yarinyar nan data maida sunanta na arna shine zata koya Miki tarbiyya,Yarinyar da kullum cikin Riga da wando take Kamar Yar arna ni haushi ma kike bani da kike Bari Yana taimaka musu da kudi har jari ya bawa Dauda idan tayi zuciya ta samo nata mijin shashashar yarinya kodaddiya idan kin shiga karki zauna haka sakaka duk abinda Kika samo ki kawo gida a hankali mu tara kadara yanzu ba a Zama haka,Nusaiba tace haba Mama Ina da wayo fa Kuma nononki na tsotsa,ai kinfi kowa Shan Nono na Sanda kina yarinya baki girma da wuri ba shi yasa ban yayeki da wuri ba sai da Kika Sha nono da yawa Suka Yi dariya,Mama tace Kinga yanzu ke ba sa'ar Siyama bace Allah ya Baki miji me kudi kin girmi kawa da ita ki tabbatar ta koma boyi boyinki a gidan mijinki kizo ki dauketa a matsayin Yar aiki ta nan zata tabbatar ke ba sa'arta bace yanzu,Nusaiba tace kin kawo Shawara Mama dole ta koyi darasi bari Kawai ayi auren
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️


         11-15

Official

By
AsmaBaffa


Page naki ne
UMMU DEEJAT

    Raudat ta ja tsaki,cikin masifa ya hayayyako ya tsani Tsaki botikin wankin nata ya dauka ya juye Mata ruwan kumfar a jikinta, tace mugu azzalumi sai na rama talaka baka da sisi kudin haya ma ka kasa biya ta dauki ruwansa na dauraya ya rike botikin tana ja yana ja yace kin San Allah Indan Kika bari na zani ki sai kin koma ja,sai kalarki ta koma ja ki kiyayeni kin San Ni waye,an ja tsakin ta sake jan dogon tsaki tace an ja tsmmmmm ta sake jan dogon tsaki tace kayi abinda zaka Yi sai gayu ba ko kwandala,Affan Kansa ya kalla yace kalleni kalli kalata kyakyawan guy,Dariya Raudat tayi tace na banza ba ai gwara mummuna me kudi koma mene yafi irinku,Takaici ya Kama Affan ya dauki bra dinta yaje ya cillata ta saman katanga tace Kaine talaka an fada maka biyu ne kacal dani,Guda biyu rak gareki haka zaki fita ragajeje kowa ya gani abinda kike iyayi da shi,abu ya zube zubabbe sai kace pillow Gwauro,yanzu da Zan baka da gudu zaka fara kaunarsa,can ya matse Miki..

   Me gidan da suke cewa Landlady itace ta fito tace Kai Wai ku baku Zama lafiya ne sai kace karnuka kullum fada me yasa bakwa ji ne? Affan bai biya kudi ba har yau Landlady tace Kai bana ta taka ba dan gidana bane kaki biyana kudi kullum bana ganinka ko ka biya kudi ko ka bar min gidana in kawo Wanda zasu iya biya,Raudat tace a biya kudi a zauna lafiya tsaki yaja yayi sauri ya shanya kayansa ya gudu part dinsa yasan bai biya ba

    Kwanan Affa shida ba a ganinsa a gidan dukkan yan gidan Basu ganinsa an rasa Ina ya tafi ashe yana gidan da asuba yake ficewa sai dare yake dawowa sabo da Kar ma Landlady ta ganshi,yau sai da asuba kafin ya tashi a bacci ta fada bangarensa ta sameshi ya tashi kenan ya idar da Sallah zaiyi shiri ya bar gidan,yace lafiya? Me ya faru haba landlady dakin Namiji ne fa Kika fado min ciki irin wannan lokaci power namaji tana tashi yanzu ne dai dai lokacin da Namiji yake mikewa Zan iya raping dinki, yanzu idan nayi Raping naki yaya kenan kina mace Kuma baki wuce 40yrs ba har yanzu zamu iya sha'awarki ni har na fara Jin ma sha'awarki, Landlady tsoro ya kamata Kar fa da gaske Affan yake tasan bata kyauta ba tace Yi hakuri to kudi nazo karba ka shirya anjima ina jiranka tana Gama fada ta fice,da sauri Affan ya shirya ya Sha tea ya fice ya bar gidan bai dawo ba sai tsakar dare,Raudat tayi zaton ma ya bar gidan ba kudi amma sai taji kamshin girkinsa na tashi a nan ta tabbatar Yana nan akwai sheka girki wajen Affan

     Nusaiba sun buga sun raya me gadi yaki Bude musu yace Kun zo daga Kauye Ina kuka sani a birni da har zaku fita yawon gantali Salon ku bace Oga ya koreni,gashi karya sukayi ba damar suce ba daga Kauye suke ba,cikin palon suka koma Charity tace muna cewa bada Kauye muke ba Masu kudi kamamu zasu Yi suce munzo bincike,Nusaiba tace mun shiga Uku gidanmu,mamata ni ke Mata tallan kosai,Abbanmu ma na shiga Uku na gama yawo,Charity Kuwa duk ac dake palon gumi take faman hadawa tace a hannun Kanin Babana nake kin San Halinsa shi da Anty matarsa na shiga Uku duk aikin gidan nan ni nake Yi ga tallan Alala da nake fita mu roki Yar aiki ta fada musu ba kwana zamuyi ba dama biki muka zo mun leko mu gaisa,haka Nusaiba tace kin iya dabara Suka samu me aikin ta shigo tana mopping, Charity tace Dan Allah kice musu su Begin at home ne ma'ana Charity zuwa mukayi mu gaisa daga gidan biki muka dan karaso yau zamu koma,Yar aiki tace to ta koma sama tayi knocking Oga Yana ta aiki a computer yece come in,Me aiki ta shiga ta sanar masa da Sakon su Nusaiba,tana cewa begin at home wai Charity yace cikin yan uwan Mum ne wannan maguzawan da suke Mambila baza a bari su tafi ba yau su nufi hanyar Taraba da Yamma haka ai kamata yayi su huta har na sati daya Mambila fa ke kinsan nisan wajen kuwa yanda Mum ke son Yan uwan ta ya kamata su huta kin San Ina son abinda Mum ke so Kar a barsu su tafi Kuma karki sake dawowa I'm busy Right now bana son fita idan kika sake dawowa na koreki daga aiki.

    Me aiki da sauri ta dawo ta fadawa su charity abinda yace tace yace Kar na sake komawa inda yake baza ku min asarar aiki ba idan zaku kwanta ga daki nan ta nuna musu wani bedroom, Nusaiba ta fashe da kuka tace muje sama da kanmu suka mike tare da haurawa,lokacin daure yake da towel zai shiga wanka kowacce kofa Suka kwankwasa ba kowa har suka kwankwasa tasa cikin masifa yace idan na fito sai na balla ko waye da gudu suka sauka kasa suka sake Zama a Palo ko zai fito Shuru Shuru ba kowa har dare yayi suka fashe da kuka, dakin da aka ce su shiga shi suka shige tap din ma kasa kunnawa suka Yi sai da kyar suka kunna  Alwala sukayi tare da gabatar da Sallah,har isha tayi basu ji motsin kowa ba suka sake fashewa da kuka gashi Basu da waya ko lambar wani babu a kansu bare ma su roki me gadi ya basu aro.
   Mun jawa kanmu mun Sha kokonmu amma Muka ki godewa Allah cewar Charity a haka me aiki ta sake kawo musu lafiyayyen abinci haka suka sake cika cikinsu amma idan suka tuna gida sai kuka har bacci ya kwashe su.

   Washe Gari Suka Yi Sallah suka fito suna tunanin ganin wani ba kowa sai me aiki tana girki sunyi sunyi akan ta fadawa oga zasu tafi Amma tace ya Mata warning baza ta je ba,Wasa Wasa har Suka kwashe kwana uku a gidan basu ga ko Kare ba tun suna cin abinci suna murna har bacin rai da tsoro ya hanasu ci,ga abincin suna gani amma sun kasa ci ba kwanciyar hankali.

    Gidan su Nusaiba tun suna tunanin yawan banza ta tafi har Suka dawo kuka da addua,Shehu sabo da Yana cikin bacin rai har da basu kudin cefane,Mama ta dafa shinkafa da wake da Mai da yaji,Ihsan tace ga shinkafa yau zamu ci amma abin haushin Aunty bata nan suna bakin ciki suna murna ta wani bangaren zasu ci shinkafa,mutanen layin sai jaje ake musu ana tayasu da addua Allah ya bayyana su Nusaiba,Shehu akan baya so ya kashe kudinsa yace ba inda Zan Kai Sadaka a tayani da addua da kaina Zan roki Allah watakil ma nafi malaman matsayi a wajen Allah muyi addua da kanmu,Mama tana hawaye komai na sana'arta ya tsaya yarta ta bace tace ai ba malamai aka ce ka bi ba cewa akayi ka bada a masallaci a tayamu da addua sai kayiwa Almajirai Sadaka,Shehu yace ai ke baki San Allah ba tunaninku mata kullum a bi malamai idan baza kiyi Addua da kanki ba ki barshi,Mama cikin jarinta ta dauki dari biyar ta bawa Ameer danta tace ungo kaje masallacin juma'a kaga yau Juma'a ka siyi ruwa na du kudin ka rabawa Alummar annabi Allah ya bayyana Mana su Nusaiba,Ameer ya karba da sauri ya tafi zai siyi ruwa ya rabawa Alummar annabi Sadaqa,Mama tana da filinta na gado ta ajiye abinta,sabo da tayi Sadaka Allah ya bayyana Mata yarta tace zata siyar da filin,Shehu Sadakar dari biyu ya kasa Amma tana daga filinta zata siyar yace zai siya ya lallaba Mama zai siyi fili,filin a Kauye yake Bai wuce dubu dari biyu ba amma Shehu yace filin Bai wuce dubu dari da talatin ba Mama bata San Kan komai ba yace ya siya zai bada kudi ya lallaba ya karbe takardu tayi signing da komai shima haka ba shedu bata fadawa kowa ba Shehu ya hana kudi tana ta binsa karshe ma Sai labari taji ya siyar da filin dubu dari uku Kuma ko ficika bai bata ba,idan tayi yaji ta tafi ta barwa wa yaranta ga yarta har sati guda shuru,Mama ta kwana takeyi tana kuka tana kaiwa Allah kukanta.

    Charity idonsu duk ya kumbura sabo da kuka basu ga kowa ba Kuma an hanasu fita,Oga zai iya sati biyu a gida ba tare da ya leko ko compound ba Haka yake shi,Sun wanke kayansu ya bushe sun maida shi jikiksu bayan sunyi wanka,Palo Suka dawo Suka zauna babu Wacce tayiwa Yar uwarta magana sunyi jugum jugum a Palo,Tv tana yi Amma ko kallonta basu Yi,kamshi suka ji ya mamaye palon,wani me uban kyau Suka gani yana sakkowa daga steps sanye yake cikin wani silk doguwar Riga Kuma armless gefe da gefe an tsagata Silver color takalminsa ma haka sumarsa ta Sha gyara na musamman fadar kyawunsa bata baki ne komai nasa na daban ne,sheki Kawai yake da walwali,kwarjininsa ya kamasu Suka kasa magana har ya samu kujera ya zauna irin Zama na isassu na masu Hannu da shuni kana gani kasan Hutu ya ratsa shi.

   Gyaran murya yayi kadan lokacin Charity tace Ina yini cike da Ladabi Nusaiba Kuwa ta kafe shi da Ido tana kallonsa sai da Charity ta dan bigi hannunta sannan tace Ina kwana au na manta Ina yini? A takaice ya amsa ya kalli Nusaiba yace ke kina kama da Baban Mum da gani jikarsa ce ko?,da sauri Nusaiba tace ae,ya kalli Charity yace ke da alama Yar Hajjo ce ta gangare ko? Charity tace ae,yace sorry Allah yaji kanta,Charity tace Ameen harda kuka dan a barsu su tafi tace ka tuna min da babana Yana can shi daya gwara na koma, Oga yace har Kun gaji baza ku tafi yanzu ba ya Dace ku huta sosai ya furta tare da mikewa ya fice suna ji ya shiga mota, Nusaiba suka sake fashewa da kuka,tunda ya fita bai dawo ba sai tsakar dare sunyi bacci lokacin harda siyo musu kayan makulashe da safe suna tashi suka gani a bakin kofar su Leda guda, Charity tace wlh da wannan kayan dadin gwara muna gidan Iyayenmu,Nusaiba ta kalleta tace hmm ai ni abin ya isheni gashi Muna fadar gaskiya za a kamamu sai gidan kaso masu kudi zasu Yi tunanin ma da abinda ya kawo mu,ai Kar mu sake mu fada Kuma Kinga Yana kamamu sai Iyayenmu sunji abinda muke yi,Nusaiba tace badluck, har suka gaji suka fito suna zaga gidan ko Ina sai da suka gani sun Sha kallo amma Sam abin baya birge su burunsu su koma gida,Palo suka koma sai gashi a zaune Yana kallon film sannan Yana latsa wayarsa.

    Zama suka Yi can nesa da shi yace hope Kuna Jin dadin birni ya furta Yana kallon Nusaiba, Charity tace sosai ma Alhmdllh amma gida muke so mu tafi yau Iyayenmu zasu Mana fada,Ogan yace ai Indai kunce a nan kuke ba matsala kadaici ya min yawa kuyi zamanku kwa dan ebe min kewa ko ba komai na dinga Jin motsin mutane, Nusaiba ce ta kalli Charity suka hada Ido idanuwansu ya ciko da kwalla zasu Yi kuka ya tashi ya haura sama shi dama ya gaji da Shuru shi kadai a gida ga Yan uwa sunzo yaji motsin mutane ko da na yan satikai ne, Yana fita Charity tace kamar fa wannan mutumin kwakwalwarsa a takashinsa take ta kowa a kansa aka Masa brain amma Banda shi tasa a takashi aka Masa ita baya tunanin Iyayen nu chab
  
     Aisha ce ta shiga motarta tana tukawa a layin har makwafta suka tsiri zuwa suna gaida su Sabo da aga ta siyi mota ko Ina da key a hannunta tana karkadawa,Sunday Yana gida Aisha anci gayu ta fito tace Maggi fa ya Kare sannan ba kayan miya ko yaji Banda shi bare nayi Mana shinkafa da wake,Farooq yace Wai ku Mata me yasa baku da hankali ne sau Nawa Ina fada miki idan Abu ya kusa karewa ki sanar min amma kinki ji sai komai ya Kare kat Zaki zo ki fada min to yanzu kin San wata yayi nisa ba kudi sai mu yini haka ya furta Yana Jan tsaki,Aisha tace Farooq kafa isheni tsakani da Allah na gaji Kai ba haihuwa kake ba how many years? 5yrs da auren mu maimakon ka lallaba ni sabo da nice ke hakuri Ina taimaka maka wajen Zama da Kai ba haihuwa Alfarma fa nake maka,for how long Zan dinga jira ba haihuwa ta juya ta saka Hijab ta fice ba ko neman izini haka tasa kudinta tayi cefane ta dafa abincinta ita kadai taci na Rana ta boye na dare Yana kallonta,tashi yayi ya fice zuwa gidan Abokinsa a can yaci ya koshi,tsakanin Aisha da Farooq an rasa waye me gaskiya tsakaninsu idan wannan yayi rashin mutunci gobe wannan ne zaiyi kullum basa shiri abinda ya damu Farooq irin gorin haihuwar da Aisha take Masa kullum,kwana biyu Babar Aisha tazo gidan suna dakin Aisha Babarta tace ke dai anyi shashasha mene amfanin aurenki da Farooq mutumin da baya haihuwa kunje asibiti yafi a irga ance a shine ai ya kamata kisa ya sakeki,ribar aure ai haihuwa ce tun wuri kisan me kike ciki,Babar Aisha haka ta gama zuga yarta daga ranar Aisha ta daina girki Farooq Yana Mata magana sai masifa tace juya Wanda baya haihuwa ka sakeni tun baya damuwa har abin ya dameshi ya sanar da Babarsa tace yayi hakuri Kawai kowa haka yake hakuri,da a baya suna yin Dan fadansu su shirya haka Yar karyar su dai sukeyi yanzu duk Aisha ta canja ba mutunci Kawai a sake ta taje ta samu me haihuwa.

    Affan ne ya fito yasha wata shadda fara yayi mugun kyau Yana kamshi Raudat itama ta fito cikin farin lace zata tafi wajen aiki Kawai taga Affan da fararen kaya Ido suka hada tace Allah ya kiyaye na saka Kaya kala daya da Kai God for bid ta juya cikin fushi ta canja wata blue atamfa ta fito Yana tsaye da mamaki Tsaki yaja ya juya zai fita tace masu appointment kullum Ina da appointment kullum meeting ba uwar komai a kasa ba Sisi,kallon baki Isa ba ya Mata yace Banda lokacinki ya Bude karamar kofar gate ya fice,ita Kuma ta bude gate ta fita da motarta yace arga akwarabas da na Shiga wannan motar gwara na tafi a kafa,Tsaki ta ja tare da Shiga motarta tazo ta gabansa Malam bani hanya gurgu kawai masu mota suke da kafa ta daga glass din motarta sama tayi gaba.

      Yau kwanan su Charity goma Sha biyu da bacewa Mama ta rame ta lalace ga bakin cikin Shehu ga bacin rai yarta ta bace Addua kullum suke ba dare ba rana,Bangaren Charity Kuwa Matar kanin Babanta wacce take Kira da Anty cewa tayi ban yarda ba Dauda yarka karuwanci ta tafi Siyama duniya Kawai ta shiga,nima Ina zargin haka cewar Dauda, Su Nusaiba kuwa sunfi sati daya basu ga ko alamar Oga ba sunci kukan har sun gaji,me aikin ma da suke gani yau ta tafi ganin gida sai nan da kwana biyu zata dawo sai ranar Suka ga Oga ya fito daga dakinsa ya musu murmushinsa me kayatarwa yace Hey,suka kalle shi Kawai yace me aiki yau ta tafi kuyi hakuri sai jibi sai ku tafi idan Kun tafi babu me gyara min gida ni Kuma bana son kazanta Dan Allah ku gyara gidan nan ya juya tare da komawa sama,ba yanda Suka iya Haka suka hau gyara ko Ina na gidan

    Bayansu ciwo suna gyara garden Nusaiba ta rike bayanta tana Nishi tace gwara tallan kosai na sau dubu da irin wannan aikin, Charity tace hmm ai nayi missing tallan Alala ashe haka talla yake da sauki kana zaune za a Zo a siya,tun ba ma an soya ba kafin ka tafi tallan sai kaci ka koshi cewar Nusaiba itama
Ai sai ma Ina zubawa mutane Ina daga zaune abina da yajina a gefe,daina tuna min cewar Charity suka ci gaba da uban aikin gidan


Ku dinga sharhi please novel zai Fara wuta nan gabaAsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

          21-25

Official

By
AsmaBaffa


Page naki ne
MRS CHIEF

         Biki Saura kwana uku Charity taga ba a sata a harkar itama bata Shiga ba uzurinta take yi,ana gobe daurin aure Nusaiba tazo gidan su Charity tace kinki zuwa ana ta shagali ba ke,Charity tace kice ana ta soya kwankwason rago,wa yake ta wani rago ana fada Miki kwankwason bijimin sa,dariya tayi ta shirya tare da yiwa Aunty sallama suka tafi,leshin da Nusaiba ta sa aka dinkama Charity ta Bata tace gashi shi Zaki sa da safe ni na Kai Miki dinki me tsada aka Miki, Charity ta ajiye Kaya a gefe Nusaiba tace an fa goge su ki Adana Kaya masu tsada ne fa sai ana kula,Charity tace hmm kawai,Nusaiba tace Ni tsoro ma nake ji Kar ki fini kyau ranar bikin yanda kike farar nan kyakyawa Ni Kuwa wankan tarwada da ma nice ke Charity,Siyama tayi dariya Nusaiba ta sake cewa ji dimple dinki sis gaskiya ki godewa Allah ya Miki baiwa,Siyama tace kema ai kyakyawa ce Nusaiba hancinki ai yafi nawa tsayi,Ni ba Fara ba Yaushe ma na Kama kafarki,sai gashi a hakan me kudin ke yace Yana so ba farar ba ko ta nan ai Kya godewa Allah ni da kin sani ma dinkin Riga da wando Kika min ban iya sa Riga da skert ko da zani ba kin sani,Baki Isa ba bikina guda ki sa Riga da wando bazai yuwu ba shegen duwawunki su ja hankalin mijina,Siyama tace da Zan ja hankalinsa ai da tuni ya gani ki daina kishi dani wlh sister bazan taba cutarki ba,Nan ta kalli Lefe akwati kusan ashirin aka kawowa Nusaiba.
   
    A gidan charity ta kwana duk wani aiki da ita akeyi tana gaba gaba ranar daurin aure 11am za a daura su Charity an Sha kyau tafi amaryar kyau duk da cewa Amarya me makeup tazo ta Mata nan take Nusaiba ta bata rai ganin Charity tayi kyau cikin Riga da skert din less kawayensu duk sunci kwalliya sun Zo Basu sa anko ba Basu da kudin siya,Ango da best friend dinsa Sabeer sun gayyaci abokai Nan da nan masallacin kusa da gidan ya cika da mutane ko Ina Yan gayu ne da manyan masu kudi lokaci na Yi aka daura auren Aslam Mu'az da Amarya Nusaiba Usman,kowa yayi mamakin Wai Aslam ne zai auro mace Yar talakawa haka Basu shigo gidan ba Suka wuce reception kowa a can yaci ya sha daga nan abokai suka wuce gidan da suke angwanci.

     Nusaiba haka aka yini ana hada hada sai 5pm duk Suka yi wanka aka Fara Shirin Kai Amarya,Shehu yasa yarsa a daki ya dinga Mata Nasiha yace ki zauna lafiya da mijinki Nusaiba Allah ya Miki zabi,ki rike mijinki da Yan Uwansa babu batun Maganar son kudi a cikin aure idan ka auri mace ko mace tayi aureka baka fata ku rabu sannan zaka tsaya ka jure samunsa da rashinsa ki Zama mace me tunani ke ba yarinya bace kin girma kin wuce shekara ashirin ki San me kike, Mahaifiyarki Aminatu kin San mu Yan asalin Rogo ne dake nan Kano,sanda na ganta Ina sonta Ina da kudi lokacin kasuwanci Yana gara min na aureta Bayan na aureta na hadu da karayar arziki daga lokacin Mamanku ta dinga wulakantani tana ci min mutunci sabo da bani da kwandala,bayan wasu shekaru Allah yasa kudina ya dawo daga nan Kuma kauna ta dawo ta dinga nuna min so Sabo da kudina shi yasa Kika ga na fita safgarta gaba Daya ba karamin wulakantani tayi ba lokacin da Banda shi to karki haka Nusaiba ki zauna lafiya a nan dai yayi ta Mata fada ita Kuwa Mama ance ga Amarya ko Zaki Mata fada,Mama tace mu yaranmu ai tun suna gabanmu mun Gama musu fada da can basu ji nasiha ba sai yanzu da ake Shirin kaita dakinta, menene basu sani ba na zaman duniya ku tafi Kawai a kaita zata Yi zamanta daram,Yan Uwan Shehu da Yan Uwan Mama Suka fita da Amarya sai kawaye motoci ne lafiyayyu sunfi talatin aka dauki Amarya zuwa gidan mijinta.

    Duk Wanda yaga gidan sai ya kasa rufe baki,Amarya Kuwa tun a mota ta Fara cewa kunga tun gidan da Muka sani ne tun Ina budurwa bai canja komai na gidan ba Amarya guda ai ya kamata ace an canja komai na gidan tana magana kasa kasa an zaci kuka ma take Yi,ko Ina kamshi ke tashi na gidan ga Amarya ta Sha gyara bayan Yan Kai Amarya sun gama ganin gida suna ta Santi Suka fito Suka tafi gaba Daya har Charity bata zauna ba,Ango ne ya shigo bayan Sallar Isha ya Sha wanka cikin shadda Yar gaske sky Yana tafiya cikin takamarsa da ya Saba Kyau Kam ba a magana Kamar shi yayi kansa,bedroom dinsa ya wuce direct ya iske Amarya abar kaunarsa a zaune saman makeken gadonsa,a gefen gadon ya zauna ya Kare Mata kallo cike da Murmushi,Hannu yasa tare da Bude mayafin data rufe fuska da shi fuskarsa ya Dora a saitin wuyanta Yana shakar kamshinta a hankali ya furta a I love you Nusaiba tace me too,wuyanta ya fara kissing Kamar Wasa Yana binta da sumbata Yana shafata jikinta sai rawa yake yana yi har ya fara cire Mata sutura a hankali Yana tsotsar bakinta Yana so suyi Sallah suci kayan makulashe amma ya kasa a cikin gaggawa yake bai iya hakura,Nusaiba tana ganin kamar Wasa taga da gaske yake,a hankali tace ji nake sai munje kasar waje zamu Fara amarcin,wacce irin kasar waje ya tambaya Yana shafata,tace ban gane wacce ba kasar waje dai ai ji nake acan zamu Yi Honeymoon?, A'a gidan zuma zamuyi ba Honeymoon ba cewar Aslam ya furta da Wasa Yana ci gaba da abinda yake,Boobs dinta ya cafka basu da wani girma ma Yan kuyas a hannunsa haka ya dinga murzasu,Nusaiba kasa komai tayi kamar gunki haka yayi kidansa da rawarsa har ya samu ya shigeta yau ta yabawa aya zakinta Harijine sosai bai kawowa da wuri tayi kukanta ta hakura sai da ya samu gamsuwa sannan ya lallabata suka ci abin dadin bayan sunyi wanka tare da tsarkake jikinsu Yana ta yabonta tana Jin Dadi.

    Bayan kwana biyu Nusaiba taga Shuru bai da Niyyar kaita kasar waje tana zaune a Palo ta Sha gayu ya fito yace wow you look good tayi Murmushi ya zauna a gefenta tace har yanzu banji ka Fara cewa mu Fara Shirin Visa ba,Aslam yace ta me fa? Honeymoon Mana ya kamata ace Muna kasar waje yanzu,Ganin ta dameshi da zancen kasar waje baiyi niyya ba Amma sabo da a zauna lafiya yace ba komai zamuje Saudiya ya Kika gani? Kallonsa tayi tace Saudiya? Makkah kake nufi? Ibada zamu je Yi kenan? Ni ban shirya zuwa Makkah ba turai zaka kaini irin su Paris,Germerny etc kana wani Maganar Saudiya shike Nan kullum Muna masallaci bazan je ba ta mike tsaye tace ka rike kudinka bazan je ba Indai Makkah ce ni na taba ganin me kudi Dan tsumulmula ma irinka,Baki Aslam ya Bude cike da mamaki duk kudin da ya kashe Mata da danginsa dan tsumulmula ne shi gaba Daya sai abin ya daure Masa kai sabo da ya samu Yar tarbiyya me nutsuwa ya nemi Yar talakawa irin Nusaiba Ashe gwara Yan masu arzikin ma.

    Tsayawa yayi Kawai Yana Shan mamaki just 3days da aure har an Fara fada,sharewa yayi ya hakura ya rabu da ita suna soyayyarsu har Suka cika sati biyu da aure Nusaiba ta shirya cikin tsadadaddjen material blue and purple ta Sha kyau ta fito sanye da takalmi me tsini da jaka ta yafa Dan siririn mayafi,Aslam bai fiye fita ba Yana gida ta same shi a bedroom dinsa Yana Shirin fita tace Baby kudin gyaran jiki zaka bani daga nan Zan biya a min make up,okay ya furta ya irga dubu ashirin ya bata,galala ta karbi kudin tace dubu ashirin kacal gyaran jiki fa nace da kwalliya,dubu biyar ya Kara Mata tace Bari dai nayi manage duk da Haka basu Isa ba,Kawai kallonta yake da mamaki,tace yawwa na manta yau Mama zata Zo da kannena anjima da Yamma,yace Allah ya kawosu lafiya Ina gida ai lokacin Zan Dan je Office na dawo Alright,ta zabi key cikin motocinsa ta Kira driver Suka fita ba inda taje wani gyaran jiki bank taje ta saka kudin a accnt dinta ta dawo gida.

     Tana dawowa ta sa me aiki ta shirya lafiyayyen abinci dama bata girki Bata aikin komai,Mama ce tazo gidan tare da Ihsan da Ameer Nusaiba ta rude tana musu Sannu da zuwa ta mike ta shiga kitchen ta cika musu gabansu da kayan Dadi sunci sun Sha Mama tace wannan irin kyau haka Nusaiba kin ganki Kuwa Alhmdllh 'yata tayi goshi,Mama ta mike tana rawa da Waka Kai 'yata tayi goshi....Yata tayi goshi...ah..ahhh....Nusaiba tana tayata suna ta faman shewa,Mama tace ya accnt iceko ya fara Nauyi? Nusaiba ta nuna Mata Alert suka tuntsire da dariya,Ameer da Ihsan Baki suka tabe,Ameer yace wlh da nine shi sakinki zanyi daga kaiki ko yaushe karbar kudi,auren miji me kudi hauka ne,Ihsan ma tace duk tallan kosan da kike Yi kin manta kenan Mama nan kwanan nan kike siyar da gasara kullum kuka Abba baya bada kudin abinci amma har Kun manta...Mama ce ta masge Ihsan tace rufe min baki mahaukata idan mun tara kudin ai da ku za a ci
   Aslam ne ya shigo ya zauna tare da gaida Mama,Mama anga me kudi harda cewa surukina ka dawo barka da dawowa suna ta hira ya haura sama sai ga Nusaiba tace anjima Mama zasu tafi Kuma gobe zasu je Kauye ya kamata a basu Dan wani Abu,Aslam bai ce komai ba yace sauri nake fita zanyi akwai kudi a kasan pillow na a ciki ki irga wasu ki bata babu ko godiya tace to, Bayan ya fita tana duba kudin taga dubu dari da hamsim gaba Daya ta kwashe kudin ta bawa Mama tace in kinje gobe ki cire na kashewa wasu Kuma ki saka a accnt dina,Mama tace ai kwandala bazan taba ba Ina da kudin kashewa gobe zanje da kaina banki na saka a account, suna ta nishadi ta rakata suka tafi.

    Sai da Aslam ya dawo ya duba yaga Babu kudin gabansa ya fadi ya Shiga kwalawa Nusaiba Kira ta shigo tace Mene ne?yace Baki ga kudin da na ajiye a Nan ba Wanda nace ki eba a ciki ki bawa Mama,Nusaiba tace ai na bata su,cewa kayi na bata Kuma na bata wani abin ne a ciki,Aslam cike da bacin rai yace baki da hankali dubu dari da hamsim Kawai Zaki bawa Mama,cewa nayi ki iba Wai me yasa ku Mata har abada tunaninku abinda akeyi a novel gaskiya ne,ance Miki mijin novel ne ni da Kawai Zan ajiye kudi ince Bude drower ki kwasa,okay yanzu sabo da na bawa Mama common Dubu dari da hamsim shine nayi laifi wanne irin Dan mammako ne kai,sannu tsumulmulatulla ta juya ta fice ta bar Aslam a tsaye kikam yace karfa abinda nake tunani ya Zama gaskiya karfa Yarinyar nan dan kudina ta aureni,Zama yayi ransa a bace babu wani so ko kulawa babu tunda ya aureta bakin ciki take cusa Masa tun Yana sharewa har ya gaji.

    Zuwa dare zuwa tayi cikin kayan baccinta tana zuba kamshi ta kwanta a gefensa,Aslam ya hadu ne ta ko Ina bata iya share shi jikinsa Kawai abin kallo ne,rungume shi tayi ta baya hakura yayi ya juyo Suka kwashi love,Watan Nusaiba daya ta shirya driver ya kaita gidan su Charity, Charity tana zuba kullin Alala taga Nusaiba da murna da ihu ta mike ta tafi da gudu zata rungumeta cikin azama Nusaiba ta ja baya tana Danna Wayarta me tsada tace karki bata min jiki baki ga a gindin murhu kike ba so kike na Fara warin hayaki, Charity ta saki baki tana mamakin Nusaiba ganin haka Kawai Charity itama ta shareta taci gaba zuba da alalarta ta bar Nusaiba a tsaye sai da Aunty ta fito jiki na rawa tace Nusaiba kece Nusaiba ta ja kujera ta zauna,bayan sun gaisa da Aunty tace dama wata samuwa ce ta taso da abin Alkhairi shi yasa nazo na Fara sanar muku,me aikina guda Daya ce ta min kadan to Zan dauki wata Yar aikin Kuma dubu talatin mijina ke biyan ma'aikatansa me zai hana ku bar Charity ta koma can da aiki ai yafi talla ta Zama kamar ma'aikaciyar gomnati dubu talatin a rayuwar nan ai ba Wasa bace,shine nace ai da bare gwara na gida Bari naji ko Charity zata yarda,Aunty dake ba yarta bace tace an gode wlh Zama ta yarda ko Dauda idan yaji ai zai yarda dubu talatin fa ai tsab zamu rage radadin talauci,Charity tace bazan je ba ni babu gidan wacce zanje bauta,Nusaiba me yasa Kika Zama marar Imani mun taso tare kina kawata Amma burinki ki ganni a kaskance a wulakance me na tare miki,ke ba abin kunya bane ace babbar kawarki da ya kamata ki taimaka yau Nusaiba kawarki Zaki dauka a matsayin Yar aiki sabo da bani da gata Charity ta karasa da hawaye,Dauda ne ya shugo Yana tambaya lafiya? Aunty ta bashi labari babu bata lokaci yace Siyama hada kayanki Alhmdllh kudi sun samu aiki har gida ke ai abin ma ki godewa Nusaiba ne Kuma gata kawarki ai baza ki Sha wahala ba tashi maza bar Alalar masu siya in sun matsu suzo gida,Charity ta mike tace Inshaallah abinda Kika min Nusaiba Watarana sai kinyi Dana sani kayanta ta ebo a Leda viva Suka fita da Nusaiba,Nusaiba ta Shiga bayan mota ita Daya tace Charity ta zauna a gaba,Siyama Bata sake magana ba har Suka Isa gidan Aslam

    Aslam Yana compound Yana hutawa ya zaci Charity ziyara ta kawowa kawarta ma yace sai yau Zaki zo munyi Fushi,Charity ta kalle shi Suka hada Ido gabanta ya Fadi ya hadu karshe,gaida shi tayi ya amsa da fara'a suka shiga ciki Nusaiba ta fada Saman kujera tana huce gajiya tace wash Kinga Charity zo ki min tausa Charity kamar gaske ta tsuguna ta Kama kafar Nusaiba maimakon Tausa sai ta lankwasa kafar iya karfinta zata balla ta,Nusaiba ta kwala ihu tare da kwace kafarta tana zagi ke wacce Dabba ce,Charity ta samu ta gallawa Nusaiba Mari ta dungure Nusaiba tace shegiya ke din banza na Miki bauta wlh kinyi kadan ta juya ta sake tallafewa Nusaiba keya ta baya ta wuce ta Shige bedroom din da Suka taba zama a gidan tare,Nusaiba ta taso a fusace tace fito ai ba gidan ubanki bane,Charity tace ai ke shi yasa Naga Shehu ne ya Gina gidan har kinyi clean Yarinyar da ni nake koya Miki daurin dankwali,Nusaiba sai dura ashar take Yi.

   Washe gari da yamma Aslam yasha suit farare ya dawo daga Office ya iske Charity zaune cikin riga Yar kanti doguwa red,Nusaiba an cakare cikin Super green,Yana shigowa Nusaiba tace karbi jakarsa ki Kai masa bedroom,Charity ta duka tare da cewa barka da zuwa Sir ta karbi brief case din ta wuce sama ta Kai har cikin dakinsa,mamaki ne ya hanashi magana ya kalli Nusaiba yace Wai meke faruwa ne?Nusaiba tace Yar aiki na Karo guda Daya ta min kadan,Kuma best friend dinki? Rokata Suka Yi dan Allah a dauki Yar su aiki kullum Charity sai ta bugo min waya,ya zanyi dole nace tazo ta Fara Kuma kawarki Baby,haba Nusaiba bai Dace ba me yasa baki da tunani ne,ba ruwanka tunda na fada maka gaskiya kaki ji,Charity ce ta fito Aslam ya Kira sunanta Siyama tace naam,Dan Allah ki koma gidanku hakan bai Dace ba ni bana ma bukatar Yan aiki, Charity tace ko na koma Babana bazai kyaleni ba dole sai nayi aikin nan Kawai idan akace yau baka da iyaye to ka shiga Uku karka damu zanyi aikin,Aslam ya buga ya buga Charity tace Zama daram,Nusaiba tace ka kyaleta na fada maka tana so
   Washe gari da wuri Charity ta tashi ta shirya musu lafiyayyen Kari waccen Yar aikin Kuma tana ta gyara gida me gadi Yana aikin compound ko Ina na gidan ya dauki kamshi...

     Affan ne a zaune Yana waya ya mike ya fito daga part dinsa Yana cewa Yaya kayi hakuri na rigada na karba kudin,Wanda ya Kira da Yaya masifa Kawai yake ma Affan tunda Kai ka kashe zuciyarka baza kayi aiki ba ka daina kassara Ni kana zuwa ka karbi kudi yanda kaga dama,an baka aiki da komai kaki Yi,na samo maka har Offer a gomnati kaki yi na baka babban matsayi a company na kaki yi,na saka a Kan business kaki uban me kake so ayi maka Kai a duniya baza ka motsa jikinka ba mace ma ta fika kokari sai dai kaci me kyau ka sha me kyau ka saka sutura ka zaga gari,Affan ka kiyayeni karka sake zuwa ka karbi kudi a wajen ma'aikatana kaje kayi rayuwarka,Affan da shagwaba Kamar dan yaye yace ni bazan iya aikin nan naku ba na wahala idan kudinka ne bazan sake karba ba ya kashe waya,Raudat tana wajen tana ji sai dariyarta yaji tace anji kunya kayi asara Kuma Namiji da Kai ka kashe zuciyarka ka zauna zaman banza zaman kashe wando, Affan yace a gidan ubanwa na kashe wandon? Wandunana fes suke kije ki gani Designers ne,Allah ma ya kiyaye ranar da za ace na kashe wando na ban canja sabo ba Idiot ya juya ya wuce dan shi Affan bai gane hausar me take nufi baAsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

         26-30

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne
MARYAM T BALIYA
UMMU ISMAIL

     Ranar Affan ya Kira Landlady dinsu yace window nake so a Kara min a part Dina daya windown ya fito ta gidan wannan Raudat din Sabo da Algungumai  dayan ma ya fito ta cikin gidanta Sabo da munafukai,Landlady tace palon Raudat ne fa Daya Kuma bedroom dinta ta Nan za a maka windunan?Affan yace ae ko ki min ko a bani kudin haya dana biya, Landlady tace Banda kudin da Zan biyaka yanzu na yarda Kawai Zan maka windunan amma sai ka biya kudin da za a kashe kwandalata baza tayi ciwon Kai ba,Ba matsala ya furta,Landlady sai da ta bari Raudat zata fita tace dan Allah bar min key dinki a hannuna Zanyi girki a gidanki gas Dina ya Kare,Raudat mutuniyar Landlady ce shi yasa Kai tsaye ta bar Mata key ta fice,masu aiki ta Kira Affan ya biya kudi aka huda katon Palo ya fito ta palon Raudat aka sa glass da komai cikin kankanin lokaci,aka sake huda wani window ta bedroom dinsa ya bullo ta cikin bedroom din Raudat shima an sa glass anyi komai,Raudat tana dawowa taga palonta ya koma wani iri ta duba taga windo ga palon Affan, bedroom ta shiga nan ma mamaki ya kuleta ta tafi wurin Landlady da sauri,Me gidan tasan zance shi yasa ta kulle bangarenta gaba daya ta fece ganin gida sai tayi sati zata dawo,Raudat ciki ta koma .

    Affan ne yake ta faman shara da kalkale kalkalen gida sai kace mace haka part dinsa yake da tsafta komai a shirye a gyare Raudat tana ganinsa ta window Yana ta faman goge goge ya gama ya Shiga kitchen ya dora abinci harda fasa kwai ya dawo jikin window Yana karkadawa Dan Kawai ya tsokani Raudat, tana kwance a saman 3seater window din ya bude ya leka ta ciki yace ke Balagaggiyar akuya,kaine balagaggen dan akuya kwarto dan taure ka isheni Malam ka kyaleni da wulakancin da aka min aka hada min window da Kai wanne irin masifa ce wannan har windown bedroom,ae ai gwara naji munsharinki ba a ja damu idan na kulla da mutum ya Shiga uku sai na hanaki Shan ruwa,Raudat ta kalleshi tace wlh baka Isa ba Kai din banza ka hanani Shan ruwa,Kitchen ya koma yaci gaba da girke girkensa tana ji kamshi na tashi bata kulashi ba,Bata ko kalli window dinsa ba ya gama ya zubo egg source dinsa da shinkafa Fara harda Naman kaza plate daya ya Mika Mata yace ungo badan halinki ba,ba kunya ta mike taje zata karba ya janye plate dinsa Yana dariya yace yanzu sai ki karba?Dan Allah ka bani na gaji dama bazan iya girki ba yanzu,ai Kuwa Zaki mutu da yunwa ya bar jikin window ya koma palonsa tare da kunna tangamemiyar plasma tv dinsa Yana kallo yana cin abinci.

    Aslam ne ya fito sanye cikin farar Jallabiya ya zuba wanka Yana shining da kamshi ya zauna a dining inda Charity ke zaune tana cin nata abincin,Ina kwana tace Masa ya amsa da fara'a sanye take cikin wata barmemiyar t-shirt yellow da wando me Fadi baki duk da haka tayi kyau Dake me kyau ce harda saka hula,dariya take bawa Aslam,Nusaiba ce ta fito sanye cikin kayan baccinta tana Mika kusan tsirara haka take amma ta fito harda yin Mika,Charity ta kalleta ta kalli Aslam tace a rike Mata,Aslam yace me? So take tace ya tallafe ta iskancin ya motsa sai taji kunya tace ba komai,Nusaiba ce ta kalli Charity ko a jikinta ta zauna Wai zuba min tea, Charity tace kinyi kadan wlh ke dai baki Isa kin sani aiki ba,a gidan aure na kike fa,Tattabara ma taci ubanta cewar Charity ,Nusaiba Tsaki ta ja tare da zuba abinda take so ta ja gefe tana ci ko a jikinta ba ruwanta da mijinta Kawai ita kudi,tana gamawa ta mike ta shiga bedroom,Aslam ya kalli Siyama wacce ta mike itama zata tafi yace Charity zo muyi gulma,Dariya ya bawa Siyama ta dawo ta zauna tace to muyi ta furta kasa kasa da muryar rada,yace bai kamata na fada Miki ba Sirrina nane sirrin iyalina amma ba yanda zanyi so nake ki Mata fada ki dinga fada Mata gaskiya ko zata yarda ni Ina son matata Ina so mu zauna lafiya amma na kasa gane kanta ba wani kulawa ba soyayya komai kudi,komai a bata kudi Aslam ya fadawa Charity duk abinda Nusaiba ke Masa yace kuma bata ganin girmana,Bata iya magana ba abinda duk taga dama yazo bakinta haka zata Yaba min,gaskiya bazan boye Miki ba idan nasan haka Aure yake da banyi ba da na hakura nayi zamana a single, Charity ta tausayawa Aslam amma tace kayi hakuri mu Mata da yawa haka muke auren kenan shi yasa ake cewa sai hakuri, Inshaallah Zan dinga fada Mata gaskiya ka Kara hakuri haka ta dinga kwantar Masa da hankali suna haka sai ga Nusaiba ta cakare ta fito tace shopping nake son zuwa,yace baza ki je ba wlh sai naje Kuma nasan Dan Kar ka bani kudi ne Kuma na eba,ta juya zata fita Siyama tace Nusaiba dama haka Kika koma wacce irin hauka ce wannan? Ke a naki haukan ma harda jahilci wlh kin bani mamaki Ashe ke jahila ce haba Nusaiba yanzu idan wani yace me zai ci da Yar talla sai kiji haushi bayan wasu ne ke bata wasu,mijinki yace Bai yarda ki fita ba amma kice sai kin fita bai baki kudi ba kin ebar Masa kudi mene hakan ke nufi,wlh kiji tsoron Allah ki gyara halinki,wani wawan Tsaki Nusaiba ta ja tace to munafuka Sannu uwata ke kin Isa ki min fada karfa ki manta Yar aikina ce ke ta sake Jan tsaki ta fice,cike da bacin rai Aslam ya mike Kawai ya haura sama Yana mugun mamaki ko a film bai taba ganin haka ba da labari aka bashi bazai yarda ba.

    Ya dade a sama Charity tana zaune a Palo itama tana Takaici da mamakin Nusaiba,Fitowa yayi yasha wata shadda da alama fita zaiyi Charity tana zaune tace dan Allah kayi hakuri Sir,ka kwantar da hankalinka karka sa damuwa a ranka Inshaallah zata gyara komai zai wuce,Murmushi yayi Kawai yace ba komai na gode ya fita,lunch ta Dora musu tasan bai fiye Zama a Office ba.

    Bayan sati biyu Charity tana gidan kullum tana kallon haukar da Nusaiba take zubawa Iskanci kala kala Aslam bai Isa da ita ba duk da haka Siyama sai ta fada mata gaskiya tana ta kokarin ganar da ita tana kwantarwa da Aslam hankali Abu yaci tura kullum ma abin na Nusaiba karuwa yake Yi,Mota me kyau ta million uku ya siyowa Nusaiba ya shigo da Fara'a yace yau zaki surprise Zo muje ki gani,Charity tana goge dining yace taho kema ki taya kawarki murna,Nusaiba tana zumudi tace ka daina cewa kawata Yar aiki na ce fa suna Fitowa ya nuna Mata dalleliyar mota sabuwa ya Mika Mata key yace gashi Taki ce,Maimakon fara'a da murna sai aka ga Nusaiba ta bata rai tace yanzu Baby ka rasa motar da zaka siyo min sai Toyota Carina matan masu kudi irinka suna Hawa manyan motoci su Marcedes benz su perari,bugati amma kamarka me kudi haka ka siya min Toyota ordinary Toyota,Da karfi charity tace Nusaiba...oh my God wannan wacce irin rayuwa ce,ke Kika nema Masa kudin,Nusaiba ki tuna fa gidanku da inda Kika fito,Tsaki Nusaiba ta ja ta koma ciki abinta tace bana so Indai Toyota ce wallahi bana so,zuciyar Aslam ji yake kamar ta fito sabo da bakin ciki da bacin rai,Charity har kwalla tayi sabo da takaicin Nusaiba da tausayin Aslam,tace kayi hakuri dan Allah,kaddara ce Allah ne ya jarabceka kayi hakuri ka cinye jarabawarka,kowanne Dan Adam da tasa Jarabawar kayi hakuri ka kwantar da hankalinka please,Aslam kasa magana ma yayi ya wuce ciki Kawai.

     Bayan wasu Yan kwanaki Aslam kullum cikin damuwa yake ko abinci bai iya ci,hankalinsa a tashe Charity ta kula da Haka amma matar tasa Nusaiba bata ma gane shi ba Kawai a bata kudi ita Kam, Yana zaune a garden yayi tagumi Yana ta waya Charity taje har Inda yake,sai da ya Gama Wayar tace sir Ina da Yar tambaya ne,yace go ahead Ina jinki,Nusaiba ce tazo wajen sanye cikin bum short da Yar wata t-shirt yace amma kin San me gadi zai iya ganinki da wannan shigar ko? Nusaiba tace naji tana tabe baki,Charity tace Naga kwana biyu kullum cikin damuwa kake ko abinci baka ci,Nusaiba tayiwa Charity wani banzan kallo up and down tace ke a wa Kuma da wannan tambayar,Aslam bai kula Nusaiba ba yace matsala na samu da kayan Dana shigo dasu gashi bashin bank na karba Kuma kayan sun salwanta ba ma custum ne Suka Kama ba jirgin ruwa ne yayi hatsari Suka nitse,yanzu komai nawa banki ne zasu karbe har gidan da nake ciki motocina da komai Ina Miki zancen yanzu Banda komai nan da sati ma bank zasu zo sabo da dana karba wata Daya nace Zan maida kudin kin San Kuma bashin banki,Innalillahi wa Innailayhirraju'un cewar Siyama tace kayi ganganci kaima daka karbi bashin bank gaba Daya ka tura aka turo da Kaya da kudin,yace duk kadarar da na mallaka Ina fada Miki baza ta biya bashin bank din ba,Wata shewa Nusaiba tayi tace wa zaka rainawa hankali Kawai kace akan jiya nace ka bani dubu dari Zan canja waya sabo da mammako baza ka iya bani ba shi yasa ka kirkiri karya Wai kayanka sun nutse a ruwa just like that,heee Aslam tsabar son kudi ne yasa sai ka min karya Allah ya kyauta idan ba karya kake ba to tabbas kazo gidanmu da karya Ashe motoci da kudin daka nuna Mana ashe duk na karya ne dama ance samarin yanzu aron mota da gida suke bayan kwana biyu su karanta maka matsala shike nan ka shiga talauci tana Gama fada ta juya ta koma ciki abinta,shi ta daina daga Masa hankali ma ba ta ita yake ba yanzu ta kudinsa yake Yi,Ya kalli Siyama da damuwa yace baza ki gane ba Siyama amma Dan kasuwa shi Ina karanta Masa zai Gane,Siyama tace na fahimta ma wlh ubangiji Allah ya mayar maka da mafi Alkhairi Allah yasa ka samu Wanda Suka fi Wanda kayi asara Allah Kuma ya Kare gaba wlh da ace Ina da kudi da na taimaka nima,kallonta yayi yace karki damu na gode

   A ranar ya sallami me gadi yace Isa baka min komai ba ga salary dinka na wata biyu ka tafi gida Zan nemeka,Isa yace Sir fatan ba wani laifi nayi ba dan Allah karka kore ni yace ba laifin komai idan na samu yanda nake so Zan kiraka a waya,Isa ba a son ransa ba ya tafi,ya Kira Daya me aikin itama Bara'atu ya sallameta yace nan gaba zai kirata itama tana takaici ta tafi.
   Washe gari Siyama ya samu tana girki ya Bata dubu sittin cash yace gashi na wannan watan da watan gaba kije gida domin nan da sati ma'aikatan banki zasu iya zuwa su kore mu daga gidan Nan,Charity tace bazan karbi ko kwandala ba Sir na bar maka ka rike Kuma bazan bar gidan Nan ba sai ranar da Yan bank Suka zo Zan biku naga gidan da kace zaka Kama haya idan naga gidan sai na koma gida Zan dinga zuwa lokaci lokaci Ina dubaku kayi hakuri da kawata kaddara ce da Jarabawar rayuwa ka Zama me tawakali kasa Allah a ranka Inshaallah shi zai taimakeka,Murmushi yayi cikin dacin zuciya yace ba damuwa,Mamansa ya Kira a waya itama da kudinsa take gadara duk da cewa a wajen Yayarta take zaune a turai,Zuciyar Mum dinsa ta kusa bugawa da taji irin bala'in daya tunkaro danta musamman da ya fada Mata halin Nusaiba abinda take Masa,itama Mum hakuri take bashi akan halin Mata tace sai yayi hakuri dole,tana so ta taho Nigeria yace Kar tazo idan tazo ma wahala zata Sha gwara tayi zamanta Kawai ta tayashi da Addua,Mum har kuka tayi danta ya samu karayar arziki taje tana bawa Yar uwarta labari.
   Tun daga Sanda Nusaiba ta tabbatar Aslam ya talauce kudinta na accnt da shi take kwasa ta fita yawon shakatawarta  ya sallami driver dinsa ma duk da cewar ma'aikatan bank din Basu zo ba tukun a taxi take fita tunda bata iya mota ba,Siyama ce ke Masa girki,yau ma tun safe bai karya ba ya fita akan matsalar data fada masa.

    Sai Yamma baici komai ba ya dawo ya iske Siyama tana Shirya Dining sallama yayi ta amsa tare da furta Sannu da zuwa,Nusaiba fa? Ya tambaya tace bacci takeyi Kai ya jinjina ko a jikinta ita, wanka yayi ya canja kaya wani yard hadadde ya fito da takardu zai sake fita Siyama tace dan Allah ka tsaya kaci abinci tukun,wa ya bani lokacin cin abinci ya furta,tace ka dai Yi hakuri ka dauki komai a nutse,Dining din ya karasa ya zauna Yana Kiran Abokinsa Sabeer Wanda tunda matsalar ta faru tare suke shige da ficensu,Jullof rice ta zuba Masa taji Hadi sai dai ba nama tace Naman fridge din ya Kare jiya Nusaiba ta kwashe ta soyesu duka suna dakinta a soye,yace kyaleta ya fara cin abincin yaji ba nama amma yayi mugun dadi yace Wai ke da Nusaiba waye ya girmi wani ne? Dariya Charity tayi tace Santi ne ko me? Yace na Dade Ina so na tambaya sai na manta yau dai na tuna,Na girmeta Mana ai Nusaiba bama sa'a ta bace Kawai dai school ne ya hadamu kasan makaranta ba lallai ace shekarunku Daya ba ni na girmeta da wurin shekaru uku Yayarta ce ni Charity Allah yayota da son girma Yan watanni ta bawa Nusaiba amma sai tayi ta cewa shekaru ta bawa Nusaiba,Nusaiba ce ta fito ita ba alamar Wasa a fuskarta tace to munafuka na hakura da aikinki ki tattara kayanki ki tafi gidan ubanki,sai wani shishigewa mijina kike Yi karuwa,Charity tace Ina zani ba inda Zan tafi Zama daram,gidanki ne Naga nina kawoki ko,to bazan tafi ba cewar Siyama har ya gama cin abinci suna fada ya mike ya fice,Yana barin gidan Nusaiba ta Kira wani mutum tace ya fita kazo ka dauki motar,Wanda ta Kira bai Dade ba yazo ya shiga katuwar motar Aslam me tsada ya fita da motar,Hijab ta saka tabi Wanda ya dauki motar,wurin siyar da motoci Suka karasa aka Yi cikin mota Wanda ya siya yace ki dawo gobe ki karbi kudi tace to ta tsaya a gefen titi zata shiga mota sai ga wani matashi a dankareriyar mota da alama Yana da kudi yace ranki ya dade barka da Yamma,Nusaiba ta kalleshi ta ja tsaki,yace Dan Allah idan baza ki damu ba ki shigo na rage Miki Hanya,Bata kulashi ba sai da ya fito daga motar wani baki ne Dan mummuna da shi yaci gayu Yana kamshi yace dan Allah ki shiga na rage Miki Hanya sai muyi magana,motar ta bude tare da shigewa Gaban motar ta zauna ya shiga shima yace ko na kaiki wurin cin abinci zamu fi sakewa a nan,tace to ya ja mota zuwa wani hadadden Joint Suka zauna yasa aka kawo Mata lafiyayyen abinci shima haka suna ci suna labari,yace tunda na ganki naji Ina sonki Nusaiba,Dan Allah ki so ni ki aureni,Nusaiba tace Ina da aure Amma karka damu auren ya kusa mutuwa,Matashin me Suna Sufyan yace Alhmdllh Allah yasa ya sakeki da wuri muyi aurenmu,Nusaiba tayi Murmushi tana kora lemo har Suka gama hirarsu wurin magriba ya kawota har bakin gate ta fita tana Masa bye bye ta Shige gidanta,tana Shiga Aslam Yana sama Yana kallonta ta saman yace daga Ina kike Ina motata da Kika fita da ita? Kallonsa tayi Kawai ta dauke Kai,da sauri ya sakko cike da bala'i bata taba sanin ya iya Fushi ba sai yau sai da ta tsorata cikin tsawa yace Ina motata,Tace karka dameni mari ya kwada Mata Karo na farko kenan,Siyama ta fito taga abinda ke faruwa yace Ina motata,Nusaiba ta firgita dafe da kumatu ta fada cikin Palo da gudu
   Wata wire doguwa Siyama ta Mika masa tace ungo ka zaneta sai ta fito maka da mota karka yarda tunda bata Jin magana,karba yayi ya bita ya zaneta tas yasa key ya kulleta a wani daki yace sai ta fito Masa da mota sannan zai Bude ta,Nusaiba ta fashe da kuka ba shiri ta Kira Mamanta,tana dagawa tace kizo Mama Aslam zai kashe ni wlh ya min dukan tsiya sannan ya kulleni a daki sai na fito Masa da mota,Mama tace karki damu gani nan zuwa gidan duk zafin talauci ne ya dame shi

    Aisha zaune take a dakinta da aka gyara Mata cikin gidansu na rufin asiri babansu ya sata a gaba da fada yace yanzu ke abinda Kika Yi kin kyauta haihuwa bata Allah bace, ba fa lallai ki samu miji kamar Farooq ba amma tunda haka kika zaba ga gidan nan kizo kiyi ta zama Allah ya bada sa'a wata haihuwar ma ba gwara babu ba da ita wasu yaran ma in Banda su addabi alumma me suke yi yanzu watakil Baki San Wanda Zaki Haifa ba Allah ya dubaki ya hanaki amma baki gode ba Kawai ke dai ki Haihu ai shike nan ya mike ya fice.
    Aisha tana gida Farooq yaje biko yafi sau Nawa Taki yarda har ya gaji ya hakura,Umma ce ke fada na gaji da kwanciyar nan taki Aisha tunda Kika zo bakya hasala komai a gidan nan sai kwanciya baiwarki ce ni da Zan zauna kullum sai dai na dafa na baki kici ko Sanda kina gidan mijinki Haka kike yi,Aisha ta mike zaune cike da Takaici domin kullum aikin gidan nan kusan ita ke Yi amma mamanta ta hanata sakewa ta Saba da gidanta sai abinda taga dama gaba Daya a takure take jinta,tashi tayi tace gaskiya ni na gaji kullum aiki kullum aiki,idan baki ba Kuwa wallahi babu ke ba cin abinci a gidan nan,Aisha ta zauna Kuwa taki tashi ita kuma Ummanta tana Gama abincin ta hanata ranar yini tayi suna fada da Ummanta kowa na Jin haushin kowa,Aisha sai gidan Yan Uwa taje taci abinci ta dawo.
  Washe gari ma Aisha ta daura gaba da Ummanta ba Wanda yace wa wani ko kazil suna ta gaba da juna,Umma bata Mata magana itama Aisha haka,Takaici yasa Umma ta Kai karar Aisha wurin Babanta tace Wai ka Haifi yaro a cikinka ya dinga gaba da kai Alhaji ka duba Aisha Wai dani zata Yi gaba,Alhaji yace ba ruwana karki sake kawo min Maganar Aisha ke Kika je Kika zugata ta fito daga gidan mijinta sai ku zauna tare gaki gata nan ai,Umma ta fito tana hawaye tace dama nasan baza ka Mata fada ba tunda ba kaunata kake ba Watarana Naga Alama Aisha dukana zata Fara Yi a gidan Nan,Aisha tana ji ko magana haka tayi mirsisi da ita ta Danna headphone a kunnenta tana Jin Waka tana bi da bakinta baza ma taji fadan ba bare ma ta sakko,kwafa Umma ta ja ta koma ta Fara wanke wankenta Aisha baza tayi ba.

      Affan tubewa yayi ya Shiga wanka ya fito daure da guntun Towel,Raudat tana bedroom itama ta window tana hango shi Yana shiryawa Yana ta faman shafe shafe da feshe feshen jikinsa da turaruka Yana ta kalailaita har yafi mace,tunda yazo taje sumarsa yafi minti talatin Yana Abu Daya akan Suma,Raudat baki ta tabe ta saka doguwar rigar baccinta me Dan kauri ta kwanta tare da shigewa bargo duk bata da sukuni sabo da Affan zai kalleta komai sai ta faki idonsa take yi,Yana kallonta duk abinda takeyi kayan baccin ma a toilet ta shirya,Dan gajeren wando ya saka sannan ya zauna a bakin bed Yana Shan ruwa,windown ta ya bude glass yace iska Wai zai Sha,Raudat ta mike ta zuge,ya sake tashi ya bude,ta fito daga bargo ta zuge kafin ta koma ya Mika hannu ta cikin window ya jawo rigarta ta manne a jikin bango rankwashinta yayi ta saki Kara yace karki dawo nan na fada Miki idan ba haka ba Zan dawo cikin bedroom dinki,Raudat da taurin Kai tace wlh baka Isa ka hanani sukuni ba ta maida Hannu zata kulle window ya taka windown ya dane ya shigo cikin bedroom dinta ta window daga shi sai gajeren wando,ihu ta saki kwarto Jama'a kwarto,yace yau sai munyi musayan bed ki kwana a nawa yau a naki Zan kwana tace Allah kiyaye ka shafa min kazantarka a gadona,takawa yayi da Niyyar Daukanta tayi sauri ta taka window tare da dirgawa cikin bedroom dinsa tana ihu,Windown ya kulle yaje ya fada saman gadonta ya kwanta,tace Allah ya Isa mugu azzalumi taci gaba da tsaiwa tana kallon dakinsa ya Sha furniture komai me tsada da kyau ko Ina kamshi yake a ciki Kal Kal Tsaki ta ja ta shiga kitchen dinsa kamar na Amarya komai akwai Raudat tace lallai ya shiryawa karya mutumin nan ta duba sosai tana Bude flask taga soyayyar kaza ta hau kaza da ci taci da yawa sai da ta kusa cinyewa sannan ta duba fridge taga wani katon juice an tsiyayi rabi a ciki ta dauka taci gaba da Shan abinta ya leka ta window Yana kallonta bata sani ba kwayar maye ya saka Mata a ciki yasan kwadayinta sai ya kaita ta Sha,Nan da nan Raudat ta Zama wata Yar kwaya ta kasa bacci taji wani karfi ai sai ta hau gyaran gidan ko Ina sai ta share ta goge ko ba dirty Bata Yi bacci ba Yana dakinta Yana sheka bacci akan gadonta ita Kuwa tana ta gyara Masa gida lungu da Sako har kasan bed sai data janye ta share ta goge ta gyara komai ta fada toilet ta wanke ta goge ko Ina ta dawo aiki bai isheta ba ta fito da kayan fridge ta wanke komai ta goge ta maida kayan neat ta dawo ta rasa me zata Yi ma ta bude kofa tsakar dare ta fita ta Fara sharan uban compound da parking space kowa na bacci tana ta fama kafin gari ya waye ta share compound din me dauke da Interlock ya dawo tsaf,flowers din dake compound har su ta share kasansu kafin gari ya waye taji jiki bata sani ba sai data gama ta fada dakinsa inda ta fito lokacin Sallar asuba yayi lokacin kwayar ta Fara sakinta ta window ta sake haurawa zuwa dakinta ta fada Saman bed bata san da mutum ba ta manta jikinta ya mutu Affan Yana bacci yaji jiki me laushi ya fado Kansa

   Tashi yayi da sauri yaga itace tana shigewa jikinsa da sauri ya dirga kasa daga bed din har zai kwanta a kasa ya tuna shi fa guy ne baya kazanta Tsaki ya ja yabi ta window ya koma dakinsa yace aikin banza warin balaga takeyi ma Yana karkade jikinsa harda shinshina inda ta fado Masa a jiki yace kaji ko warinta ya manne min a jiki irin wannan warin sai na balaga yanzu ma ta Fara balaga na rainata ma banza ta gyara min daki kwadayayya ta cinye min kazata ya furta tare da fadawa saman bed dinsa ya kwanta Kiran Sallah yaji an kwala yace ta cuceni ban karasa baccina ba ya tashi ya daura Alwala ya wuce masallaci yana doro da carbi a hannunsa Kalar jallabiyarsa kullum ko masallaci zai je carbinsa ma toomatch yake da carbi da kayansa carbinsa sunfi kala hamsim ko wanne Kaya da Kalar carbinsa ana taku dai dai ya shiga masallacin unguwar, Liman ya sanshi Yana shigowa zaka ji kamshinsa Yana bawa liman dariya sai dai Yana birge mutane duk gayunsa Sallah a jam'i kullum ba fashi ko wacce Sallah har sun Saba da liman da duk wani me zuwa masallacin.

   Sai da aka idar da Sallah Affan ya daga hannu sama Yana Addua Allah ka azurtani,Allah ka bani kudi....kudi ya Allah na halak...Liman yace samari barka da asuba Affan yace Morning liman how are you? Dariya liman yayi yace Alhmdllh, Affan ya mike tsaye yace lafiya dai liman muyi Maganar a tsaye sabo da rigata zata yamutse ka ganta ta Sha guga bana so ta yamutse na tafi hanya a haka,liman ya zaro Ido yace asuba ce fa yaro da sauran duhu wa zai ganka,Sabo da jin dadin kaina ai ni Zan kalli kaina cewar Affan,Liman ya jinjina kai Yace baka da aure ne? Affan yace wuuu Ni aure rufa min asiri da yanzu Ina nan hankali a tashe Ni da cikakken bacci munyi hannun riga,Liman Murmushi yayi yace kaga Kuma da zaka Yi auren sai kafi haka nutsuwa,Affan yace to nifa gaskiya bana son aure yanzu mace ta dameni da kudin cefane kaina ma da kyar nake rikewa,Liman yayi dariya yace baka da budurwa saurayi kamarka kyakyawa da Kai haka kowa ya ganka yaga Namiji irin Kalar da Mata ke yayi,Affan ya shafa sajensa yace ba ruwana haka Kawai soyayya yanzu sai da kudi inje in tari budurwa bani da abin bata ta ci min mutunci,Liman me kudi ne na gaske yace kaje ka kula ko wace Indai da aure kake sonta Ni Kuma ko nawa zaka Bata Yar hidimar Mata dai Zan dinga baka har muga abinda Allah zaiyi, Affan yace to yaji samun kudi yace dama Ina da budurwa Ina sonta fada mukayi akan kudin anko tana so na za ayi biki na kasa siya Mata anko kunya tasa da kaina na fece,Liman yace tayi aure ko bata Yi ba? Bata Yi aure ba jirana takeyi Kawai Liman yace ka koma ka Bata hakuri ku daidaita Yar hidimar Mata dai Zan dinga baka har a tsaida Maganar aure ya kamata ace kana da aure bai dace mutum me addini irinka ba ka zauna haka Kuma muna limamai mu zuba muku Ido bayan Allah ya hore Mana yanda zamu tallafeku, Affan yayi godiya ya fice Yana murna a ransa wurin samun kudi ya samu shi Kam Yana cewa Allah na gode ma ka amsa Addua ta sai ta fada Kan liman.

     Kwanan Nusaiba biyu a daki a kulle Aslam ya kulleta yace sai ta fito Masa da motarsa abinci ma Dan kadan yake Dan zubawa ya Mika mata,tana ta kuka ta dinga Kiran Mama a waya,ba shiri Mama ta sauka a kofar gidan Charity tana bakin kofar da aka kulle Nusaiba tace ki fito Masa da motarsa a zauna lafiya,Nusaiba tace sai naci uwarki shegiya munafuka,Aslam Yana gidan yaji ana bubbuga gate yaje ya bude yaga mama ce ta shigo tana karewa gidan kallo tace Ina kudinka? Ina motocinka makaryacin banza dama karya kaje kake Mana ka jefa yata a masifar talauci,Aslam yace kije ki fadawa yarki ta fito min da motata,Mama ta kalle shi tace butulu wato babu mutunci ba girmamawa Aslam bai kulata ba suka shiga ciki yasa key ya Bude dakin Daya kulle Nusaiba Yana tsaye ya tare Hanya Mama ta shiga tana shiga ya maida kofa ya datse ya kulle su tare a dakin yace ku fito min da motata na fada muku,Mama ta zaro ido tace dama haka yake baida mutunci,Nusaiba tana hawaye tace wlh Mama zai kashe mu Yana da bindiga,Mama tace kwantar da hankalinki yanzu Ina motar? tace na siyar da ita ko kudin ma ban karba ba ya kulle ni,a jikin kofar Mama ta tsaya tace dan Allah surukina ka Bude mu sai muje a karbo maka motarka,Aslam ya kalli Charity dake sanye da Riga da skert na Atamfa wasu kodaddu yace wlh mutanen nan sun maidani wani banza,tunaninsu Banda hankali, charity tace yo ai Basu san da hankalinka bane basu san Kai cikakken Namiji bane sai yanzu,Aslam yace dan Allah? Charity tace Allah,yanzu ni cikakken Namiji ne? Ae sosai yanzu na tabbatar Amma da ka zauna Kamar solobuyo,Murmushi Aslam yayi yace Ni kaina sai najini wani na sake girma yanzu, Charity tace ah ai sai yanzu ni kaina na ganka kato,yace haba,? Tace Allah da karami nake ganinka, dariya sukayi Siyama tace Kara sa key na uku a fito da mota,Aslam ya bubbuga kofa gam gam hankalin su Nusaiba ya sake tashi yace a fito da mota,abinda zai muku zakuyi mamaki idan baku fito da mota ba cewar Charity tana taya Aslam Kamar kanwarsa.

     Sai zuwa Safiya Aslam ya Bude kofa zai Basu abinci Nusaiba ta kwada Masa tsinin takalmi choge Nan take ya dafe Kai ya Fadi kasa a sume ga Charity bata kusa da gudu Nusaiba da Mama Suka fice daga gidan suka tafi wurin siyar da motoci zasu karbi kudi babu Wanda ya karbi mota ba alamarsa Suka tambayar duniya akace ba a sanshi ba Ashe Dan damfara ne barawon mota Kuma ya gudu da mota,Nusaiba sai da ta Fadi har kasa sabo da kudin ta gama kasafin su,ba kunya suka tashi Suka koma gidan Aslam,lokacin Charity ta shigo ta kwala ihu ganinsa a kwance jini na zuba ta Kansa da gudu ta fita ta samo wasu maza biyu Suka taimaka Mata aka sashi a mota taxi zuwa asibiti,Allah yasa Babu matsalar kirki dressing Suka Masa bayan ya farfado suka dawo gida Kansa nade da bandage Charity tana Masa Sannu sannan tana bashi hakuri har Maman Nusaiba ta shigo da gudu tana kuka tace Nusaiba ce ta Sume,Siyama ta rude ta fita taga Nusaiba a sume tayi suman karya sun hada wayo,Aslam ya fito shima da Kansa ya dauki Nusaiba Kamar bai gano su ba ya shigar da ita bedroom ya kulle ya sake sa key yace sai ta fito min da motata,Mama da tana murna Aslam ya yarda da karyar su, yace Mama tun kafin na dakko bindiga ki bar min gida,Mama da gudu ta fice daga gidan,Charity tace dan Allah kayi hakuri haka tunda motar nan sun riga sun siyar,Nusaiba tana daga ciki a kulle ta saki kuka tace wlh dan damfara ne ya gudu da kudin,Aslam saman kujera ya zauna cike da bacin rai sai da yayi kwalla sabo da bakin ciki yanzu ya tabbatar Kuwa siyar da motar tayi,yana so ya siyar da su ya biya banki kudi yanzu ta salwantar da motar gashi tafi kowacce tsada,hawaye ne ya zubo Masa Sabo da bakin ciki wannan wacce irin kaddara ce haka,tashi yayi Kawai ya sa key ya bude Nusaiba ta fito tana kallonsa tace akan wata tsohuwar mota harda kwalla lallai ka cika me son kudi Kan bala'i,waccen irin marar Imani ce ke Nusaiba Charity ta furta ranta a jagule ashar Nusaiba ta dura Mata ta haura sama tana Jan tsaki tana cewa akan wata banzar tsohuwar mota.

    Cikin kwana uku Aslam ya tattara komai na kadara ya damkawa bank gida Kawai yake jiran ranar da zasu zo,Mum ma dubu dari Uku ta turo Masa daga can kasar da take Qatar, wasu kayan girkin ma babu a gidan yau Charity ta rasa me zata dafa kwata kwata tana Jin kunya Kuma a halin da yake ciki ta tambayi wani Abu Kawai sai ta dafa wake da shinkafa da Mai da yaji,ta shiga tayi wanka ta canja cikin doguwar rigar tsohon leshi tayi kyau gata kyakyawa komai yaji,tana Fitowa ta iske Nusaiba an Sha gayu cikin wani tsadajjen material tana latsa waya,Aslam ne ya fito sanye cikin kayan Shan iska Gajeren wando da Riga me gajeren hannu sky and white yayi kyau sai dai ya dan rame sabo da matsalar da yake ciki,Siyama tace Yaya Aslam na gama abinci amma wake da shinkafa na dafa da Mai da yaji,yace oh da kin fada min ba abubuwa na manta wasu abin sun Kare da an siyo ai Allah bai hanani kudin cefane ba ai ni na manta ke kuma baki tuna min ba,Charity tace bana so na takura maka ne ban San halin da kake ciki ba,thank you ya furta,Nusaiba ko kallon su Bata Yi ba tana Danna waya sai ma tabe baki da tayi,Siyama tace amma Ina ganin da kifi zaka fi iya ci,dubu Daya ta isa? ya tambaya tace ae ta karba,Nusaiba ta ja tsaki tana kunkuni Dan karya anzo gidanmu da motocin aro ana nuna kudi an kawo Ni tankamemen gida Ashe duk na aro ne daga yin aure cikin wata uku za ace komai ya Kare bank ya cinye kudi dama ba gaskiya bane duk kayan aro ne.

    Charity ta kalleta Kawai ta yafa mayafi ta fice ta siyo salat da tumatir da kudinya ta siyo kifi manya soyayyu ta dawo ta iske Nusaiba inda ta barta ta samu Aslam a dining Yana jira,a gurguje ta yanka salat da tumatir da cucumber ta wanke ta kawo Dining,tana zuwa Nusaiba ta taso ta zuba abinci tasa Mai da yaji ta barbada Maggi zata kwashi salat Charity ta rike hannunta tace kinyi kadan yarinya wannan ba kudinki bane sai ki bari sai na zuba Miki,Nusaiba tayi zuciya ta mike tace bazan ci ba na fasa cin abincin gaba daya,Wacce Nusaiba ta zuba Charity ta ja gabanta ta saka kifi da Salat sannan ta zubawa Aslam shima da kifi da Salat ya fara ci,Nusaiba Kuwa ta WhatsApp tace anjima Sufyan saurayinta yazo ya kaita zata ci Dinner a restaurant da rawar jiki yace an gama.

    Aslam Yana fita Sufyan yazo da Yamma likis Nusaiba ta dauki wanka har bakin gate ya dauke ta ya kaita hadadden wurin cin abinci,Suka ci Suka Sha harda ciko Mata Leda da snacks Suka dawo har bakin gate ya sauketa Suka Yi sallama,lokacin Aslam bai dawo ba a taxi ya fita Charity tana kallonta basu kula juna ba.

   Bayan kwana biyu Aslam Yana gudun Kar azo a musu wulakanci Nusaiba tana gyara kayanta yace Baby ki shirya gobe zamu tashi daga wannan gidan zamu koma gidan Dana Kama Mana haya,Wani Takaici ya kama Nusaiba,Aslam yace kaddara ce kiyi hakuri kinji,Kuka Nusaiba ta rushe Masa da shi tace ka cuceni da ka min karya na aureka,me yasa baka da Imani burinka ka jefani a wahala,Aslam yace kiyi hakuri,ranar kwana Nusaiba tayi tana kuka dama yanzu bata bashi hakkinsa ta daina tunda taji ba kudi ta daina yarda da shi Watarana sai yayi Kamar zai Mata kuka take yarda da kyar.
   Washe gari taxi ya Nemo Siyama ta fito da kayanta itama ta sa a Bayan mota,Dukkan kayan sawarsa da na Nusaiba mota guda aka Yi aka Kai gidan,kayan abinci da komai aka kwashe da abin bukata sauran duk a gidan aka bari,kayan kitchen na amfani duk ya tattara komai ankai,Nusaiba tana hawaye ta fito ta Shiga taxi ya zauna a gefenta Charity tana gaban mota,mota na tafiya Nusaiba tana hawaye tana cewa babu ac ne tana fifita da hannu,Siyama ta furta Aslam Wanda ya Saba da ac baiyi complain ba sai ke sama ta Kai da can kin San ac din ne, ki min Shuru munafuka cewar Nusaiba.

    Hanky Aslam ya mikawa Nusaiba ta dauka da bala'i ta jefar,wata unguwa Suka Isa wacce ta masu rufin asiri ce da talakawa a Kano,wani dan karamin gida ne Wanda na bulon siminti ne gidan hayane Wanda ke dauke da Palo da one room kacal sai toilet da kitchen shikenan gidajen haka suke a jere iri Daya sun Kai guda goma wani me kudi ya Gina yake zuba Yan haya,Yan makaranta ma sunfi yawa a wajen Sabo da irin kankantar gidajen,Nusaiba taki Fitowa daga taxi tana kuka sai da me Taxi ya daka Mata tsawa,dama an diga an kawo kayansu duka, Ciki Suka shiga kujeru ne a palon matsagaita amma masu kyau ne sai karamar plasma tv,dama duk tiles ne har dan tsakar gidan,bedroom din Kuma gado ne shima Kalar kujerun da labile Kalar komai kala Daya Kamar wani gidan Yar maryar talaka,kitchen Dan kut da shi,Yace ki daina kuka ki shirya kitchen,Nusaiba ko kulashi bata Yi ba Siyama ce ta shirya Kaya ta gyara komai har bedroom din ta shirya sannan ta dauki jakar kayanta tace Yaya Aslam na tafi sai na sake leko ku,Yace dan Allah ki dinga dan zagayowa, Inshaallah cewar Siyama,Ya bata dubu biyar da kyar ta karba Dan Kawai bata da ko sisi ne,a nan ta bar Nusaiba a zaune tana shirga kuka.
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

           31-35

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

BK
MMN MUNIBA
HAFSA ABDULLAHI
         Kallonta yayi tana ta kuka shima yayi shuru ya gaji yace kaddara ce ta afka min ba haka naso ba ki daina wannan kukan daga karshe ya tashi ya fita abinda Babu na ci ya siyo musu ya sake zubawa a kitchen amma Nusaiba ko kallonsa bata yi ba har azahar tayi lokacin yace kin San dai lokacin Sallah yayi ko,kanta ta dago idonta jajir ta watsa shi a saman fuskarta,tashi yayi tare da daura alawala ya fice ya barta nan tana zaune sai da aka idar da Sallah sannan ta iya tashi ta shiga bedroom din ta jefa hand bag dinta saman bed din ta shiga toilet tana Jan ajiyar zuciya kamar wacce aka nadawa duka.

     Siyama Kuwa tana komawa gida ta shiga da sallama Aunty tace ba dai an koroki ba? Siyama bata boye musu ba ta Basu labarin komai Aunty tace amma Nusaiba ta bata wayonta ka samu miji haka irin mijin Novel zukeke ga kudi amma ta dinga irin wannan rayuwar gaskiya na tausaya Masa shike nan zauna mu koma siyar da alalar mu inda Muka fi wayo amma Nusaiba ta bani mamaki samun miji haka,Dauda yace to anji kin damu mutane da miji kyakyawa ne ni bani da kyan ne?kina ta wani yabon mijin wata ga naki amma baza ki yabe shi ba,Siyama tace to ai Kaine Kawu lebe Kamar sakatar kofa,zanci Ubanki Dan ubanki lebena ne kamar sakatar kofa? Siyama ta sake cewa ba lebeba hakora kamar goslow a hanyar Lagos wasu sun taho ta nan wasu ta can,Dauda yace Zaki ci ubanki ni ba ubanki bane Zaki dinga maida Ni kakanki ki kiyayeni wlh,Aunty tayi dariya tace gwara da yarka ce ta fada da nice cewa zaka Yi sai kaci mutunci na

     Mama ce a zaune tana waya da Nusaiba tace me nake ji Haka gida daki daya chab dama karyar tasa ta Kai haka,Bari dai sai nazo ta furta lokacin Shehu Yana gida kusa da Mama a zaune,yace Wai ke me kike nufi ne? Nusaiba kin hanata sakewa naji labari jiya Ameer ya fada min komai yanzu tsakani da Allah ki kalli gidan nan da a kuntace muke amma yazo ya Kara Mana dakuna ya Bude Miki shago bafa ni ba ke ya budewa shago ya bani jari Kuma na koma kasuwa sosai ya auri yarki yanzu tsakani da Allah dan karya zai iya yin wannan taimakon,a tunanina ke me yiwa Nusaiba fada ce ashe ke kike zugata, Babu abinda zaka fadamin Shehu dakata kana ciyar damu?, Tunda na taso a gidanka wahala nake Sha Ni da yarana,Sanda Ina da hali ba kece kika cinye kudin ba suka Kare Kika tsaneni komai nayi Miki ban birge ba ya Zan Miki face na zura Miki Ido ke da yaranki tunda kince ba abinda nake tsinana muku,Hakkin Yara a kanka yake kwarai kuwa na sani amma idan na baki kudin cefane kina bari ki basu abincin ba kadan kike dafa musu ba ki siyar da sauran komai na baki siyarwa kike yi,Mama tace to ka kyale min yata ba ruwanka yace Ina da hakki na fada Mata gaskiya,yanzu bazan magana ba tunda bai kawo kararta ba amma duk Sanda ya kawo Kara Nusaiba zata Gane kurenta auren me kudi hauka ne da arziki da talauci duk na Allah ne Kuma wlh kuji tsoron Allah ya mike tare da sa takalminsa ya fice.
    Mama Kuwa Ameer ta samu ta balbale shi da fada akan me zai fadawa Shehu.

    Charity Alalarta taci gaba da yi amma yanzu tallan ma bata fita ake zuwa a siye a gida,Nusaiba tunda Suka koma gidan haya bata girki ficewarta takeyi su hadu da Sufyan saurayinta a restaurant in taci ta koshi ta dawo gida,Aslam da Kansa yake dafa ma Kansa abinci bai iya ba amma haka zaiyi jagwalgwalonsa ya ci,yau da Yamma Siyama sai gata a gidan sanye da hijab har kasa da Leda a hannunta tayi sallama ta shigo Murmushi ya saki shi ta iske a palo yace manyan kasa ne yau a gidan, Charity dariya tayi ta rusuna tare da gaida shi ya amsa,Ina matar fa? Ta fita ta tafi gidansu yace,Siyama tace okay dama abinci na kawo maka ban sani ba ko tana girkin,yace wow na gode Kamar kin San yunwa nake ji,ledar ta Bude ta dakko abinci a robobin take away har kala biyu tace kaga wannan Fried rice ce dazu Muka Yi da Aunty wannan Kuma tuwon shinkafa ne miyar Egusi,Kawuna nane ya samu kudi shine yau Muka ce bari muji Dadi kaci kaji da Dadi harda nama,mikewa tayi ta dakko spoon a kitchen tace gashi ya karba Yana kallonta cike da mamakinta tafi matarsa sau dubu,Fara cin abincin yayi gaskiya yayi Dadi ya furta Yana ci Siyama tana Kare Masa kallo,kallon fuskarsa takeyi Yana ci har ya cinye daya ya Sha ruwa pure water yace dayan sai dare tace to,Charity ta tura dayan kasan kujera tace gashi a nan na boye maka Kar marar Imani tazo ta dauke,dariya yayi yace na gode ta hada ledarta da roba tace tafiya zanyi tunda bata nan, yace da wuri haka kiyi zamanki ki tayani hira dama na gaji da kallon film,tace to ta zauna tare da tambayarsa har yanzu baka samu aiki ba ka fara?

    Ae yace Mata amma Ni da abokina Sabeer Muna ta fafutukar nema ko za a dace, Charity tace to Allah ya kawo tana Jin kunya tana satar kallon Aslam ba karya ya hadu gashi Kamar balarabe fari tas ita Kuwa ja ja ce, gidan ta kalla kaca kaca tace gidan naku yayi dirty yace a haka ma Ni nake sharewa,mikewa tayi ta hau shara ta gama tayi mopping ko Ina ta gyara kitchen,toilet din ma ita ta wanke musu ita kal kal ta dawo Palo ta zauna suna kallon film game yakeyi a wayarsa ps tace game kake Yi? Yace kin iya ne? Tace ae na iya wani abokina ne Hunaif yake bani wayarsa Ina Yi,yace ko dai saurayinki ne? Dariya tayi ya kalli kyawawan hakoranta reras gata kyakyawa sosai tace ya taba cewa Yana so na danginsa suka hanashi sabo da Ina saka riga da wando Wai Yar Lesbian ce ni,Dariya Aslam yayi Yana latsa waya yace ai maganinki kenan da kike saka riga da wando  ke ba a kudu ba kin San wani Yana kallonki shedar da zai Miki ta banza shi yasa ake so a dinga kiyaye shiga,da shiga ake Fara gane mutumin kwarai ga sunanki Charity kowa Charity,Siyama tace ai Riga da wandon ne yasa a unguwa aka saka min suna Charity idan na nuna bana son sunan anfi kirana da shi that's why na karbi sunan Hannu bibiyu,Riga da wandon ma kana ganinsu manya manya nake sawa bana saka damammu Kuma yanzu na rage sakawa tunda nake Yana damaging Image dina,yace yawwa ko ke fa ai yafi amma dole ace Yar lesbian ce tunda barma barma kike sawa Kalar na maza,dariya ta sake Yi akwaita da fara'a,tace Allah ya tsine musu wlh masu lesbian ga maza can suna nema Mata suna musu mugunta,dariya Aslam yayi ba shiri yace Charity kenan ke kam ba ruwanki da boye boye kamar Yar kudu haka kike Charity tace idona ne ya Fara tsikewa da duniya mu fa Yan talla ne iya shege ba Wanda bama ji,sai da na Fara talla na gano illar barin ya mace tayi talla

    Kaga idan mace tana talla ko wanne gara Wanda ko a Hanya Bai Isa ya Miki magana ba idan kina talla kowa zai kulaki ko wanne gaja ne Kuwa,sannan akwai Wanda a hanya bai Isa ya iya ko magana ba Amma sabo da talla zai fada maka Maganar da yaga dama,sannan me talla kowa Yana da lasisin da zai Mata magana ko a dinga tsokanarta ko wani ma yaci Mata mutunci,mace me talla Namiji zai iya janta da zancen banza ya ja mayafinta ya daketa wani ya mareta wasu Kuma duk Magana ta banza yarinya tun tana karama Matukar tana talla za a dinga Yi a gabanta,tunda waje ne na maza idan Suka taru akwai kalaman banza da bai dace taji ba amma za a dinga Yi a gabanta wasu ma su dinga janta da Harkar banza irin wannan ke sawa Yan talla suke lalacewa yau da gobe zata Saba har ta daina kunya,sannan ga gogayya da maza mutane manya daban daban zai sa idonta ya bushe ta dawo Bata da kunya Kuma bata tsoron kowa kadan daga illar talla ga ya mace,Aslam yace hakane Nima sai yanzu naga hakan, Uhm ta furta tana kallon Wayar hannunsa me tsada

    Sabeer ne yayi sallama tare da shigowa shima,Sai yau Siyama taga Sabeer,gaida shi tayi Yana binta da kallo ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa ya zauna yace ko kece Siyaman? Charity tace ae yace Sannu mun gode fa,Sabeer ya dameta da kallo,Aslam Yana kallonsa,Siyama mikewa tayi tace zata tafi,sai yaushe? Aslam ya tambaya tace sai an ganni Kawai yace muje na rakaki Suka fito tare suna tafiya a hankali suna hira tana ta bashi dariya.
   Nusaiba aka sauke a taxi ta tsaya tace Charity sai da Kika sake biyo mu Nan dan masifa yanzu ba kudin da za a  baki to,Tsaki Siyama ta ja tare da furta banda lokacinki Nusaiba,Nusaiba ce tace zo wahalalliya Ina son magana dake,Charity ta ja gefe Nusaiba tace tunda taku tazo Daya da Aslam dan Allah kisa ya sakeni,ki fada Masa Ni takarda ta nake so ya sawwake min na gaji bazan iya rayuwa da shi ba,Siyama ta kalleta tace ki kalli Namiji irin Aslam hadadden mutum Kamar shi yayi kansa kice Wai kin gaji da shi,ae dan Allah ni na gaji bana son auren ya sakeni,kinfi so ki Zama bazawara ae gwara haka ke karuwai ma suna nan su da karuwanci suke Yi suna zaman su a duniya Lafiya bare ni Dan an sakeni na Zama bazawara,wlh idan Bai sakeni ba Kara Zan kaishi wajen Yan Hisba,Siyama juyawa tayi tare da komawa wajen Aslam ta fada Masa abinda Nusaiba ke so saki,yaji Matukar ciwo ya danne,Yana komawa gida tace wallahi yau ba zaman lafiya sai ka sakeni,Aslam yaki kulata rigarsa ta rike ya samu ya kwashe ta da Mari ya sake zabga Mata Mari Wanda ba shiri ta sake shi tana kuka wallahi sai ka sakeni,yace baki ji kunya ba mahaukaciya aure wata hudu na sakeki Baki da hankali,kuka Nusaiba takeyi sosai yaki sakinta haka Suka kwashe satikai kullum da masifar da zata fito da ita a saketa sabo da bai da kudin da zata karba yanzu Kuma sai takalo rashin mutunci iri iri shi Kuma yaki sakinta,harda daina kwana a dakinsa ta dawo palo a nan take kwana kullum.

    Yau Mama ce tazo gidan tana zuwa ta saki ihu a palon tace a Nan yata take Zama daki nawa ne? Nusaiba dake zaune tace daya,Daya tal yanzu idan da kwana zanyi bani da wajen bacci kenan tab amma Aslam ba karamin azzalumi bane ka ajiye bawa me rai a nan, Nusaiba tace zauna Mama bari na Miki girki dama bana dafa Masa abinci,Mama tace kinyi dai dai tana zaune Nusaiba ta dafa Mata shinkafa da Miya harda kazar da ya siyo jiya Mama taci ta tauna Kashi ta sha ruwa me sanyi ta sake zuga yarta tace Kai Kai kamarki a wannan gidan daki Daya sai Palo kujerun ma ba na kasar waje bane ba Yan Dubai ba Yan nan Kano ne,Nusaiba tace kalleni Mama yanda na girma nayi kiba nayi wani fresh kowa ya ganni yaga kalar hutu amma matsiyacin ya makale yaki sakina,gida ko filin tsakar gida babu kalli tv din ma karama sai kace ta Office din principal din makarantar sikandire cewar Mama,wani takaicin Aslam ya sake rufe Nusaiba,Mama Kuwa sai sake zugata takeyi,tashi tayi ta leka kitchen ai wani ihu ta saki tace hodijam inji Dan fillo wannan kina samun balance kuwa? Sai dai manage Mama shi yasa bana shiga

  Suna haka Aslam ya shigo sanye cikin wata shadda Yar ubansu grey color cikin kayansa na baya masu tsada ya saka ya shigo da takardun makarantarsa,Mama ta Bata rai tare da kallonsa shekeke ta tabe baki tace kamar gaske akwai kudin Kai karya bata Yi ba,Aslam ko kulata baiyi ba ya wuce bedroom dinsa,Mama tsabar rashin son zaman lafiya tace sai na dawo kwana zanzo na kwana biyu haka,Nusaiba tace Allah ya nuna mana Mama  sannan ta fita ta tafi gida,Aslam ya fita bai dade ba ya dawo da Leda a hannu yayo cefane harda Naman rago da yawa,tun kafin yayi magana Nusaiba tace wlh sai dai ka dafa da kanka Kuma abinci daga ni sai uwata na dafawa mun cinye,bata ko rage Masa ba gashi Yana Jin yunwa Charity bata da waya bare ya Kira ta, tashi yayi ya fita bai ko saurari Nusaiba ba ya shiga Napep zuwa gidan su Charity

   Yana Fitowa daga Napep Suka hadu da Shehu Baban Nusaiba,Shehu da fara'a da murna yace surukina gobe nake so nazo gidan naka jaje wlh ashe haka Abu ya faru marar Dadi,Aslam ya duka zai gaida shi yace tashi tashi  Aslam ubangiji ya maida alkhairi,yace ameen,Shehu yace ya Nusaiban iceko lafiya kuke? Aslam baiyi kasa a gwiwa ba ya zayyanewa Shehu komai,Shehu Baki ya rike yace wallahi ban San me ake ciki ba abin wato har ya Kai haka,duk uba bazai so a saki yarsa ba amma tunda Nusaiba take maka haka na baka dama ko nine iyaka abinda Zan iya kenan na saketa,Dan Allah kayi hakuri Kai mutumin kirki ne,har gobe Ina ganin mutuncinka Kuma bazan fasa zumunci da Kai ba ko da ace baka tare da yata,Aslam yaji dadi da farin ciki,Shehu yace ka kyale Maman Yarinyar tunaninsu daya taho muje gidan Yar uwata ka huta a can,Shehu yaja Aslam zuwa gidan Yar uwarsa Alawiyya ba nisa da gidansa ita me rufin asiri take aure komai nasu me kyau ne,kana ganin Aslam zaka Yi tunanin da kudinsa tunda Yana da sutura,palon Alawiyya Suka shiga babbar dattijuwa yace mijin Nusaiba ne,Alawiyya tace Shehu ai na gane shi,Aslam ya gaishe da ita ta fita ta kawo musu lafiyayyen girki Aslam dama yunwa kamar zai mutu baiyi Kara ba ya zage yaci ya koshi shi da Shehu Kamar ba surukai ba suna yin Sallar la'asar Aslam yace zai tafi Shehu ya rakoshi har kofar gida Suka Yi sallama shi ya koma cikin gidan wajen Yar uwarsa,Aslam Kuma ya karasa kofar gidan su Charity,Yana tura yaro ciki sai gata ta fito zata siyo manja,taga Aslam ba zato,Murmushi ta saki kayatacce tace Ina yini ya amsa da fara'a tace Ina kaje haka? Yace cefane nayi tace baza ta dafa ba nama ne zai lalace shi yasa nace Bari na kiraki ko ki dafa min ko kizo ki dauka ki kawo gidanku kuci Kar ya lalace,Charity tace nama guda wa yaki dadi har kasa yawuna ya tsinke,ya saki Murmushi ba shiri,ciki ta koma tace Aunty ga kudin ki aiki yaro Aslam yazo nema na,Aunty tace Kuma dan Iskanci sai ki dawo da kudin,Bata tsaya ji ba tace ki fadawa Kawu matsala ce a gidan zanje wajen Nusaiba,Aunty tace to a kula dai tace to,ta fito tare da cewa muje Suka fito tare Suka Mike suna tafiya suna Hira har yaji sanyi a ransa

   Titin kwalta zasu tsallaka Yana ta tunani ya tafi bai kula da mota ta kusa zuwa inda yake ba Siyama ce ta taho da gudu ta fisgi hannunsa tace mota da sauri suka tsallaka suna tsallakawa motar ta wuce da mugun gudu,ta kalleshi tace tunanin me kake Yi haka ta furta tana kokarin zare hannunta a nasa Wanda ya damke hannun nata cikin nasa Yana Jin wani shock da bai taba jinsa a jikin wata ya mace ba,Napep Suka shiga zuwa gidansa Siyama ce ta biya kudin ta hanashi ya biya kudin,suna zuwa Nusaiba chatting take abinta ga ledar kayan nan a gefe,Siyama tana zuwa tace ke ballagazar matar aure shashashar matar Aslam, kallon Charity Nusaiba tayi Kawai ta ja tsaki,Siyama ta zari ledar Aslam ya zauna tace Ogana me za a dafa Murmushi ya saki yace kiyi farfesu Kawai sai Dan abincin dare,an gama ta furta tana kallon Nusaiba tayi fatali da kafar Nusaiba dake mike a hanya tace matsa can Yar banza Yar wofi,wawiyar banza,Dariya Aslam ya shiga yi Nusaiba ta galla Masa harara tace dan uwarki ba Charity kike ba ko Ngozi kike nafi karfinki wahalalliya me bauta a banza, Siyama ta yiwa Nusaiba dakuwa ta shiga kitchen tare da kunna gas ta Fara aikin girkin sai wurin magriba ta gama farfesun ta ebi dan kadan a roba me murfi ta rufe,Ta fuskanci yana son tuwon danyar shinkafa shi tayi Masa da miyar danyar kubewa ta Gama komai yayi Alwala zai fita masallaci tace na gama, yace Banga kinci ba tace gashi na eba ta nuna Masa robar, tare Suka fita ta shiga napep shi Kuma ya wuce masallaci.

     Nusaiba tunda tana zuwa restaurant bata damu da abincin Aslam ba Sufyan Yana mugun kashe Mata kudi yanzu burinta Aslam ya sake ta,washe gari Mama Shehu ta tambaya tace zata je kauyensu ya barta tana tafiya sai gidan Nusaiba da Yar Jakarta wai tazo zata kwana biyu a gidan yarta,Nusaiba ta dauki Jakarta ta Kai bedroom ta hau girke girke Aslam Yana zuwa yaji kamshin girki na tashi yasan da dalili shigarsa bedroom kenan ya iske Mama a ciki yaga Kuma jakar tata tabbas kwana zata yi, mamakin suke mugun bashi,Mama ganin ya shiga ta fito,a gabansa a palo Suka zubo abincinsu Suka ci Suka koshi ko tayi basu Masa ba Yana Jin yunwa sai fita yayi yaci a resturant bai dawo ba sai 10pm lokacin Mama da Nusaiba sunyi Shirin bacci sun kwanta a saman gadon me gidan sun shige bargo tare,Aslam ya dan leka ya  girgiza Kai yace idan baki  da kunya Mama kin hadu da Dan zamani,bedroom din ya Shiga Mama ta bude baki,toilet ya Shiga suna ji Yana wanka Mama tace yau na shiga Uku da fitsararre,sai da yayi wanka ya fito daure da guntun towel,Mama Hannu ta dora a Kai tare rufe Ido tana yau na shiga Uku yau Naga jaraba,cikin bargon ta Danna kanta,turaruka ya fesa ya zura Jallabiya arsh,Kawai Saman bed din ya nufa yace Mama Dan matsa gefe kadan gadon zai iya daukar mu mu uku ba damuwa,Mama taga da gaske hawa zaiyi ya kwanta ta dirga kasa harda faduwa tace amma Kai ba dan arziki bane ban taba ganin suruki marar tarbiyya ba sai kai ta fice Palo tana cewa Nusaiba Miko min jakata a Daren nan Zan koma gida,Nusaiba ta mike tana hararar Aslam ta dauki jakar Mama da tarkacenta ta fito,Aslam ya kwanta a saman bed dinsa tare da Jan tsaki yace iskancin banza tunaninku ku kadai ne Yan iska uwar banza ya lulluba da bargonsa,Ita Kuwa Nusaiba a daren ta fita ta samawa Mama Napep ta koma gida,Shehu sai ganinta yayi ta dawo,yace ya na ganki ke da Kika ce Zaki kwana a kauye,Mama tace Wlh mutan gidan da naje domin su sunyi tafiya basa gida shi yasa na dawo,Shehu yace ke Kika sani kuma.
Washe gari da wuri Nusaiba ta Kai karara Aslam Office din Yan Hisba tace so take a fadawa mijinta ya saketa bashi da lafiya baya iya biya Mata bukatar Aure sannan ma ita ta daina sonsa ya Fadi abinda ya kashe zata biya shi ya saketa,Aslam yana gida ya fito zai fita Kawai yayi arba da jamian hisba mutum biyu suka Mika Masa takarda ana nemansa a Office din Hisba yasan Nusaiba ce kawai Sabo da haka Kawai sai ya nufi can a Napep.

      Wacece Raudat

Raudat Ibrahim Waku 'yace ga Ibrahim Waku hamshakin me kudi ne dan asalin jahar Gombe Wanda ke zaune a Oyo state,tunda kasuwanci ya kaishi can ya shahara ya Zama hamshakin me kudi na gaske ya tattara da yaransa su Raudat gaba daya ya koma Oyo da Zama,matarsa daya tal Hajiya Rahmatu itama Yar Gombe ce, yaransu biyar Raudat ce babba sai kannenta biyu maza biyu mata,Raudat tana gama secondary ta samu Saurayinta Hussain dan Kaduna state,Hussain talakawa ne a zahiri ba son Raudat yake ba irin masu auren Mata ne dan kudinsu dan ace Kawai ya auri Yar me kudi,Baban Raudat tunda yaga Hussain da Kuma cewar baya sana'a ko kadan yace ta hakura amma taki ji Sam dole aka Yi Mata auren wuri

    Bayan anyi auren Raudat da Hussain Baban Raudat shine ya Kama musu gida haya a Kaduna sannan gara ma kayan abinci mota guda aka ajiye da komai sannan baya Bari yarsa Raudat da talauci,Raudat komai ita ke Yi a gidan ta koma itace mijin ba karya akwaita da hankali ga hakuri duk wani kyan haki Raudat tana da shi dai dai gwargwado,Hussain Kawai sai dai ya kwanta an bashi jari ya cinye an sake bashi har Karo na uku amma sai ya kashe,tunda Raudat ta aure shi bai taba kwanciyar aure da ita ba Basu taba sex ba sabo da bashi da lafiya amma yaki yarda fada bashi da lafiya,abinka da yarinya itama sai ta kasa fadawa kowa suna zaune haka har kusan shekara Hussain ga mugun son Mata bai da aiki sai kula Mata duk kudinsa Yan Mata ke cinyewa shi Kuma dayar ma da ya aura ya kasa biya Mata bukata amma Yana hangen na waje,a Haka ko Raudat bata bashi kudi ba sai wulakanci da cin mutunci iri iri Indai tana son zaman lafiya to ta bashi kudi,abinda yake batawa Raudat rai Shan giyarsa sai ya Sha giya yazo ya Mata dukan taiya,duk ta rame sam bata San mene dadin miji ba,ana haka ya fara Mata sharri sai ya shirya zance na karya ya fadawa dan ginsa da abokansa,akwai Sanda ma yace bata bashi abinci Kuma har zaginsa takeyi,Watarana ma ya dinga fadawa abokansa ai maza take bi da Aurenta har kunnen Danginsa zance.

Su Kuma dangi ba bincike ba komai suka saka Raudat a gaba Babar Hussain da kanta ta sa Hussain ya saki Raudat dama bai damu da ita ba itace take sonsa kawai a hakan ma da ya saketa sai da ta Sha kuka auren shekararsa Daya da Dan watanni ta koma gidansu,tayi jinyar zuciyarta sosai kafin ta hakura da son Hussain shi kuwa Hussain baya ta tata Sam,Babanta ne ya maida ta school tayi degree tana gamawa ya samo Mata aiki Babba da NGO su Kuma duk inda aka turaka aiki dole sai ka je,Kano Suka kawota supervisor ce sune suka rabawa irinsu sababbin motoci masu tsada,dama Kuma a can Oyo tana da tata motar da Babanta ya siya Mata,shi yasa tazo kano ta Kama gidan haya har Suka hadu da Affan suke fada Kuma kusan a tare Suka zo Kama gidan ta Sha Matukar wahala a hannun Hussain kafin Allah ya yanke mata.

        Affan

    Affan Kuwa asalin Fulanin Zamfara state ne, sunansa Aliyu A. Aliyu,mahaifinsu su biyu Maza ya Haifa Yusuf shine Babba an haife shi da shekaru hudu aka samu cikin Affan,da cikin Affan Allah yayiwa babansu Aliyu rasuwa,Babar su tana haihuwa aka sakawa Affan sunan Mahaifinsa wato Aliyu shine aka boye sunan ake kiransa da Affan, su biyu Suka taso a hannun mamansu a Zamfara duk da cewar babansu bai mutu ya bar wata kadara ba face wata gona layi biyu,bayan Yusuf da Affan sun gama secondary School babu kudin ci gaba da karatu,sai Mamansu ta siyar da gonakin nasu ta hada kudin kaf ta Kira Yusuf da Affan tace kunga kudin nan nasan bazai isheku kuyi karatu ba ku biyu Kuma ina so a cikinku wani yaje yayi degree a rayuwa ya kuke gani Kai Yusuf gadon ku ne idan Kuma kowa bazai iya barwa kowa ba to sai dai mu Kama sana'a da kudin,Yusuf ya kalli Affan yace gaskiya ni bazan iya barwa Affan kudina ba,Affan Kuwa Nan take yace Yaya Yusuf ni na hakura da karatun dama kaga nine karami na bar maka kudin gado na halak malak kaje kayi karatu idan ka samu aiki daga baya ka biya min ni nayi karatun daga baya ai ba'a girma da karatu,Yusuf yayi farin ciki sosai karshe aka Nemo admission lokacin baya wahala a ABU Zaria Yusuf ya shiga ya gama degree dinsa gashi Allah ya hadashi da Abokinsa Dan gidan me kudi ya ja shi cikin Harkar kasuwancinsu na siyar da gwala gwalai har aka zo ma ana tura Yusuf kasar waje yana siyo kayan, a hankali a hankali Yusuf ya Zama me kudin gaske ya kera katafaren gida a Kaduna gida na gani na fada,ko aikin gomnati ma bai nema ba,ya manta da halaccin da Affan ya Masa ya kasa tunawa ya sashi a university,karshe da yazo zamfara da galleliyar motarsa Wai yazo daukan Mamansu zai maida ta can Kaduna kusa da shi,Mama tace Yusuf Saura Affan Yana ta Zama ba karatu burina ka biyawa Affan shima yayi karatu ya shiga University yace to zaiyi cikin ikon Allah watan mamansu Uku kacal a gidan danta ta kamu da ciwon sugar farar daya ta rasu dake Affan shima Yana gidan Yusuf din tun asali Allah yayo shi da son
Gayu da tsafta ga iya daukan wanka dama Kuma gasu kyawawan gaske.

    Bayan mamansu ta rasu da watanni Yusuf ya fara wulakanta Affan kamar ba gidan dan Uwansa ba,karshe Affan har ya gaji ya fara sana'a haka Kawai sai ya saro irin Guava ya dinga siyarwa Yana samun kudinsa baya kula kayan Yayansa,ya koma sarar irin su safa da handkerchief yana bin titin kwalta a hannu Yana siyarwa,ya dawo ya koma koma siyar da su charger a gefen titi da Haka ya samu ya shiga University amma shi BUK ya samu a Kano ya dawo Kano Hostel a school ranar da ba school ya tafi siyar da kayansa a gefen hanya,har ya hadu da wani babban mutum yace yazo ya dinga zauna Masa a shago a kasuwar kofar wanbai Harkar Yan robobi,ya koma can Yana fama a Haka ya kammala degree ga Yayansa can kullum arzikinsa Kara gaba yake amma sisi baya bawa Affan bai ma San Ina yake rayuwa ba,Affan wata yarinya ya samu Yar talakawa Suka Fara soyayya Nabeela,Yana mugun kaunarta Kamar ransa a Kaduna take

   Mamanta tana da ciwon zuciya kullum Affan akan taimaka musu yake duk abinda ya samo a wajen Maman budurwarsa yake karewa wajen nema Mata lafiya,Neman kudi yake Yana samu amma Maman budurwa kullum a asibiti can yake Kai kudin,magunguna shine ke siya, Basu da abincin ci shi zai siya musu a Haka jarinsa ya tarwatse babu ko sisi,Watarana Affan yaje zance Sabo da Nabeela ya koma Kaduna,ta rako shi gefen titi kenan Suka hadu da Yayansa Yusuf zai wuce a mota ya tsaya,Affan yace Yaya Suka gaisa ya nuna Masa Nabeela yace  itace budurwata yace Nabeela ga yayana uwarmu Daya uban mu daya tace oh suka gaisa Yusuf sai kallonta yake gaba Daya Nabeela ta tafi da imaninsa,bayan Affan ya shiga Napep ya tafi sai ya dawo da motarsa ya Sha Gaban Nabeela yace ta shigo ya rage Mata hanya,Bata kawo komai ba ta shiga motarsa Suka tafi har gidansu har take fada Masa rashin lafiyar mamanta ya shiga gidan Suka gaisa tashi Daya ya basu dubu dari biyu,zuwa sati Yusuf ya koma gidan su Nabeela yace ta shirya zai fitar da mamanta kasar waje India nemo Mata lafiya Suka dinga murna
   Affan ma tuni Suka daina ta tasa idan yazo ma bata taba fada Masa Yayansa Yana zuwa ba ko dan kudi ya bata sai Taki karba tace Alhmdllh karka damu yanzu Allah ya hore mana, bata fada Masa zasu je India ba Kawai Yusuf ya musu visa da komai Suka je can ai Kuwa Maman ta warke ta samu lafiya Suka dawo garau da ita,Sabo da irin kudin da Yusuf ke kashe musu Yana cewa zai turo manya Suka ce ba matsala,ya turo da danginsa na zamfara Kuwa aka tsaida ranar aure, Affan Yana ta zuwa zance bai taba sani ba yaji dai Yayansa zaiyi aure,ranar data Kama daurin auren Nabeela da Yusuf sai Allah ya kawo Affan yazo zance da safe Dan lokacin ma a gidan wani Abokinsa yake zaune ai Kuwa ya iske abin mamaki Yayansa ya aure Masa budurwa har an daura aure ma ana ta hotuna,Nabeela ta fito Suka hada Ido da Affan ta fashe da kukan munafunci,Affan mutuwar tsaye yayi Kawai hawaye na tsiyaya a idanunsa tunda ya tabbatar Kawai ya juya ya bar gidan.

    Yusuf Yana ta Neman Affan yasan yayi laifi, Affan Kuwa yafi sati biyu Yana cutar so,Abokinsa sayyeed shine ke ta tausarsa har ya dan Fara hakuri ya Sha wahala ya rame sosai ya fita hayyacinsa Yana mugun kaunar Nabeela,lokacin Nabeela ma tuna abinda tayi na cin Amana ya hanata sukuni a gidan miji,Yusuf ya kasa Gane kanta dole ya Nemo Affan yazo har dakin Abokinsa ya samu Affan yace Affan sai dai fa kayi hakuri,na kashe kudi...Affan yace dakata Mallam ni kasan me na musu jarina kaf na karar bani da shi na iya taimakon su Kai Kuma kana da arziki idan kayi ma baka birge ba domin nasan da Kaine a halin da nake ciki na talauci baza ka iya sadaukar da arzikinka garesu ba,Indai akan macece kaje na hakura na bar maka har abada Kai jinina ne amma idan kayi da kyau ma ka sani idan ma baka Yi da kyau ba ka sani kanka Kuma Allah Yana kallonka,Suna haka Nabeela Katsam sai gata itama ta fito daga gidan auren nata tana cewa Dan Allah Affan ka yafe min,Affan ya kalleta yace bazan taba yafe Miki ba Nabeela kinfi Yusuf Laifi tunda da baki bashi kofa ba keda mamanki da Haka bata faru ba na tsaneki a rayuwata nayi nadamar saninki a rayuwata mayaudariya makaryaciya suna kallo ya hada kayansa ya dakko kudinsa da ya Dade Yana tarawa a asusu ya fice da akwatinsa,Yusuf ya rike hannun Affan yace ka tsaya na samo maka aikin gomnati,yace bana so ko karatun Kai ka saka Ni? Yace to ga jari Zan baka Affan yace bana so ya fisge hannunsa,yace Zan baka aiki a company na dake kano yace bazan taba zuwa aiki ba bani bukata,Yusuf yace jarin milliyoyi Zan baka Affan yace bani bukata,Yusuf yace kafi so kayi ta gayunka kana zaga gari ba sana'a? Yace ae ya fice abinsa ya tafi ya shiga motar Kano daga nan ya irga kudin asusunsa wajen dubu dari hudu ya tara asusun ya Dade tun yana secondary yake uban yawo da shi Yana jefa duk abinda ya samu,Yana zuwa shine ya Kama gidan haya gidan da Raudat ta Kama yace yanzu ya daina wahalar da kansa,duk yawan uban wankan da yake dauka yace ya fita Yana da appointment kasuwa yake zuwa ya zauna a shagon wannan mutumin Alhaji da yace ya dinga zamar Masa Yana biyansa Kuma ba laifi Yana samu sai dai abinda ba naka ba Sam baya isarsa komai sai dai Yana kashe Yan bukatunsa kanana,ranar da baya zuwa kasuwa Kuma Friday,Saturday,Sunday to sai yawo wurin Yan abokan arziki,gashi ya Kama gida me tsada Kuma Kaya me tsada yake sawa yanzu yace ya girma ya gaji da Shan wahalar rayuwa dole sai yaji Dadi,shine data kure Rannan ya rasa ta ya zai biya kudin haya yaje company na Yusuf Yayansa yayi awon gaba da wajen dubu dari biyar ya kirashi ya dinga masifa Wai ya bashi ayyuka da jari duk yaki Yi shine zai ebar Masa kudi bai San dole ce ta sa ba badan dole ba Affan baya bukatar abin hannun Yusuf

    Raudat bata San ta Sha aiki haka ba sai da safe bayan ta shirya tana karyawa ta tuna da irin aikin da ta Sha jiya sai take ganin kamar a f
Mafarki,fita tayi bata sake kula Affan ba bare suyi fada ta tsorata da lamarinsa,taga lallai da gaske ya daura dambar fada da ita,bata San shi Affan ya tsani Mata ba tun daga Kan Nabeela abinda ta Masa,shima Affan bai San Raudat ta dawo daga rakiyar maza ba tace ita da aure har abada haka soyayya ma baza ta sake ba.

  A hanya Suka hadu da Affan ya dau wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai ya Sha kyau dukkan matan dake Compound din basa iya dauke Ido da kallon Affan Dan gayu haka,ta fito zata Shiga motarta Saura kadan suyi karo da juna tace Sannu Ina kwana,Kallon up and down ya Mata ba karya ta zuba kyau ta Sha wata Arabian gown me shegen kyau da tsada kamar Yar India kyakyawa da ita dagwas,Baki ya tabe yace Ina da appointment karki bata min lokaci da gaisuwarki in Banda gulma yaushe Kika Fara gaishe ni a gidan nan,Raudat ta tsaya tana kallonsa ya Mata kyau,yace banyi Niyyar aure yanzu ba fa ko kin kalleni a banza duk wata mace tayi hakuri Affan  ba yanzu ba na Mai rabo ne,Allura ce a ruwa me rabo ka dauka,Dariya ya bawa Raudat ya kalleta yace no..no.no fari da kwarkwasa basa Jan hankalina ki Adana abinki ga sugar Daddy dinki,Dariya ta sake saki yace baki da aikin yi ya juya ya tafi Yana wani taku cike da takama irin mazaje,Raudat ce ta fito da motarta daga gidan Yana tafiya a gefen titi har wani tattalewa yake Yi tsabar gayu Yana basarwa wani lokacin Kuma asa Hannu a hantsar Jean din a tattaro Cuccumber yanda gayu ke yin wannan iskancin a titi,Raudat a hankali take binsa a baya da motarta tana kyalkyala dariya tana kallon gayu,Masallaci taga ya shiga ashe Sadaka ya saka ta dari biyar a cikin asusun masallaci ya fito ya Kara gaba tana ta binsa har ya shiga Napep tana bin Napep din Yana kallonta ya gane motarta,cumb ya zaro ya shiga taje Suma kamar me,Dan karamin turare ya dakko a aljihunsa ya fesawa sumar zuwa sajensa Raudat tana saitin Napep din,Lekawa yayi da Kansa yace uwarka ya zageta yana turo mata pink lips dinsa gaba,Dariya ta sake yi ta daki sitiyari Yan dubu dubu na dubu uku ta dago Masa ta glass da hannu yace ta Miko su Ina son su,Raudat glass ta sauke kasa tana kallon titi tana Miko Masa kudin ta napep din kowa na kallo a titi ga Wanda ya kula Affan yasa hannu har cikin motar Yana cikin Napep zai karba Me Napep ya taka da gudu,Yace dalla slow down yayata ce zata bani wasu canji Zan siyo Mata kifi,Me Napep yace sorry Malam yayi Slow Raudat ta sake mikowa tana tuki da hannu daya wuf taji Affan ya karbe kudin kamar zai fado daga Napep din Saura kadan Allah ya kiyaye,motarta ta take da gudu tayi youturn ta wuce Office abinta,Shima ya tafi uzurinsa.

   Aslam Yana zuwa Office din yace sai jibi zaizo ayi magana yau baida lokaci babarsa ce ta dawo daga kasar waje tana airport zaije ya dakkota Suka ce ba damuwa,Nusaiba ta dinga Jin haushi ita ta matsu ya bata takardarta,Mum ce tazo ya sameta a airport,tana ganin danta a taxi ta Fara hawaye,karasawa yayi ya shiga share Mata hawaye ta rungumeshi tana kuka tace haka Allah yaso Dana, yace Mum me yasa kika zo ban sani ba nace sai na samu aiki zance kizo,Hankalina ya kasa kwanciya sai naga dana,kana ganin Mum kasan itace ta haife shi Fara ce tas shi Kam har ya fita fari ma,da sauri ya siya Mata lemo da ruwan roba Suka shiga taxi zuwa gidan hayarsa,Mum ganin gidan shima sai da tayi kuka,suna shiga ciki Nusaiba ta dawo tana zaune tana kallo,Sallama sukayi ta amsa da kyar ko kallon Mum bata Yi ba,Mum tace yata baki ganni bane ko ba Nusaiba bace nasan ai kin Sanni tunda kafin ayi auren nazo ganinku,Nusaiba baki ta tabe tana Mata kallon banza tace Ina yini daga haka bata sake magana ba,Aslam ne yace Mum zauna ya Kai Jakarta bedroom dinsa,yaje kitchen da Kansa ba abinci ba a dafa ba gashi yaji tana cewa yunwa take ji,Fitowa yayi yace Nusaiba dan dafawa Mum wani abu,direct tace na gaji,da sauri Mum ta kalleta tace ke Wai ko baki da tarbiyya ne? Ae sai kizo ki koya min,Aslam ne yaje ya kwashe ta da Mari uwar tawa zaki fadawa haka ya fisgo wayar charger,Mum ce ta rike shi tace kayiwa Allah ka kyaleta Ina da Yan Uwa Ina da gidan Zama wajen dangina karka damu Indai nice,kaga dakko min jakata muje can,Mum hawaye ne ya zubo Mata tace tabbas Aslam Allah ya jarabceka,Siyama ce ta shigo da sallama,Aslam yaji wani sanyi da farin ciki da ya dade bai ji ba yau yafi murna da zuwan Siyama,Tana zuwa ta Gane Mum ta taba ganinta sau daya da bikin Aslam da Nusaiba,Durkusawa tayi ta gaishe ta,Mum ta amsa da fara'a,Aslam yace kawar Nusaiba ce nasan baza ki gane ta ba,Mum tace Masha Allah ziyara Kika kawo? Siyama tace ae,ya sunanki? Siyama cewar Charity,Yaushe ta zo ne ta tambayi Aslam yace yanzu fa Kinga Ina cewa ta tsaya ma ayi Mata girki taci Wai zata tafi gidan Yan uwanta Mum guda tayi Fushi da gidan danta,Dariya Siyama tayi tace ai kuwa girkina Mummy zata Fara ci a kasar nan ta shiga kitchen da sauri,Mum ta kalli Aslam tace ya haka Kuma kawarta ce da shiga kitchen haka? Nusaiba mikewa tayi fuuu ta Shige bedroom,Aslam ya zauna Yana bawa Mum labarin Siyama da komai ma bai boye Mata ba da irin abinda Nusaiba ke Masa da Neman saki da Nusaiba ke yi,Mum tace mu gama gobe Zan je gidan su Nusaiban da kaina karka damu

     Siyama ce ta leko tace me Zan dafa mata tana tambayar Aslam da Ido a hankali yace tuwo tafi sonsa,ai da sauri ta sake fitowa ta yafito Aslam da hannu yazo kuwa da sauri ta lissafa Masa abinda babu ya fita bai Dade ba ya kawo Mata tayi tuwon shinkafa miyar taushe,Mum ta dinga godiya tace kin samu ladana yarinya kinji yunwa ta gama dani, Mum ta baje tuwo a plate da Miya tana ci suna Hira da danta shima a kwanon Mum din yasa Spoon suna ci tare,Siyama ta zubo itama tana ci,Mum tace yata miyar tayi dadi kin iya girki,Siyama tace ai Dan Ina sauri ne shi yasa Amma da sai tafi haka Dadi,Mum tace Allah? tace ai yanda na iya girki ko a gidan sarkin garin nan sai haka,Nifa na Gama kwarewa hannuna ya fada,Mum da Aslam suna ta dariya Siyama tana yabon kanta,tace sai ma na yanka Miki salat inda kisan Amarya kin San Mum yankan Amarya ma na daban ne tace kwarai kuwa Siyama,Aslam yace ki bari dai a fada amma kina ta yabon kanki mu baza mu yaba ba.


Masu sharhi Ina godiya
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

        
           36-40

Official

By
AsmaBaffa
Page naku ne
FUTURE RM
RAHMATU ALIYU KUNDE
BK

          Siyama Shuru tayi tana jira a yabe ta tunda Aslam yace idan tana yabon kanta su baza su Yaba ba,Sai da Suka gama cin abincinsu Suka koshi sannan Mum tace itafa baza ta zauna a gidan ba dole Suka fito gaba daya har Aslam da Kansa ya Kai Mum gidan Hajiya Zainab Yar uwarta ,Siyama tuni tayi gidansu itama ta samu Kawu Dauda ya dawo ya kalleta yace Siyama Ina mamakinki yanzu yanda kike saka kayanki Wanda duk mace ke sakawa harda hijab sakawa kike Wai lafiya? Dariya tayi tace Kawu ba komai girma ne yasa na canja gaba daya, Amma wannan girman naki ya kyauta kin tashi daga Charity gaki kullum a mutunce kike fita dama Ina bakin cikin kayan nan naki da Kika nacewa gasu su ba masu kyau ba Alhmdllh da Allah ya shirya min ke, Siyama tace Ina aure zanyi reverse wlh sai dai idan baza kuzo gidana ba amma kayan da Zan dinga sakawa Ko Kai Abbu sai kayi Allah wadai da su,Kawu yace a'uzubillah Allah ya tsare uba da ganin yarsa a haka mijinki kadai Zaki sawa ai,Siyama tace to Ni ba Mai hanani sakewa a gidana Wanda baya son gani Kar ya zo,Aunty tana girki tana jinsu tace ke ki bar zubar nan kizo kiyi sauri ki min talge tafiya tayi ta kamawa Aunty girkin

   Allah dai ya kawo Miki mijinki kema na gari cewar Aunty tana kallon Siyama wacce ta furta ameen anko wanne kala zamu fitar,Aunty tace yau naga duniya ba mijin ma amma kina zancen anko wacce kala Siyama me yasa baki da kunya ne? Talla ne yasa da baki daura min talla ba ai da idona bai bude ba,Aunty tace talauci ne yasa Watarana kina ganin Kamar Ina takura Miki sabo da baki da iyaye ba haka bane Watarana yanayi shi yasa ake dorawa yaro talla ba kowa bane yake tura dansa talla ba sabo da son abin duniya wasu dole ce ta sa hakan,sannan yanzu ba gashi ba da Kawunki ya samu jari a hannun Aslam mun samu ci gaba yaushe rabon da ace mun yini bamu ci ba,tallan ma gashi an daina sai dai a siya a gida,Gidan Nusaiba da mukace kije kiyi aiki har ga Allah mun zaci da zuciya daya ta daukeki ba wani aiki zaki ba duk da bai dace bama kamarki kije gidan kawa aiki kina budurwa haka Kuma gidan kawarki munyi son zuciya a nan kiyi Hakuri,Siyama tace ba komai Aunty ai nasan bakwa zaluntata takura min da kukeyi da aiki da zuwa makaranta nasan gata ne dan na koya ne ni Kuma a lokacin Banda hankali sai Naga kamar Dan bani da iyaye ake min haka,dama wasu da yawa yaran ruko ba zaluntarsu akeyi ba sune suke ganin kamar Dan an sasu abu Kawai ai basu da iyaye ne yasa cewar Aunty Suna ta hirarsu dai.

   Aslam sai dare ya koma gida ya bar Mum a gidan Hajiya Zainab Yar uwarsu Yan maza zar suke da Mum,Nusaiba ya samu ta kamo channel din disco ta kure volume kida har waje tana bi da baki ga malti narta a gefe,Sallama yayi bata ji ba ya dauki remote ya rage Volume, dagowa tayi da sauri Suka hada Ido tace mene haka hutawar ma baza ka bari na huta ba Ni bana son irin wannan mutum baida ko sisi da zai iya daukan nauyina sai takura ta dauki Remote ta Karo karar kidanta,Idonsa kyawawa ya lumshe window ta bude  tace gida ko ac babu mutum zafi Kamar zai kashe shi anzo an kawo mutum gida kamar kejin  kaji,Aslam Yana zaune Yana jinta,wakar data ke kallo shima yake kallo ganin Yana kallo ma'ana ta birgeshi sai ta kashe tv din gaba daya Wai bazai kalla ba,bai kulata taci gaba da cewa kullum da safe ko dankalin turawa babu tunda nazo mayen gidan nan ba a bani ba,Haka doya ma da Dan kwai duk babu da safe sai dai na karya da shayi da Kosai,Aslam a nan yayi magana yace da shi Kika Saba ai kosai sana'arki ce ke baki ji kunya ba Wai? Dan Allah bakya Jin kunyar maganganun da kike fada bana so na Miki gori baza kiji dadi ba matar da ko kanzo Watarana Babu da za aci amma kina da bakin magana,Yunwa ce ta fado daku gidana har na sanki wannan kaddarar ta aurenki ta fada min,Nusaiba tace ai Babanmu Yana da kudin bamu ne bayayi sabo da haka ba talauci yasa ba,dariya yayi yace kinji kunya wlh Wai kina Maganar ac no ba ac ba kankara za a kawo Miki kalli jikina kalli naki waye yafi Kalar hutu,Kaga Malam saurara karka ci min mutunci nace ka sakeni dole ne auren,Aslam yace ihun banza kike yi ya tashi ya shige bedroom.

  Zuwa dare sha'awa ta Kama Nusaiba tana so Aslam yazo rokon ta bashi hakkinsa idan tayi Masa yanga sai ta yarda tunda tana so yau ai Kuwa ko kulata baiyi ba,bata kwana a Palo ba Yana jinta ta kwanta a bayansa tare da rungumeshi jikinsa ya janye,ta sake rungume shi tana goga Masa kirjinta a bayansa Cucumber ta mike sosai Nusaiba tace ka bani hakkina Malam yau wata biyu kenan baka Yi min komai ba,Aslam yace bazan iya ba ni da bani da lafiya Hannu tasa tare da taba Cucumber dinsa tace gata nan ta mike wlh ka bani hakkina,yace wlh baki Isa ba karewar mikewa ta tashi sama bazan Yi Miki komai ba,Nusaiba tace Allah Yana gani bazan yafe ba ta fashe da kuka dan Kawai ta hanashi bacci taci gaba da uban kuka a zaune a Kan gadon tashi yayi da pillow daya ya koma Palo saman kujera a can ya kwanta ta biyoshi tana tattaba hannunsa tana kuka tace wlh yau babu bacci a gidan nan haka Suka kwana baiyi bacci ba itama bata Yi ba Kuma bai Mata abinda take so ba tunda shima wulakanta shi take yi a Kai tun Yana nema har ya hakura.

   Washe gari Mum ce ta shirya da Yamma zuwa gidan su Nusaiba,Mama ce kadai a gidan duk yaran suna makaranta Ameer Yana shago,Mama ta gane Mum sai ta bata rai ta hade rai ko tabarma Mum ce ta gaji da tsaiwa ta jawo kujera ta zauna tace Ina yini, gatsine Mama tayi sannan ta amsa da lafiya bata sake magana ba,Mum tace nasan kin ganeni zuwa nayi akan Maganar Nusaiba abinda takeyi bai dace ba a matsayinki na uwa....dakata cewar Mama ta daga hannu sama tace Kinga nifa bance danki ya zauna da yata dole ba a sakar min yarinya dole ne mun gaji da talaucinsa makaryacin banza yazo da mota ya Mana fafa da kudi ashe karya ne a saketa idan an gaji Zaki Zo kina Mana ihu a gida,Mum Ido ta zaro tace abin har ya Kai haka? Ya wuce haka ma ehe sabo da Haka Kar na Kara jin kin ce ma ke surukata ce,Mum ta mike tace Allah ya kyauta ubangiji ya ganar daku,ameen sai me Kuma cewar Mama,Mum tace babu fita tayi daga gidan Suka hadu da Shehu yace ahhh Kece a gidan ya akayi baki jira na dawo ba? Sannu da zuwa yaushe Kika dawo? Mum tace hmm jiya naji abubuwa marasa dadi har Nusaiba ta Kai karar Aslam Office din Yan hisba Wai ya saketa shine nazo sasanci Amma Maman Yarinyar nan ta bani mamaki taci min mutunci,Shehu ya dinga bawa Mum hakuri yace wlh abinda nake fuskanta Nima kenan,sabo da mamansu nayi kuskuren Hana yarana abinci,Mum tace ashsha bai kamata ba Shehu ko me zata Yi ka dinga ciyar da yaranka,yace Inshaallah ai na Fara gyarawa yanzu Kam Ina Basu abinci amma fa kullum sai dai na auno sabo da idan na zube kayan abinci siyarwa takeyi duk da bai kamata na fada Miki ba amma Abu ne Wanda muke fuskanta Ni da danki ya kamata kisan Nima ta gagareni wlh ban Isa da ita da Nusaiba ba sauran yarana dai na Isa da su amma Banda Mama da Nusaiba kuyi hakuri yaushe za aje Office din Yan Hisban? Mama tace kayi bangarenka Kawai basa ji ne karka damu mun San Kai mutumin kirki ne wlh amma gobe Inshaallah Dana zai saki Nusaiba kowa ya huta,Shehu yace ba damuwa bazan ga laifinku ba,a nan Suka Yi sallama da Mum shi Kuma ya Shiga gida ya budewa Mama wutar masifa amma ko a jikinta tace a saki yata a huta da ya saketa zai sake ganinmu ne,Shehu yace Matukar aka saki Nusaiba to kema kin daina Jin Dadi a gidan nan,dalla rufe min baki me zaka iya, yace ana sakin Nusaiba kema wlh sai naci mutuncinki,Mama tace wlh ba inda zaka Yi Dani ko sakina kayi Ina nan gidan yarana nane sai nayi zaman Yaya na.
   Yau Nusaiba da bala'inta ta dora tana cewa Allah ya Isa idan baka sakeni ba,Azzalumi ka kawo ni gidan wahala gidan talauci macuci tana ta zage zage.

   Washe gari ranar da za a koma Wajen Yan Hisba Nusaiba ta riga kowa zuwa har da saka katon Hijab,Abbanta ta gani yazo Shehu sai Mama itama tazo,Mum tazo tare da Aslam,ana zuwa shugaban hisba yayi magana yace Nusaiba Kin nemi saki Kuma kin Fadi dalilinki mijinki bai da lafiya baya iya biya Miki bukatunki bashi da lafiya Nusaiba tace kwarai kuwa,Yace kin shirya biyansa kudin da ya kashe kafin aurenki har sadaki? Ko kin shirya Yi Masa wani auren? Nusaiba tace na shirya biyansa abinda ya kashe,Shehu yace kinyi asara Nusaiba yaushe Kika Zama haka,Aslam yayi murmushi Kawai,Dan hisba yace Aslam me kace kai? Yace ba damuwa taje na saketa Saki daya,Takarda ya rubuta ta saki ya mikawa Nusaiba ta karba harda saka Hannu biyu tace na gode Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biya bukata na gode na gode wayyo Allah dadi kashe ni, ta kalli Mama tace Mama Kinga takardarta ki tayani murna yau an sallameni freedom ya samu,Mama ta karbi takardar sakin tana cewa kawo na sa Mata Albarka 'yata,Kowa kallonsu yake da mamaki a wajen,Shehu yace mahaukatan banza.

    Aslam ya kalleta Kawai ransa a bace bayan an gama Shehu yace akwai shagon da Aslam ya budewa Uwar Yarinyar nan Nusaiba sabo da Haka a maida Masa da shagonsa,Yan hisba suka ce wannan kyauta yayi sai idan da Kansa yace a biya shi,ai kuwa Aslam yace a biya ni,Mama ta bude baki tace dama taimakonka badan Allah kayi ba Dan iskan yaro mutumin banza matsiyaci,Aslam bai saurari Mama ba yace hukuma ta sheda na barwa Shehu Baban Nusaiba shagon gida Kuma dama shi na gyarawa ba ku ba,Shehu yace bani mukullin shago ya Zama nawa,Mama tace akan shagon banza kaje can danka ne a ciki ka karbi shago kayi arziki da shi,Shehu yace ae naji,Aslam yace Ina bukatar sadaki na,Nusaiba nan take tace kawo account a maka transfer, Ya kalli Shehu yace Abba bata accnt dinka Shehu ya karanta nan take Nusaiba ta tura kudin Sadakin dubu dari,Aslam yace Suma kudin na bar maka Abba,Shehu yace Saura lefenka Aslam yace ai sutura ce tazo ta kwashe kayanta na bar mata,Mama tace to mun rabu karka sake na ganka a gidanmu,Aslam yace dole nazo gaida Abba Watarana,Shehu yace kwarai kuwa zamu ci gaba da zumuncin mu

   Mum tace to Alhmdllh Muje Aslam aka kashe magana kowa ya Kama gabansa,Suna Fitowa Nusaiba ta Kira Sufyan tace an sake ni fa,Sufyan yace Alhmdllh Mama tace kashe wayar sai kinyi Idda yazo ta kashe kuwa Nusaiba sai gida suna murna da shewa Kamar Wanda aka musu gafara
   Suna zuwa unguwar su ta Fara zuwa gidan su Charity duk gidan ba kowa sai Charity a gida tana zaune tana Jin radio sai ga Nusaiba tayi sallama amsawa tayi

   Nusaiba ta bude jaka tare da dakko takardar sakinta ta mikawa Siyama tace kin gani na gama da shi idan kina sonsa kije ayi dake ni nan da kike gani na gama da shafinsa, Charity ta karanta tace Yanzu ke a tunaninki farincinki kenan? Nusaiba tace yes Yana da kyau ya cika Namiji amma baida kudi bashi da magana,takardar ta karbe tare da maida ta jaka tace gobe Zan ebo kayan sawata sabo da haka idan kina ciki kije ayi dake ni bani bukata ta juya ta fice,Siyama tayi Shuru tana tausayin Aslam Kamar taje gidan ta duba shi sai kuma ta fasa Sabo da shi kadai ne yanzu bai da Mata ko taje ma baza ta shiga cikin gidansa ba.

    Bangaren Aslam kuwa Mum ya maida masukinta ya koma gidansa ya kwanta saman kujera shi kadai a gidan Kamar maye shi Kam yaga wulakancin mace ya zauna Yana tunani shi kadai Kamar maraya abin tausayi tashi yayi Kawai ya tafi gidan su Sabeer Abokinsa sabo da ya rage kadaici ,Babar Sabeer tace Aslam mutumin naka Yana bangarensa Dake su Sabeer masu rufin asiri ne Baban Sabeer Doctor ne,Sabeer Yana aiki shima a bangaren ministry of Finance Yana da motarsa me kyau baiyi aure ba amma Yana da budurwarsa Na'ima gaf suke da aure,Aslam Yana zuwa ya bawa Sabeer labarin saki,Sabeer yace Alhmdllh Kai Kam ai ka samu hutu dama Siyama ka aure,Aslam yace kawarta ce fa ni bayan nan ma yanzu ban shirya aure ba sai na huta,Sabeer yace hutun me Kuma yanzu ka Saba da mace gwara ka Fara Shirin aure dan Watarana zaka ji Kawai dumin jikin mace kake bukata,Sabeer yace rabu dani Kai na gaji,Nabeela ce ta shigo dakin Sabeer tare da ajiye musu abinci da lemo,Nabeela ta Kaduna tsohuwar budurwar Affan mamanta yayar Maman Sabeer ce ubansu daya,Nabeela watanta biyar a gidan mijinta Yusuf yayan Affan ya saketa.
  Tana fita yace ko na hadaka da Nabeela Yar uwar mu ce bazawara sakin wawa ce kwana nan tayi barin Yan biyu bayan mijinta ya saketa cikin ya zube da zaka aureta ma,Aslam yace hmm amma Sabeer ya dage Yana ta faman yabon halayen Nabeela Yana so lallai sai ya hada aure tsakanin Aslam da Yar uwarsu Nabeela,yace har Babarta suna nan gidan mu sun dawo nan da Zama gaba daya sabo da can Kaduna su kadai ne a gidan,Yarinyar nan ta Sha wahala a hannun tsohon mijinta,Sabeer bai San hakkin Affan ne ke bibiyar Nabeela ba,Aslam dai Yana Jin Sabeer.

    Yau Raudat Fitowa tayi zata siyo abu Affan ya fito da 3qtr da riga Armless ya ganta Murmushi ta Masa yace Hajiya Aunty Ina kwana,yau nice Hajiya Kuma Aunty a'a Kaine Yayana,Affan yace baza ta sabu ba bindiga a ruwa dole kece Aunty kuma Hajiya,yace Zaki iya sawa a toshe window din dana hada mana ke macece bai dace ba Kuma ba muharramata ba,Raudat tace a barshi Kawai Zan saka labile yau yace hakan ma yayi yanda kike so,tace Ina zaka je ne Haka ko Appointment ne? Murmushinsa me zauta Yan Mata ya saki yace ai banyi Shirin fita ba kalleni fa a haka Zan fita shago Zan je na siyo kayan tea nawa sun kare,Raudat tace nima can zani yace aha yayi gaba abinsa yana tafiyar gayu,Raudat daga baya ta karasa tana Shiga ciki ta dinga jido manya manyan Madara na gongoni kayan shayi na kirki komai ta hada ta Mika ATM card dinta aka zare kudin ta mikawa Affan katuwar ledar kayan tace gashi ka huta siye,ya kalleta ya kalli kayan yace Allah sarki Ashe mutuniyar kirki ce ke ban sani ba ta gari ce ga kamun Kai ba ruwanki da kowa da wata ce da yanzu mun gaji da ganin samari iri iri,Raudat tayi Murmushi kawai,ya karbi ledar yace gaki da kunya Kuwa Allah ya Miki Albarka ya karbe Kaya ya Kara gaba abinsa.
   Liman ne ya samu Affan yau bayan Sallar asuba yace yaya budurwar taka Kuwa na jika Shuru? Affan yace naje ta wulakantani bani da kudi Wai, Liman yace da zaka yarda da na baka manager a gidan Mai na dana gama ginawa kwana nan,Affan yace me zai hana na karba manager fa na gode ubangiji ya Kara girma,Kamar Wasa sai ga Liman a cikin gidajen mansa ya bawa Affan manager a guda daya,Wanda Affan me zamarwa a shago ya sanarwa suka Yi sallama ya taya Affan murna Affan ya koma Zama a office dinsa Dake cikin gidan mai ai tunda ya fara Kama kudi wanka ya ninka na baya amma Liman Yana ganin gaskiya Yana ganin aiki da ci gaba a harkar,farin ciki yasa liman ya siyawa Affan Mota dalleliya ta matasa,Affan ya Karo wulakanci,ba ruwansa da Raudat yanzu sun daina fada baya shiga safgarta itama Haka sannan window dinsu ma ta saka labile,Affan Kara rike aikinsa yayi Hannu bibiyu sun Zama kamar Da da uba tsakaninsa da liman sanadin zuwa masallaci

    Bayan kwanaki Raudat kullum bata da aiki sai tunanin Affan da shi take kwana da shi take tashi tun tana jurewa har ta kasa ta window take zuwa ta dan bude labilenta tayi ta leken Affan tana kallonsa tana Jin dadi a ranta.
  Taji Sanda ya shigo da motarsa da sauri ta bude labilen window dinta kadan ta leka cikin palon Affan akan idonta ya shigo sanye cikin shadda Yar gaske laptop ce a hannunsa sai ledar take away na abinci a Palo ya ajiye ya nufi bedroom ai Raudat da gudu ta fada bedroom dinta ta window din ciki ta sake lekawa tana kallonsa tace na Shiga Uku meke damuna haka mutum bai damu Dani ba amma na damu da shi haka fa nayi akan Hussain na Kare a wahala,jikin window din ta bari ganin Yana kokarin cire kayan jikinsa
  Bayan wasu satikai Liman ya Kira Affan zuwa gidansa,Affan yaje aka Masa iso palon baki ya shiga Suka gaisa da Liman,Liman yace Affan na yaba da hankalinka da irin rike Amanarka tabbas na yaba akwai wata Alfarma da Zan nema a wajenka fatan zaka min, Affan yace Inshaallah bazai gagara ba,yace Ina da babban aboki Yana da yarinya budurwa ce amma nutsatsiya ce ta dace da kai idan ba damuwa Ina so na hadaku aure,Affan yaji ba dadi bai zaci haka ba shi Kam baya son auren wata mace ko wace amma idan ya duba abinda liman ya Masa bazai iya kin tayinsa ba haka baya so yace na amince Mallam ai Kamar mahaifine a wajena nasan baza ka min zaben tumun dare ba, Liman ya washe baki yace na gode da ka daukeni a matsayin uba mahaifi ubangiji yaji Kan iyayenku,Affan yace a Ina matar da Zan aura take? Liman yace a nan kano take Babanta ya Dade da rasuwa a hannun yayan Babanta take,Affan yace ka bani address sai na Fara zuwa zance,Liman ya fara karantawa Affan gidan su Siyama, gumi ne ya Fara ketowa Affan yace Mallam ya sunanta? Yace Siyama,Affan gumi yake gashi ya amsa bazai iya yiwa liman Musu ba har ga Allah shi sunan ma Siyama yayi Masa local a harkarsa ta gayu, jikinsa a sanyaye ya basar yace shike nan zanje abinda mukayi da ita zan dawo na sanar maka,Liman yace Alhmdllh ka taimaki marainiyar Allah tausayi suke bani Babanta  abokina ne amini,Affan dai ya tafi gida jiki ba kwari.

  Raudat yau tana compound ita da Landlady suna Hira Affan ya shigo da motarsa a fusace yayi parking ya fito cikin bacin rai ya shiga part dinsa yana huci,Raudat ta tsura Masa Ido har ya kule, Landlady tace yau Baban wanka meke damunsa haka Kinga yanda yake fushi,Ni abin mamaki ma a Ina yake samun kudi yanzu Kamar fa yanzu yana zuwa wajen aiki duk da ba abinda ya iya sai karya amma a Ina yake samo kudin Kar dai ko barawo ne? Raudat ta bata rai tace Allah ya tsare min shi da Zama barawo Kuma Yana zuwa aikinsa babban aiki ma ki daina fatar Masa masifa ehe ta mike ta Shige part dinta da sauri tana yiwa landlady masifa,Landlady ta bude baki tace me nake gani haka mutanen da kullum basu da aiki sai fada amma yanzu sun daina Raudat ma wani Kare shi takeyi ita da take zaginsa tana gulmarsa yau taki yarda a aibata Affan harda Jin haushina uhm to meke faruwa tsakaninsu oho.

     Aisha bayan tayi idda tayi sabon bazawari Bashir,Bashir Yana da rufin asiri domin lecturer ne yana da Mata daya da yaransa biyu,Bashir Maganar aure tana kankama ya tura manya ba bata lokaci aka sa ranar aure da wuri Maman Aisha ta dage sai da aka daura auren Aisha da Bashir sabo da ta isheta a gidan sai da tayi nadamar zuga Aisha ta dawo gabanta sabo da rashin kunyar da Aisha ke mata,Bashir ya Kama gidansa me dan kyau na Amarya sati na zagayowa aka yiwa Amarya Aisha jere Yan Uwa da kawayenta suka rakata dakin mijinta cikin motoci uku da ango Bashir ya turo.
   Ango ya shigo Suka ci Suka Sha tare da gabatar da Nafila sannan ya Fara soyewa da Aisha,ranar Aisha taji wahala mugun Hariji ne na gaske Ita Farooq ba haka yake Mata ba abinsu dai dai da dai dai,gashi Bashir baya Wasa da jikinta wajen jiyar da ita Dadi Sabanin Farooq da yake zama yayi Wasa da ita sosai Kuma yanda yaji Dadi haka yake Mata itama sai taji dadi ta gamsu ya iya sarrafata sosai sabanin Bashir da Kawai Kansa shi Yana Jin dadi shi ba ruwansa mace ko ta gamsu ko bata gamsu ba shi ba ruwansa,Ranar kwana yayi Yana gurzar Aisha har sai data dawo tana tureshi tana cewa zafi dan Allah ka bari sai da ya Mata rauni ya hakura.
   Washe gari da safe ya Dora daga inda ya tsaya har sai da Aisha ta koma kuka kawai tana rokonsa ya kyaleta gashi da kekasashe sai jaraba

    Bayan sati daya Aslam bai je gidan su Siyama ba itama bata duba shi ba,ji yayi bai kyauta ba yace yau da Yamma zaije ya gaida Siyama,Siyama kasa Zama tayi bata ji Aslam ba ko bai da lafiya bata sani ba,ana gama abinci tayi wanka tare da shiryawa cikin atamfa sabuwa karama riga da skert ta yafa mayafi tayi kyau matuka ta zuba shinkafa da miyar da ta dafa ta zuba salat a Daya robar ta shirya komai a ledarta ta fito ta tsaya ta siyi kifi soyayye manya me zafi na dubu daya ta saka a ledar ta shiga Napep sai gidan Aslam,shi Kuma yayi wanka sosai ya Sha kana Nan kaya ya zuba kyau abinka ga me kyau da aji ya bude kofa da Niyyar zuwa gidan su Siyama sai ya ganta tana Shirin biyan me Napep kudi,Me Napep ta tsayar tace to gashi ma na ganshi karka tafi tsaya ka maidani gida,Aslam ne yace me Napep jeka Zan maidata,Siyama tace bafa shiga gidanka zanyi ba yanzu baka da Mata bazan shiga gidan Gwauro ba,Murmushi Aslam yayi yace me Napep jeka Kawai don't mind her, Me Napep yayi gaba abinsa,Siyama ta tsaya a gaban Aslam ya kalleta yace kina Jin dadi Siyama irin wannan wanka haka,dariya tayi ba shiri tare da Mika Masa ledar abincin tace tafiya zanyi ni,yace Kinga nan wajen duk student ne ki saki jikinki ga waje can mu zauna to a waje,Kan wani tudun siminti me Fadi Suka zauna ya bude ledar ya dakko abincinsa a wajen ya fara ci ya saka kifinsa soyayye Yana ci yace kamar kin San yunwa nake ji,Siyama ta kalle shi tace karka yabi yanda na iya girki ni bana so ma yanzu, Wai dan ya yabeta taji bai yaba ba shi yasa ta Fara Masa hannunka me Sanda,Dariya Aslam ya fara sosai,tace ae Kar dai ka yabeni nace, fuskarta yake kallo yasa hannu a hancinta ya cire Mata wani dan zare baki da ya makale mata,sai da ya cinye abincin tas tana kallo sannan ya Shiga gidansa ya Sha ruwa ya fito ya sameta yace tashi muje yawo,Siyama ta mike Suka jera suna tafiya suna Shan iskar gari suna tafiya Kamar saurayi da budurwa,Siyama tace kawata dai ta matsa an saketa, Aslam yace tayiwa kanta ta rasa saurayi me tashe,Siyama ta kyalkyale da dariya har da durkusawa tana dukawa kasa tana dariya,Aslam yace get up sarkin dariya ya riko hannunta tare da janta sama ta mike tana kwace hannunta,sai Yamma likis Siyama tace zata tafi Napep ya tare Mata ta shiga shima ya Shiga tace ya naga ka shigo Kuma?

   Yace gida Zan kaiki da kaina Suka tafi tare again Suna sauka a Napep Suka yi arba da Nusaiba da Mama sun dawo daga unguwa,Mama ta nuna Siyama da hannu tace ke butulu ashe kadan kike jira dama kaga maciya amana,Nusaiba Kuwa dariya ta hau shekawa tace Siyama kice da gaske kina ciki yanzu wannan gidan Zaki shiga hhhhhhh ta sake kecewa da dariya tace asha talauci lafiya karki ji kunya Ni Kam na bar miki wlh bana Yi,Siyama ce ta kalle su tace mahaukata Jahilai an fada Miki tsoronki zanji ko bai sakeki ba kina jin Zan kasa aurensa idan nayi niyya,Kuma wallahi da Sannu sai kunyi kuka Watarana,Aslam Yana jinsu yace Kinga let's go Siyama kina saurarar Wanda basu San me suke ba a duniya magana da su ai bata lokaci ne,Mama tace iyye wato Aslam yanzu na zama waccen ban San me nake ba ka manta Sanda kake zuwa kana roko a aura maka Nusaiba,Aslam hannun Siyama ya rike tare da janta Suka tafi,Mama tace yau Naga dan iskan karshen zamani Kinga harda rike hannunta wato mu gani Yana sonta,Nusaiba tace Mama ke Kika damu dashi ga sabon me kudi nan new Money Sufyan muje Kawai Suka tafi gida tare da Mama ko a jikinsu.
  Aslam kuwa Kuwa a kofar gidan su Siyama ya tsaya Suka ci gaba da hirar su cike da nishadi da farin ciki.

 

   
    Waye Aslam
  

AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

            41-45

Official

By
AsmaBaffa
Page naki ne

Fateemah Farouk
Ameerah Abdussalam
Hanana Smart        Aslam Shareef Alhassan cikakken Fulanin Mambila ne gaf da Cameron fulanine usil,babansa Shareef Alhassan me tarin arziki ne na shanu da kadarori sannan Kuma Yana da ilimin addini Dana zamani Alhaji ne sosai a Mambila,auren zumunci aka Masa da Yar uwarsa Zuwaira wato Maman Aslam Mum,sai da Aslam ya girma bayan an haife shi yana secondary Suka dawo Kano da Zama lokacin kasuwancin Shareef ya shahara ga siyasa Yana yi Katsam Allah ya Masa rasuwa sanadin hatsarin jirgin sama zuwa India,Bayan komai ya lafa Juwairiyya mum wacce suke cewa Zuwaira itace taci gaba da kasuwancin Kamar Namiji tana daukan nauyin danta Aslam yayi ilimi har ta kaishi kasar waje America karatu lokacin Mum arziki yaci gaba sosai ta bunkasa komai Dake Allah yayita da kwazo da fasaha Kuma itama tayi ilimi har matakin Diploma a hannun mijinta tayi Diploma sannan komai nasa Yana shawara da ita da taimakonta ake komai sabo da Haka Yana rasuwa ta Haye karagarsa taci gaba da juya Dukiyar Aslam Allah Kuma yasa shi kadai Suka Haifa dama dangin su Mum kusan basa haihuwa da yawa daga me haihuwa Daya sai me haihuwa biyu haka suke,tunda iyayensu Suka rasu gashi Basu da yawan dangi sosai tunda basa haihuwa da yawa wannan yasa zumuncin ma Sai lokaci lokaci suke zuwa can,Sai Kuma Yan Uwa Wanda suke aure a Kano ko Kaduna.

   Aslam a haka ya Zama saurayi kyakyawan Matashin hadadden gaske ga iya daukan wanka ga saka sutura duk inda ya wuce kamshi yake zubawa Kamar me,gashi da addini ga hakuri ga hankali gaba Daya iyayensa ya gado a kyakyawan hali ya samu tarbiya da ilimin boko Dana addini,Yana yin masters sannan Mum ta kyaleshi ta damka Masa dukiyarsa a hannunsa ya koma juya abinsa,Aslam sai da ya Zama hamshakin Mai mudi Kai da gani ba karya bai fuskanci wani Jarabta ba ba ko daya kullum a huce yake,Mum gaba daya sabo da Yana damunta da aiki ya Masa yawa sai ta gudu Qatar inda kanwar Babarta ke aure a can suke zaune abinsu ,duk haka Aslam sai Sanda yaga dama yake zuwa Office Sai wasu kamfanunuwan nasa da yake lekawa Yana kula da ma'aikata tsabar son hutunsa idan yaga dama Sai yayi sati biyu a iya samansa ba tare da ya sakko ko kasa ba,har Allah ya hada shi da su Nusaiba ya sota Kuma ya aure ta a Nan jarabtarsa take shi kam.

   Aslam fari tas kyakyawa ne ajin farko,dogo ne amma ba can ba haka ba ramamme ba baza Kuma ace me kiba ba,sumarsa baka wuluk ce me yawan gaske taji gyara style style yake Mata Kamar dan turai,hancinsa dogo ne ba can ba bakinsa karami me dauke da jajayen lips,idanuwansa matsagaita masu kyau,sannan fuskarsa ba me Fadi ba Kuma ba sirirya ba komai nasa chas dai dai kowacce mace ta ganshi sai ta kyasa.

        Siyama
Siyama Ahmad Sani Yan Niger ne asalinsu buzaye ne amma tun iyaye da kakanni a Kano Suka taso a Kano Suka gansu daga zuwa Neman kudi Suka dinga hayayyafa har Suka tara dangi a Nan Kano Kuma sun watsu gari daban daban wasu a kauyen Kano wasu a birni,Baban Siyama Ahmad Wanda suke cewa Amadou kanin Dauda ne kawun Siyama bayan Dauda yayi aure Allah bai bashi haihuwa ba gashi su biyu ne rak a wajen iyayensu,Dauda Yana ta aure aure amma ko wacce mace rashin haihuwa yasa take ficewa har ya gaji da aure ya hakura,shi kuwa Ahmad Yana aure shekara daya Matarsa Maryam ta Haifi yarta kyakyawar gaske fara,ai Maryam tana haihuwa abinka da zumunci irin na da Amadou ya kira yayansa yace yayi 'ya matata ta Haifi mace amma na bar maka ita halak malak sabo da haka Suna ma Kai zaka zaba Mata,Dauda harda kukan farin ciki yace na zabi Siyama a saka mata,ai Kuwa yarinya taci suna Siyama,Dauda dalilin kyautar yarsa Siyama ya nemi Hajara wato Aunty wacce bazawara ce itama bata haihuwa Kawai ya aureta tunda lalurarsu iri daya ce.

    Ranar da aka yaye Siyama Amadou ya dakko Siyama da kayanta kaf ya kawowa Dauda har gidansa Dake rijiyar lemo Kano yace Yaya ga yarka na kawo maka ta damemu da fitina,Dauda yace a bani a bata dama duk kewarta ta dameni ya karbe Siyama,Amadou akan hanyarsa ta komawa gida mota ta bige shi Nan take ya rasu,Dauda Kamar zaiyi hauka har gobe idan ya tuna Amadou sai ya zubar da hawaye,Siyama ta taso cikin gata so da kulawa sai abinda take so duk duniya ba Wanda Dauda yake so sama da Siyama,itama Aunty ta dauki son duniya ta dorawa Siyama sakamakon bata taba haihuwa ba,macece me iya Zama da mutane ga iya raino da kula haka ta tsaya akan Siyama har ta Isa zuwa makaranta Suka sata a makarantar boko da Islamiyya,data Kara girma har makarantar dare take zuwa shi yasa Siyama take da kokari primary ma private aka saka ta shi yasa take Jin turanci sosai,..

    Sun taso a unguwar tare da Nusaiba dake layinsu daya ita Nusaiba ma har primary ta gomnati tayi sabo da talauci,Sanda Shehu yayi Dan kudin nasa basu taso ba,Kuma ba kudi bane rufin asiri ne Kawai, ana Kai Siyama Secondary school Suka hadu da Nusaiba a can,ko a class Nusaiba dama bata da mutunci idan ta Raina kurar mutum zaiga wulakanci,Bata kawa da mutum sai tasan kun fita arziki shine zata Shige maka abinda ya hadata kawance da Siyama kenan idan taje gidan su Siyama zata ci shinkafa da Miya su kuwa gidansu sai a kwashe wata guda ba ayi shinkafa da Miya ba,suna Ss2 Nusaiba ta daina zuwa makaranta sai tallan kosai kannenta ke zuwa sabo da talauci gwara ta Nemo musu ko zasu samu abincin ci,Siyama Kuwa ita da sauran sun Gama secondary school suna da shekaru 19 tana zaune sai dai tallan su har ta Kara shekara hudu Wanda da akwai kudi da tuni sun Gama degree,yanzu sun Kai 23yrs, Yan Mata ne sosai .
  Siyama doguwa ce Fara me round face me dauke da dogon hancinta zarkadede,idanuwanta manya dasu masu kyau kamar tana Jin bacci haka take sai ka rantse bacci take ji kullum a Haka take,gashi ne da ita sosai gata da dan jikinta mul mul ba Kashi sai dai ba me kiba za a ce ba,komai mashaallah.

       Nusaiba Kuwa Yan asalin Rogo ne wajen jahar Kano Shehu dan dangi ne Yana da Yan Uwa da yawa sai dai Basu da Hali duk talakawa ne a kauyen Rogo,itama Mama tana da nata Dangin da yawa a Rogo amma guda Daya ce wacce suke uwa Daya uba daya sauran duk dangi ne, Amma duk cikinsu babu me iyaye duk sun mutu tunda Suma sun tsufa bare iyayensu sai dangi,Mama me Suna Bara'atu Yar asalin kauyen kayau ce a Rogo ma a wani mugun Kauye take Wanda basu karatu Babu ilimin Addink bare boko,a haka Shehu ya nace sai ita shi yaga fetsarariya dama sai da aka fada kaf gidan su Mama basu da mutunci a kauyen basu da Kara Basu da kunya su kamar a jininsu yake Imaninsu kudi Kawai,Shehu yace ba komai zai sata a makaranta,Bayan ya aureta tun Yana zuwa cikin birni cirani har ya mallaki filinsa ya Gina ya dakko Mama daga Kauye ya dawo da ita birni,ya sata a makarantar yaki da jahilci ta matan aure inda ake koya musu ilimin addini da karatun hausa

   Mama ita ko a makarantar ma dakikiya ce sam bata ganewa sai ta dade a aya Daya,aya daya sai ta kwashe satikai bata iya ba,a Haka ma dan Shehu Yana koya Mata a gida,idan Suka Zo karatu ta dinga kunkuni da masifa kenan Shehu har rankwashinta yasha Yi sabo da jahilci da kin karatu,Fatiha ma Sai da ya tsaya a kanta sosai ta iya,ya koya Mata wankan haila da komai,Sallah ma Shehu ya koya Mata,a hankali Mama ta Fara Zama tsagera a unguwar,duk Sanda Shehu ya siyo kayan abinci kwana kadan sai yaji tace ya kare, sai da masu shagunan unguwar Suka fada Masa cewar matarsa fa tana kawo musu su shinkafa,taliya etc suna siya ya sa ido Ashe siyarwa takeyi ta soke kudin,Shehu ya Kai kararta gidansu yafi a irga karshe ma Dangin Mama suci ubansa ya dawo bashi da bakin fadawa Yan Uwansa tunda dama tun farko sun hanashi yaki ji,ana Haka Mama ta haifo yarta mace,Shehu yace zai maida sunan uwarsa Mama tace bai Isa ba ita tun tana yarinya take mafarkin yarta ana fada Mata a mafarki sunan yarki Nusaiba,Shehu yace sai kace wata manzo ko waliyiya to baki Isa ba,Suka dinga fada karshe dole ya hakura ya saka suna Nusaiba ta Haifi Danta na biyu Nan ma ta kafa ta tsare tace Ameer ake yayi shi za a sawa danta,Shehu ya saka,ta haifo Ihsan

    Tace yanzu an waye sunayen larabawa ake yayi Ihsan kawai,Shehu ya kyaleta ya saka sai da kyar da ta sake haihuwa ta yarda aka sa sunan Babar Shehu Asmau ai Kuwa tace Husna Kawai ita fa ta waye Kuma baza ta boye ba ai ba uwarta bace haka ta Haifi yaranta karshe ma Shehu Yana son haihuwa tace ta gama tayi planing shike nan ta tsaya da haihuwa abinta, gaba Daya tafi karfin Shehu ya rasa inda zaiyi da ita,wulakanci iri iri,da kudinsa Shehu zai siyi abinci amma idan ta dafa ta hanashi sannan yaranta kadai zata bawa Kuma Suma kadan sai ta siyar da sauran taci tsire da kudin, idan taga dama zagin Shehu ma takeyi shi Kuma Shehu hakuri yake da ita Kawai Sabo da yaranta,duk sabo da yaran data tara yake kyaleta sabo da idan ya koreta ma ya zaiyi da yaransa sannan rashin uwa a zamanin nan ba karamin matsala bane ga Yara shi yasa Kawai yake hakuri,akwai Sanda ma idan Suka Yi fada to da wuri zata rufe gidan idan Shehu ya fita masallaci Sallar Isha ya Sha kwana a masallaci
  Ita Kuma bata ganin hakurinsa haka tunaninta Kawai Dan ta Isa ne ko masifarta ce tasa,ya rasa ya zaiyi da ita Kawai ya daina bata ficika Kuma ya daina bata abinci Wai ko zata Yi hankali,wannan talaucin yasa Mama tayi laushi ita da Nusaiba Kawai ta ya zasu ci su koshi suke yi amma gashi Aslam Yana zuwa Suka samu kudi sai wulakanci Kuma Wanda yafi na baya ma,gidanta Kuma da Shehu yace ya siyar ba siyarwa yayi ba gani yayi akan Addua yarta ta bace  zata siyar da gidanta yaji tsoro ne Kar ta koma bin bokaye abin bazai Yi da kyau ba shi yasa yayi Mata wayo ya nuna ya siyar da shi,duk wani zalunci sau tari ba zakuntarta yake Yi ba  Yana yi ne sabo da nemawa Kansa sauki sai gashi dai karshe sai da ta kaishi ga zaluntar yaransa da matar ma tunda ya hanasu abinci Wanda hakkinsa ne,ita Kuma
Nusaiba tun tana karama zuwa tasha talla da yawan rike kudi shi ya jawo idonta ya bude da kudi da shegen son kudi Idan kaci kayan me talla ka hanata kudi zaka ga rashin mutunci shi yasa takewa Aslam haka ta Saba fada da maza a wajen talla dama mafadaciya ce Kawai dai ita ba Yar iska bace bata bari a kawo Mata iskanci amma talla Yana daya daga cikin abinda ya jawo Nusaiba tafi karfin kowa bata tsoron kowa komai girman mutum ga Kuma gadon su na uwa wajen rashin mutunci da rashin sanin ya kamata,Mama sabo da rashin karatunta shi yasa Bata damu da ilimin yaranta ba.

   Nusaiba wankan tarwada ce Kuma ba laifi tana da kyanta dai dai gwargwado baza ace Mata mummuna ba,itama doguwa ce sai dai siririya ce amma ba can ba sannan tana da shape dinta dai dai ita Kuma dama Indai ta samu Kayan kwalliya to Yar kwalliya ce sabanin Siyama da tun tana karama bata kwalliya ita sai dai ta sa Riga da wando Bata taba saka skert ko zani kullum da Riga da wando har ta girma take zuwa wajen gwanjo ta zabo kala kala masu Fadi manya manya  hakan yasa aka sa Mata suna Charity tace Begins at home taji ta karba shike Nan sunan ya bita Indai baka ce Siyama Charity ba Babu me ganeta ko kace Siyama sai ance wacce? Sai kace Charity sannan za a gane.
   Charity saka Riga da wandonta ya jawo Mata bata samari da yawa sai dai dai kadan amma Nusaiba Kuwa Allah ya bata kowa sonta yake sabo da Yar kwalliyarta,Kuma Charity gata kyakyawa Fara amma Riga da wando yasa ba a zuwa ma wasu ma zaton su Yar Igbo ce in ka ganta haka,Nusaiba Kuwa iyayinta kadai da gwalli Yana jawo Mata samari amma bata taba samun me kudi ba sai Aslam shi yasa Kawai ta aure shi Dan kudin ita Indai Namiji me kyau ne baya birgeta tafi son kudi duk kyansa bata bukata
  Siyama Kuwa Samarinta Basu da yawa amma duk na kirki ne masu sonta tsakani da Allah Kuma masu rufin asiri ne kowanne ba na banza lokacin bata son zancen ma aure harkarta takeyi tunda Dangin Hunaif Suka Mata sharrin Yar lesbian ce ta daina kula kowanne Namiji harkarta Kawai takeyi,kowa kallon wata Yar duniya yakewa Siyama ana yiwa Nusaiba kallon mutuniyar kirki,Haka Kawai ma Siyama bata Yi komai ba za a dinga Mata kazafi a layin ana gulmarta musamman samarin layin sun sata a gaba. wannan kenan

    Yau Affan yayi Niyyar zuwa gidan su Siyama,Liman ya bashi number Dauda kawun Siyama yace idan yaje ya Kira shine kawun Yarinyar, Affan wata sabuwar Shadda ya bare gal dinki me kyau na manyan samari masu tashe da ji da kansu, Yana furta Siyama...Wai Siyama yo ai naga Sima ma karewa, shiri ya Fara ya sa wani short tight ya matse shi sosai ya kalli Kansa yace yawwa Yana kallon Sandar girma wacce ya matse ta da wando yace ke sarkin rashin hakuri baza ki kunyatani ba ke sarkin son aiki ke dai ayi aiki ko to Kuwa baza ki samu ba  kije kisa naji kunya a wajen yarinya yanzu kuwa da na matse ki ai ko motsi bakya Yi ba sarkin aiki lokaci baiyi ba ki Kara hakuri,Boxers ya sake dorawa a Kai sannan yasa wandon shaddarsa ya shafa turaruka kala kala sannan ya saka rigar shaddar wata ita ba milk ba ita arsh ba haka take,hula ya dakko a ledarta sabuwa Kalar shaddar ya feshe hular da turare me kamshi sannan ya sake taje sumarsa tare da wani dan dasa hular a gaban goshi yanda samarin zamani ke yi, Suma gata Nan a baya da yawa tari guda,sajensa zuwa gemunsa ya gyara ya shafa musu Mai me kamshi da spray dinsu ya feshe ya fesawa shaddar Kalar na kaya,sabon takalmi ya dakko shima jaraba kalar shaddar sabo da shi ya zura a kafarsa na Yan gayu yayi bala'in kyau abinka da me kyau da haske domin shi Affan Kalar skin dinsa Kalar ta Yan Latin ce Kamar irin Dan Brazil haka skin dinsa take,hancinsa dogo ne babu wacce zata ganshi ace bai birge ta ba, Fitowa yayi tare da kulle part dinsa ya juyo Yana waya da Abokinsa Sayyeed dan kd yace Ina Kano na kusa karasowa gidanka nan da 30mnt,Affan yace Zan bar maka key a wajen wata idan kazo gidan kace wace Raudat zata baka key sai ka bude ka shiga kafin na dawo,Sayyeed ya amsa da to an gama Yana kashe wayar ya dago Suka Yi Ido biyu da Raudat ta dawo daga wajen aiki ta gaji sosai yau sunyi meeting ogansu yaci mutuncinsu ya bata Mata rai,Amma tana ganin Affan komai ya canja ta manta da bacin ranta gaba Daya farin ciki ya kamata

  Bata taba ganin ya Mata kyau ba irin yau kallonta yake yi bata sani ba botin din rigarta ya bude daga kirji ana hango shatin boobs dinta,tana aikin kallonsa shi Kuma Yana kallon kirjinta sai kace maye har sai da ta lura tayi maza ta gyara mayafinta da sauri ya dauke Kai kamar bai gani ba ya basar yace Hajiya Aunty Sannu dan Allah ga key dina ki ajiye a wajenki abokina zaizo zai karba a wajenki karki Yi nisa ai kina gida ko? Raudat ta karba da sauri tace to Inshaallah,yace zaizo ne bazan jira shi ba  zance zanje nafi so na dawo da wuri Kar ta gaji da jirana ta ce ta fasa ko ya Kika ce? Raudat nan take taji zuciyarta ta dau zafi Kamar tayi kuka dama tunda taga wankan ta firgita,Affan yace Hajiya Aunty ya Kika ce nayi? Kina ganin zata Yaba? Raudat kokari tayi ta danne tayi Murmushi dole tace sosai ma ai yau sai ta kusa Suma Ina tabbatar maka sai tace tana sonka,Affan ya daga Mata babban yatsa ya Bude motarsa wacce ta Sha wanki kal kal tare da shigewa ya bar gidan,Yana barin gidan Raudat kasa tafiya tayi daga wajen bakin ciki da bacin rai yasa ta zauna ragwaf a bakin kofarta ta zuba uban tagumi abin duniya ya Mata zafi tana tunanin bata San Sanda ta Fara hawaye ba har ta koma kuka sosai wiwi,a haka Sayyeed yazo ya samu Raudat yace baiwar Allah lafiya? Raudat da sauri ta tsaida kukanta tare da goge hawayenta tace rasuwa aka min tayi karya,yace Allah yaji Kan rai Dan Allah wace Raudat a gidan Nan?tace nice,yace ashe ma yarinya ce budurwa na zaci Babba ce,Murmushin karfin hali tayi tare da bashi key ta mike ta Shige cikin palonta,tana zuwa ta shiga kitchen ta shirya abinci lafiyayye ta window Sayyeed yaji ana cewa bakon Affan ga abinci,mamaki ya kamashi ganin windows har biyu ta cikin dakunanta suke labile ta janye tare da zuge glass ta Mika Masa tire Kato ya karba Yana kallonta, chocolate ce amma me haske haka Kalar Raudat take kyakyawa ce harda Yar karamar wushiryarta me Yar karamar Fuska jikinta Kuma Kato domin doguwa ce Kuma akwai uban mazaunai da boobs  kana ganinta kasan ba karya akwai kudi Hutu da Jin dadin ya ratsata kalarta Kalar yaran Madara ne,Sayyeed dama yunwa yake ji ya zauna Yana ci yana Jin Dadi lallai Raudat tayi yace a ransa gaskiya Ina sonta Indai zata so ni Zan aureta bai San Sabo da Affan ake Masa tarbar ba,window ta sake budewa ta Miko Masa fruits cikin wani bowl ya amsa yace thanks,ta rufe window din,kitchen ta koma ta Fara tunani me Zan bashi ne ya Kara ta shiga tunani sai Kuwa ta bude fridge ta zaro kaza me kankara tayi melting kankarar sannan ta dora farfesu ta shirya shi me Rai da lafiya me dadi kadan ta ragewa kanta ta zuba Masa a flask me kyau da tsada ta sake komawa ta bude window tun kafin ma tayi magana Sayyeed ya Miko Hannu tuni Yana dariya,itama dariyar tayi ta bashi ya karba Yana godiya,yaci ya bar wani ya rufe cikinsa sai da ya cika dam sannan Raudat ta tafi ta gyara gidanta tayi wanka tare da chakarewa cikin Riga da skert na wata sabuwar Atamfa me tsada shape ya fito komai cas da ita Kamar a saceta abinka da Yan gayu wayayyu compound ta fito tana jiran dawowar Affan itama Wai yaga wankanta,Wajen Landlady taje Suka fito compound suna Hira abinsu amma hankalin Raudat yana Hanya.

     Siyama Kawunta ne ya kirata yace Siyama zo,har dakinsa ta shiga tare da durkusawa tace Kawu gani yace Siyama Kar kiga Kamar na takura miki,Babanki mahaifi Yana da babban Amini Mai suna Mallam Arifullah,amininsa ne na gaske duk duniya bai da aboki sama da shi tun ainihi liman ne me tarin ilimi Yana da matan sa biyu da yaransa Tara,Bayan babanki ya rasu duk wata sai ya kawo Mana Kayan abinci har Kika girma Kuma tun kina karama duk shekara sai ya Miki dinkin Sallah kala biyu nasan kin sanshi ma Zaki ganeshi domin Yana zuwa gidan nan sosai mutumin kirki ne,Siyama tace na ganeshi Kawu har nake ce Masa Liman amma me kudi,yace yawwa kin gano shi Yana da arziki sosai to shine dai yace Yana da wani yaronsa Wanda ya yaba da nutsuwarsa da tarbiyyarsa me zai hana idan Kun dai daita kuyi aure Kar kice na takura Miki,Siyama tace kawu ya kake Abu Kamar ba Kawuna ba nasan ai baza ka cuceni ba ko,Kuma baza a min auren dole ba sai idan na Amince yace hakane Siyama tace to ba matsala yazo,Kawu yace dan Allah karki watsawa Mallam kasa a Ido Yana kaunarki Yana kaunar mahaifinki,Siyama tace to ita Kam duk duniya bata ga Kamar Aslam ba,duk shi bai nuna Yana sonta ba ya zata yi gwara idan ta samu mijinta Kawai ta aure shi ta huta.

    Wanka tayi da kwalliya cikin leshinta me kyau na bikin Nusaiba da tasa Aslam ya dinka mata da shi taci kwalliya ta Sha kyau ta zauna tana jiran Wanda aka ce zai zo.
   Affan ne yazo har kofar gidan da motarsa cikin wankansa shi duk gidansu bai dame shi ba yasan shima a baya talakan ne sosai shi yaga ma gidansu da kyansa ba laifi ba ruwansa da wani talaka da Mai kudi duk Daya suke a wajensa,Wayar Kawu ya Kira Suka gaisa yace ya karaso,Kawu yace Siyama yazo Yana kofar gida shigar da shi dakin zaure tace to ta mike ta yafa mayafinta sannan ta fita cikin takunta me kyau,Yana cikin mota ya hangota ta fito ba karya tana da kyau ta hadu ta Kai a so ta amma shi Kam gaskiya wankan Raudat yafi Masa kyau gwara ya kalli Raudat sau dubu,Dake Affan yasan mutunci Fitowa yayi daga motar da gayunsa ya amsa sallamarta,tayi Murmushi tace ka shigo ya bita Suka shiga palon Wanda ba komai sai red carpet dake malale a kasa, Affan baya son Zama a kasa Kar kayansa su yamutse haka ya hakura ya dan dosana duwawunsa,Ruwa da lemon da Kawu ya siyo taje ta kawo Masa sannan Itama ta zauna can gefe,Ina yini tace,ya amsa lafiya Alhmdllh ya mutan gida tace lafiya lau,yanda taga Yana kwalisa bata zaci mutunci haka daga gare shi ba, Affan bai son wulakanta dan Adam shi Kam,baiyi zancen soyayya ba bare zancen aure,bai ma Yi zancen Liman ba Kawai Yana duba wayarsa ya dago Suka hada Ido da Siyama wayarsa aka Kira ya daga Wanda yake siyen shadda a wajensa ne yace ka duba WhatsApp na turo maka da latest,Affan a waya Suka dinga labarin wanka da gayu ita dai Siyama tana ji har ya gama ya duba chat ya gansu zuka zuka,ya nunawa Siyama yace Kinga colors tayani zaba,Siyama ta leka Wayar ta nuna Kalar ta Mata pink tace wannan color yayi,Affan yace ke baki San Kalar maza ba na Mata Kika sani matsa can gefe

  Siyama tayi Murmushi ya Gama zabensa pink din data dauka a ciki ya sake nuna Mata yace sai wacce color Kuma? ta sake zaben dark blue,yace sai kace Dan fulani sukayi dariya bai dade ba ya mike yace zai tafi har sun Dan Saba ta rakoshi jikin mota kenan yace me color din Mata sai Watarana kuma,tace to ka gaida gida na gode tana Murmushi dai dai lokacin Aslam ya karaso kofar gidan a motar Sabeer ganin ya fito Gaban Siyama ya Fadi Haka Kawai taji kunyarsa da tsoronsa ya kamata tana zance,kallon Affan yayi Kawai Aslam ya bata rai ya daure Fuska tam juyawa yayi ya koma cikin mota yace Sabeer muje kawai,Affan bai sani ba ya zaro kudi dubu biyar yace gashi ki sa Kati bai San ko waya Bata da ita ba,Aslam ya kura musu Ido gashi Yana yiwa Sabeer masifa muje dalla malam
    Siyama kin karbar kudin tayi Affan yace mene haka Kuma bana so nayi kyauta a maida min,Siyama juyawa tayi Kawai ta Shige gida duk ta firgice ta tsorata, Affan baki ya tabe yaja motarsa ya wuce,Aslam tuni sun tafi.

    Siyama tana komawa gida tace kawu ya tafi Aunty na dawo Suka ce to sai bayan Isha Kya bamu labari tace to tare da fadawa dakinta ta kwanta akan katifarta ta fashe da kuka Wai Aslam ya ganta tana zance har da cewa na shiga Uku na shiga dubu tana rusa uban kuka Kamar wacce aka Mata mugun duka,Aunty ce taji kukanta ta fado dakin da gudu tana cewa me Zan gani Siyama lafiya? Saurayin ne yaci Miki mutunci ko me? Marinki yayi? Siyama tace shike nan tawa ta Kare na gama yawo ta sake sakin kuka tana shesheka tace Aslam ne Aslam,Aunty tace mutuwa yayi? Siyama tace Aunty Aslam Aunty wash...shike nan Aunty Aslam ya kamani ya ganni Ina zance Innalillahi, Subhannallahi,Ashahdu Allah ilaha illallah ta Dora Hannu aka tace Aslam kuru kuru ya ganni,Aunty Tsaki ta ja tace ke dalla rufe Mana baki mahaukaciya amma dai sonsa kike dama ko? Charity tace Mijin Nusaiban haba Aunty mijin kawata kuma abin kunya ne ai,Aunty tace to rufe Mana baki sakarya, Kawai ki Fara Mana kuka sabo da rashin aikin yi,Siyama tagumi ta zuba tana goge hawaye ta kasa tashi Sam sabo da jimami.
 
   Aslam kuwa suna tafiya Sabeer yace zamuje park din? da masifa ya furta ka kaini gida Malam Babu Maganar park din banza kaini gida gwara nayi tunani me kyau na huta,ka fasa zuw...bazan je ba karka dameni ya furta da masifa,Sabeer yace kaga nifa bani naje zance wajen Yarinyar Nan ba bare kace,to ni nace maka naji haushinta ne Ina ruwana ta kula maza dubu ma Ina ruwana,Sabeer dariya kawai yayi Yana tukinsa yace tana da saurayinta kana ganinsa dai sharr da shi gwara ka auri Nabeela, Allah ya kiyaye na auri sakin wawa Nima fa sakin wawan nayiwa wata nasan me tayiwa mijinta ya saketa ba duk bazawara ce ta kirki ba gwara wacce ma mijinta ya mutu amma Wanda ake sakowa na tsorata da su wa yasan me Suka aikata aka sake su,Sabeer yace wallahi akwai Wanda laifin mazajensu ne,Aslam yace ae naji naji bana so bata min ba ni da wata kafarta a gwame,nufinka idan ta sa min riga da wando haka Zan na ganin Ball leg dinta sun kantare,Sabeer dariya Kamar me yace yaushe kaga kafafunta maye yanzu har ka San tana da Ball leg? Kwarai kuwa ko zaka ce karya ne? Sabeer yace tabbas wlh ba musu lallai mutumin auren Nusaiba ya sake gogar dakai da ko kallon Mata baka yi,Aslam yace dan Allah ka kyaleni bana son surutun me gwamammiyar kafa dai bana Yi karka sake min zancenta ana Neman macen kirki kana kawo min bage,Sabeer yace sorry na Siyama yana dariya,ance maka son Siyama nake Yi wai nifa ban shirya aure ba ku sani ma ya furta Yana turo jajayen lips dinsa yace kaini wajen Mum ma gwara na ga uwata na huta da duk wata ya mace.
   Wajen Mum suka tafi can Suka zauna har dare Mum har ta Fara damun Aslam cewar ka Nemo Mata ta gari Aslam gashi ma Kai naga Kamar baka da niyya Wanda hakan hatsari ne ga duk namijin da ya taba aure bai dace ya zauna ba Mata ba ka dinga dubawa kaji,to Aslam yace kawai.

    Affan kuwa akan idon Raudat ya shigo da motarsa gidan tana tsaye ta juya baya ita da Landlady suna hira ya wuce da mota abinsa Yana yin parking ya fito Raudat tana kallon inda yake fitowa,part dinsa ya Shiga da sauri,Raudat ta sauke ajiyar zuciya ta Shige part dinta ita ma,ai tana Shiga ciki taji suna tafawa da Sayyeed suna magana Affan yace Kai Kuma wannan tarkacen flask din da tire Ina ka samo su? Sayyeed yace ai baka sani ba budurwa nayi Raudat ce ta dinga Miko min ta window ashe windown ku daya, Affan yayi dariya yace Kai dalla ba sonka takeyi ba mutunci ne da ita Haka take da kirki ita tana ma da mijinta matar wani ce aiki ya kawota weekend take komawa gidanta, Sayyeed ya zaci da gaske ne yace eyya na hakura gwara da ka fada min,ai Kuwa tana da kirki kalli girki ya shiga budewa Affan Yana kallo,yace ta hutar Dani dama da tunaninka na dawo na nema maka abinci,Raudat tana jinsu suka hau Hira Sayyeed har yayi wanka Affan yace ko zamu fasa gari ne?Raudat ta Riga su fitowa ta tsaya kamar zata Shiga motarta,Affan ya fito tare da Sayyeed,Affan yace Hajiya Aunty fita zakiyi ne? Tace ae Ina son fita amma bana son driving din na gaji,Affan yace muje to Mana na kaiki ni Naga yanda Kika karrama abokina na gode fa,Hmm ba komai cewar Raudat zata Shiga Bayan motar Affan yace shigo gaba Sayyeed sai ya Shiga baya shi,Sayyeed ya Bude baki matar wani Kuma Affan yace Kawai dai Sayyeed ya Shiga Bayan mota,Affan ya tashi mota Suka wuce Raudat bata San inda zata je ba,Affan yace Ina za a kaiki? tunawa tayi da wata kawarta da suke aiki waje daya wata Hafsat ta nuna Masa gidan har ya kaita kofar gidan Hafsa yace yaushe za a zo a daukeki? Raudat tace sai 10pm,Affan ya zaro Ido yace haka Kawai ki zauna a gidan wata matar tana da aure fa har goman dare ki takura musu idan mijinta Yana son yayi Yar harka fa gaskiya bai dace ba,Raudat tana dariya tace to karfe nawa Zaka dawo? Yace gaskiya 8pm Haba kina mace a dinga sakaki dake bazai yuwu ba,To sai ka dawo cewar Raudat yace yawwa 8pm ki shirya har ta juya yace Aunty ta juyo da sauri yace ba ruwanki da mijinta sawunki a likkafa ki dauke idonki dan mazan yanzu ba mutunci gare su ba wlh sai yace Yana sonki ato ki kula Kar azo kawa ta nada Miki duka a gidanta irinku Aunty sai kusa mijin wata ya kifa yaci ta ka,Dariya Raudat keyi yace gaskiya nake fada Miki ki Kama kanki ba ruwanki da mazan wasu,Raudat tace to sai dai ka dawo ta juya ta Shige tana dariya,Affan sai da ya daina ganinta sannan yace da Sayyeed Kai katon gardi dawo gaba Kuma wallahi karka sake muna kwance ko yatsanka ya taba min fatata nasan baka iya kwanciya ba na tsani jikin Namiji ya taba Ni da ace dai macece aha wannan is okay Sayyeed ya koma gaba yace nasan halinka ni a Palo ma Zan kwana Kuma kaji tsoron Allah kana kula matar wani,Affan yace ai mun Saba da ita, Sayyeed yace naga alama dalla karka Raina min hankali let's go,Suka tafi yawonsu.

    Tun kafin 8pm Suka koma gida da kayan ciye ciyensu ya bar Sayyeed ya sake zuba wankan 3qtr da riga me gajeren hannu farare ya tafi dakko Raudat,8pm dot yayi horn dit dit Raudat taji ta shirya tare da yiwa Hafsat Sallama,Hafsat ta rakota tare da mijinta har mota ta Mika Mata turarukan wuta masu kyau a Leda,Affan ya kalli Raudat kadan ya juya da mota Suka hau kwalta sannan yace mijinta har da rakiya Ina ruwansa dake Kai wasu mazan ma Sai a barsu gaba Daya wasu rako Suka yo,Raudat ana ta Jin dadi har da narkewa a jikin mota taki magana ta rasa yanda zata Yi sabo da murna,yace naji kinyi shuru? Raudat ana wani tararrabewa an samu waje tace kaina ke min ciwo a ranta tana istingifari da karyar da ta shararo, Sannu ya furta tace yawwa,yace a tsaya a siya Miki paracetamol? No ta furta Ina da shi a gida yace sai a kyaleki kina cuta Kuma, yayi parking bakin wani chemist ya shiga ya siyo Mata paracetamol da ruwan roba ya dawo dauke da Leda a hannu daya hannun a aljihu Yana taku dai dai yana zuwa ya Mika Mata yace Sha,ai Raudat tabara ta fara tace bana son magani Allah,yace ashe Kuwa baza mu koma gida ba a nan zamu zauna harda gyara parking,farin ciki yasa Raudat ta Kara narkewa tace please kayi hakuri,Affan tsigar jikinsa tashi takeyi idan tana Masa Shagwabar nan tana tuna Masa da Nabeela,Murfin robar ruwan ya balle ya balli paracetamol biyu ya zuba a cikin murfin ya dan zuba ruwa ya wani narka maganin sai kace zai bawa dan yaye yace tsaya na baki to Yana kallonta,sabo da shine zai bata kalau take amma tace to tayi wani kasa da kai lagaf, Hannu yasa tare da dago kanta a hankali harda cewa haa  ta bude ya zuba Mata ta shanye ji tayi kamar ta Sha alawa sabo da shi ya bata, ruwa ya bata a baki ta shanye abinta ta wani kwanta a saman kujera Yana cewa sannu yaki tashin mota sai data kwashe 30mnt tace naji sauki har na daina ji sannan ya yiwa motarsa key

    yace me kike son ci? tace Ice cream ai Kuwa ya tsaya ya siya Mata wata katuwar roba guda biyu da su yogourt me sanyi ya dawo ya leko ta windown ta yace abinci fa ranki ya dade Hajiya Aunty? tace naci a wajen Hafsat,duk da haka sai da ya siyo Mata tsire lafiyayye sannan ya shiga mota Suka tafi, ana tafiya tana Shan ice cream dinta Yana driving  yace ni bazan Sha ba? tace Sorry gashi yace tuki nake ai tace to sai munje gida,yace ki bani a Baki ,Ido Raudat ta zaro taji kunya tace bazan iya ba,yace kaji locality me nake ji ba dadi haka sai kace wani suna Siyama,dariya tayi taki bashi bai ce komai ba har ya kawota gida tayi godiya ta wuce part dinta shima ya shige wajen Sayyeed,tana zuwa tayi sufa akan gadonta tana tsalle da murna.

     Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan bana so shike nan Kuma bana sonsa,Aslam ya sake cewa bari mu Fara ja baya Siyama tace kash kajika da wani zance akan Affan din me aka yi aka yi shi wani banza da shi zaka bani kunya Allah yawa kake yi,Aslam yace to shi kina ganinsa me kudi,kudin me wa yake ta kudinsa nawa ya tara,Aslam Yana ta bugar cikin Siyama bata gane ba,sai da ya gama Jin komai sannan yace to Hajiyar wanka in tafi ko na tsaya akwai labari? Siyama tace jeka,yace oh korata ma kike Yi kenan,Siyama tace nayi Fushi sai ka dinga min wasu maganganu haka marasa dadi,Aslam a hankali yace Ina sonki Siyama.....Baki ta bude tace so kuma Aslam? Yace ae ba sai kin so ni ba Kawai na fada Miki mind dina na gaji da hiding, idan Kika bari Kika auri wani laifinki ne na daina kulaki Kuma har abada ko a hanya gwara ma ki aure ni,Siyama ta rasa wanne irin murna zata Yi ta boye tace tun tuni sai da ka bari aka turo min wani wajena yanzu ya zanyi da Kawu? Yace ki San yanda Zaki yi  please I love you,ban taba son wata haka ba sai ke sai Ina kusa dake nake gane ni Namiji ne tun tuni tun farkon zuwanku gidana na zaci ba so bane Kawai yasa Naga Nusaiba tafi min na aureta,Siyama ta rufe baki a ranta tace zuki ta mallen maza kenan sabo da ba Nusaiba,ganin bata da Niyyar bashi amsa ya juya ya Mata sallama ya tafi,Siyama Kuma ta Shige gida da sauri tana zuwa tayi ball da bahon wankansu ya fashe fas,Aunty tace Yar nan lafiya? Siyama ta kankame hannu tace wayyo Yana sona dadi kasheni cikin farin ciki ne, Aunty rungume ni dan Allah Zo ki rungumeni, Aunty taki kulata zuwa tayi ta rike jikin bango tana zan sume Iska zata daukeni wayyo Sanyi dadi Allah na gode maka tayi ihu,Aunty tace wallahi sai kin siyo Mana sabon baho akan Namiji Kika fasa Mana baho,za a siyo karki damu ta fada dakinta harda rawar sanyi tsabar farin ciki sai kace tana Jin sanyi haka take karkarwa.

    Aisha watanta biyu a gidan Bashir duk ta rame tayi baki ta fita a hayyacinta gashi Hariji sannan Kuma Babu abincin kirki Yana samun kudi amma ya daina bata ci na kirki,a wata biyun ta samu ciki amma shi Bashir baya son haihuwa,ga mijinta can Farooq Yana son haihuwa basu samu ba taje tayi aure Kuma inda ga haihuwar amma ba a son yaran,gaba daya Bashir ya tsaneta sabo da ciki,ko ya ta bashi haushi sai duka a Haka cikin nata ya zube Aisha tayi barin Yan biyu twins,tayi kuka sosai ga rama ta kekashe ta bushe,Farooq Kuwa har wasu lokuta baiyi aure ba ya kasa kula kowa har ya gaji Mamansa ta hada shi Nabeela bazawara ita Kuma Maman Farooq kawar Maman Sabeer ce a can taga Nabeela,Aisha sai labari taji Farooq yayi aure tayi bakin ciki tayi kuka ta gode Allah har ta samu wani cikin,Bashir tsana ta dawo sabuwa dal

    Nusaiba bayan ta Gama Idda da kwana uku Sufyan yazo gaida Shehu,Shehu ya sauke shi yace yaro daga yin iddarta da kwana uku har yaushe ta sanka da zaka ce zaka turo wannan ya nuna cewar tun tana da aure ka Santa dama kana sonta ko karya ne? Sufyan yayi mukus yace bazai yuwu ace daga Gama Idda da kwana uku Wai har kazo daga wata uwa duniya kana sonta Kai ba dan unguwar nan ba a Ina ka ganta sai dai idan dama tun tana da aure kana zuwa,Mama tana ji tayi gatsal tace yata shi take so kuma shi zata aura,Shehu yace ba matsala Kai Sufyan gaka ga Nusaiba duk abinda tayi maka karka soma kawo min kara ba ruwana ya tashi ya fice abinsa,Nusaiba ce tazo tace karka damu dashi Indai Mama tana sonka an gama,Sufyan Yana murna sosai ya tafi,Bayan kwana uku ya turo da kudin aure cikin sati biyu Mama ta yanke aure za a daura,Shehu ba ruwansa a ciki sai da daurin aure yazo sannan ya shige gaba Sabo da yarsa ce ba yanda zaiyi aka daura auren Sufyan da Nusaiba

  Nusaiba takanas ta tafi gidan Aslam ta kwankwasa ya zaci wani ne ya bude sai kuwa ta shiga ciki tana yiwa gidan kallon banza harda cewa to Ina Aslam Dan karya gashi na riga ka aure Kuma na sake samun wani me kudin Allah ba Azzalumin bawansa bane bazai barni cikin wahala ba na sake tafiya gida me ac sai naga ta tsiya Kai Kuwa gaka nan tsiya tsiya kalli wannan dirty smelling House din naka nafi karfinka tana Jan tsaki ta juya ta bude kofa ta fice tace aci gaba da Shan talauci lafiya,Aslam baki ya tabe ko a jikinsa yace Wanda ya kulaki shine banza baki da ajin da Zan saurareki,Nusaiba tana jinsa ita Kam tayi gaba abinta.


Masu sharhi Ina Matukar godiya
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

          46-50

Official

By
AsmaBaffaPage naku ne

MRS SAS
YAR AUTA       Sufyan Isa,Dane ga Isa Yan garin Ajingi ne Kano amma a cikin Kano suke danginsu ne a Kauye amma uwarsa da ubansa da kannensa guda bakwai suna Kano kofar Ruwa,Sufyan shine Babba a gidansu talakawane, Allah yasa Sufyan yayi degree ya samu babban aiki na gomnati yayi aiki da shekara hudu haka Kawai ya ajiye aikinsa ya fito takarar Chairman ya koma siyasa,bayan anyi zabe ya Sha kasa ko kansilan nadi ba a bashi ba,karshe talauci ya sake baibaye su ya Shiga Neman aikin kamfani bai samu ba sai da ya kwashe shekara biyar sannan ya samu aiki a wani kamfanin shahararren me kudi ya bashi C.E.O ga Albashi me tsoka yana aikinsa sosai bai da wani aibu sai dai dan Adam kowa Yana da Hali me kyau Kuma ba a rasashi da hali na banza ko ya yake,ana haka ya ginawa iyayensa gida me kyau shima ya gina nasa gidan me kyau sosai amma bai Kama kafar gidan Aslam da bank Suka kwace ba Babu hadi ma,
ya mallaki motarsa me kyau har ya hadu da Nusaiba ya aureta Kuma.

     Kwana uku da daura aure Nusaiba ta Sha gyara ta ko Ina tayi kyau sai kamshi take yi,ranar Kuma aka Kai amarya gidan mijinta me kyau kana gani kasan ba gidan talaka bane,zaune take a saman gadonta dake dama Kawai daga ita sai lefenta da kayan sawarta Amma komai na furniture ya zuba abinsa.
  Sari ne a jikinta Riga da skert maroon ta yafa mayafinsa kyau Kam tayi,9pm angon ya shigo da Sallama hannunsa dauke da ledar kaji da kayan makulashe,Zama yayi a gefenta yace Alhmdllh Ni Kam nafi ko wanne Namiji dace a duniya,yau na mallakeki burina ya cika,Nusaiba tayi Murmushi tare da bude mayafin data rufa a kanta,yace tashi kiyi Alwala,mikewa tayi ta sheka wanka da Alwala ta fito shima ya shiga,shiryawa tayi cikin kayan baccinta masu daukan hankali sannan ta daura zani tasa hijab har kasa bayan ya fito shima ya shirya ya sa jallabiyarsa sannan Suka gabatar da duk abinda akeyi na addini da na al'ada,ledar ya jawo ya bude musu kaji ne da su Yogourt da sauran kayan makulashe da fruits

    Plates ya dakko ya zuba musu ta kalli Naman tace Wai brolas ne ko Maja? Sufyan yace Ina Zan sani ni da na gansu a gashe na siyo,tace maza dai har abada baza kuci gaba ba,tunda aka halicci iyaye da kakanni kowa kaza kaza dai ankonta kuke Yi ko wanne ango ankon kawo kaza,Sufyan Yana Murmushi yace to me kike so? tace Ina laifin ma tattabara tana magana Yana bata naman a baki tana lamushewa amma tana kushewa,sai da suka koshi suka gama komai sannan ya dauketa suka haura saman bed abinka da bazawara tsagera zagewa tayi Suka farantawa juna rai Suka jiyar da juna dadi sosai Sufyan sai yabonta yake yace Yan unguwarku sunyi sakaki na daukeki shike nan,Rungume shi tayi tana I love you a haka har bacci ya kwashe su.

    Siyama ce ta zubo shinkafa da wake da Mai da yaji sai salat ta toza wani katon plate kamar mutun uku ne zasu ci tasa a gabanta zaune a tsakar gida saman Sallaya da yamma sanye take daga ita sai vest fara da English skert wani me kyau brown Mai adon fulawowi fari,jikin nan nata sumul sumul komai Masha Allah,ta sa Hannu tana ci baza ma tasa cokali ba,Kawu ne yayi sallama ya shigo sai ga Aslam ma a bayansa sun shigo yasha farin wani yadi me kyan gaske yayi kyau Kamar baza a mutu ba,ya shigo Yana takunsa na Izza,Aunty ce ta amsa sallamarsa,Siyama kunya ta kamata sabo da irin abincin data zuba tana ci ya kamata,Aunty ce ta dakko tabarma tare da shimfida Masa ya zauna Suka gaisa

     Siyama tace Ina yini amsawa yayi Yana murmushi,ta mike ta kawo Masa ruwa pure water Yana faman binta da kallo,Kitchen ta Shiga ta zubo Masa abinci a plate ta rufe ta kawo plate din salat da Maggi star ta ajiye komai sannan ta koma ta zauna a gaban abincinta,sabo da kunya Siyama tace Aunty kin siyo min maganin tsutsar cikin nawa Kuwa? Aunty tace wanne tsutsar ciki sai dai ki boyewa Aslam amma kowa yasan irin mugun cinki,Siyama baki ta turo tace to ba tsutsar ciki ce ba suke tashi suna neman abinci,Indai suka farka daga bacci to sai na Fara Jin yunwa shike nan ba zaman lafiya idan ban ci ba Kuma fa,Aslam Murmushi yayi ya kalleta ya kalli abincin Siyama tana cin abinta,da Ido tace kaci mana,juyawa yayi ya kalli Aunty da Kawu yaga ai hirarsu suke Yi hankalinsu baya wajensa ya kalli Siyama da Ido ya fada Mata bazai ci ba harda makale kafada,Murmushi tayi tana leka su Kawu sabo da Kar su Kama ta,tashi Aunty tayi da Kawu Suka Shige daki suka basu waje,Siyama ce ta leka palon taga sun shige bedroom da sauri ta jawo abincinsa gabanta ta tona gefa tasa salat da su tumatir ta ebo a Spoon ta Mika masa a Baki ya tsaya Yana kallonta bai bude bakin ba,cikin muryar rada tace kayi sauri kafin su fito fa bazan iya baka a gabansu ba,Baki ya dan bude ta zuba Masa Yana ci ta sake lekawa dakin su Kawu taga dai basu da niyyar fitowa taci gaba da bashi a baki yana ci,sai da ya koshi Yana Shirin cewa ya koshi Kawu da Aunty Suka fito ai da sauri Siyama ta tura plate din Gaban Aslam tana basarwa taci gaba da cin abinta,Aunty ta fito sanye da hijab tace Aslam har ka koshi dan Allah ka cinye ta nan fa ba wajen Kara bane,Kawu yace ke Siyama ku tashi ku koma dakin zaure ko yafi sakewa a.....kafin ya karasa Siyama ta mike tsaye ta kwashi abincinsa da ruwa,Shima mikewa yayi ya zaro dubu biyar ya mikawa Aunty yace gashi Aunty Kya sa ko Kati ba yawa,Aunty tace harda kokari haka to fa an gode  an gode Allah ya Kara sutura yace Ameen Suka koma dakin zaure Wanda ya Sha gyara sai kamshin turaren wuta yake Yi.

     Suna shiga Siyama ta dawo ta dauki nata abincin ta wanke hannayenta tare da daukan wani spoon din ta shiga daki ta saka hijab me hannu ta koma wajensa,tana shiga ta iske shi a tsaye tace baka zauna ba,yace tsutsar cikina ce ta tasheni,dariya Suka Yi gaba daya suka zauna tace dan Allah kaci da yawa nasan baka ci komai ba,yace indomie naci Mana,indomie abinci ce?  please....ta karasa da shagwabar da hankalin Aslam ya tashi Yana Mata wani irin kallo cike da so Wanda yasa yace kin San me tace sai ka fada yana kallonta Ido cikin Ido ya furta Ina sonki Charity na matsu na jiki kusa dani, Charity tayi Murmushi tace hmm ban baka labarin wata kawata ba Haleesa wata daya da aure jiya naje gidanta na samu tana sheka amai nace haleesa lafiya? Charity tana wani magana ana Yi da hannaye ana style da hannaye Wanda sun Sha lalle me mugun kyau Wai dan Aslam ya gani,tace Ina fada maka ta sake daga hannayen tana jujjuyasu tace dan ubanki Charity ciki ne dani, ai tunda na bude baki kasa rufewa nayi,tana bawa Aslam labarin shi Kuma ita yake kallo kamar tv Yana dariya tun dazu yaga lallen amma ya nuna Kamar bai gani ba shine yanzu labarin ma Sai an sake nuna Masa lallen.

    Magana yayi yace ya birgeni haka ake son Namiji kema Watarana haka Zan Miki naki,Charity ta bude baki kunya ta kamata ta rufe Ido da tafukan hannaye tace ba ruwana ni dai Kawai sai a ga Yar Baby ta ace Yar gidan Charity ce wallahi haka zance duk Wanda taji yace da mamanta Charity Kar ta sake ta yarda,Aslam yayi Murmushin Jin dadi yace har na hango kanmu,Ki fadawa Kawu Zan turo a kawo kudi,Siyama tace da wuri haka? Yace kin San Kuwa yanda hankalina ya tashi da naga kina zance bazan iya ba wani yazo a samu matsala,Siyama tace Ina tsoro Kar Kawu yaki yarda sabo da Nusaiba,Aslam yace karki yarda a hanaki aurena kinji dan Allah bance ayi musu rashin kunya ba dole muyi musu biyayya abi a hankali amma ki dage kice sai ni,Aslam Yana yiwa Kansa campaign yace wasu tanadi da na mana sai dai munyi aure,Siyama tace duk abinda ake ciki ka dawo jibi,yace gobe Zan dawo ni ban gaji da ganinki ba tace Allah ya kaimu,mikewa yayi yace zanje wurin Mum,tace kace Ina gaishe ta yace zata ji itama ya zaro dubu biyar ya bata taki karba yace bana son musu,ta karba tare da furta na gode ka manta ledarka da ka shigo da ita tana kusa da Aunty,Aslam yace wayarki ce,waya na siya Miki Zaki ga Simcard din a cikin ledar ki saka sai na kiraki anjima ya rike hannunta ta zame a hankali yace Ni kike ma Haka Yana Murmushi tace muna yin aure kazo kayi ta rikewa,an gama ya furta Suka fito ta rakashi da motar Sabeer yazo ya shiga abarsa ya tafi ta koma ciki taci gaba da dura abincinta.

    Washe gari da safe taje gaida Kawu Aunty tana dakin tace Kawu ya amsa tana kunya tace Aslam yace zai fito,Kawu yace daga Ina zai fito? Takara zai fito ko kuwa daga daki? tace zai turo nake nufi,kawu ya gane fa yace baro zai...a'a fa kawu zai turo da manyansa neman aurena ,Kawu yace Yar jakar uba ai na gane so kike ki jawo Mana zagi da abin kunya a unguwa,yanzu idan aka ji mijin kawarki Zaki aura ai mun shiga uku a layin nan da zagi,Aunty tace sai ace ma itace ta rabata da gidan mijinta gashi Yanzu ta aure mijin nata ai ki auri Affan yafi Miki Siyama,Kawu yace rabu da Yar banza Ni baza ayi haka dani ba ki jawo min zagi,Baban Nusaiba Yana ganina da mutunci ace haka ta faru ai ba mutunci,Kece fa babbar kawarta kaf unguwar nan tare aka sanku yanzu sai aji kin aure tsohon mijinta bazai yuwu ba sannan naga Alama kina son Aslam baki son Affan zanje na bawa liman hakuri abin bazai yuwu ba amma ki sani bazan aurawa Aslam ke ba,nasan ya cancanta mutumin kirki ne amma ya auri babbar kawarki ya dawo ya aureki haba Siyama ai da kunya

   Siyama tace to ni shi nake so bazan taba son kowa ba sai dai na mutu ba aure Kuma ai lokacin da yake baku kudi karbewa kuke Yi baku ce mijin kawata bace bai Dace ba sai ku karba ko musu bakwa Masa Sabo da lokacin Yana da kudi Sanda zanje gidansa wanke wanke da shara kune kuka Amince baku gano rashin dacewa ba budurwa dani katuwa naje gidan best friend dina wanke wanke da shara bakuyi tunani haka ba kuka Kora ni naje can yanzu Muna son juna shine zaku ce mijin kawa ne Kuma ai ya saketa tayi Aurenta Kuma ita tace a saketa tazo ma tace idan na gani Ina so naje ayi Dani sabo da haka na gani Kuma Ina so a aura Masa ni Yana so na shima Kawai in Kuna son zaman lafiya ku bashi ni a huta,rufe Mana baki shashasha abinda babba ya hango yaro ko ya hau bushiyar rimi bazai hango ba, wallahi wani yaron ba amma ni abinda babba bai hango ba na hango cewar Siyama,zageni ki huta Siyama cewar Kawu, Siyama ta mike tsaye tana hawaye tace da Ina da iyaye ai baza suyi min Haka ba Dan anga ubana ya mutu uwata ma ta mutu shine ake ta nuna min iyakata ta nufi kofa zata fita ta sake cewa Kuma Allah Matukar a watan gobe ba ayi aurenmu ba sai naje ya min cikin Shege,sai na jawo muku abin kunyar da yafi na auren tsohon mijin kawata da wancen abin kunyar gwara na wannan ta juya ta fice ta sake cewa Kuma za a gani kwana nan Zan Fara amai,Kawu da Aunty Suka saki salati Aunty tana yau ga zamani karshen duniya kaga Dauda ka barta ta aure shi wallahi yaran yanzu basa Jin magana basu da hankali ba irin yaran da bane masu biyayya yaron yanzu sai hakuri da addua duk inda ka kai da tarbiya sai addua,Siyama dai bata Mana musu tana Mana biyayya tsakani da Allah tunda kaga ta dage a wannan gaskiya da matsala.
    Kawu yace ke har kin tsorata karya take baza ta iya ba ni nine ubanta bazan yarda ta jawo min zagi a gari ba,Aunty tace gaskiya ka ba yarinya zabinta mene aibun Aslam kaima wallahi butulu ne tunda har ya baka jari ka tsaya da kafafunka yanzu bama cikin wahala amma yanzu akan wata banzar Nusaiba da mutanen gari za kayi butulci,Dan Adam ai ba a iya Masa ko kayi ko kar kayi sai ka samu masu zaginka da masu yabonka haka duniya take bare Nusaiba da uwarta Wanda kowa yasan me Suka aikata ai Bari kaji ba a birge dan Adam
   Kawu tashi yayi a fusace ya fice daga dakin gaba Daya.

   Siyama an kifa Kai a jikin katanga ana sharbar kuka tana Jin fitowar kawu ta Fara Zan mutu ubana mahaifi da zaka dawo duniya bakin cikin yayanka shi zaisa ka Fadi ka sake mutuwa ta biyu,idan da zaka dawo duniya kaga yanda yayanka ya rike yarka gudan jininka da nan take zuciyarka zata sake bugawa,Ummata kiyi fatalwa kizo kiga yarki za ayi Mata auren dole yarku ana Mata rikon sakainar kashi,Kawune yazo zai wuce ta kusa da Siyama tace sai nayi cikin Shege Aslam Zan dinga zuwa,Kawu Yana fita ya samo bulalar dalbejiya ya dawo ya hau tsulawa Siyama ta sake barkewa da kuka Yana tafkarta yace Dan ubanki sa'anki ne ni,har kin Isa ki dinga furta mummunar kalma akan Namiji Zaki je ya Miki cikin Shege da Amadou na raye na tabbatar dukan da zai Miki yafi nawa,Siyama taji duka ba sauki Kawu ba wasa zaneta yake ta fada dakinta da gudu ta kulle,Aunty tace ka bani kunya Dauda wallahi ka daina Dakar min yarinya ai da gaskiyarta kowa yasan Aslam mutumin kirki ne mene laifinsa,Siyama tana daga daki ta leko ta window Ido duk hawaye tace dan ma ka samu suruki me addini

   Siyama yau yini tayi ba ci ba Sha sai kuka a daki,Aunty tayi tayi ta fito taki,Kawu Kuma ya shirya ma ya tafi Kauye sai bayan kwana biyu zai dawo,Aunty tana son yarta tace Siyama so kike Hawan jini ya kamani ko bari to na Kira Aslam a waya yazo idan yazo shi ai Kya bude ki fito,Siyama ta bar Wayarta tun safe a dakin Kawu Aslam Yana ta Kira ba'a dagawa,Aunty tana daukan Wayar Infinix Kiran Aslam ya shigo taga an sa My life,dagawa Aunty tayi Suka gaisa da Aslam yace Aunty Ina Siyama fa?Aunty tace dan Allah kazo kaga tun safe gashi har magriba tayi Taki Fitowa ta kulle kanta a daki ba ci ba Sha,Aslam yace sabo da me? Kazo gidan zan fada maka komai,Aslam yace gani nan,ya taho da sauri.

    Affan ne ya dawo daga Office Raudat ta fito tana tafiya a durkushe ta rike mara zata shiga mota tana cije lebe, Affan har zai wuce ya dawo yace  lafiya? Yaga Raudat tana hawaye tace asibiti zanje bani da lafiya ciwon mara nake yi, Affan ya bude baki yace ahh kice Kawai abin ne yazo,ke Haka kike naki? Rushing day ne? Raudat taki kulashi tana Jin kunya shi ba kunya ce da shi ba,key din motar ya karba yace na gaji amma muje asibitin na kaiki da kaina fatan kin Sa pad karki bata motar,Raudat ta shiga da sauri ya Shiga Suka tafi Suna tafiya yace Allah ya taimake mu da ba maza ne suke abin nan ba ai da mun Shiga uku,Raudat tana fama da kanta bata magana shi kadai yake surutunsa.

Na gaji bakwa sharhi yauAsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

        51-55

Official

By
AsmaBaffaPage naku ne

~s97863205
Aeesha


      Har Suka isa asibiti bata magana private ya kaita ya bude mota ya fito ya zaga ya bude Mata kofar hannunta ya riko ta fito da kyar Suka Shiga ciki,dake private ne komai kudi dandanan suka ga doctor,suna shiga namijj ne likita ya tambayi meke damunta,tace period ne duk wata nake fama fa ciwon mara Kamar Zan mutu da dai na daina amma yanzu ya dawo,Nan take likita ya rubuta wasu gwaje gwaje  suka je aka mata Affan ke biyan kudin da komai,suna dawowa wajen likita ya karbi test din ya duba yace ah kina da aure? tace a'a yace budurwa ce ke? tace ae,yace ai ke ba matsala ma kina yin aure Zaki warke, magunguna ya rubuta Mata yace ki dinga siyen wannan duk wata idan Zaki Fara,tace to Suka fito,takardar ya karba ya siyo magungunan kala biyu tana cikin mota tana jiransa Yana kawowa ta balle ta sha dake wannan ciwon bana karya bane
    Mota yaja Suka wuce gida tun kafin su je gida Taji sauki sai gata tana cewa kaini gidan wata kawata ba wacce Muka je rannan ba,yace ba inda Zaki je ke kullum a gidan kawaye gida zakije ki huta,Baki ta bude tana kallon ikon Allah kamar ubanta yace na gama magana bana Kuma magana biyu ya wuce gida direct,Shuru tayi har Suka dawo ta fito garau da ita yace take your medications properly ya wuce bangarensa itama ta Shige palonta tana hutawa.

    Sai dare ya leka ta window palonta jin kida na tashi yasan tabbas kallo takeyi a zaune ya hango ta a kasa ta mike kafafu tana cin gyada tana bushewa kallonta yake sosai ya furta liman me yasa baka zaman abokin Baban Raudat ba sai ka Zama abokin Baban Siyama,ko a suna ba hadi Raudha wow inda Manzon Allah ke kwance  haba wa ma zai hada,Liman bazai yuwu ba dole mu tafi Oyo state daga nan ma har Ondo duk ba matsala,Raudat ce taji Kamar ana magana kasa kasa window ta kalla ta ganshi harda dage Mata labile mikewa tayi a hankali ta karaso jikin window ya zama tana palonta yana. Nasa shima Suka tsaya suna kallon juna babu kyaftawa,juyawa tayi da niyyar komawa yace ya jikin a hankali,da sauki ta furta tana Murmushi tace na gode,ko Oyo zamu tafi ne? Harda rera waka wai Affan Ina zaka je ne.....Ni zani Oyo na kwana....tana ta dariya tace da gaske zaka rakani? a ranta tace ai kuwa da jibi jibin nan zamu tafi idan Kuwa baza ka raka Ni ba to gwara nayi zamana a nan Ina ganinka kullum,katse Mata Maganar zucin yayi yace da gaske nake yi Indai babu matsala ni sai nayi masauki a hotel ke kije gidanku,tace ae da gaske gwara naje gida naga Iyayena jibi ka shirya mu tafi,yace an gama zanje wajen ogana na sanar masa tace to tare da komawa ta zauna shima ya juya cikin palonsa ya zauna cike da farin ciki

     Aslam ne yayi sallam a gidan su Siyama Aunty tana zaune a bakin kofar Siyama Kamar me jira a fito a bata wani abu,Shigowa yayi gidan Aunty ta mike tana cewa sannu da zuwa Aslam,yace yawwa Aunty ya durkusa ya gaida ta da fara'a ta amsa masa sannan tace yarinyar nan daga magana tace Wai zaka Aiko da manya,Kawunta yace shi gudun abin kunya yake tunda ka auri babbar kawarta Kar a zage shi a gari,nace tunda Yara suna San juna ayi abin nan yace shi zagi yake gudu yanzu sabo da Allah ta bari Mana abi abin a hankali Kuma shine sai ta tashi hankalin mutane shine ta kulle kofarta tun sassafe ko ruwa bata Sha ba,Aslam a ransa dadi yaji yace a ransa ta min dai dai a fili yace zata fito ne kiyi Hakuri Aunty Ina kawun fa? Ya tafi Kauye sai jibi zai dawo ta window ya leka dakin Siyama ya ganta ta mike tsaye Kamar an kulle barawo a daki,Murmushi ta sakar Masa shima haka da Ido yace ta fito,jigin windown ta karaso cikin rada tace na fito? Yace ae,tawaye nayi fa,ba a yiwa iyaye tawaye  ba nace abi komai a hankali ba,kasa control nayi my anger tayi rising yace to tayi falling down please come out, tace a siyo min Madara a hada min tea Kamar koko sabo da kauri,yace naji fito Aunty ta ganki,na Basu hakuri? Aslam yace a'a ba yanzu ba sai sun Amince sai kice kawu Nima nayi kuskure ka yafe min kin gane tace ae tana dariya tazo ta Bude kofa,Aunty tana ji suna ta kus kus ba a Jin me suke cewa sai gani tayi Siyama ta fito tace marar ji wlh Siyama bakya ji,Aslam yace a Ina za a siyi madarar?Aunty tace wacce madara? Ya kamata ta Sha Abu me zafi hanjinta ya warware,Aunty tace Indai kayan shayi ne akwai na Kawunta karka bata kudinka,Yace ai ba a shanyewa Kawu nasa ba ya juya ya fita a wajejen ya tambayi kanti aka nuna masa ya siyo mulu madara,Milo,Lipton,da duk wani kayan tea manyan gwangwani kobwanne,Sugar cube ma wurin kwali goma ya siya musu ya kawo,Anty ta bude baki tace wannan hidimar fa? Yace naki ne ke da Siyama Aunty ku kyalewa Kawu nasa,Aunty tace dan nan duka haka an gode Allah ya bar zumunci,Ruwan zafi tazubowa Siyama a cup da spoon ta kawo Mata,harda siyowa da bread me kwakwa,Siyama ta loda Madara da Milo na musamman ta hada abinta murtuk tana yagar bread me kwakwa da ya hado dashi Yana zaune ta shanye ta cinye rabin katon bread din,yace dole ki dinga kiba wannan duk a cikin ki, tace ya zanyi da tsutsar ciki ta min yawa ba ni kadai bace,Aunty abincin rana a zubo min tun jiya banci komai ba azumi Kawai na kusa yi saura kadan,Aunty ta zubo Mata tuwon shinkafa miyar gyada, ta sake kawo na Aslam again,Siyama tana sanye da t-shirt dinta me gajeren hannu da skert wata kalar dark green da ado a jiki,hula ce ta zamani me kyau a kanta taci abincinta,Aslam kuwa ya koshi yau bai ci ba,sai wurin magriba ta rako shi kofar gida yace Zan tafi sai nazo,Banda rigima a bisu a hankali,Siyama tace baka San kawu ba idan yayi magana baya canjawa, Inshaallah a kanmu zai canja akwai rabo tsakaninmu

   Siyama tace yanzu da ka Haihu da Nusaiba da yanzu tana da cikinka,Allah ya taimakeni bata samu ciki ba ta haifar min masifar jininsu,Siyama tayi dariya ya juya yace Zan makara a masallaci ya ja hancinta kadan ya wuce Yana dago Mata hannu bye,Siyama ta tsaya tana cewa nace ya dinga hakuri sai anyi aure baya ji,ta koma ciki bayan sunyi Sallar Isha Aunty ta zaunar da ita tayi ta Mata nasiha da fada kamar ta dauka tayi luf da ita tace shike nan Aunty Zan gyara,Aunty tace ko kefa Haba Siyama kin girma ke ba yarinya ba ki dinga yi Mana haka tace na daina to,Aunty tace kinyi alkawari? Charity a ranta tace bayi ba a fili tace nayi Aunty tana murna...

   Satin Nusaiba biyu da aure tayi kyau ta Kara kiba duk da cewa tana nuna Hali amma Sufyan wani abin Yana Dan biye Mata,Mama ce tace ta fadawa Sufyan Kar ya fita yau zata zo tace to,Yana zaune tana kwance tayi pillow da cinyarsa tace Honey Mama tace karka fita zata Zo yau,yace ai kuwa ya Zama dole na fita Sabo da Ina da aikin da zanyi yau a Office in tana so tazo da yamma ko ta jira ni,Nusaiba tace what Honey Mama ce fa yace to sai na fasa zuwa aiki kin San muhimmancin aikin nan a wajena Kuwa mikewa zaune Nusaiba tayi tace kaga Malam saurara aure fa ba hauka bane, Dan Kana mijina baka da damar taka ni yanda kake so,dama Ina Jin haushinka nace muje Kasar waje Honey moon kace na jira sai ka Gama wani aiki na hakura Ina jira Shuru na dawo nace tunda America baza ta samu ba ka kaini Moroco Nan Africa Abu yaci tura okay na dawo nace ka kaini nan Niger ko banza maga Sahara,ga Sefa dinsu me daraja sabo da bakin Hali kana min story story, kace muje yawon shakatawa ka wani siyo min English gown me araha kana nufin na saka na fita ga latest nan da ake kawowa daga manyan kasashe na fada maka ka dauki rigarka ka kaita inda zaka kaita ban sakawa wani muje Abuja nayi me a Abuja,a Abuja Zan bude Ido mene a ciki na gida Nigeria fa,yanzu Mama baka kyale ba zaka ci min mutuncin uwa wlh kaci mutuncin uwata sai na rama a Kan taka,Tsaki Sufyan ya ja yace kina haushi Kamar karya kullum haushi wan wan wan banda lokacinki na fuskanci ke kanki na rawa ko jahilci yana taba ki ya dauki wayarsa da key din mota ya fice ya barta tana zage zage

     Tana haka Mama ta shigo tace lafiya Nusaiba daga aure? Tayani ji Mama wannan Sufyan din,Mama tace ki kwantar da hankalinki har yanzu fa bamu ci kwandalarsa ba ki Bari tukun mu Fara morarsa Mana zai ci ubansa kyale shi kin San fa wannan Bai kai Aslam kudi ba haka bai Kai Aslam kyauta ba,jeki ki shirya min girki me Dadi ki tabbatar yaji nama,Nusaiba tace Kai Mama suna dariya su a dole duniya ta samu sabuwa,Bayan Mama taci ta koshi tace Karo min karfin ac na Sha kafin na tafi,tana karewa gidan kallo tace oh God ta turawa yata kinyi dace Allah yasa ki Haihu da shi danki ya samu gado me tsoka,Nusaiba tace Ameen Mama kuma namiji Zan Haifa

    Sai Yamma likis Sufyan ya dawo ya iske Mama a Palo,Zama yayi tare da gaisheta da ladabi Yana Mata Sannu da zuwa,Mama tace dama yanzu nake Shirin tafiya gida sai gaka,dama zuwa nayi Naga gida sannan na muku Nasiha,Dan Allah ka zauna da yata lafiya Ni nasan yarinyata Yar albarka ce bata da matsala Matukar ka kiyaye hakkinta kayi Mata abinda ya kamata abinda ya dace tayi Murmushi hehehe abinda ya dace wato duk abinda ta nema kana yi to zaku zauna lafiya zaka sameta  me biyayya,Sufyan yace Inshaallah Mama,mikewa tayi zata tafi ya bata dubu goma ta karba tana tabe baki suna signa da yarta Nusaiba Wai baiyi abin arziki ba dubu goma kacal haka Mama ta tafi,tana tafiya Nusaiba ta rungumeshi tana shafa kirjinsa tace Kamar kudin da ka bawa Mama sunyi kadan,Sufyan Yana son Nusaiba shi yasa in tayi wani abin shi baya ganin laifinta yace karki damu idan munje gaida ta sai a Kara mata yafi haka tace sai mijina Suka haura sama suna dariya cike da so da kauna.

     Aisha bayan barin da tayi bata fi wata ba ta sake samun wani cikin,ai Bashir Yana ganin ta Fara laulayi ya sameta a zaune duk ta gama lalacewa,yace Aisha tunda ke baki da kwakwalwar ganewa na nuna Miki haske kin kasa fahimta bari na fito kuru kuru kiji bana son haihuwa dalilin da yasa na auro ki naji labarin tunda Kika Yi aure da tsohon mijinki baki taba haihuwa ba ni nafi son mace juya,tunanina ke juya ce shi yasa na aureki sabo da na huta da jikinki amma ana taba ki sai samun ciki daga anyi abu sai ciki bazan iya ba,idan kina so mu zauna tare ki zubar da cikin nan idan Kuma bakya so to kije na sawwake Miki,Aisha tana kuka tana nadamar barin gidan Farooq tace ina son cikina,ya nuna Mata kofa yace jeki na sakeki saki daya ya rubuta takarda ya Mika mata,Aisha tana kuka ta hada kayanta sai gida.

    Ummanta tana ganinta gabanta ya Fadi tace Aisha me Zan gani ba dai an sakeki ba? Aisha ta fashe da kuka,Umma tace ba kece da kuka ba nice da kuka Aisha,yanzu Zaki zo ki addabeni ki buwayeni ki damu rayuwata,ki dinga wulakantani nayi nadamar rabaki da gidan mijinki Farooq,Nice na zugaki laifina nane dama ance Indai yarinya ta wuce zaman gaban iyayenta to idan ta dawo sai ta kusa dukan uwarta,Aisha tace ai kece Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala kalli yanda na koma sai kace Jimina,wa yace ki yarda da shawara ta,ai da kina da hankali tunda ni Kika ga na kauce Hanya sai ki gyara min ai Nima ban wuce ayi min fada ba tunda na Fara manyanta kullum kwakwalwata sake kwancewa takeyi Saura kadan Aisha tayi dariya yanda Umma tace kwakwalwarta ta kwance, Aisha ta kwashi kayanta ta koma ciki wani sanyi taji a rayuwarta.

   Farooq Kuwa da Nabeela amarci suke Sha amma zuciyar Nabeela Babu dadi tunanin Affan takeyi Ina zata ganshi ta nemi yafiyarsa sanna son Affan take kamar hauka ko sex sukeyi da Farooq sai ta tuna Affan take gamsuwa sunayi tana ganin Farooq kamar Affan ne ke Mata sai tayi ya jin Dadi,Indai bata tuna Affan ba to baza ta gamsu ba ranar, gashi kunyar Affan take tunda yazo ya samu an daura Aurenta da dan Uwansa bata sake farin ciki ba a rayuwarta wannan yasa ta tsani Yusuf gaba daya basu zauna lafiya ba,ta dinga nunawa Yusuf halin ko in kula tun Yana binta har ya gaji Suka Fara fada kullum basu da kwanciyar hankali har ya koma wulakantata karshe ma ya saketa hakki ne ya Kama su kwata kwata Allah bai bari sunji dadin auren ba,Farooq Kuwa zuciyarsa tana ga Aisha Kawai gangar jikinsa ce a wajen Nabeela nan ma dai Nabeela bata Yi dace ba.

   Kamar yanda Raudat tace Affan ya shirya suje garinsu ranar na zuwa wani wanka Affan ya dauka da jakarsa ta kaya me kyan gaske in ka ganshi ka rantse turai zai tafi,Raudat kuwa wata doguwar Riga tasa na leshi dinkin manyan Mata masu ji da kansu ta Sha dogon takalmi da Jakarta ta kayan sawa sai hand bag komai coffee and white,tana Fitowa ta mikawa Affan flight ticket,wani yaron Affan ne yazo a motar Affan ya kaisu airport suka shiga jirgi ranar farko kenan da Affan ya Shiga jirgi tsabar gayu sai kace Wanda ya shekara dari Yana shiga yanda yake tafiya Yana gabatar da komai nasa,ga sit dinsa ga na Raudat suna zaune idan ya saci kallonta sau daya sai ya dauke Kai itama sai ta juyo ta saci kallonsa haka suke faman Yi har suka sauka lafiya,suna zuwa wani driver ne da mota me tsada Yana jiranta,suka Shiga mota da Affan ta Fadi sunan wani Hotel a garin ta rigada ta Masa booking Bai kashe kwandala ba,suna zuwa Hotel ne me tsada da kyau har room dinsa sannan tace Zan tafi zan dinga kawo maka abinci daga gida idan Kuma kaci a nan baka bukata ka fada min a waya tana kallonsa tana Murmushi,yace to sai ki ta min abu da kudinki karfa Watarana a min gori ni bana so nasan halin Mata bana Jin Dadi ki dinga kyaleni Ina biya Mana please bana so idan ba Haka ba Zan koma gida Kawai kin maidani yaro,Dariya tayi tace afwan to ka huta ,yace karki kawo min abinci nifa ba yaro bane ba Kuma duhun Kaine dani ba sannan Ina Jin turanci,tace to sorry na daina tace zanzo da dare muje yawo ta Kai hannu zata ja Masa gemu ya goce yace wannan fa raini ne ke ba matata ba sannan ba budurwata ba Zaki lalatani ya juya tare da rufe kofarsa,ta tafi tana Murmushi dama tsokanarsa tayi tasan fadin ransa.

     Yau Kawu yana dawowa Siyama ta masa Sannu da zuwa ya amsa ta karbi kayansa ta Kai daki sai tsarabar Kauye lafiyayyen nonon shanu kindirmo cikin katon wani bowl,Kwan zabi,etc Aunty tace Sannu da zuwa Suka shiga daki Siyama kuma ta Kira Aslam,kashewa yayi tare da kiranta back sallama tayi ya lumshe Ido yanda muryarta ke tafiya da Imaninsa,inyini yaya ya aikin,lfy Alhmdllh ya furta Yana gyara kwanciyarsa saman kujera tace Kawu ya dawo yanzu,yace Allah mun gode maka tunda ya dawo lafiya daga nan Suka fada hirarsu ta masoya har Kawu ya fito yayi wanka tare da gabatar da Sallar Isha Yana Jin Siyama ta makale murya tana ta yiwa bawan Allah shagwaba,bata San yana jinta ba,tana kwance a tsakar gida suna Palo shi da Aunty ita Aunty ma bata ji me take cewa ba amma Kawu hankalinsa na kanta,karaf yaji tana cewa kasan Ina sonka nima amma sai kayi ta cewa Kai kadai kake so na gobe zaka Zo da Yamma,yace bayan kin daina zuwa layin mu ma,tace zanzo ne ,Kawu ya zaci Siyama gidan Farooq take shiga bai san ko taje unguwar ba a waje suke Zama Kuma tunda Nusaiba ta bar gidan sau daya taje,Kawu a ransa yace wato Siyama ba Wasa take ba zuwa zatayi ya Mata cikin shegen amma gobe zai gani idan zata fita, gajiya yayi da ji ya fito,Siyama tana ganin ya fito da Fushi tace Zan kiraka Yaya ta kashe wayar amma sai tayi kamar bata kashe ba taci ga da cewa ka jirani gobe zanzo gidanka da Yamma,Dariya tayi tace hmmm sai dai na zo,kawu yace Siyama zo magana tayi Aslam Kawu na kirana ka kirani anjima
Kawu ne ya daka Mata tsawa Allah yasa dama ta kashe wayar, yazo ya fisge Wayar tunaninsa wayar suke da Aslam ya Kara Wayar a kunne Yana masifa yace duk abinda ya samu yata Kaine wallahi Matukar aka lalata min yarinya Kaine ya Danna wajen red ya kashe bai kula ba dama a kashe take,yace ke Kuma Siyama duk abinda zaku yi kuyi bazan bashi ke ba ya juya ya koma daki.

   Siyama ta fashe da kuka kasa kasa karshe ma ta koma dakinta ta kwanta,washe gari Kawu ya kafa ya tsare Yana jira yaga ta Ina Siyama zata fita,4pm yaga tayi wanka ta shirya ta saka hijab tace Aunty zanje karbo Miki Humrar, Kawu yace gidan ubanwa Zaki je,Ashe da gaske kike Siyama gidan Namiji Zaki je,tace nife ba can Zan je ba jiya ma kawai fada nayi amma na kashe wayar,Ni kike tsokana sabo da ni sa'anki ne ya taso zai sharara Mata Mari tace a'a bada Kai nake ba da Kaina nake tsokana,yace to daga yau ba inda Zaki je na hanaki fita ko kofar gida Kuma ki fadawa Aslam din Kar ya sake zuwa min gida tunda ba alheri kuke shukawa ba,ke Zaki iya sani inyi abinda banyi niyya ba.

  Siyama bata ce komai ba tace kayi hakuri kawu ta koma ta zauna a dakinta,Aunty ta fito tace wallahi abinda kakeyi ba tsari gaskiya duk abinda yaron nan yayi maka idan yaji ka hanashi zuwa gidan nan ai mutuncinka zai zube dan Allah karka Yi haka ai da kunya,Siyama baza ta aikata ba wlh ba abinda zai faru me yasa kake haka wai,Kawu ne ya mike ya fice,Yana fita ya hadu da Maman Nusaiba ta dawo daga unguwa ta Masa kallon banza tace oh Mallam Dauda sai muka ji Kuma wannan matsiyacin zaka aurawa Yar rikon ka sabo da ba yarka bace za a zalunci yarinya a bata me karayar arziki,da yarka ce ai da baka yarda ba,Kai Kam juya marar amfani,ai Kai hoto ne a duniya mutum mutumi tunda baka haihuwa mene amfaninka baka San ciwon haihuwa ba baka San zafin da ba,in Banda Kai kwangiri ne kana gani 'yata ta fito sai da muka sa ya saketa sabo da bakin talauci shine Kai zaka Kai Yar wani sabo da zalunci me za aci da Aslam,ka duba Nusaiba yanzu ta shiga daula fantamawa takeyi yanda take so, tsohon banza ta juya ta wuce,Mamaki ya Kama Dauda ya bude baki haka Kawai shi ba kulata yake Yi ba ta bude baki taci mutuncinsa haka ta tafi,yace irin wannan annoba ne ga al'ummar duniya wannan matar Shehu Yana fama ai fasa fitar yayi ya koma gida,Yana zuwa ya fara bawa Aunty labari kaf har gwadawa yake yanda Mama tayi Masa,Siyama ta kyalkyale da dariya ta dinga dariya tace hakkin marainiya ne,hakkina ne wlh a guji batawa maraya rai gashi Allah ya saukar da aya,wlh Kawu Ina jiye maka Kar rabo ya kasheka lokacinka baiyi ba,rabo kisa yake watakil sai baka raye za ayi,gwara ka hakura Kar lokacin zuwan 'ya'yana duniya ya matso kazo ka hana zaka iya mutuwa,Kawu tunawa yayi yanda akace rabo na kisa tsoro ya kamashi Kar ya mutu,Shuru yayi tare da lulawa tunanin duniya,Siyama ta dinga dariya ta mike ta ebo kindirmo ta zuba sugar tana juyawa tana cewa rai ,Kawu yayi Shuru Aunty tace ayi bawa da kafiya haba Dauda.
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

         56-60

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

UMMY M
MARYAM BASHIR
MBELLO


     Dauda Yana zaune bai ce komai ba,Siyama tana kallonsa ko zata ji zai ce ya yarda amma sai ji tayi yace idan na mutu ma kwana na ne ya kare dama Allah yayi kwanana ya kare sabo da haka Ina Kan bakana Kuma karki sake yazo min gida,kwana uku Kawu ya hanata fita Kuma ya hana Aslam zuwa zance,Siyama duk ta Shiga duwa,Aslam ma Sai dai suyi waya a boye kasancewar yace sai ya kwace Wayar in ya sake ji suna waya,ai Kuwa Watarana Kawu ya Kama Siyama tana waya da Aslam,tana tsaka da waya sai ga Kawu Katsam ya Miko Hannu yace bani Wayar,Siyama tace Yaya Aslam karka kirani idan kaji Shuru Kawu yazo zai kwace Wayar,Aslam yace alright bashi I love you karki yarda a raba mu please,tace Inshaallah Muna tare har abada,Wayar Kawu ya fisge ya kashe ta gaba Daya ya juya ya tafi da wayar, Kawu Yana Fitowa  ya fice daga gidan,Siyama ya bari tana kuka Aunty ce ta shigo ta zauna a gefen katifar Siyama tace kiyi hakuri Siyama,duk aure da Kika gani idan aka Yi sak ba wani kalubale to bai ma fiye Danko ba ko Mene zaka Nema idan da nasara sai an samu matsaltsalu sai an Sha wahala,abinda nake so dake kici gaba da addua idan Aslam ne Alkhairi Allah ya baki shi idan Kuma ba Alkhairi ne bane Allah ya zaba miki mafi Alkha....ba wani mafi Alkhairi Aslam ne Alkhairi na Kawai idan ana son zaman lafiya a bashi ni tun kafin na kangare na daina Jin magana gwara ma ki fadawa mijinki tun kafin na Fara fetsara a gidan nan,Aunty tace to fa ku Yara idan kuka tsunduma bakwa Jin Kira ai sai kiyi tunda bakya Jin magana..

      Siyama ranar haka ta yini sukuku ko aiki bata taya Aunty ba,Aslam kuwa gidan da Mum take yaje ya sameta a Palo ita Daya,bayan ya gaida ta,Mum tace Aslam kamar kana cikin damuwa kwana biyu Naga Kuma kamar ka Dan rame lafiya? Marairaicewa yayi sannan ya Fara bawa Mum labarin komai,ita Mum Murna takeyi danta ya samu mace,yace Mum kina murna baki ji me nace ba Kawunta yace bazai bani ita ba Kuma ya kwace Wayarta sannan yace Kar na sake zuwar Masa gida,Mum ta kalli Aslam tace Inshaallah zai hakura karka damu ka kwantar da hankalinka,Mum taya hankalina zai kwanta idan ban sameta ba fa ya zanyi,Ni ban taba son wata haka ba,ka kwantar da hankalinka nace Inshaallah zai hakura Kuma ko waye haka zaiyi  a matsayinsa na uba babbar kawar yarsa dole ya hana,Addua zaka Yi sosai,Aslam yace yanzu Mum baza kije min ba? Wannan yakin naka ne Aslam ka dage kawai,Shuru yayi Kawai ya zuba tagumi ya tsinci muryar Mum tana cewa Amma na maka sha'awar Siyama,Ki daina sha'awar min Mata Ni kadai nake son abata Wai yaji haushi tace baza taje Masa ba, Mum ta dinga dariya tace to aci gaba da sonta lafiya,tashi ma yayi ya bar gidan.
   Bayan kwana uku Aslam duk ya wani fututtuke ya tashi hankalinsa ya rasa inda zai sa Kansa rashin Jin Siyama,itama bangaren Siyama haka.

    Zuwa Yamma Siyama da Aunty Suna tsakar gida saman katuwar tabarma suna Jin radio Kawu Yana zaune saman kujera aka sako wakar soyayya Siyama ta mike zaune tana saurar wakar
   Mawakiyar tace kaine      tunanina,Siyama tana bada amsa uhmmm Aslam ne wannan wakar sak tamu, mawakiyar ta sake furta Kaine ruwan Sha na,Siyama tace me gardi ma ruwan, kaunarka tayi girma a zuciya tace tabbas haka ne Aslam dina,Zo ka kula Dani me so na inji me wakar, Siyama harda hawaye tana Jin wakar Kawu ya tsaya kawai Yana kallon ikon Allah shi da Aunty, kuka ta saki sosai tasa tafukan hannayenta tare da rufe fuskarta,Aunty tausayin Siyama ya kamata,tana shesheka tace amma Aunty ke da Kawu ba auren soyayya kuka Yi ba da alama baku San mene so ba,Kawu ta kalla tace Kawu kasan Kuwa me nake ji a raina ka tausayawa yarka Kawu ,shi kuwa ko kulata baiyi ba.

    Zuwa dare Aslam ya kasa daurewa yazo da Kansa gidan ya Samu Kawu ya tafi wajen abokansa Bayan Sallar Isha,Aunty tana daki sai Siyama a tsakar gidan zaune ta hada Kai da gwiwa,Aslam da Kansa ya shigo gidan ba Sako ba,tana Jin taku da kamshi ta dago da sauri,Siyama ta mike Zumbur tana kallonsa,tsoro take ji Kar Kawu ya shigo ya samu Aslam hannunsa ta ja da sauri tayi maza ta turashi dakinta,tana turashi ciki Kawu ya shigo gidan Aunty ma ta fito tayiwa Kawu shimfida a tsakar gidan Sabo da ana zafi a waje suke kwana,Siyama ta dora Hannu a Kai tana kallo Kawu ya kwanta,Aunty ma tayi nata shimfidar gefen Kawu ta kwanta,Siyama ta Fara tunani ta ya Aslam zai bar gidan oho,Aunty tace kin tsaya Mana a kai ke baza kiyi shimfidar ba? tace sai can anjima,Kawu yace bar algunguma ita ga Yar soyayya,Siyama dakinta ta Shige ta kulle kofa harda sa key sun zaci duk fushin soyayyar ne.

    Ta samu Aslam a katifarta a zaune,a kasa ta zauna shi Yana katifar tana Murmushi wani sanyi take ji Yana ratsa ta,kallonta yake sanye take Riga da skert na Atamfa masu kyau,Ina yini tace tana Jin kunya amsawa yayi kasa kasa,ya furta ya kike kwana biyu naga ma kalau kike ai ko missing Dina baki yi kawai cin abincin ki kike Yi kina koshi Ina can hankalina a tashe,Siyama tace ka taho min da wata Wayar? yace no Kawu ya hana muyi hakuri yanzu idan na baki wata zai ce mun raina shi bai kamata ba,Siyama tace to shike nan ta turo baki tana cewa ai ba ni kadai ce na damu ba na daina damuwa ma,na daina tunani Kawai uzurina zanyi,dariya Aslam yayi Wai masifa takeyi nan bayan kasa kasa take magana a hankali Kar aji wai,da dan karfi yace haka zaki min,zaka jawo Kawu yaji kayi kasa kasa ta furta tana rufe baki da hannunta, Murmushi ya saki hankalinsa kwance ko a jikinsa yace ki daina fara'a a gidan nan yarinya karki bari a hanaki Saurayinki idan Kika yarda babu Wanda ya Isa ya aure ki,Siyama tace ai Ina ta yin tawaye yau ma kin cin abinci nayi sai 2pm,dariya ta Kama Aslam yace ai baki gwaninta ba dan 2pm kowa lokacin yake cin na rana,tsutsar cikina ta tashi kwana biyu rashin mutunci suke ji,dariya yayi ba shiri yace to kici ki koshi karki zauna da yunwa kinji,Siyama har da kuri tace gobe za aga bala'i sai 4pm zanci abinci,Aslam yasan baza ta iya ba amma yace ni dai na fada Miki karki sake a baki wani sai ni,tace af bata bakinka kake Yi ai ka lashe zaben zuciyata ta nuna kirjinta ta bangaren hagu tace Kaine a nan barin ta sake nuna hagu tace nan ma ka Sha kwana ta nan barin Kaine,tsakiya ma Kaine ka gama mamayeta,dariya yayi yace na gode haka nake so nima haka ko Ina kece  you are my world,yace Ina so na tafi,tace ai kuwa Kawu basuyi bacci ba ka jira kawai,Allah yasa da motar Sabeer nazo tare muke , Alhmdllh tace suna ta hirarsu ta masoya ko bacci basa ji har Suka shiga labarin duniya,Siyama tace ta wani Yoruba malamin mu yace babu makaryaci irin bahaushe yanzu idan bashi da lafiya kana cewa ya jiki zai ce da sauki bayan 20mnt sai aji ya mutu,dariya Suka yi Aslam yace su ai idan ba sauki Kawai ba sauki mu musulmai Kuwa ba haka tsarin musulunci yake ba,Wai yasan ba sauki sai yayi karya yace da sauki amma sai aji ya mutu,suna ta nishadinsu basu sani ba sai gani suka Yi 11:30pm,Siyama tace bari na duba maka ko sunyi bacci,Fitowa tayi a hankali taje ta leka fuskar kawu har da sa Hannu ta fifita fuskarsa Shuru Yana ta baccinsa,Aunty ma haka ta sake lekata a hankali tace Aunty Aunty, tana ta bacci shuru da sauri ta koma ta fadawa Aslam sunyi bacci muje,Takalmansa ta kwashe ta rike a hannunta Suka fito Yana gaba Yana tafiyarsa normal har Suka je bakin kofa a hankali ta bude Masa kofar gidan ya fita sannan ta ajiye Masa takalman ya saka ya dawo zauren again sai kace maye tace ka tafi Kar Kawu ya tashi ya Kama ni,rungumeta yayi kamshinsa ya cika Mata hanci me dadi, tace Kai bafa kyau amma shedan yasa tayi Shuru harda lumshe ida ta zagaye shi da hannayenta dagata yayi sama a haka,dariya ta danyi ya ajiyeta a kasa sannan ya janye jikinsa tare da furta good night Yau ki kwana kina mafarkina Kuma ki ganni na aureki Muna soyayya,dariya take kasa kasa tace hmmm ai da na fika murna Zan hango mu a Palo ina zuba maka abinci,zanyi na ganmu a kitchen Muna girki,Aslam yace ban iya girki ba fa ni,dole ka dinga tayani Kuwa Indai kana gida,ki dinga Jin tausayina Baby,ai sabuwar hira Suka dasa ya manta ma Sabeer Yana jiransa a mota,yace zanzo jibi da dare yanzu na gane yanda zamuna yiwa su Kawu tace to sai kazo dare yayi fa 12am ,yace Kuma Sabeer Yana jirana ba,fita yayi ta tsaya a bakin kofar tace sai jibin Zan jiraka yace ko kiss Babu?

  Tace sai a gidanka yace Allah yasa ta furta ameen Hannu ya Miko Mata ta kai zasu tafa ta janye,dariya ta bashi ya tafi gari duk ba mutane,sai da ya kule sannan ta maida kofa a hankali ta rufe ta dawo tana shigowa Kawu ya farka tare da hasketa da touchlight me mugun haske kamar ta Kama barayi,yace daga Ina kike? tace kofa naje rufewa na zaci ba a rufe ba Kuma ma Ina zanje babu mayafi,Kawu yace to wuce ki kwanta tace to Sum sum ta wuce dakinta ta kwaso kayan shimfidarta ta shimfida a gefen Aunty ta kwanta cike da nishadi sai Murmushi takeyi ita Daya.
    Aslam kuwa Yana komawa Sabeer har yayi nisa a bacci cikin motar ya tashi Yana masifa a Ina ka zauna haka? Na fada maka fa ka shirya jirana domin Zan iya dadewa tunda gidan Zan shiga nan ya bashi labari a dakinta Suka buya,yace amma ka cika Dan Iska Aslam tab wannan ai ganganci ne,Tsaki yaja yace ba abinda bazan Yi ba akan Star dita,zaka ga star ya yiwa mota key Suka tafi gida a gidan su Sabeer ya kwana yau.

    Siyama kuwa ta kwanta yau soyayya ta hanata bacci in Banda Aslam ba abinda take tunawa a ranta Katsam taji Aunty tana kiranta kasa kasa kamar munafuka,Siyama tayi Shuru a zuwan bacci takeyi,karaf a kunnen Siyama taji Kawu Yana magana kasa kasa tayi bacci? Aunty tace ae yayi nisa ma baccin,Siyama harda Jan munsharin karya,Kawu yace tashi mu tafi Aunty ta mike kamar barayi Suka Fara tafiya Sadaf Sadaf suka fada daki,Siyama tace iyye tana dariya a boye tace an shiga Uku yanzu Kawu dama bai bar Harkar nan ba ya tsufa ai wannan sai yara,can Kuma tace na tuna Aunty da kuruciyarta itama tana bukata,lallai Kawu dama haka yake Dan is....bakinta ta rufe tace amma ni ya hanani sakewa da masoyina shi ya ja tasa sun tafi duniyancinsu ba komai akwai Allah.
    Washe gari da safe farkawa tayi taga Auty a shimfidarta kawu ma a tasa,Siyama tace wato da aka gama sai aka dawo dama haka ake Mana wayo,yau zanga tsiya wlh kaima baza kaji Dadi ba Allah ya kaimu dare cewar Siyama,Kawu yace ke sai Rana ta fito ne zakiyi Sallah? ta mike taje da brush tayi tare da Alwala ta koma dakinta bayan tayi sallah taci gaba da baccinta hankali kwance.

    Wani Daren Yana zagayowa Siyama ta koma palon Aunty tace yau a nan Zan kwana Naga ta tsiya,Siyama tayi baccinta Aunty ba yanda bata Yi da ita ba akan ta koma dakinta taki tashi Wai ita a nan zata kwana,Aunty fita tayi inda suke kwanciya a tsakar gida ta guntsawa Kawu tace nifa yau a matse nake da wuri nake so ga Siyama ta kwanta a palon tace ita a nan zata kwana,Kawu yace rabu da ita bata ji ai,Aunty tace ni a daki Zan kwanta ma  can cikin uwar daki,Kawu yace jeki idan baccninta yayi nisa Zan shigo,ai Kuwa Siyama Taki  bacci tayi alwala ta saka hijab ta Fara Nafeela ai da tayi raka'a takwas sannan ta zauna saman Sallaya,ga dare Yana yi gashi ko yaushe Kawu ya leka tana zaune a sallaya tana lazimi, window din bedroom din Aunty Kato ne a bude yake dan tsaf mutum zai wuce Siyama tana can bata sani ba tuni Kawu ya haura ta window dama matan aure da iya sanin makamar wayo Aunty tasa kawu ya rufe Mata Baki Kam karma wani sauti ya fita suka gama abinsu ras Kawu ya sake haurawa ta Window ya dawo saman katifarsa Siyama Bata San me akeyi ba tana Palo,Aunty ta gani ta fito tace Siyama gwanar addini a dinga sawa da mu,yau zafin da akeyi yafi na jiya bari na sake sheka ruwa a jikina,Siyama a ranta tace aha yau baza ku Shana ba sai dai ku kwana a haka, Aunty kam Kawu ta zubawa ruwa yayi wanka tare da tsarkake jikinsa Aunty ma tayi Suka dawo Suka kwanta aka bar Siyama bau a Palo har bacci ya kwasheta a nan.

    Washe gari Kuwa gani Suka Yi Siyama tana ta kwalimar dakinta ta Masa wani uban gyara na musamman ta kunna turaren wuta ta kulle ko Ina ya dauki kamshi, da Yamma tasan Kawu bazai bari ta fita ba abinda take so ta yiwa Aslam duk bazai siyu ba dole Wayar Aunty ta dauka a boye ta Kira kawar Aunty me yin snacks na gidan biki tana yi ma ana order,tace tayi Mata meet pie me dadin gaske da Samosa sannan ta siyo lemo juice babba ta hado da shi ta bawa yarta ta kawo mata,idan ta kawo sai ta bata kudin ta kawo Mata Suka Yi lissafi tace ana yin Sallar Isha take so a kawo matar tace to ba damuwa
   Siyama sai gaf da Sallar Isha ta fesa wanka ta saka doguwar rigarta ta larabawa wata maroon taji ado kawar Aunty ce ta bata da taje aikin Hajji bara rigar tana Mata kyau shi yasa take Adana ta,ta yafa mayafinta taje ta shafa humrar Aunty ta dan zubo wata a Yar karamar kwalaba,Aunty tace ke Kuma Ina Zaki je? Siyama tace to bana fita an hanani fita Kawai sai na bar kayana su rube bana sakawa,Kawu Yana jinsu ya tashi ya tafi Sallar Isha,Aunty ta shiga daki Sallah aka kawowa Siyama order dinta ta karba a boye ta biya kudin Yarinyar Yar budurwa Siyama ta kalla tace ungo kudin kice na gode sauri ki ta tafi bana so Aunty ta sani,Yarinyar ta tafi da sauri,Siyama ta Kai ledar daki ta kwaso plate biyu ta zuba meet pie din da Samosa a plate ta rufe ragowar ta boye a abinta ta ajiye lemo da cup kusa sannan ta fice,sai ga Aunty ta fito da Hijab tace zanje gidan kawata Jamila yarta ta haihu sai 10pm Zan dawo ki kula da gidan,Siyama tace to Kawu fa? Aunty tace baki ji yace yau gidan liman zai je ba abokin babanki ya gayyace shi walima an Haifa Masa yaro ai Kawunki yau sai an ganshi, tana murna dake gidan su Jamila ma ba nisa a layin ne tace Aunty a dawo lafiya tace yawwa ta fice,tana fita Siyama ta fito tayi sauri ta karbi wayar me shago ta shigar da number Aslam ta Kira,bugu daya ya daga ta matsa gefe tace ka taho kuwa? Yace gani a layin ma Sabeer ya saukeni zai dawo ya daukeni,tace kace ya dawo tara da Rabi,yanda tace haka aka yi,tana waya sai ganin Aslam tayi a kusa da ita Yana kallonta,me shagon ta mikawa wayarsa ta Masa godiya Suka jera Suka tafi,Yana faman kallonta yace yau kin Sha kyau haka ni aka yiwa kwalliyar,Murmushi tayi tace ae Suka Shige gidan har dakinta bata kulle kofa ba tasan ba kowa ta kawo Masa pie din da lemo,yace harda tanadi tayi dariya Yana ci yace yayi Dadi kuwa suna ta zuba hirar soyayya abinsu 9:30 Sabeer yazo suka tafi Siyama harda rakashi har cikin mota Suka gaisa da Sabeer ta koma gida ta cinye Su samosarta da lemon tayi Shirin bacci tayi kwanciyarta har Aunty ta dawo.
   Haka lokacin na tafiya Aslam duk Sanda yaga damar zuwa sai sun faki idon Aunty da Kawu suke samu su Shige su Sha Hira ya tafi basu taba Kama shi ba.

    Siyama ta gaji da halin Kawu tace wlh yau Zan Bari ya kamamu,ai Kuwa Aslam yazo yana dakinta dama da shi aka shirya plan din,bai taba kwanciya a katifar ba sai yau,Suka dinga hirarsu Kamar ba matsala ko an gansu da karfi yanda kowa na gidan Yana ji har dariyarsu ana ji,Kawu Yana tsakar gida daga shi sai dogon wando da Singlet,Aunty ta mike ta zauna tsoro taji ma ko aljanune a dakin Siyama suke Hira maganarsu ta fito fili,Kawu yace Siyama ke Siyama,Siyama Suka Yi kus Kamar ruwa ya dauke can tace naam ta fito har da nuna rashin gaskiya,Kawu ya mike ta koma dakin da gudu zata turo kofa Kawu ya Danna da karfi Siyama tana dannawa amma yafita karfi ya Bude ta karfi ya shiga ya Iske Aslam a kwance sanye cikin shadda Yar ubansu,Kuma ko a jikinsa ko tsoro bai ji ba tunda Yana sani,Kawu ya Fara salati harda rufe Ido ya fito gashi Yana Jin kunyar Aslam sosai bazai iya ci Masa mutunci ba,Aunty ma ta leka ta dawo baya tana salati tace kaga abinda nake fada maka ko da alama ba yau Suka Fara ba na dade Ina zargin Siyama dan Kuwa akwai Sanda takeyin kwalliya ta musamman da dare to gashi ka gani da idonka har cikin dakinta,Siyama ta fito tana kukan karya Dan Allah Kawu kayi hakuri dama Kaine ka hanashi zuwa shine nace ya dinga zuwa Muna buya Watarana ma Sai 2am yake barin gidan nan laifinka ne Kawu,Aunty tace yanzu kaga duk abinda zai faru ma ya faru,Aslam ne ya fito Kamar gidan Ubansa ko ajikinsa Yana takunsa,Siyama tace ai Kaine Kawu.....Mari ya zubawa Siyama sabo da Takaici,Aslam ya riketa da sauri,ta juya Masa Fuska tace tayani gani fuskata Kuwa tana nan,Aslam yace tana nan sosa min wajen,yasa Hannu ya Sosa Mata,Kawu yace Aslam Ina ganin mutuncinka ka sani Allah Yana ganinka,yata ce duk abinda ya sameta Kaine wlh,Aunty ta ja tsaki tace mene ma bai faru ba kana gani dai wlh ka Amince ayi sauri ayi bikin nan tun kafin masifa ta danno Mana gida,Kawu ya tsorata matuka tunda Aslam yake iya zuwa cikin gida har dakin budurwa su raba dare to komaima zai faru,Kawu cikin bacin rai yace Dan ubanki kinwa kanki Babu ke ba kayan daki cokali bazan siya Miki ba,Kai Kuma gobe gobe ka turo manya ka sani ficika bazan kashe ba Kuma babu taro auren bazawara ma Sai yafi naku armashi in Banda Yan daurin aure kar naga uban kowa a gidana,Kuma Babu me Kai maka Amarya ana daurawa kazo ka dauketa,Aslam yafi kowa murna a ransa yace mun Zama turawa Haka ake so ai,Siyama tace Wlh Kawu ba abinda mukayi Wanda ya sabawa Allah,Kawu yace ai tun daga Kebewa da kuka Yi daki Daya Kun sabawa Allah kuci gaba da istingifari Kawai mutanen banza sakarkaru Kai ka girma Namiji ka dinga biyewa mace,Aslam harda durkusawa yace dan Allah Kawu ku yafe Mana,Itama Siyama ta durkusa baza mu sake ba,,Kawu yace kanku kuka yiwa bazan siya Miki komai ba ko tukunya baza a Dora ba,Babu shagali ba gayyata,Aslam yace hakan ma yayi mun gode,karma ku gode ku tashi ku bani waje,Suka juya Suka fice Siyama ta diinga murna,Aslam yace Ni dama ban damu da wani taron Iska ba,Siyama tace shike nan ba anko ba gayyata ta furta da tausayi,Aslam yace nan da sati za a daura kin Zama amarya yau bazan Yi bacci ba, Siyama tace Ina waye ya bani bacci ai sai addua,Aslam yace yanzu an gama yakin karshe ki Fara bawa kawu hakuri lokacin bashi hakuri yayi ai suka Yi dariya ya Mata sallama ya tafi.
  Siyama ta shiga gidan harda durkusawa Kawu tace Mahaifina ka yafe min,sai yau Wai zata mahaifinta ta bawa Aunty dariya, tace Kawuna ka yafe min na tuba bazan sake ba dan Allah Kar kayi Fushi dani sai Allah ya tsine min na tuba,tashi ki bani waje Yar banza fitsararriya tunda nace zan bashi ke Kuma mene na damuna,Siyama tace Kawu ka sa min Albarka to,duka ya Kai Mata ta tashi da gudu tana dariya ta koma dakinta sai tsalle da murna harda cewa Babana dake lahira yayanka Amadou Yana rike yarka Amana yanzu,su Kawu suna jinta tana ta hauka iri iri.

   Raudat bayan taje gida ta huta suna ta hira da kannenta kanana su biyar da Mamansu,haka Babansu ya dawo daga Office tana murna yace a'a Raudat zuwa haka ba sanarwa tace Papa nayi missing naku shi yasa nazo ranar Monday Zan koma,yace Alright ya aikin naki? tace Alhmdllh Papa na iskeku lafiya yace lafiya lau,ciki ya shiga ita Kuma taje tayi bacci ta huta da Yamma lis tayi wanka ta fito cikin hadaddun kayanta English fited gown ta Sha me dogon hannu,kyau Kam ta Sha shi tayi rolling da mayafinta,hand bag ta dakko ta fito tare da yiwa Umminsu Sallama tace Zan dan zaga gari,Ummi tace to a dawo lafiya ta koma part din Papa tace papa Zan Dan zaga gari bani mukullin farar motarka please yace duba kasan pillow, ta duba ta zaba a ciki sannan ta Masa sallama ta fita abinta kannenta suna Aunty zamu je tace ba Zan je da kowa ba
   Affan ta Kira a waya ya Gama bacci ya tashi yayi wanka Yana shiri ta Kira ya daga tace fito mu tafi,kana nan Kaya ya Sha wani wando pencil creazy da shi me kyan gaske sai riga me Fadi Yar sarau sarau bata da kauri daga baya ta zobe baya yafi gaba tsayi Suma Tasha gyara sai da Raudat ta gaji da jira daga cewa Kaya Kawai zai sa ya gama komai Yana ta kalailaitar jikinsa ya gama ya fito Yana kamshi ana taku dai dai da wayarsa me tsada,tun daga nesa take kallonsa yanda ya Sha kyau Kamar a turai,Raudat harda kwantar da kanta a saman sitiyari tana tunaninsa horn tayi kadan sannan taci gaba da kallonsa har ya bude Gaban mota ya shigo,duk kamshin da takeyi nasa sai da ya doke nata,yace Hajiya Aunty,tace dan Allah ka daina ce min Aunty ni bana so ka girmeni sosai ka dinga ce min Aunty,yace alright Yana dariya an gama Hajjaju ta,ta sake kallonsa kamar zata Yi kuka sai kace tsohuwa,yace to Raudat shike nan, tace haka gatsal kuma,yace to me zance? Ina laifin ma kace min Queen,Queen dina my Queen ya furta tayi Murmushi tace naam Affan International yanda taji Sayyeed Abokinsa Yana fada Masa,Dukkan abokansa sai kace Affan International ake ganewa,dariya yayi yace wannan fa Yan school ne suka saka min,Affan International.

   International na wanka ko? Yace yes tana driving tace ni Kuma Affan Appointment,dariya ya saki suka je wani hadadden wajen cin abinci acan Suka ci Suka Sha sannan ta Kai shi wuraren shakatawa suna ta yawo cikin nishadi,Affan wani Kara son Raudat yake ji Kamar ya hadiyeta, sai wurin goma ta kaishi masauki baya so su rabu itama haka, Suka zauna a motar juyowa tayi kadan tana kallonsa shima ita yake kallo, hannunta ya rike a hankali tsigar jikinsu ta tashi kasa hakuri yayi tana mazaunin Driver a haka ya rungumeta yace Ina sonki Raudat ya sake kankameta Yana shakar kamshinta,jikinta ta janye yace please ina kaunarki na Dade Ina sonki na kasa fada miki dan Allah muyi aure,Raudat tace kana saurayi Ina bazawara ai bazai yuwu ba Affan International,yace ni ba komai ina sonki haka ba ruwana da wani bazawara Annabi ma ya auri Zawarawa bare ni,Raudat tace ku da samarin zamani ne sai budurwa,dan Allah ki daina fadar haka mene a virgin Ni ke nake so,Raudat tace ka bani lokaci to,zuwa yaushe? Koma yaushe ne in Naga ka cancanta shike nan, Affan yace au yanzu ban cancanta ba sai ma kinyi tunani,ya kalli Kansa yace mene Nawa bakya so ko bani da kyau ko dirina bai Miki ba? Raudat tace wane mutum akwai wacce ta Isa ma tace baka Yi ba,Zan baka amsa ai yace Allah yasa naji Alkhairi tace ameen ya bude mota ya fita tace sai gobe  karfe nawa zanzo? 11am lokacin na tashi a bacci,tace gobe zamu je ka gaida su Ummi da safe sai kace ranar zaka koma kaga washe gari sai mu tafi,Affan yace ban gaji ba mu Kara kwana biyu tunda kullum zamu dinga yini tare tace no Monday da aiki yace ni na sanarwa Oga ai farko sati Daya Kika ce,kasan aikinmu ko yaushe za a iya Neman mu,Aslam yace gaskiya gwara aikin gomnati bazan iya barinki ki dinga fita haka yanda Kika ga dama ba,a Haka suka rabu Raudat ana ta murna Kamar zata kashe kanta.

    Washe gari Affan harda saka wani yadi me tsada me karamin dinki ya Sha kyau sosai cikin fararen kaya za aje gaida suruki,Raudat tazo a wata kalar motar har room dinsa ta shiga tana shiga ya mike,ya ganta da ledan kayan abinci na take away yace ai na karya Ni naci abinci,a Ina? Yace fita nayi na samu waje tace nace kaje ne da zaka tafi kaci abinci a wani waje Yan garin nan fa Mata mayun maza ne so kake wata ta nace mak..tunawa tayi ta dauke wuta duf harda fuskewa tace hmm to ba komai fito muje gidan namu,Aslam ya fito Yana Murmushi ana kishinsa,katafaren gidan su Raudat suka je dama ta fada a gida wani da suke compound daya zai zo ya gaishe su yazo garin,Raudat har ciki ta Masa iso,Ummi ta fito ya durkusa tare da gaidata tana fara'a ta amsa shima Papa yazo Suka gaisa Yana cewa na gode na gode fa shi Kam Affan ya Masa ya kwanta Masa a rai, Ummi harda Zama ta saki jiki suna ta hira da Affan,shi Kuma an wani nutsu Kamar ba shi ba,kannen Raudat Suka zo Suka gaida shi,last born Dan yaro Affan yace boy zo Nan ya dauke shi yace ya sunanka? yace Irfan,Yana tsokanarsa ya Dan dade har yace zai tafi ya rabawa yaran kudade ya fito Raudat ta rakashi,tace zata maida shi masauki yace da Kansa zai koma shi zai Gane.

   Kwanan su Raudat biyar a garin nan suna shakatawa kullum tare da shi suke yini kwanciyar bacci ke raba su,ranar kwana na biyar Suka dawo gida Kano,Raudat tana shiga part dinta ta hau gyara shima haka,ta Riga shi gama aikinta shi ya fita kalailaitar masifa,Yana goge kujeru ta leko ta window ya duka ta wajen saitin windown ta dan yakushi bayansa ta koma ta buya ya duba yaga ba kowa ya koma yaci gaba ta sake lekowa da cokali ta dan karci bayansa ya juyo da sauri ya kamata dariya Suka Yi yace dama naji ajikina kece ai tunda Kika yakusheni ban ji zafi ba naji wani Dadi da shock nasan kece Affan da karya yakushinta ma Wai dadi ba zafu,Raudat har yau bata bashi amsar tana sonsa ba sai aji take ja Masa tun Yana tambaya har ya gaji.

   Aisha wannan karon tana hakurin dannewa basa fada da Mahaifiyarta suna zaune lafiya Sabo da sunyi nadama Matukar gaske,aikin gidan kaf kusan Aisha ke yinsa,tana son cikin nan nata duk da uban dan baya so amma ji takeyi da cikin nan,har tayi kyau ta Fara murmurewa, Farooq yayi murnar fitowar Aisha amma yaji haushi da aka ce tana da cikin wani ba nasa ba,Aisha tana ta murna zata samu danta ko ya Kawai tana wanke kayanta dana Ummanta ta Fara zubar da jini,ta tsorata sosai Suka tafi asibiti har da Baban Aisha aka je, lokacin cikin Aisha ya zube gaba Daya har ma sai da aka Mata wankin ciki,sabo da taji jiki kwanan su biyu a asibiti sannan suka dawo gida taci kuka ta koshi sai da Babanta yayi ta Mata nasiha sannan ta hakura,Ciki na zubewa mutane munafukai suka kaiwa Farooq gulmar cikin Aisha ya zube ta wani bangaren yaji Mata ciwo ta wani bangaren yaji Dadi.

    Bangaren Siyama kuwa sati Daya Kawai dangi aka fadawa Suma kawu yace ba taro Yan daurin aure ne Kawai zasu Zo,Dangin uwar Babar Siyama ma haka ya fada musu,Babu Wanda aka ce yazo sai iya maza Yan Uwa,shima Aslam ya fadawa Mum, Mum tace amma nayi maka farin ciki son ai gwara ma haka ba sai da taron ba babu komai an gode amma duk da haka ayi order abinci a Kai musu su bawa danginsu Suma mu dai ta bangaren mu tunda dama wannan iftila'in ya fada maka dama bamu da Niyyar taro sai na Yan daurin aure Kawai Nan Suka Yi kulla kullarsu da Mum dinsa yanda baza suji kunya ba,Haka aka tura manya da kudin komai da komai ko Siyama bata sa rai da lefe ba,Aunty dai ta dage tana ta gyara yarta sannan tana zuwa gyaran jiki, Saura kwana uku biki aka kawo lefe sunyi mamaki akwatina goma cif Kaya na gani na fada ba abinda babu,aka dinga zuwa kallon lefen a unguwar,Maman Nusaiba taji labari ta kyalkyale da dariya tace dan karya ne haka yakeyi yanzu ana kaita zaice yaci bashin bank ba kudi sun shiga uku ta sake sakin dariya,Shehu yace kinyi asarar halinki ke dai Kam tir.

    Aslam ne ya fito tare da Siyama yazo zance Suka Yi kicibus da Nusaiba mijinta ya kawota a mota ya juya,Aslam bai ma ga ko motar ba lokacin yayi nisa tuni ya bar layin,Nusaiba ansha wanka kana ganinta kasan tana hutawa ko kallonta Aslam baiyi ba ta gefenta ya wuce, har da kallon Siyama tayi dariya tace an kusa cin bashin banki ki daina murna an kawo Miki akwati goma Nawa kusan guda ashirin ya kawo amma karshe a ya na kare da talaucinsa, Siyama tsaki taja,Aslam yaja hannun Siyama yace let's go My Heart Suka wuce,Nusaiba ta bisu da kallo tace a hau taxi lafiya nasu ko kalleta ba abin Kuma ya Mata mugun ciwo a rai wato Aslam Kamar ma bai taba saninta ba haka yake nuna Mata ta wuce gidansu dai tana takaici.

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️ AUREN MUπŸ›’️

            61-65


Official

By
AsmaBaffaPage nakuli ne
Rukey Muaz

       Ana gobe daurin aure Siyama tasha gyara sai kamshi take zubawa Kawai ta Sha lalle,Kawayenta ta gayyata Zulfa'u,Sakna,Raihanatu da Nana sune Kawai a gidansu suke tayata Zama,sai bangaren Dangin mahaifiyarta Mata su biyar,sai bangaren dangin Aunty Mata su wurin goma haka bangaren Kawu da Mahaifin Siyama Suma sun kai goma gida ya cika tam duk da Kawu yace bazai taro ba dole sai da aka zo Masa,haka Aslam ya dinga dariya Jin Kawu yace bazai taro ba amma iya dangi sun cika gidan haka ya Aiko musu da kayan abinci shinkafa ta dafawa da danya ta tuwo,mangyada manja,Maggi iri iri,kayan Miya buhu biyu,su Alayyahu,kabewa, Albasa,Taliya macaroni  komai sai da aka kawo da yawa su Aunty Suka dinga mamaki kamar me kudi haka ya aikowa da Kawu dubu dari biyu,ya bawa Aunty dubu hamsim haka Siyama ma ya Aiko Sabeer ya kawo Mata kasonta sai,Kawu ne yaga mutane sun cika gidan ya Kira Aunty gefe yace nace fa ba shagali ba biki ya akayi Yan Uwa Suka cika min gida to wlh babu wacce zata Kai Amarya ko wacce gobe ta bar min gida,Aunty tace to tunda an sanarwa Yan Uwa ai ba wacce zaka kora idan Kuma zaka iya bismillah,Kuma biki babu wacce aka yiwa aure ba dangi sabo da Haka itama Dole Yan uwanta suzo Amarya Kuma ba komai ango yazo ya dauki matarsa ai dai an daura aure ko to Alhmdllh,Kawu Yana magana kasa kasa Kar dangi suji yace Ni dai ba wacce na gayyata biki,Kai ka sani cewar Aunty ta juya ta koma suna ta girke girkensu Kuma ta gayyaci Yan unguwa Wanda suke mutunci da kawayenta.
  Washe gari daurin Aure ranar asabar karfe 11am,Aslam shi Kam yayi gayya sosai Suka Zo da danginsu na jini Yan uwan Uba dana uwa aka taru a masallaci Shehu ma shine wakilin Aslam shi ya karbi auren Aslam aka daura akan sadaki dubu dari,ana daura Aure Aslam Yana cikin abokai yaga Affan da liman sunzo Yana sani Aslam da abokansa yace Dan Allah a nuna Mana Wanda na kasa a samarin Amarya,Sabeer yace waye Muka zo muka kasa Muka cinye  shi da yaki? Affan ya gane da shi suke,yace gani nan ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa yace Congratulations a zauna lafiya,Aslam yace Kar ma a zauna lafiya,Affan yace to fa Yana dariya yasan kishi ne kawai,Sabeer yace Wanda Muka kasa ayi Hakuri banda gaba,Affan ya dinga dariya shi ko a jikinsa ya tashi Yana kwambonsa ya wuce,Liman ma ya taya Aslam murna sosai ,Aslam yau anji shadda ta musamman Fara tasha aiki da babbar riga da hula yayi kyau kamar a sace shi ga abinci da yayi orda fried rice da rabin kaza har da masu rabawa ana ta bawa mutane a ledar take away a zuwan gidan Amarya ne Suka kawo.

     Siyama kuwa ta Sha leshi dan ubansu golden and white,Kawu yace babu batun shagali ko angon bai je wajen Amarya ba Kawu ya Hana,Amarya tana zaune cikin Yan tsirarin abokanta suna cin abinci Kamar ba Amarya ba komai bata akeyi tana lashewa da ance gashi zata ci abinta, sun Kuna Bluetooth speaker suna Jin kidansu suna nishadi tunda ango ya bugo Mata waya yace sai na Zo daukan Amarya,Siyama tana Jin kunya tace ka daina zumudi fa period na Fara jiya da dare,Aslam yace ba komai bukatar maje hajji Sallah tunda an daura yanzu hankalina a kwance yake nasan kin Zama tawa,Murmushi yace 4pm zanzo daukan abata ki shirya da wuri,Siyama Wayarta ma ta kashe duk sai taji ba dadi abinka da wacce bata taba barin gida ba kullum kana tare da iyayenka dole idan za a rabaka da gida kaji ba dadi,Siyama kuka ta Fara Yi tun da wuri kawaye suna tsokanarta ta dauki pad dinta ta Shige toilet tana hawaye a cikin toilet din ta fashe taci kukanta ta koshi duk ta bata kwalliyar tata sai fuskar ta wanke gaba daya ta fito idonta yayi alamar Kuka,Aunty tana Sallamar baki ta kalli Siyama Suka hada Ido tace ke Kuma meye na kukan duk rashin kunyar tana ina? Yan Uwa Suka saki guda da shewa Siyama sai sabon kuka ya taho,dangi Suka Yi caaa a kanta da tsokana sabo da kowa ya Santa da baki amma yau Kamar ba Siyama ba,kawaye suna Mata tsiya Kawai ta kwanta a katifa ta juya musu baya tun tana hawaye har bacci ya kwasheta kowa yazo Ina Amarya sai aga tana shakar uban bacci tun 12 har kusan 3pm bacci takeyi,ana ta posting pics din ango da na Amarya a online Wanda suka Zo bikin duk da cewar ma basu dauki hoton tare ba, ai Yan layinsu suna fara zuwa bikin Suka tasheta da tsokana wata tazo ta Dana Mata duka a gadon baya ke dalla tashi Amarya da bacci ki tashi kiyi wanka aka taru akan Siyama sabo da mutane da yawa ana Wasa da ita ta ko Ina caccakarta akeyi,4pm Aunty tasa tayi wanka tare da canja Kaya wani material ta sa me shegen kyau na lefe,suna bikinsu dai Kafin dare aka Kai Yan biki gidan Amarya duk me son ganin gidan Amarya Aslam ya turo wasu bakin abokansa sun kaisu a mota har Aunty taje taga gidan yarta komai yayi Mata itakam,Yan bikin ma suna ta yabawa da yan uwa,na nesa sun tafi ma tuni sabo da Kawu dama ya fada musu ba taro shi yasa Basu zauna ba,Aunty Kuwa dama ta fadawa mutanenta Kawu ne zai Kai Amarya da Kansa shi yasa babu macen data zauna zuwa magriba kowa ya watse sai Yan uwan Aunty su Uku suna ta aikin gyara gidan,Sabeer ne yazo ya kwashi kayan lefe duk wani abinda Siyama take so ya tafi,Aslam ce Masa yayi ya bar kayan a motarsa da ita zai dakko Amarya idan sunje gida ya cire kayan gaba daya,Kamar Aslam bazai Zo daukan Siyama ba sai dare Aunty tace tayi wanka ta shirya ya yo waya yace gashi nan,Siyama tace ban dade da yin wankan ba fa to ai na Amarya ne idan Kika Yi yanzu ai kin huta Yi a can,Siyama haka ta fesa wanka tazo ta Gama shafe shafenta ta saka wani Leshi da Kawu ya dinka Mata na biki me shegen kyau sea blue and black mayafinta me shegen kyau Kalar kayan da takalmi da jaka komai same color tayi kwalliyarta me kyau ta shafa turaruka tana shiri Kawu da Aunty Suka shigo Suka zauna a dakin Suka Fara Mata nasiha iri iri tana ji ta fashe da kuka suna Yi tana kuka kanta a kasa har Aslam yazo tana kuka,Aunty itama harda hawaye ta fada bedroom dinta ta kwanta tana ta kuka Aunty zata rabu da yarta,Kawu shi ya tasa keyar Siyama tana kuka kanta a kasa ta rufe kanta da mayafi tana kuka ya kaita har mota inda Aslam ke mazaunin driver sanye cikin wata shaddar Yar ubansu ruwan kwai,Shiga tayi gefe ta zauna Kawu ya rufe dama ya yiwa Aslam tasa Nasihar tuni,Siyama ta sauke glass din motar tana shesheka tace Kawu..... Kawu yace a'a Siyama karyar rashin kunya ta Kare ki daina nemana gaki ga Aslam aje ayi ta samun ciki idan Kinga dama ki Haihu sau goma a shekara Allah yasa Albarka,Aslam Murmushi yayi Kawu ya yiwa Aslam godiya yace su tafi Aslam yaja mota Suka tafi Siyama na kuka.

    Affan dawowa yayi gida daga wajen daurin Aure Raudat ta tsaya a jikin window tace Ina kaje ne haka? Yace yau ki tayani jaje an min gora,Nasha Sanda da Kaye an min mugun Kaye budurwa ta aka daurawa aure Bata so na wani take so,Raudat taji wani farin ciki tace amma ya Naga baka damu ba? Juyowa yayi Yana kallonta yace sabo da ke nake so,Raudat baki ta bude yace yes ke nake so  fa na fada Miki kince sai kin duba shike nan ai rayuwa ce harda yin Kalar tausayi,Raudat tayi dariya tace ai zan baka amsa ne nan gaba,Affan ya girgiza Kai a ransa yace zanyi maganinki.
    Washe gari da Yamma wata budurwa ce Yar kwalisa Fara ta dau wanka ta sa key ta bude part din Affan kawai ta Shige a gaban Raudat dake Compound,Raudat ta bita da kallo yarinya Shuru Shuru bata fito ba har Raudat ta gaji ta shigo ranta a bace tace ke wai wa kike jira? Yarinyar tana yanga tace Affan, Raudat tace a Ina Kika samu key dinsa? tace shi yaje gidanmu ya bani yace na jira shi, Fitowa Raudat tayi cike da kishi hankalinta a tashe ta zaune a compound Affan ya dawo da sauri ya fito ya shiga part dinsa Kuma ya rufo kofa,Shuru Shuru ta ga bai fito ba shigowa tayi ciki ta same shi a zaune shi kadai bakuwar Kuma tana kitchen tana girki kamshi na tashi,Raudat zuciyarta ta jagule ta rasa inda zata sa kanta a duniya taji san yi fita tayi cikin fushi ta koma bedroom dinta ta kwanta a saman bed dinta ta Fara hawaye kafin kace me ta fara ciwon kai ko Hussain bata taba sonsa haka ba bare ma tayi wani ciwon Kai a kansa amma Affan bayan ciwon Kai harda zazzabi ya lullubeta,Affan Kuwa Yana ganin Raudah ranta ya baci ya mike ya shiga kitchen yace Safara'u zo ki tafi gida kin gama aikinki, Safara'u ta fito tace Yaya Affan ka manta sakon da zaka bani na bawa Mallam,Yace af na manta ya mike da sauri ya dakko Mata kudi yace gashi kice ragowar kudin gidan Mai ne da nace Zan kawo tace to tare da ficewa,tana tafiya dan Masifa kunnen Raudat taji Sanda tayiwa Affan Sallama tashi Raudat tayi tare da saka hijab sai palon Affan.

    Kishi ya gama cika Mata zuciya ta banko kofar ya mike zai shiga bedroom tace waccen wacece? Yace wa? Who is she? ta furta da fada tana rawar sanyi yace baki da lafiya ne? Ban sani ba mayaudari kace min Ni kake so kana zuwa ka kawo wata macen mene baka fada min ba,Affan yace Yar Liman ce fa uban gida na a'a Yar gidan sarkin musulmi ce karewar limanci si ba muharramarka bace da zaku kebe dan ubanta tazo tace zata maka girki Kawai kace sonta kake yi Kuma bana sonka bana bukatarka gaba daya ta juya ta fice Kamar zata tashi sama.
   Affan yaji Dadi yace yawwa kin Kama kanki ya zauna Yana murna sosai tana sonsa,washe gari ogan Raudat yazo zai dauketa zasu tafi aiki,taji sauki ta fito cikin shirinta da simple doguwar Riga marar nayi ta fito da takardunta,Affan yau hutawa yake a gida yaga Raudat an dauketa a dalleliyar mota ya zaci saurayi ne ya kule sosai Kamar zaiyi duka.

   Yamma nayi ta dawo Affan ya tareta a Hanya waye wancan? wa? Wanda ya daukeki a mota,abokin aikina nane ai gwara ni ba namiji na kawo dakina ba,Tambayarta yayi a nutse Raudat mu daina irin wannan kina so na ko bakya so na? Tsayawa tayi tana tunani Kawai ya juya ya Fara tafiya abinsa tace wait bai tsaya ba ta bishi da sauri tace Ina sonka kayi hakuri,tsayawa yayi cak Yana murna,gabansa ta dawo ta tsaya tace Ina sonka wlh kayi hakuri,sabo da murna ma kasa magana yayi,takardunta ya karba yace mu je na Zama mijjn Kan tace suna tafiya abinsu Suna hira abinsu amma kishin masifa ne da Raudat duk da haka tana zargin Affan ko suna shiri da Safara'u.

     Aslam kuwa tsohuwar unguwarsu yaje unguwar masu kudi ita Siyama tana ta faman kuka a lullubeta cikin Mayafi har age gida bata sani ba sai da yace fito ta dago da kanta Mamaki ya kamata  tace me za muyi a wannan gidan ta kalli gidansa ne katafaren gida na da Wanda ta sani Sanda Yana me kudi,Kuma duka ga motocinsa nan har da wasu sababbi ma,masu aikin gidan tsofaffi Wanda ya sallama ta gani ya dawo dasu kenan,ga inda an Kara gyara shi ya koma wani irin mugun hadadden gida har ya da a baya tsaruwa,baki ta bude yace Baby fito Yana Murmushi ya jawo hannunta ta fito tace ba dai duk talaucin da kace ba karya ne? yace ki saurareni Baby kiji ba abinda ya faru da dukiyata tun daga lokacin da nace Nusaiba ta ebi kudi a cikin kudina ta bawa Mamanta ta kwashe kudin duka na Fara zargin sabo da kudina ta aureni badan Allah ba shine nayi Mata haka Kuma ko Mum da Sabeer ban fada musu komai ba tunaninsu da gaske na talauce,Siyama ta Fara mamaki tace yanzu kana nufin duk banki da kace sun kwace komai karya ne? Yace ae,Fuska ta bata tace amma ka dauki hakkinmu hawaye ya zubo mata tace me yasa kayi Mana haka, rudewa yayi ganin ranta a bace,tace ta ya za ayi ace dama Kawai fada kayi ka shirya zance Muka dinga Shan wahala a kanka muna Jin tausayinka hawaye ya zubo Mata,yace please Baby kiyi Hakuri ke kin San dalilin da yasa nayi haka sabo da na San me so na tsakani da Allah kuma gashi na sani ya karasa Kamar zaiyi kuka kiyi hakuri muje ciki ta shiga yasa me aikin ta shigar Mata da kayanta kaf bedroom din Amarya,ya zauna Yana aikin lallabata ya Sha fama kafin ta hakura ta sakko hannunta ya rike kin zauna a Palo Baby muje sama Suka haura sama jikinta a sanyaye tace ya akayi Naga motar da Nusaiba ta siyar maka Wanda tace Wanda ya siya ya gudu bai bata kudin ba? Yace ai Wanda ya siya motar yarona ne tunaninta ban me nake ba ni na tura shi ya siyi motar ya gudu Kuma,Saurayinta data aura ne kadai ban sani ba ban ma taba ganinsa ba amma komai da takeyi Ina sane

    Suna Shiga bedroom dinsa ya rungumeta a jikinsa yace ko za a hanani yanzu? Murmushi ta saki tace yaci gaba da rungumeta Yana shafa wuyanta,tsigar jikinta ce ta tashi Wanda ya jawo ta lumshe idonta,yace kinyi wanka a gida ko yanzu zamu Yi Yana magana yana goga Mata Hajiya Babba wacce ta mike sosai,tace yanzu nayi wanka yace Nima Haka, toilet dai ta Shiga taci gaba da kukan barin gidansu ta wanke fuskarta ta fito tare da zabo rigar bacci ta gaske  ta saka shi yayi shirinsa ma,kayan makulashe Suka lashe sannan Suka Yi brush ta Fitowa ya dauketa sai saman bed ya kwantar da ita a hankali...

   Nabeela ce ta samu ciki a gidan Farook murna wajen farouk ba a cewa komai,Kamar gaske sabo da bata son Farook taje a boye ta zubar da cikin aka Mata Allura,Bayan ta dawo gida cikin dare ta fara bleeding yayi yayi ta bari a tafi asibiti taki yarda sabo da Kar a ganeta sai da ta kusa mutuwa Farook ya kasa jurewa ya dauke ya dauko Mamansa Suka tafi asibiti,ai Kuwa bayan komai ya lafa likitoci sun samu nasarar ceto ranta, likitan yace Farook ya same shi a Office,bayan Farook ya shiga ya zauna likitan ya dago ya kalli Farook ya Fara fada taya za ayi a Mata allurar zubar da ciki me karfi haka,Farook yace Allura Kuma?likita yace Kai mijinta ne ko kuwa cikin Shege ka Mata sakamako ya nuna Allura ce me karfi ta zubar da ciki,idan matarka ce ka binciketa gaskiya,Farook duk da ransa ya baci amma ya danne bai nuna ba Sam Sai da aka sallamesu bayan kwana biyu taji sauki sosai ta warke ya sameta a bedroom tana zaune,Yace Nabeela wacce Allura Kika yi na zubar da ciki? dama kin San bakya kaunata Kika aureni,kin San wani kike so Kika zalunceni na aureki, Nabeela tace waye ya fada maka? Wayo ya Mata yace Wanda Kika je ya zubar Miki cikin,tunani tayi Kawai da gaske an fada masa tace Ni bana son haihuwar, gau kake ji ya kifa Mata Mari hagu da Dama yace amma ke azzaluma ce Ina son yaran Kika zubar min da ciki, ya zari zai Fara zaneta ta gudu Daya dakin ta saka key tana Cewa Allah ya Isa,idan ya zageta haka ta rama Kawai takarda ya dakko ya saketa Saki daya ya bata takardarta ya sallameta,ita duk Affan take so akansa take kashe aurenta har da murna zata je ta nemi Affan dama taji labarin inda yake Zaune can zata tafi ko Idda baza ta bari tayi ba.

     Nusaiba Kuwa soyayya suke bugawa da Sufyan abinda take so yake Mata komai ya samo a gindin Nusaiba da uwarta yake karewa,duk ta rabashi da danginsa Wanda da shi Suka dogara shike Basu ci da Sha amma Nusaiba tasa yanzu ok gaida iyayensa sai yaga dama yake zuwa,Basu da cin yau bare na gobe amma yaki ya taimake su,Ummansa ce ta gaji ta shirya ta tafi gidansa,Lokacin ya tafi Office tana zuwa ta shiga palon Wanda ta iske yar aiki tana ta gyare gyare,Yar aiki ta gaisheta Umma ta shiga ta zauna tace me aikin ta Kira Mata Nusaiba,Nusaiba tana sama taci gayu ta kishingida a saman gado tana latsa Wayarta ac na ratsata,Me aikin ce ta shiga da sallama ta durkusa a gaban Nusaiba tace Kinyi bakuwa Hajiya,Nusaiba da aka Kira da Hajiya tana yatsina tace wace? umman Alhaji ce,uwarsa ce Maimuna Wai?Me aiki tayi mamaki uwar miji guda ake Kira da sunanta gatsal haka,me aikin tace ae itace,tsaki Nusaiba ta ja tare da furta je kice Ina zuwa,tunda me aiki tace gata nan Nusaiba tafi hour guda bata fito sannan sai gata tana sakkowa daga bene tikasai tikasai tana taku dai dai tazo ta zauna tare da furta gani naji ance kina nemana,Uwar miji tace dama Sufyan nazo gani ko Yana gida?kin San Yana wajen aiki bai dawowa sai dare in kuma Zaki jirashi to ta mike tana kunkuni tana cewa miji ma sabo da Masifa baza a barka ka zauna lafiya ba uwar mutum tabi ta isheka ta Shige kitchen,tana zuwa kitchen ta samu me aiki tace idan Kika sake Kika Bata ko ruwa sai na koreki yau,Umman Sufyan tana ji a kunnenta mikewa tayi ma kawai ta bar gidan ta koma gida inda ta bawa Baban Sufyan labarin irin wulakancin da aka Mata,Baban Sufyan yace kyale shi ai Allah shike ciyar da mutum Kuma shi ke raya bawa kyale shi zaizo ya same mu watarana tunda shi mace tafi iyayensa.

    Bangaren ango Kuwa Nafila yayi shi daya da adduoi Siyama tana zaune a gefen bed tayi Shuru tana tunani da farin ciki yau itace a gidan nan tangameme haka,gida na gagara,mijinta hadadde ga kudi duk natane Allah take godiya har ya idar Yana sallamewa ya juyo Yana kallonta cike da farin ciki Yana Murmushi ya mike tare da haurawa saman bed din ya jawota jikinsaAsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️ AUREN MUπŸ›’️

        
            71-75

Official

By
AsmaBaffa
Page naki ne

Bestynbeelat
       Suna dawowa gida mota ya bude ya fita ya zaga tare da bude mata kofa hannunta ya riko ya fito da ita sannan ya bude bayan mota tana rike a hannunsa ya dakko take away nasu Suka shiga ciki ba kowa me aiki ma tana bangarenta,waist dinta ya riko suna tafiya Murmushi tayi tana kallon gidanta Kamar mafarki take gani ta kalli gidan ta kalli mijinta sai farin ciki takeyi tana tunani dama Yan uwanta da akai kaisu ganin gidan Amarya nan aka kawo su Suka kalla da yabawa suna cewa me kudi ne ashe tunaninsu Kawai zuzutun Mata ne, daukan Siyama yayi Suka karasa sama Bedroom dinsa Yana cewa gaskiya wannan rashin tsarkin naki ya min cikas da ace na San Haka ne tabbas sai na roki kawu a daga bikin a Kara sati daya,Kai fa kace baka damu ba auren shine me wahalar,kayan jikinta ya fara cire Mata Yana cewa ki daina sa min bra Indai Kika fahimci Ina mood,kallon sa tayi tace da Ina maka kallon kamili ashe kaima guda ne,na taba ce Miki ni Kamili ne? no na taba cewa bana son wagga harka? Da wani ustaz kike ganina? Siyama tace ae har tausayinka nake,Murmushi yayi yace to ki daina sarkin musulmai ma Yana son sex da Zaki ga Liman dinku sai kin daina binsa sallah,Dariya Suka yi tare da Mika Mata hannu Suka tafa

    Yana kallonta yace Ina sonki tana Jin kunya yace bari nayi Sallah ya mike yayi Alwala zai tada Sallah ta mike tare da dagewa ta ture shi tana dariya tace yau baza kayi Sallar Isha da wuri ba sai na karya ma Alwala ta rungume shi,Zama yayi ba shiri saman Sallayar ta koma gefen bed ta zauna,juyowa yayi Yana kallonta Yana Murmushi yace wlh ta karye,Dan Allah da gaske daga dan runguma,Yace ai kina jona min jikinki ta karye ya mike ya fita plate yaje dakkowa me aiki ma ta shigo zata ajiye kwano tace Sannu Alhaji yace yawwa tace Allah ya barka da Aunty Siyama,nan take ya saki Murmushi tare da furta ameen ameen ya zaro 2k yace gashi Kya sa Kati ki Kira Yan Uwa,Karba tayi tana godiya tace Allah ya baku zaman lafiya ya kawo kazantar daki,Aslam yace Banda kazantar dai Yara na gari Zaki ce,to Allah yasa ta fice,ya koma sama ya iske har tayi Shirin bacci cikin wata Nighty blue ta Sha kyau gaba daya surarta a bayyane take,yace my Choice ni kizo mu ci na matsu Yana magana ya riko hannunta ta zauna a jikinsa suka ci cikin shauki,suna gamawa ya Dora ta saman bed sannan yabi lafiyarta Suka fara farantawa juna, Siyama sai kunya take ji.

     Period din Siyama kwana hudu take yi yau ta cika 4days amma bata fadawa Aslam ba gudun Kar ya dameta da zumudi,Yana hutun amarcinsa ya Kira Yaronsa a wajen aiki Yana fada taya za ayi baka rubuta abinda nace ba har yanzu baka tura min ba,Naga alama tunda naji labarin kayi aure Sam baka kula da aikinka Wasa kake Yi,Watarana ma baka zuwa sam idan baka bukatar aikin ka fada min Zan iya sallamarka,Hakuri ya dinga bawa Aslam yace anjima da yamma zan shiga Office din kazo mu hadu a can yace an Gama oga
   Zuwa yamma ya shirya cikin Riga Armless da 3qtr me fadi sky and white ya Sha kyau,Siyama ta fito zata rakashi tana Fushi Wai dole sai ya tafi da ita,yace kiyi hakuri yanzu Zan dawo ba lalle ma nayi 1hrs ba,tana shagwaba tace to sai ka dawo Allah ya tsare ta Bude Masa mota ya shiga,ya daga mata Hannu sannan yayi driving Kansa zuwa Office dinsa.

   Nusaiba ce ta Kira mijinta tace Ina Kan hanyar gida,Sufyan yace jeki Office dina ki jirani idan na zo sai mu taho tare bazan iya barin matata tana yawo a Napep ba,Nusaiba tace kamata ai ma bai kamata ba babu tsari ace Ina shiga Napep, taci gayu na gaske cikin tsadajiyar shadda Blueblack doguwar riga,Address ya tura Mata na Building din ta wuce can,tana zuwa kowa kallon dai dai take Masa Sabo da mijinta ne C.E.O a wajen sai yanga tana uban gadara ta haura sama a lift tana dubawa ba tare da ta tambayi kowa ba lokacin ma ma'aikatan gaba Daya suna ta tafiya sun tashi 5pm tayi sai daidaiku suma Kuma Shirin tafiya suke yi,tana Bude office kowanne a kulle da key Kuma tafi karfin ta tambaya sai kace na ubanta,tana zuwa hawa na uku taga wani hadadden Office na musamman tace ga na mijina nasan ma nan ne tana murdawa taji ya bude ta Shiga,haduwar Office din ta Kai haduwa sanyi da kamshi ke tashi kawai komai unique ne a Office din,kujera ta samu ta zauna tana jiransa sai kallon Office din takeyi tana Jin dadi yanzu nan na mijinta ne,Aslam ne ya fito daga wani daki a cikin Office da wani cup a hannunsa,yayi mamaki ganin Nusaiba tana zaune,Fuska ya daure itama ta daure Fuska a ranta tace oh a nan aka dauke shi aiki mijina ne ya dauke shi ashe me shara da gogeg goge ne Alhmdllh zai ga wulakancin duniya,kallon up and down take Masa sai yace ranki ya dade me kike bukata? tana harararsa tace Office din mijina nazo kaga Mallam dalla kawo min lemo Kai baka iya kula da bakin oganka ba ta ja tsaki,Aslam ya kalleta tare da furta Sorry Hajiya ya shiga inda aka tanada wajen da yake zuba kayan coffee dinsa,tea da lemuka,ya bude fridge tare da dakko wani lemo me mugun tsada ya dakko ya kawo gabanta tace zuba min mana Yana tausayinta a ransa ya zuba Mata tare da Mika Mata ta karba tana Masa kallon banza ta Sha lemon tana tunani a ranta lallai lemon nan na musamman ne,ta sake cewa I wonder har yanzu wani kamshi yake me Dadi ya fa kamata mutumin nan talauci yasa aji Yana wari amma kullum fes da shi,wani kyau ma yake da kiba,muryarsa taji yace shike nan abinda kike bukata? Wani kallon banza tayi Masa ta ja tsaki tace kaga karka tsaya min a kai ci gaba da share sharenka....kafin ta rufe baki Sufyan ya shigo da sauri Yana zuwa gaban Aslam ya rusuna tare da furta dan Allah kayi hakuri Sir wallahi abubuwa ne Suka Sha kaina kayi hakuri dan Allah wallahi na manta shaf amma Zan rubuta anjima kadan na tura maka,Aslam yace kayi sauri please Zan jira a gida ka tura min ta Email don't waste my time, Inshaallah Sir Inshaallah ,Nusaiba Ido ta zaro tana kallon ikon Allah amma duk da haka bata wannan take ba ita ya aka Yi Aslam yake da kudi kenan ba talaucewa yayi ba,Kai ta dafe Kamar zata yi kuka ta fara tunanin ta ya zata koma wajen tsohon mijinta mamaki Kuma ya kashe ta dama Sufyan yaron Aslam ne a karkashinsa yake aiki,Aslam Yana kallonta ransa a bace ya hade rai ya wuce ta gabanta zai wuce gida,Sufyan ya mikawa key yace ka rufe min Office ya fito,da sauri Sufyan ya ja hannun Nusaiba da tayi mutuwar zaune Suka fito ya rufe Office din suna Fitowa Suka samu Aslam ya Danna remote din mota tun daga nesa ya bude ta ya shiga,Nusaiba kallon motar takeyi tabbas itace Suka Zo a cikinta tare da Siyama,Kawai kallon ikon Allah takeyi,motar Sufyan ta kalla wata kucakar mota wani takaici ya lullube ta haka ta bishi Suka shiga sai gida,Aslam kuwa mamaki yake yi dama Sufyan ne ya auri Nusaiba amma take Masa iyayi,dariya yayi wani farin ciki ya kama shi tabbas yanzu yasan Nusaiba tana cikin wani hali, cike da farin ciki ya koma gida Siyama tana Palo Yana shigowa tazo ta fada jikinsa tana furta Oyoyo ya dagata sama Yana murna,tace wannan murnarfa? Ya Shiga bata labarin abinda ya faru tsakaninsa da Nusaiba ai Siyama har kasa ta durkusa da hannu biyu ta kwaso Shoki yayi dariya ta sake kwasowa tana waka da baki tace yau Nusaiba ba bacci Yar banza,mijin nata ma ashe yaron mu ne,na Kara maka farin ciki? Yace da me Yana Murmushi ya manna ta a kirjinsa tace yau Ina Sallah na gama period,Aslam harda ihun murna yace ai yanzu ba jiran wani dare ya dauketa Kamar jaririya sai bedroom dinsa Yana cewa first Evening zamuyi ba first night ba

   Nusaiba Kuwa suna komawa bedroom Suka shiga shi Sufyan ma bai San matar Ogansa bace yace Wai lafiya Naga kin rasa sukuni sai gumi kike yi,Nusaiba mayafinta ta jefar ta zame dankwalinta ta jefar tana fifita da hannunta tana huci tace Aslam oganka tsohon mijina ne shine Wanda ka zuga ni na kaishi Kara ka zugani na karbi takardar sakina a hannunsa,Sufyan ya dora Hannu a Kai Yana wayyo Naga ta kaina Ogana ne na Shiga Uku aikina,Nusaiba tace wa yake ta wani aikinka yanzu ya fika kudi dama ashe da kudinsa,ya zanyi na Shiga dubu ma ba uku ba, gashi Siyama ta aure min miji ya zanyi,Sufyan baki ya bude yana kallon ikon Allah yace Ina ta aikina kina ta wani kudi baki da hankali Wai dama? Nusaiba tace dalla karka dameni mafitata nake hangowa,Sufyan mamaki ya kashe shi yace amma ke butulu ce baki San arziki ba,Iyayena nake hanawa ci da Sha sabo dake sabo da ke na kasa tara komai,Sai kayi Kuma cewar Nusaiba,sai nayi fa Kika ce? ta duro ashar tace burar.....kafin ta rufe baki mari taji ta ko ina,daina gani tayi na wani lokaci ya nade hannun riga ya hau jibgarta Kamar ya samu katon gardi tana ihu nan take idonta ya kakkafe ya juye numfashinta ya koma sama sama sai ta Fara furzo da jini ta bakinta amma Sufyan ko asibiti bai kaita ba sai da Allah ya taimaketa numfashinta ya dawo dai dai ta kasa tashi sabo da dukan data ci sai Jan jiki da Haka ta jingina jikin bed tana cewa ni ka sakeni wallahi wajen Tsohon mijina Zan koma ga me kudin gaske,Tsaki Sufyan ya ja sabo da zai iya kisan Kai ya fice ya barta a gidan tana ta tunanin kudin Aslam Yaya za ayi ta koma wajensa.

    Affan kuwa kyale Raudah yayi sai da aka kwashe kwana uku ya tabbata ta huce sannan ya sameta a compound zata fita ya tareta yace Raudah ta,Baki ta turo gaba,yace my Life, Mene ta furta yace dan Allah kiyi hakuri,wa Zan so in bake ba,Ina nuna Miki cewar ke kadai nake da,kece kadai a zuciyata,ki rage kishin nan My life tsohuwar budurwata ce fa me zanyi da ita,Raudah tace sau Nawa kuke komawa wajen tsofaffin budurwarku kuce ai ita kuka Fara so baku mantawa da juna,Banda ni to Ni ai na baki labarin abinda Suka min ta ya Zan koma wajenta ai da na cika marar zuciya,Kiyi hakuri ba laifina bane,Raudah ta kalle shi tayi missing dinsa tace idan na sake ganin wata tazo wajenka duk abinda na maka Kai ka jiyo,Affan yace ae ki mare ni ma,Murmushi tayi tace ko da kudi ai ban iya marinka,key din motar ya karba yace muje na kaiki Office,Kar ka ja min a wajen aikin nan namu akwai Yan mata,ke Kam kishi ya Miki yawa,tace ya zama dole ai indai akanka ne,Key din ta kwace ta Shige mota tace da kaina zanje ta Shige mota taja ta tafi tana Murmushi tare da dago Masa Hannu.

    Aisha Kuwa babban abokin Farook ta kira tana rokonsa ya taimaka ya yiwa Farook magana,bayan kwana Daya ya samu Farook ai Kuwa Farook ya Masa kaca kaca Indai akan Aisha ne yaki saurarar kowa har wasu abokan sun Masa magana yace ba ruwan su,idan ta kirashi baya dagawa aikinsa yake kawai yana Kara gyara gidansa sosai  gidan yayi mugun kyau sai da ya gama komai,Aisha har ta cire rai ma ta hakura taci gaba da zawarcinta tana daukan wanka Kai ka rantse bata taba aure ba tayi kyau da kiba haskenta ya dawo,tsohon mijinta Yana ganinta ya dawo biko Yana so ya maidata Taki yarda tayi Masa fata fata wasu mazan dama lafiyar mace suke wa,da sun ganta fes sai su dawo idan ta koma Suka lalata sai su koreta,tana zaune da Yamma yaro ya shigo yace Aisha tazo inji Farooq,Kamar a mafarki haka taji bata yarda ba ma shine,Mamanta sai Murna take Yi tace maza tashi ga dan Albarka nan ya dawo da Kansa ya huce,Aisha tace maybe ma ba shine ba,shine Inshaallah cewar Mama,Aisha ta gyara ta canja Kaya harda kwalliya sannan ta fita ta ganshi a dalleliyar mota sabuwa ya fito Yana jikin motar, Aisha ta karasa tana Masa Sannu da zuwa ya amsa da sakin fuska yace zuwa nayi naji idan kin shirya komawa gidana ko me haihuwar kike jira? Dan Allah Farooq ka daina zancen nan kayi hakuri ka yafe min nayi kuskure Kuma Inshaallah Zan gyara baza ta sake faruwa ba,Farooq yace ai kin ci mun mutunci Aisha kin nuna min iyaka ta,ko a mafarki ban taba zaton Zaki min haka ba,kayi hakuri dai nace yace munyi magana da Baba yace next week za a daura Mana wani auren shine nace bari na tambayeki naji,tace ba matsala na shirya,daga Haka suka fara hira tace kasan kawata Sayyah ko? Yace tace ai dana fito ta dinga cewa Kar na koma gidanka ashe bata kaunarmu,Haka ma fa Kawu Jinjiri Dan uwan Baba ka gane shi ai? Farooq yace ae tace ai ya dinga zuga Mama Wai Kar na koma gidanka,Farooq yace dama nasan baya kaunata tun auren mu na farko cewa yayi ma ni mayaudari ne a kula Dani ai daina gaishe shi zanyi,Wai kawarki Naja'atu ce ta ganni taki kulani tunaninta mun rabu kenan to ta Allah ba tasu ba,Mata da miji sai Allah shi yasa ko mene ya faru karka tofa zancenka a ciki duk Sanda Suka shirya to sai sun fadawa juna waye yake son su waye kuma baya son su  Kai da ka shiga fadan karshe Kaine da kunya zasu koma su hade kansu.

      Nusaiba washe gari da katon rauninta a kumatu tazo gidansu ko izinin Sufyan bata nema ba,Mama ta ganta ta shigo tana kuka jikinta duk rauni,Shehu Kuwa ko baki bai sa musu ba bai Kuma tambaya me ya faru ba,Mama tace lafiya Nusaiba,tana kuka tace ta Kare min Mama,na gama yawo wash Ina Zan sa kaina,mutuwa zanyi,Mama tace Allah ya kiyaye, Mama gwara na mutu na huta Kawai bakin ciki ne zai kashe ni wash Allah tana kuka sosai,Mama ta rude tace Wai lafiya? ta sake cewa Mama Sufyan mijina da Kika sani Ashe yaron Aslam ne a karkashinsa yake aiki,ashe Aslam gwada mu yayi ba talaka bane kudinsa Yana nan Sufyan Yaronsa ne,Mama tace ban gane ba Wai me kike nufi sake min bayani,Nusaiba ta sake cewa Mama Sufyan dai mijina Sufyan boyi boyi yake a wajen Aslam,Sufyan dan Boyi boyin Aslam ne ,Mama ta saki ihu ta dora hannaye a Kai tace mun mutu amma ki kwantar da hankalinki sai aurenki ya mutu zamu Zowa da Aslam sabon salo,Nusaiba tace yawwa Mama kiyi wani abu na koma hannunsa tace an gama yanzu ki kwana uku a nan ki huta sai ki koma gidan mijin naki kafin mu samu dabara,Nusaiba ta hada Kai da gwiwa ta zuba tagumi tana tunani,Shehu Yana jinsu ya dinga farin ciki da haka ta faru.

     Aslam kuwa Yana ajiye Siyama saman bed ya rude ya gigice kamar yau ya Fara sanin mace sai rawar kafa yake sai da ta tsorata yanda yake kissing dinta Yana Shan bakinta kamar ba gobe,a hankali ya zare Mata doguwar rigar dake jikinta,da baki ya balle bra dinta ya bi sassan jikinta da lasa Yana tsotsa Kamar ba gobe kasa tayashi tayi abin yafi karfinta sai dai gaba Daya ta Zama wet, a hankali yace cire min wandona taji kunya ta rufe ido,Murmushi yayi dama tsokanarta yayi, a hankali yake binta amma komai da zafi zafi yake yinsa,Siyama ji tayi Yana neman hanyarsa tace munyi mantuwa da babbar Sunna fa yace ai gata wannan itace babbar Sunna ya Fara Adduar saduwa da iyali tun kafin ya shigeta ta Fara salati itama ta daure tana karanta Adduar ta saduwa yaga kokarinta matuka,Yana shiga tare suka shide ita na azaba shi kuwa na dadi ya fara sambatu ya haukace Mata abinda bai taba yi ba Kuma bai taba ji ba sai a wajen Siyama,Kalaman soyayya yake furtawa Yana yabonta Yana harkarsa,Hawaye Kawai Siyama takeyi na azaba ta Fara shesheka shi kuwa ko a jikinsa tace ya Isa haka dan Allah cire da zafi,yace Ni a haka nake so na dawwama da zai yuwu Yana Nishi da kukan dadi,sabo da ya taba aure ta Sha wahala a hannunsa bai Mata da Wasa ba,Boobs dinta yake murzawa da hannu biyun Yana buga harkarsa sai da zai kawo ya kankameta a jikinsa Kamar zai rugurguza Mata kashi,bayan ya gamsu sai da ya dan huta sannan ya zare jikinsa ya koma gefenta Yana shafa Mata gashi wanda ya hargitse gaba daya ya kwanta Yana lallashinta Yana lashe Mata hawayen tare da kwantar Mata da gashi, tsokanarta yayi yanda take cewa Aunty kizo yarki zata mutu,Murmushi tayi ba shiri tana ajiyar zuciya,shi Kam cikin nishadi yake marar misaltuwa sai yanzu yasan yayi aure, kallonta yayi yace ashe sai yanzu nayi aure a baya ba aure nayi ba,Sai wurin magriba ya dauketa Suka Yi wanka Suka fito da Kansa ya shiryata sannan yace zanje masallaci yanzu Zan dawo,Siyama ta daga Masa Kai tana boye Fuska sabo da kunya bata so ma su hada Ido,yana Mata wani kallon so yace na fita? Uhmm? Kai ta sake daga Masa Kamar kurma,yace sarauniyar  zaki da gardi na,dariya tayi ba shiri tana rufe Fuska da hijab din Sallarta,fita yayi kowa ya ganshi yasan a cikin nishadi yake Yana zuwa bakin gate dubu biyar ya zaro ya mikawa me gadi kyauta,Yana ta godiya bayan an idar da Sallah a masallacin ya dinga raba sadakar dubu biyu dubu Daya yara Kuma dari biyar dari biyu,daga nan ya fito Yana tafiya yana waya da Mum dinsa tana tambayarsa iceko Kuna lafiya? Fatan kana da kudin abinci? Yace ae zanzo gobe Mum,tace Allah ya kaimu a gaida Siyama,gobe yake so ya nunawa Mum shi bai talauce ba a goben yake so duk Wanda ya sanshi yasan shi ba talaka bane har Abokinsa Sabeer.
    Yana zuwa ya iske Siyama tana kuka kwance a Kan bed,yace me ya faru ya zauna a gefenta Yana taba jikinta tace zafi wajen yace bari na Kira doctor ya rubuta Miki magani,Haka ya Kira likita ya turo Masa sunayen magungunan ta message yaje ya siyo Mata ya bata ta Sha da kyar.

    Washe gari da sauki sosai ta tashi Babu abinda ta gaza yi na girki da gyaran dakinta da nasa,yayi wanka ya shirya ta shiga tana fesa Masa turaruka jikinsa ta dakko wayoyinsa ta Mika Masa da key din mota takalmi ta zabo Masa ya saka ya fito Shar da shi tace muje na rakaka cikin mota Yana farin ciki Suka fito Yana tuna Nusaiba ita komai sai kudi a bata kudi,suna Fitowa Palo ta dakko wani hadadden flask Suka tafi Yana shiga mota ta ajiye flask din a Daya side din tace na Mum ne,ta ajiye wata ledar katuwa tace da wannan ma,ya Bude ledar yaga Sabulai masu kyau da kamshi na wanka da turare kala biyu Murmushi yayi yace tana godiya wato so kike ki siye min uwa shike nan ki kwace min ita ta hana na Miki kishiya,idan munyi fada taga laifina ko to Baki Isa ba,Dariya tayi tace ni na isa tsakaninka da Mum sai Allah,wannan farfesun ai Kai ka kawo kajin,yace ita kawarki ta bata ne duk da ni na kawo shinkafa ma hanata tayi,tace to ka Mika min gaisuwa kace zanzo na gaisheta,Murmushi yayi yace na manta ma Aunty tace a gaishe ki na kirata,Kawu Ina kiransa yace karka dameni 'ya ce na baka mene na damuna,dariya Suka yi tace nasan dama haka zai ce Nima Zan Kira shi,motar ta rufe ta Masa bye bye ya fita,Yana tafiya yace yau har gidan Shehu zanje wayyo Aslam bai San Nusaiba ta tana gida ba da sai yafi Jin dadin zuwa ma sabo da ya cusa Mata takaici.


AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

          66-70


Official

By
AsmaBaffaPage naki ne

Mrs Chief

        Aslam ya furta wai ni me yasa ake min haka ne tunda aka daura auren nan sai guduna kikeyi ya furta tare da birkitota jikinsa tana saman kirjinsa ta daga Kai sama Kamar miciji abinka da ba sababa dariya yayi tare da kwantar da Kan nata a kirjinsa,Ni kunyar ka nake ji ta furta da shagwaba,oh dama kina Jin kunya ta? kanta ta tura a kirjinsa me laushi tana shakar kamshinsa me mugun dadi hannayensa ya nade a saman mazaunanta,tudu yaji da tsoka ya Shiga shafawa tana jinsa tana Jin kunya,hannayensa yayi amfani da su wajen tallafo fuskarta zuwa saitin tasa fuskar suka kurawa juna ido,bakinsu ya hade waje daya yana tsotsa a hankali cikin Salo,Siyama kasa komai tayi sabo da kunya shi kuwa sosai yake abinda zai samu nutsuwa da ita,tana jinsa tana Jin dadi tana fuskewa har ta kasa hakuri ta Fara tayashi tana kissing dinsa Kamar ba Siyama ba sai kace zata cinye Masa baki yaji wani Dadi marar misaltuwa cikin rada yace yawwa cinye shi ki huta Ido ta rufe tana Murmushi zata koma kunyarta yace uhm uhm..please ci gaba alright ta furta taci gaba da Masa abubuwa na musamman Yana Jin dadi.

     Rigarta ya cire Mata gaba daya wow cikakkun Boobs dinta Suka bayyana ya gansu manya yanda yake so ba irin na Nusaiba ba, shafasu yake a nutse Yana murza Mata su,gaba daya ta gigice bakinsa ya dora a Kan nipple dinta Yana sha,Siyama daga ita sai pant dinda da pad, yana sarrafata yanda yake so,tuni ba Kaya a jikinsa cucumber ya saka a tsakanin boobs dinta Yana gogawa zuwa wani lokaci ya kawo a saman kirjin nata,Siyama tana shagwaba tace ka goge min kirjina ji yanda ka bata ni,Tissue ya dakko tare da goge Mata kirjin inda ya baci shima ya goge jikinsa bayan ya huta wanka yayi ita Kuwa Siyama kirjinta ta wanke ta fito ta maida kayanta ta kwanta a nan yazo ya sameta bayan yayi wanka ya tsarkaka,zuwa yayi ya kwanta a jikinta ya makalkaleta suna Hira sama sama har Suka Yi adduar kwanciya bacci Bacci ya kwashe su.
   
    Affan kuwa Liman da Yan Uwansa ya tura gidan su Raudah aka Kai kudin aure bayan sunyi bincike a kansa,daga baya aka tsaida ranar aure nan da wata uku,Raudat ana ta murna gidansu daya amma Affan zance yake zuwa abinsa,yau da yamma ma waya ya Mata Yana office yace zanzo ki shirya,tace to tana ta shiri har da wani yi Masa girki Kamar bako tayi wanka ta tsara kwalliya cikin fitted gown ta leshi maroon taci dauri dama Raudah ta iya dauri kala kala,Affan Kuwa wani hadadden gidan wanka ya shiga yayi wanka a can da gidansa da komai amma Wai bazai koma ba zance zai je,a can ya shirya cikin wasu kana Nan Kaya na gaske wasu fararen takalma ya saka me tsadar gaske na manyan Yara kamar Wanda ya sauka a jirgi,ya fito Yana sheki da kamshi,kayan da ya cire ya saka a bayan mota ya shiga ya tafi Shopping mall ya shiga ya siya Mata wasu Kaya masu kyau readmade sannan ya tafi tare da sake kiranta yace Yana Hanya,Bayan dakunansu ta can Bayan compound bishiyu ne da flowers a can Raudaj ta shimfida musu katon Sallaya ta jere kayan abincinta a gefen Sallayar, Landlady da wasu Wanda suke estate din dariya suke basu abinda suke yi,15mnt Aslam yayi parking a gidan ya kirata a waya nazo,Fitowa tayi da mayafinta karami Kalar kayan ta yafa,har jikin motarsa Yana Murmushi Yana kallonta tace muje ya bita inda suke Zama suyi zance Suka zaga Suka zauna,Ina yini ta gaida shi yace lfy Alhmdllh ya kike fari tayi sannan tace Lfy lau,irin wannan kyau haka ai sai ki sa na Suma,Dariya tayi  ya zuba Mata Ido Yana kallonta tana Jin kunya,Maganar Landlady Suka ji tazo tace Affan kazo kayi bakuwa,yace bakuwa Kuma? landlady tace wata dai budurwa ce Yar ja haka da ita me Kama da Yan Fulani,Nan take Raudah ta bata Fuska ta cokalo dan baki gaba,yace ki kawo ta nan bazan iya tashi ba lokacin wife dina ne yanzu, Landlady taje ta taho da Nabeela Affan sai ganin Nabeela Kawai yayi yasha mamaki ta ya ta gano inda yake

    Nabeela tana zuwa Gaban Affan ta tsuguna tana hawaye ta durkusa tana kuka tace dan Allah Affan kayi hakuri na tuba ka yafe min,nasan mun ci Amanarka dan Allah ka yafe min mu dawo Kamar da wallahi ko yayanka Dana aura ban taba Jin dadin aurensa ba, ban samu sukuni ba bare na bashi kulawa haka ya sakeni Sabo da nadamar abinda nayi maka,yanzu Ma Yusuf din ya talauce Wanda suka dora shi akan kasuwancinsu sunce zaluntarsu yake Suka kore shi Yana da aure Kuma komai da ya mallaka Suka kwace Wai da kudinsu ya siya yanzu ma a gidan haya yake zaune da matarsa ko keke baida shi duk wannan hakkinka ne Affan dan Allah ka yafe min ka dawo gareni Zan gyara halayena ka sake bani dama, ka so ni a baya ka sadaukar da dukiyarka a gareni ka tallafa Mana da karfinka da arzikinka da lafiyarka amma na butulce maka maimakon ma na auri wani sai ma na auri yayanka uwa daya uba daya kaico na,na nemeka na rasa har na sake auren wani Farook a kanka na kasa Zama yanzu na dawo dan Allah ka yafe min ka dawo mu koma soyayyar mu Kamar a baya,Affan sai da ya gama jinta ta gama sannan yace ni ai daga ke har Yaya Yusuf na yafe Muku ban rike ku a raina ba a baya dai nace bazan yafe Miki ba amma danayi tunani na yafe miki,dadina da gobe saurin zuwa yau gashi kin dawo na aureki to bari kiji na Miki warning daga yau Kar na Kara ganinki a gidan nan kinzo nemana bana sonki yanzu na tsane ki,kalli wannan ya nuna Raudah yace ita Zan aura an kusa bikinmu

    Nabeela ta sake rushewa da kuka tana dan Allah ka aureni Affan ko da kishiya ne Zan zauna ko cikin Mata uku ne, kar kaga nayi aure har biyu farjina fes yake ba abinda ya same shi ban Bari na haihu ba a matse nake gam wajen bai bude ba kuma .....kafin ta karasa Raudah ta kwadeta da wani shegen mari tare da Mata tsawa rufe Mana baki munafuka algunguma,makira a gaban nawa? Kaji kwartuwa,Nabeel tace ni Kika mara dafe da kumatu Raudah tace an mareki ko Zaki rama ta mike tsaye ta koma kusa da Nabeela tace ko Zaki rama dan uwarki in Miki shegen duka yanzu,Nabeela ta kwaso kafafun Raudah ba zato Allah yasa ta fada Kan Affan kirjinta gaba Daya a Kan hannayensa,Affan yaji Dadi yayi luff a haka kamar gunki yaki motsi,kafin Raudah ta mike Nabeela ta rufeta da duka amma Affan sabo shi dadinsa yake ji sai motsa hannaye yake Yana tabewa Raudah kirji nan Kuma Nabeela tana dukanta ta ko Ina,Allah yasa Raudah ta mike ta Kama Nabeela da jibga Kamar Allah ya aikota ta tuge Mata dankwali gashin Nabeela Dan kwaikwayayye amma yasha gyara abinta,Nabeela Munafuka har da zuwa ta fada jikin Affan, Affan ya zuba Mata duka a baya ya sake zuba Mata wani dukan ta mike ba shiri Sabo da zafi dan bai Mata na Wasa ba yace kazama Zaki lalata min kaya, Raudah kishi da zuciya kamar zata Suma ta dauki glass cup zata kwadawa Nabeela Aslam ya kwace ya rike hannayenta tana Nishi tana fisgewa tana ka sakeni wallahi na nuna Mata Dan burar....ta dinga ashariya,Nabeela taga abin na gaske ne har sai da Raudah ta bata tsoro yanda tsabar masifa take kakkafe Ido,Affan yace kiyi hakuri Sweetheart,Ina Raudah Bata Jin Kira fisgewa tayi ta damko Nabeela ta turmusheta ta sake surar plate din tangaran zata kwada Mata Affan ya kwace,ganin Haka ta mike da gudu ta dakko wani katon dutse,Nabeela tayi asalin tsorata Raudah ba jira Affan Yana cewa Kar ta wullo amma sai da ta jefowa Nabeela ya sauka a goshin Nabeela ji kake kwas wajen ya tsage jini Yana fita duk da Haka bata hakura ba wani ta dakko Nabeela ta tashi ta fita da gudu ta bar gidan,Affan yaje zai riketa shima ta jefa Masa dutsen Allah yasa Bai same shi ba gaba daya Raudah ta haukace,Yana cewa kiyi Hakuri sai kuka tace na daina sonka bana sonka me kule kulen Mata ko yaushe mace tazo wajenka na daina sonka a fusace ta bar wajen tana kuka ta koma dakinta ta kwanta tana kuka zuciyarta na Mata zafi, Affan shi bai San haka take da fada ba  ma Yana ta mamaki gemunsa da sajensa ya shafa yace wannan Nabeela ta cuceni Ina soyayya ta,yace Kai Raudah wannan masifa haka ni na Fara ma jin tsoronta,gashin Kansa ya birkita tare da furzo iska daga bakinsa yace shike nan Affan ka shiga Uku mijin tace ya tabbata ba Kai ba kula wata ko da Wasa wannan baza ta bari na Mata kishiya ba,ah ba ruwana babu ni ba Kara aure daga yau sunana mijin mace daya na Raudah Kawai,ya dawo yace bari na Fara dabarun lallashinta naga ta kaina.

     Aisha tana yin Idda itama a boye da sassafe ta tafi gidan farook,Yana dakinsa a kwance sai yaji ana Kwankwasa Masa kofar palo Fitowa yayi tare da budewa,Yana budewa yaga Aisha, direct ta durkusa a gabansa ta Fara Neman yafiya,tace nayi kuskure Farook ka yafe min,Farook ya bita da kallo Kawai tace dan Allah kayi hakuri ka yafe min ka dawo dani gidanka Farooq kallonta yayi yace tashi,da sauri ta mike tsaye ya nuna Mata kofa yace get out bana bukatarki a rayuwata ya hankadota waje tare da rufe kofarsa,kukanta ta gama ta tashi tare da karawa gaba,tana komawa gidan su sai kuka,Ummanta tana ta bata hakuri tana kwantar Mata da hankali tace Aisha Ina da laifi nice sanadin kashe Miki aure kiyi Hakuri Inshaallah zai dawo,Aisha tana kuka tace Allah ne ya jarabce mu sakamakon mu muke gani, Umma bamu da aiki sai fada da juna lokacin Muna tare,na fada Masa Maganar da naga dama shima haka zai min abinda yaga dama bamu da aiki sai karya dan mu birge mutane, irin wannan da mutane ke yi muna ganin Kamar ba laifi bane irin wannan kana nan laifin Allah yakan nuna Mana sakamako tun a nan duniya ya jarabce mu zaman auren ma yaki yuwuwa,Umma tace to Allah zaba Mana mafi Alkhairi, Allah Kuma ya shirye ku masu karya,da rashin mutunta juna ga ma'aurata suna zaluntar kansu Allah yasa ku gane ,Aisha tace Inshaallah bazan sake ba amma a baya ai Yana zagina Nima Ina zaginsa, Subhannallahi cewar Umma tana mamakin yaran zamani masu iya zagin mijinsu,Aisha Kuwa waya ta dauka ta Fara Neman abokan Farook Wanda tasan Yana Jin maganarsu don su Shige Mata gaba ta koma gidanta.

     Siyama Amarya washe gari ta riga Aslam tashi da asuba Yana jikinta ta Fara masa Kiran Sallah a kunne idonsa ya bude a hankali ya kalleta murmushinsa me tsada ya sakar Mata tare da sake rungumeta kam Yana magana a hankali yace ki barni a haka ni,tace anyi Kiran Sallah tun dazu,makarar angwaye zanyi yau,no yaushe ma kasha zakin tukun da zaka Fara makara,dariya ta bashi ya mike zaune Yana kallonta sannan ya sauka ya shige toilet, brush yayi da alwala sannan ya fita masallaci, bata Sallah baccinta ta koma taci gaba da Shaka har ya dawo ya kwanta a jikinta shima ya dora baccin sai 9am ta tashi tare da zare jikinta a nasa ta shiga toilet brush tayi sannan ta sheka wanka ta fito ta zauna shafe shafenta sannan ta saka doguwar Riga Yar kanti marar nayi me hannun vest sama ta dame kasa ta dan bude ta fito tana kamshi ta saka hijab ta Shiga zaga gidanta tana murna kugu ta rike tace da na zauna a bikina Ina kukan banza dama Ina sani na dinga yin wani kukan har da Kari ma don ace Ina jimamin rabuwa da Kawu nan Kuwa ba ruwana,dan ba a San zuciyata bane ta zaga ta baya ganin babu me ganinta ta cire hijab din ma ta kwashe da gudu a gidan tana shawagi,tayi juyi ta juya ta tsaya cak tana ta ganin katafaren gidan ta rasa ma wanne murna zata Yi tayi tsalle yafi biyar tace gidana gidan mijina,dawowa tayi ciki ta iske me gadi a bakin gate Suka gaisa,sai  me aikinta mace tana ta gyara gidan Suka gaisa da ita cikin fara'a da mutuntawa, kitchen ta shiga ta Fara soye soye tana yiwa kanta Waka Amarya Ce Siyama,Charity ki Sha sha'aninki...tace wallahi duk Sanda Naga Nusaiba ta zo ko unguwar nan ko layin nan sai na ci ubanta Kai ko wucewa zata Yi ma, tana aikinta tana zancenta har ta gama hada breakfast dinta ta shirya a dining,Me aikin ta tambaya abinci fa tace ai ni nake yi Mana tare da me gadi tun tuni ma mun karya Kuma abinda muke so oga yake siyo Mana Yana kitchen din part Dina komai Muna da shi,Siyama tace Masha Allah an gode Masa ya kyauta ai mutumin kirki ne,kinyi dace wlh cewar me aiki,Siyama tace ni kuwa nasan nayi dace ke Kinga love gashi da hakuri wlh ba ruwansa,Haba ke dai bari Aunty baki ji yanda ake yabonsa ba cewar Yar aiki Siyama ta dage sai yabon miji takeyi kwana Daya kacal da kawota,ko Ina an gyara dakin Oga Kawai ta gyara da kanta,sai da ya gama baccinsa ya tashi tare da shiga toilet yayi wanka da brush sannan ya shirya cikin wani sabon yard me shegen kyau coffee color ya fito Yana zuba kamshi,Siyama ta fito dauke da flask tayi sauri ta ajiye a dining tana cewar takawarka lafiya barka da fitowa,dariya yayi ba shiri tace me kudi uban matsiyata na Siyama sa gabanka inda kake so,Wanda ya gaji arziki ba taka haye ba kenab,kaga na Charity me komai 100 ba dozen ba ,dariya ce ta kwacewa Aslam,Siyama taci gaba da cewa ga amaryarka me kayan aiki ya sake fashewa da dariya,ta nuna kirjinta da hannu biyu tace Kai kake da nan, a taba can a latsa nan sai na Siyama ikon Allah ta furta tana nuna Boobs dinta ,Affan Yana dariya ya rungumeta tare da dagata sama,tace ban gama kirarin ba fa,a lafiya dai....Baki ya rufe Mata da nasa yana sha

    Tace yau fa mu fita zamuyi yawo ba batun wani amarya duk inda zaka je sai na bika, yace to duk abinda kike so,Siyama ta Fara murna zata fita ba kulle,bayan sun karya a Palo Suka zauna yana zaune a doguwar kujera ya bude kafafunsa daya kafar a mike a saman kujera Daya kafar tana kasa Siyama ta kwanta a tsakiyarsa gadon bayanta Yana saman kirjinsa Yana koya Mata game a waya sun rike Wayar tare da hannayensu duka tana gwadawa suna ta fama suna nishadi.
   Zuwa Yamma Suka dau wanka kamar zasu je party tasa wata arniyar Arabian gown black taji ado silver color, takalmita da jaka Silver shi Kuma shadda ya Sha Silver me tsadar gaske kana gani kasan ba karya ya rike hannunta Suka fita wata rantsatsiyar Jeep dinsa,wani katafaren Joint Suka je duk Wanda ka gani a wajen to ya Isa,suna shiga rike da Hannu Suka iske Nusaiba a wajen mijinta ya kaita amma Abokinsa ya kirashi ya fita yace ta jirashi nan da 30mnt Yana fita su Aslam Suka shigo,sun ga Nusaiba amma kamar Basu ganta ba Suka zauna a kujera Aslam ya jawo Siyama ta zauna a saman cinyarsa yana sani yayi hakan,Siyama ta kasa Zama sabo da kunya ta koma saman kujerarta ta zauna,Nusaiba ta firgita taga Aslam Kamar a wata hadaddiyar mota Suka fito amma bata kula ba sosai lokacin,Siyama ce tace Honey bani key din motarka na ajiye maka a handbag dina,Nusaiba mikewa tayi ta kalli motar duk wajen babu me irinta tunani tayi tace maybe arowa ma yayi karya ne talakane har yanzu wai ni za a yiwa burga ta ja tsaki ta zauna tare da gallawa Siyama Harara,Siyama ko kallon Nusaiba bata Yi ba,ganin Nusaiba tana ta kallon Aslma tace please Ni ka canja mana joint muje Cenema kallon film yace alright ya riko hannunta yace sai abinda Kika ce ai shi za ayi Baby yaja hannunta Suka fita,Nusaiba tace karyar banza bibiyata sukeyi shi yasa Suka zo za a min burga ni Ina mamaki ma da har yanzu yake kamshi me dadi haka sutura me tsada ya kamata na Fara ganin wuyan rigarsa ya kode ya yage Yana wari amma kullum mutum kamshi Kamar namijin karuwa,harda aro mota azo za a rude ni Yan Iska Yan karya Yan Yan yan...ita Kuma Wai sa car key din a jakata sabo da naji suna da mota fake....ta ja tsaki,tashi tayi ta leka bata ga kowa ba motar da take tunani a ita Suka Zo bata ganta ba tace sun shiga taxi matsiyata Yan karya me motar ya dauki abarsa ta juya ciki.

  Siyama kuwa zasu shiga Cenema Kawai Aslam yaji sha'awa shi bazai iya jira ba,matarsa yake so ya murza,order ya musu na take away kaji da su ice cream da sauransu tana rike a hannunsa yace muje gida an fasa kallon Watarana sai mu zo bazan iya barin sabuwar Amaryata ta huta na hours ba ace bana taba komai ke muje bazan iya ba na fasa yaja hannunta Suka Shiga mota,Siyama tace mun fasa? Yace ae Nima ai ganganci nayi da na fito da Amaryata bazan yarda ba gaskiya wayo zaki min muje gida haka Kawai kowa idan yayi aure Yana hutawa ni shike nan na zauna a kallon film zaki min wayo,dariya ya bawa Siyama yace haka Kawai sai kalle min matata akeyi a banza...
Masu sharhi Ina godiya
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️ AUREN MUπŸ›’️

           76-80

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

AUTARESS      Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da  ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi

    Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba ya koma gida abinsa.

    Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya zubo Masa Yana rokonsa yace tashi ka bar min gida cikin tsawa ba shiri ya tashi ya fice,ran Aslam yayi mugun baci sai da Siyama ta fito ta zauna a gefensa tace lafiya yace Wai ashe Wanda ya auri Nusaiba tun tana da aurena yake bibiyar min Mata Yana fita da ita,Siyama nan take kishi ya motsa tace to sai me tunda Kun rabu shi ka kore shi mene na wani cewa Yana bibiyar maka Mata,au dama matarka ce shine harda tashin hankalinka haka da damuwa akan wata banzar Nusaiba,okay na gano son abarka kakeyi sai ya saketa ka dawo da ita,Aslam yace Allah ya baki hakuri ni ba haka nake nufi ba nufina a lokacin ai tana matata ba Wai yanzu ba,Juyawa tayi tace ba komai,fisgota yayi ta fado jikinsa yace ban yarda ba ai Indai kaji bahaushe anyi Masa laifi yace ba komai to wlh da komai dawo nan, dariya ya bata amma ta maze tace ka sakeni nace ba damuwa,yace akwai fa ayita ta Kare a nan baki Isa ba,baki ta turo yayi kissing dinta tare da furta to kiyi hakuri bazan sake ba Ni dai magana ta wuce ya mutu,tace amma kasan.....kafin ta karasa yace dan Allah da annabi kiyi shuru Allah ya baki hakuri ni dai Indai akan wannan ne,Siyama tayi Shuru tana zaune a cinyarsa,yace to ki min magana Mana kiyi murmushi,tace cewa fa kayi dan Allah nayi shuru to nayi shuru,Aslam yace kai Ina Shan wahala dake ai dai nace kiyi hakuri, tace na hakura karka sake min zancen Nusaiba wallahi idan ba Haka ba zaka ga danyen kai,dariya yayi yace to naji bazan sake ba yanzu ma kuskure ne ke kika fassara ni daban,cike da shagwaba tace mutum Kawai ka kawo zancen wata ballagazar banza bazara iskar damuna,Boobs dinta ya cafka ya shiga sarrafata ba shiri tayi shuru duk da cewa ba wani abu zaiyi ba face rage zafi sai ta warke tukun.

    Washe gari Sufyan Ya sake zuwa gidan Aslam bai same shi ba ya fita yayi murna dama Siyama yake so ya gani Yana compound me aiki tace Wai tazo inji Mijin Nusaiba,Siyama Hijab ta saka ta fito bayan sun gaisa rokarta ya dinga Yi dan Allah madam kisa baki me gidanki ya maidani bakin aikina,Siyama tace kasan kayi kuskure Babba kaima Wanda gaskiya ko ni bazan iya Masa magana ba a kanka kayi hakuri tunda yace a'a to fa sai hakuri kayi hakuri Allah ya baka wani aikin,Yace dan Allah Siyama ki taimaka min,Siyama tace Ina ma Zan iya taimakonka da nayi amma bazan iya ba kayi hakuri Kawai ta juya ta tafi abinta haka Sufyan ya fita jiki ba kwari,washe gari Aslam ya Kira Sufyan ya bashi takardarsa ta sallama daga aiki Yana ta rokonsa amma Ina baya Jin Kira.
   Sufyan Yana komawa gida ya iske Nusaiba ta dawo daga gidan iyayenta Wanda ko tambayarsa bata Yi ba,takardar ya wulla Mata ransa a bace yace Kinga abinda Kika jawo min ko,kin gani ko Yar iska dabba wacce bata San me take ba jahila,Yar talla, kin Sa na bakantawa Iyayena kin jawo an koreni daga aiki Allah ya Isa tsakanina dake kuma ki koma inda Kika fito gidan ubanki na sake ki saki daya,Nusaiba tace ka sakeni ? Yace ae zata Masa rashin kunya ya hau jibgarta ya Mata jina jina sannan yace wallahi ko hankici baza ki dauka a gidan nan ba baki zo da uwar komai ba duk ni na siya Miki sabo da Haka ki koma gidan ubanki haka,Nusaiba tana kuka jiki duk kulun duka tafi karfin ta taba komai Dan kuwa shi ya siya mata,Haka ta mike tana dingishi zata tafi,Hannunta Sufyan ya fisga ta Fadi a kasa ya dinga janta tana ihu Kamar wani buhun gishiri haka ya bude gate ya jefata waje ya kulle gidansa ya barta a nan tana ta uban kuka har ta gaji ta mike da kyar ta shiga Napep sai gida,tana shiga da kyar take tafiya tana kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi.

    Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera tana kallon hadadden Office din tace Sannu da aiki yace yawwa suna haka sai ga wata arniya ta shigo da wasu takardu sanye da gown ko gwiwa bata Kai ba komin surarta a waje ta Sha kitson attach tayi kyau gata da hips,Raudah baki ta bude tana kallo shi bai kula bama Signing ya Mata tare da Mika Mata ta karba ta dauki Hanya zata fita tabi ta gefen Raudah,da yatsa Raudah ta dan taba Duwawun matar, Affan yace mene Haka beb? Tace wannan wace? Yace Secretariat ta ce,tace kana nufin kullum sai kaga wannan? Yace mene ne Wai? Baza ka kawo Namiji ba sai mace to duwawunta kake kallo ko me,kalli fa duwawunta kullum da safe sai ka ganta Ina can na saki baki hai a bude Saurayina yana nan yana kallon duwawun Chinaza,wlh Affan idan ka kalli duwawunta bazan yafe ba,Affan yace Wai in tambayeki baki yarda dani ba,haba Raudah kishin nan naki yayi sau nawa zan fada Miki ke kadai nake da ita,bazan iya cin amanarki ba,I will never ever cheat on you Karki bari muyi auren zargi so kike kishi ya halakar dake,Ni wlh Kawai ka canja sakatariya zuwa sakatare Namiji gaskiya ban yarda ba,yace ba laifin data min baki Isa kisa na sallameta ba Kuma bani na kawota ba Liman ne ai kin san gidansa tunda munje tare kin gaishe shi je ki fada Masa ya canja ta Indai kin San haka zaki  to karki sake zuwa Office Dina ya mike tare da dukan table sai data tsorata yace tashi ki tafi gida bana son zargi bana taba ko hannun mace akan kishin banza kizo ki sani gaba ki hanani sakewa ba ke kadai kike da saurayi ba sannan idan niyyar cutarki nayi ta ya Zan Bari ki gane, tashi ki tafi bazan cuceki ba Ina sonki babu wacce nake so sai ke bana ko budurwa bare neman Mata bana son zargi,Raudah mikewa tayi  ta Fara hawaye yace oh my God me na miki? tace ni dai karka kalli duwawunta,yace to naji bazan kalla ba idona ma Zan rufe muje na rakaki mota a haka ya lallaba Raudah ta koma gida.

    Tunda ta koma gida part din Landlady ta shiga suna Hira tace karki yarda da Maza Yar uwa maciya amana ne duk yanda kike da kyau sai sun kula Mata,ki kula da Affan sosai yanda yake da kyau Mata bibiyarsa suke kisa Ido akansa idan ba Haka ba wata ta kwace Miki shi,Landlady ta dinga zuga Raudah,Raudah har da bata labarin sakatariya,tace to ki shiga ki fita a sallameta a canja masa Namiji ko mace me addini, Raudah ta Fara tunanin ya zata yi ai da yamma ta shirya sai gidan Liman
   Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana ta godiya.

    Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi, Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama.
    Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta dakko Masa file sai da ya gaji ya taho da Kansa ya isketa tana ta dukan kirjinta tsawa ya buga Mata tana Adduar bata daina ba tace Sir Allah ya maka gida me kallon bangon gabas,Allah ya baka mace me zikiri....tsawa ya Mata shut up Ina file din da nace ki dakko? tace Sayyadina manzo na shi zai agaza min na ganshi, Assalamualaika ya rasulillah.... Affan yana masifa yace ke lokacin Addua daban lokacin aiki daban,Rabbana.....Rabbana...taci gaba,Affan ya zaro Ido yace ke tafi gidanku na koreki you are fired,zata roke shi ya daka Mata wata uwar tsawa wacce tasa ta fice da gudu,nan take ya Kira Liman ya sanar Masa komai Liman ya canja masa wata macen arniya ce amma Kamar musulma haka take shigarta bata dame jikinta Kuma nutsasiya ce sai dai ita Kuma akwai bin maza Kamar karya haka take in Banda son maza babu abinda ta sani, Raudah tana bala'in sawa Affan Ido akan Shige da ficensa

    Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa, Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa.AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️ AUREN MUπŸ›’️

           76-80

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

AUTARESS      Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da  ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi

    Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba ya koma gida abinsa.

    Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya zubo Masa Yana rokonsa yace tashi ka bar min gida cikin tsawa ba shiri ya tashi ya fice,ran Aslam yayi mugun baci sai da Siyama ta fito ta zauna a gefensa tace lafiya yace Wai ashe Wanda ya auri Nusaiba tun tana da aurena yake bibiyar min Mata Yana fita da ita,Siyama nan take kishi ya motsa tace to sai me tunda Kun rabu shi ka kore shi mene na wani cewa Yana bibiyar maka Mata,au dama matarka ce shine harda tashin hankalinka haka da damuwa akan wata banzar Nusaiba,okay na gano son abarka kakeyi sai ya saketa ka dawo da ita,Aslam yace Allah ya baki hakuri ni ba haka nake nufi ba nufina a lokacin ai tana matata ba Wai yanzu ba,Juyawa tayi tace ba komai,fisgota yayi ta fado jikinsa yace ban yarda ba ai Indai kaji bahaushe anyi Masa laifi yace ba komai to wlh da komai dawo nan, dariya ya bata amma ta maze tace ka sakeni nace ba damuwa,yace akwai fa ayita ta Kare a nan baki Isa ba,baki ta turo yayi kissing dinta tare da furta to kiyi hakuri bazan sake ba Ni dai magana ta wuce ya mutu,tace amma kasan.....kafin ta karasa yace dan Allah da annabi kiyi shuru Allah ya baki hakuri ni dai Indai akan wannan ne,Siyama tayi Shuru tana zaune a cinyarsa,yace to ki min magana Mana kiyi murmushi,tace cewa fa kayi dan Allah nayi shuru to nayi shuru,Aslam yace kai Ina Shan wahala dake ai dai nace kiyi hakuri, tace na hakura karka sake min zancen Nusaiba wallahi idan ba Haka ba zaka ga danyen kai,dariya yayi yace to naji bazan sake ba yanzu ma kuskure ne ke kika fassara ni daban,cike da shagwaba tace mutum Kawai ka kawo zancen wata ballagazar banza bazara iskar damuna,Boobs dinta ya cafka ya shiga sarrafata ba shiri tayi shuru duk da cewa ba wani abu zaiyi ba face rage zafi sai ta warke tukun.

    Washe gari Sufyan Ya sake zuwa gidan Aslam bai same shi ba ya fita yayi murna dama Siyama yake so ya gani Yana compound me aiki tace Wai tazo inji Mijin Nusaiba,Siyama Hijab ta saka ta fito bayan sun gaisa rokarta ya dinga Yi dan Allah madam kisa baki me gidanki ya maidani bakin aikina,Siyama tace kasan kayi kuskure Babba kaima Wanda gaskiya ko ni bazan iya Masa magana ba a kanka kayi hakuri tunda yace a'a to fa sai hakuri kayi hakuri Allah ya baka wani aikin,Yace dan Allah Siyama ki taimaka min,Siyama tace Ina ma Zan iya taimakonka da nayi amma bazan iya ba kayi hakuri Kawai ta juya ta tafi abinta haka Sufyan ya fita jiki ba kwari,washe gari Aslam ya Kira Sufyan ya bashi takardarsa ta sallama daga aiki Yana ta rokonsa amma Ina baya Jin Kira.
   Sufyan Yana komawa gida ya iske Nusaiba ta dawo daga gidan iyayenta Wanda ko tambayarsa bata Yi ba,takardar ya wulla Mata ransa a bace yace Kinga abinda Kika jawo min ko,kin gani ko Yar iska dabba wacce bata San me take ba jahila,Yar talla, kin Sa na bakantawa Iyayena kin jawo an koreni daga aiki Allah ya Isa tsakanina dake kuma ki koma inda Kika fito gidan ubanki na sake ki saki daya,Nusaiba tace ka sakeni ? Yace ae zata Masa rashin kunya ya hau jibgarta ya Mata jina jina sannan yace wallahi ko hankici baza ki dauka a gidan nan ba baki zo da uwar komai ba duk ni na siya Miki sabo da Haka ki koma gidan ubanki haka,Nusaiba tana kuka jiki duk kulun duka tafi karfin ta taba komai Dan kuwa shi ya siya mata,Haka ta mike tana dingishi zata tafi,Hannunta Sufyan ya fisga ta Fadi a kasa ya dinga janta tana ihu Kamar wani buhun gishiri haka ya bude gate ya jefata waje ya kulle gidansa ya barta a nan tana ta uban kuka har ta gaji ta mike da kyar ta shiga Napep sai gida,tana shiga da kyar take tafiya tana kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi.

    Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera tana kallon hadadden Office din tace Sannu da aiki yace yawwa suna haka sai ga wata arniya ta shigo da wasu takardu sanye da gown ko gwiwa bata Kai ba komin surarta a waje ta Sha kitson attach tayi kyau gata da hips,Raudah baki ta bude tana kallo shi bai kula bama Signing ya Mata tare da Mika Mata ta karba ta dauki Hanya zata fita tabi ta gefen Raudah,da yatsa Raudah ta dan taba Duwawun matar, Affan yace mene Haka beb? Tace wannan wace? Yace Secretariat ta ce,tace kana nufin kullum sai kaga wannan? Yace mene ne Wai? Baza ka kawo Namiji ba sai mace to duwawunta kake kallo ko me,kalli fa duwawunta kullum da safe sai ka ganta Ina can na saki baki hai a bude Saurayina yana nan yana kallon duwawun Chinaza,wlh Affan idan ka kalli duwawunta bazan yafe ba,Affan yace Wai in tambayeki baki yarda dani ba,haba Raudah kishin nan naki yayi sau nawa zan fada Miki ke kadai nake da ita,bazan iya cin amanarki ba,I will never ever cheat on you Karki bari muyi auren zargi so kike kishi ya halakar dake,Ni wlh Kawai ka canja sakatariya zuwa sakatare Namiji gaskiya ban yarda ba,yace ba laifin data min baki Isa kisa na sallameta ba Kuma bani na kawota ba Liman ne ai kin san gidansa tunda munje tare kin gaishe shi je ki fada Masa ya canja ta Indai kin San haka zaki  to karki sake zuwa Office Dina ya mike tare da dukan table sai data tsorata yace tashi ki tafi gida bana son zargi bana taba ko hannun mace akan kishin banza kizo ki sani gaba ki hanani sakewa ba ke kadai kike da saurayi ba sannan idan niyyar cutarki nayi ta ya Zan Bari ki gane, tashi ki tafi bazan cuceki ba Ina sonki babu wacce nake so sai ke bana ko budurwa bare neman Mata bana son zargi,Raudah mikewa tayi  ta Fara hawaye yace oh my God me na miki? tace ni dai karka kalli duwawunta,yace to naji bazan kalla ba idona ma Zan rufe muje na rakaki mota a haka ya lallaba Raudah ta koma gida.

    Tunda ta koma gida part din Landlady ta shiga suna Hira tace karki yarda da Maza Yar uwa maciya amana ne duk yanda kike da kyau sai sun kula Mata,ki kula da Affan sosai yanda yake da kyau Mata bibiyarsa suke kisa Ido akansa idan ba Haka ba wata ta kwace Miki shi,Landlady ta dinga zuga Raudah,Raudah har da bata labarin sakatariya,tace to ki shiga ki fita a sallameta a canja masa Namiji ko mace me addini, Raudah ta Fara tunanin ya zata yi ai da yamma ta shirya sai gidan Liman
   Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana ta godiya.

    Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi, Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama.
    Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta dakko Masa file sai da ya gaji ya taho da Kansa ya isketa tana ta dukan kirjinta tsawa ya buga Mata tana Adduar bata daina ba tace Sir Allah ya maka gida me kallon bangon gabas,Allah ya baka mace me zikiri....tsawa ya Mata shut up Ina file din da nace ki dakko? tace Sayyadina manzo na shi zai agaza min na ganshi, Assalamualaika ya rasulillah.... Affan yana masifa yace ke lokacin Addua daban lokacin aiki daban,Rabbana.....Rabbana...taci gaba,Affan ya zaro Ido yace ke tafi gidanku na koreki you are fired,zata roke shi ya daka Mata wata uwar tsawa wacce tasa ta fice da gudu,nan take ya Kira Liman ya sanar Masa komai Liman ya canja masa wata macen arniya ce amma Kamar musulma haka take shigarta bata dame jikinta Kuma nutsasiya ce sai dai ita Kuma akwai bin maza Kamar karya haka take in Banda son maza babu abinda ta sani, Raudah tana bala'in sawa Affan Ido akan Shige da ficensa

    Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa, Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa.AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

          81-85Official

By
AsmaBaffa
Page naki ne

FUTURE RM      Kuka Raudah ke yi yaki daga Wayarta Yana can wajen abokansa sai kusan 12 na dare ya dawo Yana bude kofarsa ya ganta a palonsa,tana ganinsa ta mike tsaye yazo zai wuce ransa a bace ta zube har kasa ta durkusa tana hawaye tace dan Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba,Affan ya kalleta shi mamaki take bashi yanda taci kuka,kamar bazai hakura ba yace tashi na hakura ni ki daina durkusa min haka,na hakura ya zanyi Dake tunda Ina sonki na fada Miki bana son kishin zargi idan kishi yayi yawa zargi yake sawa idan nayi niyyar kula wata har zan bari ma ki gane kin San maza kuwa,bana son zargi a rayuwata bana so karki sake min irin haka,Raudah da tana ganin Affan Kamar sai yanda tayi da shi sai taga ashe ba haka yake ba baya takuwa ko kadan Namiji ne bai son raini,tuni ta Shiga hankalinta,yace kije kiyi bacci,ta mike sum sum har ta fita ta dawo tace baka ce kana so na ba,bazan fada ba yau Banga dama ba ya furta Yana hararta,tace to ni Ina sonka yace can da yawarki,tafiya tayi dai zuciyarta ba dadi da safe bata je aiki ba Monday guda Affan bai ce Yana sonta ba tana nan tana bacin rai, Tuesday ma kin zuwa tayi tace bata da lafiya sai ta warke,Affan yaga motarta kwana biyu ba inda ta fita ko a compound basu hadu ba Kuma ko ta window bai leka ba bata leko ba zai shiga mota ya fasa yazo yayi knocking door nata ta bude ya ganta ras da ita taci kwalliya,tace Ina kwana lfy Alhmdllh kwana biyu bakya fita lafiya? Kai nake jira kace kana so na sai na fita,Affan Ido ya zaro yace kina da abin mamaki Raudah....kuka ta saki kaji ko kaji ko Beb dinma ka daina fada sai Raudah,Murmushi yayi Yana kallon ikon Allah,yace sai ance ana sonki dole shine Kika San ana sonki? tace ae ni Indai ana so na Kuma ana son zaman lafiya kullum sai ance min I love you morning, afternoon and night,I love you ya furta tace naji na yanzu Saura bashin na jiya sai da ya fada yafi sau biyar sannan tace yayi haka a dawo lafiya,ya tafi Yana dariyar Raudah.

     Siyama ce ta zuba wani abinci zata ci Aslam yace yayi kadan ki Karo a gidanku ba haka kike ci ba,tana shagwaba tace ai tunkafin ayi min aure Sam bana iya cin abinci bana son ci ma dole nake yiwa kaina Aslam a ransa yace to ga  Kawu yace idan yaga ta rame akwai matsa dole na samo Mata multivitamin,tashi yayi yace da kin fada min tuntuni ai da na samo Miki maganin cin abinci ki dawo normal haka akeyi,Bari naje chemist tace to,yaje chemist din layin yace Multivitamin zaka bani maganin cin abinci babba,me chemist yace Kaine baka iya cin abinci? Yace ae me chemist shi ba likita bane Yar makarantar ma school of health technology ya Fara aka kore shi ai Kuwa ya dauki me karfi maganin boosting din apetite da Kuma multivitamin ya bashi me kyau me karfi yazo ya ebo ruwa ya balla ya bata ta Sha ashe muguwar yunwa yake sawa tare da shegen bacci,Minti talatin ta shafa cikinta tace ji nake Kamar an sace min kayan cikina Honey wayam ba komai,abincinsa da bai ci ba yace sai anjima ta dauke ta cinye tas,tana ci wani mugun bacci ya kamata ta mike tsam ta tafi bedroom dinsa ta kwanta bacci take ba ji ba gani har dare bata tashi ba,zuwa yayi Yana tashinta yace wannan wanne irin bacci ne magriba ta wuce fa har na dawo daga masallaci Daukanta yayi tare da direta a kasa tana tangadi ta shiga toilet da kyar tayi Alwala da Sallah a wajen ta kwanta sai bacci Aslam yaji gidan ba dadi abokiyar tasa tana ta bacci Sallar Isha ma da kyar ta iya tashi ga jikinta ya mutu,Har 11pm tana bacci Aslam sai me aiki ya sa ta Masa girki, yayi wanka tare da Shirin bacci yazo Kawai ya dakko rigar bacci wata sabuwa ya cire Mata kayan jikinta garin cire kayan bacci sha'awarsa ta motsa ya fasa sa Mata kayan yaja ta suka Shige bargo tare zaiyi shagali tana ta faman bacci jiki a mace Yana Fara taba ta sai dai ta bige hannunsa tace ni bana so wlh ka kyaleni bacci,Aslam takaicin magani yasa ya kwashe su tare da watsa su a dustbin yace baza a sake shansa ba haka Kawai ya jawo min tsiya

      Magani dai sai da safe ya saki Siyama da safen ma ba sosai ba,zata tafi kitchen ya riketa yace kalli hannuna yanda ya dawo red sabo da dukanki,dariya tayi tace maganin nan ne gaskiya,Nima Naga alama tace baccin Dadi a Kara min,yace na zubar da dan Iska jiya ya hanani Jin dadi sai hakura nayi amma yanzu ba fashi Siyama tace ai banci abinci ba yunwa nakeji yace to gama aikin ,ta fita ya koma baccinsa,tana kitchen din amma ciye ciyenta takeyi tun kafin ta gama Kamar zata cinye abincin gidan,tana gama soye soyenta ta zauna ta karya ko jiransa baza ta iya ba sai data gama ta koma bedroom dinta wanka tayi ta shirya cikin  Dan Bum short black sai wata rigarsa silk white da digo digon baki me dogon hannu ce da kwala,pcap ta saka me black da adon fari,gashinta kwance a baya tayi bala'in kyau,ta fito daga room dinta sai gashi ya fito sanye cikin Jallabiya arsh Yana kamshi, ka tashi har kayi wanka ashe,Yana can Yana aikin kallonta bai ji me tace ba sai da tace hello sannan ya dawo hayyacinsa,tace ka tsaya kana ta kallona,kinyi kyau da yawa ne shi yasa,jawota yayi jikinsa Yana shakar kamshinta
    Bayan ya karya ya dauketa sai dakinsa domin bazai iya hakuri ba a matse yake,Haka ya soye ya barta da jinya.

     Amarci suke Sha Kamar ba gobe zuwa wata uku Siyama ta murza kiba tayi wani kyau da haske kana ganinta kasan tana hutawa hankalinta a kwance yake,lokacin tace zata je gida ta gaida su Kawu,Ranar wata Sunday  Suka shirya cikin sutura me tsada sunyi kyau matuka Suka fito Yana kallonta yace dole Kawu yace na iya kiwo ya bude Mata mota ta shiga sannan ya zaga ya Shiga yayi driving din su zuwa gidan su Siyama,Yana yin parking ya fito kenan ya Bude mata kofa ta fito sai ga Nusaiba ta dawo daga shago hannunta rike da leda ta siyo manja bai fi na dari ba,ta rame tayi baki sai kallon Siyama takeyi da Aslam tana zare Ido,Aslam ko kallonta baiyi ba,Nusaiba kishin Siyama take yi Bata kulata ba,Siyama ce tace Yar budurwar bazawara daga Ina,Nusaiba Tsaki ta ja tayi gaba fuuu,dariya ta bawa Siyama tace Nusaiba kawarki ce Charity fa Nusaiba ko kulasu bata Yi ba ta fada gidansu tana kuka a gaban Mama,Mama tace wanne Iskanci ne wannan wallahi Kika fasa manjan nan sai dai kuci shinkafa da waken nan babu mai wallahi kudin cefanen da ubanku ya bayar na dauke dari biyar na zuba a dashi dama da irin wannan Yar cuwa cuwar muke yin dan adashin nan namu,Nusaiba tana hawaye tace ni gwara Ina gidan mijina ko gidan Sufyan ne ya fiye min,Mama tace ki Bari kiyi idda Inshaallah hannun Aslam ma zaki koma,ai na kusa iddar Ina sane dake akwai abinda zanyi karki damu yarinya,Nusaiba sai lokacin ta danyi murmushi.

     Aslam kuwa gidan Kawu Suka shiga Aunty sai Murna Siyama tayi kiba an Kara kyau alamar kana gani kasan tana cikin kwanciyar hankali,Kawu ne ya fito Yana kallon Siyama yace fatan dai Jin dadi ne ya sa Kika canja haka ba Sha ka fashe kike Sha ba da Kuma wannan kwayoyin na Karin hasken fata,Siyama tace ni da nake Fara Kawu Jin dadi mana,yace to madalla Allah yayi albarka ya Kara muku zaman lafiya yaro ka iya kiwo gata nan ta canja haka ake so to ke Kuma Kar naji Kar na gani na fada Miki karki sake a kawo min kararki na fada Miki,Aunty tace to ai taji dan Allah,a gida ya barta ta yini ranar sai magriba ya dawo Suka tafi gida ya kaita wajen Mum ta kwashi gaisuwa a nan taji Mum zata tafi Qatar ta koma can ta huta Wai ta fasa auren Indai Shehu ne bata sonsa,daga Nan ya kaita gidan su Sabeer Wanda shima gaf yake da aure.

      Raudah biki ya matso ta koma gidansu can tana Shan gyaran jiki iri iri iri,Affan ma bangarensa ya gama gina gidansa me kyan gaske dama tunda ya samu aiki fili ya Fara siya ya Fara gininsa a hankali gidane flat me shegen kyau,Raudah Kuwa Babanta me kudin gaske  ne Furniture dinta da duk wani kayan da za a zuba Mata a gidan daga kasar waje aka kawo su na musamman,ana Saura kwana uku daurin aure duk wani gyara an gama anzo an shirya Mata kayan gidanta a Kano unguwa ce me kyau ta masu hali dama shi Affan sarkin gayu da son wanka komai sai me kyau,sun gama gayyatar mutane ranar Alhamis duk Dangin Affan maza Suka tafi daurin aure da da abokansa duk acan zasu kwana a daura aure su taho da Amarya,Yan uwansu na zamfara duk sun tafi,an musu masauki a hotel duk mutum biyu daki daya haka Suka kwana washe gari ana yin Sallar Juma'a aka daura Auren Affan da Raudah Kan sadaki Naira dubu Hamsim,Affan Yana gaisawa da mutane Zo kuga wanka wajen ango kowa sai kallonsa yake sabo da gayu,ya juyo kenan Suka hada Ido da Yusuf Yayansa ya saka Dan Yadinsa da gani kasan wahala yake Sha,Cin Amana ba kyau,Affan ya karasa wajensa suna mugun Kama yace yaushe kazo Yaya? Baka gayyace ni ba naji labari nazo ai, Affan gefe ya ja shi yace a Ina kaji labari? Yace Nabeela ce ta fada min komai naka har IV ta tura min a waya,Na dade Ina Neman Ina zan ganka na roki gafararka Affan ban ganka ba sai da Allah ya hadani da Nabeela ta fada min inda kake da aikinka da kake da aurenka,Affan kayi hakuri ka yafe min,nasan naci amanarka a matsayinka na dan uwana,ka sadaukar da komai naka a kaina dan na samu ilimi nayi kudi na dawo na dauki nauyinka amma ban saka maka da komai ba sai jefaka cikin kunci nasan na zalunceka Affan na jefaka cikin kunci ka yafe min Affan na gane kuskurena Kuma Inshaallah Zan gyara ka karbeni a matsayin dan uwanka Karo na biyu,ka bani dama na gyara kuskurena,Yusuf Yana hawaye Yana magana yace I missed you Affan,Affan yace ba komai Yaya na yafe maka da Kai da Nabeela na yafe muku,tazo wajena naji abinda ya faru da Kai Allah ya kiyaye gaba,Yusuf yace Ameen yanzu da kyar na samu Offer teaching a secondary school kasan aiki a kasar nan,Affan yace karka damu Yaya Inshaallah Zan sa uban gidana ya baka jari ko da milliyan uku ce ka Fara kasuwanci ko ya yake kaga kana aikinka kana kasuwancin ko yaya ai yafi,Godiya Yusuf ya dinga zubawa yace ba komai ai kai dan uwana ne jinina bani da kamarka Yaya,muje ku gaisa da Liman shine uban gidana ya jashi Suka gaisa,ya kaishi wajen surukinsa Baban Raudah suka gaisa daga nan mutane duk sun tafi kowa ya hada karensa daga Sayyeed sai Ango sai Yusuf.

    Hotel Suka koma Affan cikin kayan da yazo dasu akwai shaddar da bai saka ba sabo da tela Wai ya Masa Katon dinki me Fadi Yusuf ya Fishi kiba kadan sai ya bashi yace yayi wanka ya saka suje yaga Raudah yawa ne aga Yayana guda da local yadi,Dariya Yusuf yayi yace kana nan dai Affan Kai da wanka Amana ne haka yayi wanka yasa shaddar dai dai shi yayi kyau Kuwa ya fito Suka tafi,Raudah anci gayu Yarabawa sun cika gidan suna ta kade kadensu na yarabawa suna tikar rawa,Raudah ma tana cikinsu sabo da abokan arziki ne Kawai, Affan ya kirata a waya tazo su gaisa da Yayansa,Raudah ta fito harda Jin kunya ta rusuna harda durkusawa ta gaida Yusuf ya amsa Yana cewa tashi tashi Raudah na gode Allah ya baku zaman lafiya,kin ganni feel free duk abinda ya Miki ba daidai ba just call me,dariya sukayi Sayyeed yace mu wuce dare da nayi,Affan a gurguje ya sa Mata number Yusuf ya bawa Yusuf Number Raudah Suka taho gaba dayasu Uku a jirgi Affan shi ya biya Yusuf.

    Suna zuwa Kano sai da ya kaishi gidan Amarya da ya gida ya gani,Yusuf yace gidana da ka sani da fa sun kwace amma dana dage da addua sun dawo min da gidana motocin Suka rike Kawai, Affan yace Allah zai baka wata Inshaallah
   Zuwa dare aka kawo Amarya a jirgi daga Yan Uwa sai wasu yarabawa Mata su Uku abokan arziki,a gidan Liman ake shagali can aka sauki bakin Amarya da amaryar gaba daya tana can gidan Liman,Yusuf a wajen Su Affan zai kwana gidan hayar Affan inda suke zaune da Raudah can aka sauki baki maza,Suna kwance a bed daya Affan da Yusuf sai hira suke Affan yace muyi bacci ni gaskiya bacci zanyi gobe Ina wajen Amarya bani ba bacci gobe gwara nayi nawa yau,Yusuf yace zumudi Affan ko kunya babu, ya kamata idan anyi nisa da amarci kazo kaduna gidana kaga matata da yaro na,Affan yace zanzo amma ya kamata ka maida Nabeela tunda gaba dayanku Kun gane kuskuren ku,Nabeela Bata so na Affan sabo da kudina ta aureni lokacin amma a gaskiya Kai ta ke so ni yanzu na samu me so na tsakani da Allah Waheeda matar arziki ta isheni idan ta samu miji tayi aure, Affan yace to shike nan Allah ya bata na gari ni dai gobe i yanzu Ina can ana min shagwaba da kuka,dariya Yusuf yayi yace wlh karka daga kafa ranar farko ta wuce ka tafi ko wacce rana dadi,Affan yace ahaf ai sai dai in Suma naga tayi  Suka Yi dariya suna hira har bacci ya kwashe su.

    Washe gari da Yamma Amarya Raudah tayi wanka ta hade cikin wani material pink ya hadu ta zuba kyau dinkin fitted gown kamar readymade ta sha mayafi me daukan Ido shima pink komai pink takalmi da jaka pink lady in pink,Wanda Suka kawota ne Suka kaita gidan Miji ko digon hawaye Raudah bata Yi ba sabanin ta taba aure sannan Kuma ba a gida take zaune ba idonta Kar a cikin Mayafi.
   Abokan ango duk sun ware Yusuf Kuwa Affan Dubu talatin ya bashi cash cikin gudunmuwar da ya samu ya tafi gida abinsa Yana farin ciki.

    Yan Kai Amarya suna kaita Suka bi jirgi Suka koma tun yamma aka bar amarya ita kadai sai Landlady data Kara gyara Mata gidan ta kunna turarukan wuta ta fesa room freshner a ko Ina bedroom uku ne a gidan ko wanne room da toilet Palo guda biyu sai kitchen sai wata toilet din kofarta daga wajen Compound,akwai tsakar gida yaji interlock da flowers,ga parking space zai ci mota hudu suna zaune da Amarya da landlady,Landlady tace ki sa Ido akan mijinki Kinga kyakyawa Kika aura mazan yanzu sai ka sa Ido in ba Haka ba zai barki a nan gida yaje Yana kula wasu a waje,motsi idan yayi ki dinga kula da shi sannan ki Masa biyayya ki rike mijinki Hannu bibiyu amma karki barshi haka sakaka maza mayaudara ne mazalunta ne,Kinga Raudah Namiji ba dan goyo bane ki kula da Shige da ficensa,Raudah tace na gode ya zama dole na sa Ido akan mijina,Affan da Yamma rana Kiri Kiri 4pm ya shigo gidan yazo ya tsallake Landlady ya ajiye hularsa a saman bed kusa da Raudah ya shige toilet Yana ce musu sannunku,Alwala yayi ya fito ya fice,bayan an idar da Sallah ya sake shigowa gidan ya bude wani daki ya fito ya Shiga dakin da su Raudah suke gabanta yaje ya duka tare da Kai bakinsa saitin kunneta yace kinyi Sallah? Kai ta daga masa Yace to me Zaki kici cikin rada ance min tun safe baki ci komai ba kinki cin abinci ko sai na baki da kaina,Murmushi tayi ba shiri tace ae, Landlady bata San me suke cewa ba ya gama ya fita,ba afi 15mnt ba ya dawo ya sake shigowa cikin akwatunansa na kaya ya bude akwatinsa daya ya dauki wani turare ya zuge ya fita, Landlady ta dinga dariya tace yau kin shiga Uku Raudah tashi zanyi na tafi tun kafin ya koreni da Kansa,Raudah ta rike Landlady tace dan Allah karki tafi yanzu ki bari sai dare wallahi kina tafiya Affan bazai kyaleni ba Raudah harda hawaye, Landlady taci gaba da zama suna Jin Affan a tsakar gidan yana duba gidansa Yana kakale kakale dole shi sai yaga Amaryarsa ga Landlady taki tafiya,a daddafe ya hakura ya dawo ta jikin windown baya ya bude tare da lekowa bayan ya janye labilen gefe da hannunsa,Raudah da Landlady Suka juyo ya kalli Raudah tare da sakin Murmushi ya daga Mata gira daya, tace mene ne cikin sanyi yace babu sauro a gidan ko? tace ae,yace okay ya rufe window din, ciki ya sake shigowa ya wuce su yayi Alwala ya fito ya tafi masallaci,Suma Sallar sukayi,ai Affan ka rantse ya Riga liman yin Sallama ana idarwa sai gashi ya dawo ciki yace yau da wuri Zan kwanta  Landlady Wai a nan Zaki kwana ne na nuna Miki bedroom dinki? Ki tashi ki tafi gidanki mana,Raudah ta rike Landlady,Affan yace nifa babu me Kaiwa zuwa Sallar Isha a gidana anyi magariba na gaji hutawa zanyi, ba shiri Landlady ta mike ta yafa mayafinta ta dauki Jakarta tace na tafi sai Watarana kuma,Affan harda daga Mata hannu yace bye... Ya bita a baya ta shiga motarta ya bude Mata gate ta fita lokacin Abokinsa ya kawo Masa katuwar Leda ta kayan ciye ciye ya rufe ya garkame ko Ina ya dawo ciki yana cewa harka iya harka.

   Yana shigowa ya yasa hannaye ya dauki Raudah tare da dan shillata Yana murna dariya tayi ba shiri ajiyeta yayi ya dakko plate tare da zuba musu nama ga fruits Salat ga su Madara da sauransu,Raudah yunwa take ji amma tsabar gulma wai bata Jin yunwa yace Kinga ni dake babu haka ko kizo muci ko na Miki dura ko kici ko ma baza kici ba yau a gidan nan sai nayi abinda nake so dake,Raudah ta sakko kasa ya jawota jikinsa taji wani kamshi yake fitarwa na musamman Affan yayi ta furta a ranta tace sabanin Hussain shi idan ta sa kanta wajen hammatarsa har wani wari tana tashi tana bugawa da hamami Affan Kuwa sai kamshi da kamshi,Raudah tace in baka labari? Affan yace Ina jinki tana dariya tace wallahi tsohon mijina Hussain warin hammata yake har dauke numfashina nake Watarana sai yayi kwana uku baiyi wanka ba,Affan bata rai yayi sai kace wacce ta yabi Hussain din yace ku Wanda kuka taba aure Kuna auren wani sai ku dinga zancen tsohon mijinku,Raudah tace Yi hakuri ai ba yabonsa nayi ba,ae amma kin kwanta a jikinsa ai har kinji warin hammatarsa Raudah tace tab mutumin da bashi da lafiya sai fa muyi sati nawa bamu hada shimfida ba sabo da yasan ba abinda zai iya sau tari ma Yana wajen Shan giyarsa idan ya dawo sai bacci fa bamu hada makwanci ma,nice ma nake dan zuwa,Affan yace ae ke ga mayyar Banana ko to ai gata kin samu ta me lafiya,Raudah tace Allah baka hakuri yace ameen karki sake min Maganar Hussain ko Hassan ne ba ruwana,Juyowa tayi suna facing juna tace I said I'm sorry ko,shuru ya mata,chakulkuli ta Masa tun Yana fuskewa ya Fara dariya sannan da kanta ta Fara bashi Naman itama tana ci har suka gama ciye ciyensu sannan tace bari naje bedroom Ina zuwa ta mike ta tafi bedroom dinta ta shiga wanka,Shima brush yayi sannan ya Fara wanka Kamar zai cire fatarsa haka dama yake wanka,har ta fito ta shirya cikin kayan baccinta green me digon digon yellow ta sha kyau ta shafa turaruka tare da gyara gashinta,Abaya ta dora a Kai da hijab ta dawo dakinsa har ta dawo Yana ciki Yana uban wanka a haka ma Wai sauri yake har ta gaji da jira sannan ya fito sanye da rigar wanka Fara Yana goge sumarsa da towel ya fito ya Fara Shafa lotion dinsa me kamshi ya gama ya dawo ya gyara sumarsa Yana fesheta da kayan kamshi ya gama,yazo ya shafa turarukansa masu kwantar da hankalin me Shaka Jallabiya ya bare sabuwa Fara ya saka ya juyo ya kalleta Yana Murmushi Suka tada Sallar Isha sannan yayi Nafeela ya musu addua yanda addini ya koyar,jallabiyar ya cire daga shi sai boxers yace Amarya tashi a cire Miki Kaya yau juice dinki Zan sha,Raudah ta fara Jin wani tsoro

    Ya zare Mata abayar Ashe harda rigar baccin ya hado gaba daya,Raudah ta saki Kara tana Kare jikinta, Affan Yana gani ya zauce ya rude ya wani susuce,saman bed ya turata a hankali ta fada,tace a kashe light kunya nake ji,yace Ina dole na kalli komai nawa,ya samu Raudah ya Fara murzata jikinsa Yana tsuma yace kwalele dai ya Kare yau kin Zama tawa, Raudah ta fara hawayen tsoro ya fara shafa kirjinta yanda yaga dama bai san Sanda yace Hussaini kayi asara babba ka cuci kanka,tunawa yayi ance bashi da Lafiya yace Allah ya baka lafiya Usaini ka samu kalarka me wari,duk ya rasa ta inda zai Fara,Raudah ya kalla yace ta Ina Zan Fara ne abin dadin naku yayi yawa,Raudah da mugunta tace ta tafin kafa zaka fara,yace amma bakya kaunata ya Fara Mata ta yatsan kafa Yana lallasheta a nutse,Abinka da dama a kusa ake Raudah tuni ta daina wani iskancin hawaye tana karbar darasi,Yana sarrafata idan taji wani dadin sai ta Fara tayashi suna jiyar da juna dadi,kirjin Raudah yau yaga ta kansa da bakinta,har ya gangaro down Yana Mata salo basa iya magana sai Nishi da kuka sweet,Affan gaggawa yake Yana Jin Raudah  wet ya nemi hanyarsa gam gam da kyar da kyar ya samu Hanya,Raudah sai kukan shagwaba da kisisina,Affan Kuwa Kamar mayunwacin Zaki ya samu nama gashi abokai sun zugashi yaje Wai an bashi maganin gyaran jikin maza Wai Mata kullum a gyara suke idan Namiji baiyi gyara ba shima zai kasa aiki ai Affan yasha magunguna shima Wai ya gyara kansa ai Kuwa ya dinga surfa aiki sai da yayiwa Raudah jaga jaga,Tasha uban kuka ta godewa Allah amma dake da wayonta Bata yin irin kukan tsiya na yaran Yan Mata ba,Affan Yana ta lallashi an rasa wace macen a ciki sabo da farin ciki da Dadi sai wani narke Mata yake a jiki Yana shagwaba,Yana goga fuskarsa a tata yace yau kin samu Nutrients ko? I love you my one and Only Raudah kiyi abinda kike so, Inshaallah bazan taba cin Amanarki ba,tashi muyi wanka harda wani dan ihun murnarsa ya dauketa sai toilet.

   Tunda ya kaita yake faman gasa Mata jiki sai data ji dadin jikinta sannan ya Fara Mata wanka da Sabulu, a iya wanke Fuska ma an cinye lokaci me tsawo,aka dakko Intimate wash na wanke gaban mace masu kariya daga infection,Raudah ta kwace ta wanke da kanta da ruwan zafi,ya Fara Mata wanka Kamar baza a daina ba sai da Raudah ta gaji ta saki kuka sannan ya kyaleta ya dauraye Mata jikinta tayi wankan tsarki ta fito da kyar,shima yayi ya fito Yana ta faman nishadi Kamar zai goyata haka yake ji da ita.

    Washe gari daga gidan Mallam aka kawo musu lafiyayyen kari,Affan Yana ta fama da jinyar Raudah ana lallabata har dare ya sake yi tana kwance a saman bed tana latsa waya,Shi Kuma Yana zaune yana aiki a laptop dinsa tana saman cinyarsa Yana shigar da aikinsa,wayarsa ce tayi Kara ya duba yaga wata Yar BUK ce da Suka Yi Service tare Mardiyya,Wayar ya daga tare da furta hello Mardiyya ya kike,Ai Raudah tana ji ya Kira sunan mace Mardiyya ta mike zaune,Yana gaisawa da Mardiyya ta dawo jikinsa ta baya ta hade kirjinta da bayansa sannan ta Mika kunnenta jikin Wayar Wai sai taji me take cewa,Yana jinta yaci gaba da wayarsa ya aikin to kwana biyu kin buya,Raudah ta zaro Ido waje tare da sake tura kunnenta jikin Wayar Affan Yana ji,Mardiya tace dama Kira nayi mu gaisa yace na gode na gode ya kashe wayar, Wayar hankalinsa na Kan system Raudah a hankali tace wacece? Yace wata ce da Muka Yi service,Kuma macece fa Baby, tana da aure? Yace Ni kin tuna min ma na manta na tambayeta Yaya saurayinta da zai aureta naji auren Yana nan,Raudah tace au saurayine ma da ita ba Miji ba? Akwai danger gaskiya,yace menene haka Raudah? Kince fa kin daina yanzu Zaki Fara halinki ko,Raudah tace to ai laifinka ne Sanda nazo na Kara kunnena zanji me kake cewa shine kayi waye ka rage Volume Dan Kar naji,Affan yace wanne irin rage Volume nu ban danna komai ba kina gani waya Kawai nake,Raudah ta sake manne jikinta a nasa tasa hannunta tare da sakalo shi ta wuyansa tace ni na gani Sanda ka Danna Kaine baka kula ba,Ohhhh Wai me yasa kike min haka,Raudah tsoron fadansa taji tace okay naji amma dai ka kula saurayine da ita fa ba Miji ba,Affan ya girgiza Kai Kawai yace to aiki nake koma ki kwanta,Raudah tace oh korata kake Yi sabo da kayi waya da mace har ka Fara gajiya dani kwana daya,yanzu laushin kirjina fa kake ji duk ban kyauta ba because of that useless girl Mardiyya, Affan yace yi hakuri ni ba korarki nake Yi ba Yi zamanki a Haka,Raudah ta gyara sosai tare da makalkale shi a haka yake danna system din,Yana gamawa ya juya kanta,ta jawowa kanta Yana ta kokarin barinta sai ta warke amma ta jawo sha'awa baza ta bari ya kyaleta ba ya koma tare da hakkewa a kanta tana kuka tana rokonsa amma Ina Sam babu daga kafa.

   Suna ta soyayyarsu da Raudah kamar zasu lashe juna har sati daya sannan ya koma aikinsa shima badan ransa ya so ba,5pm Raudah gida yaji gyara ko Ina ya dauki sheki da kamshi ta gama girki ta shirya a dining taci uban gayu na musamman,Yana shigowa ta tareshi tace Kai da kace 5 zaka dawo kalli time 5:30pm fa Ina ta jira,yace wani dan aikine ya rikeni,kayan jikinsa take karewa kallo taga wani waje yayi Kamar Kalar Powder ta Mata,tace mene wannan Kamar powder din mace,bani hannunka ta jawo Hannun Affan ta shinshina tace bani dayan naji shima ta shinshina tace yawwa babu komai,Raudah tayi kasa ta Fara kokarin janye Masa wando tace tsaya na gani,Affan ransa ya baci cikin tsawa yace Raudah tsorata tayi ta sake shi da sauri ta Fara bashi hakuri,yace Kamar fa kin Fara haukacewa kishi ne zai haukataki idan baki Wasa ba,wallahi idan nayi niyya ke baki Isa ki hanani kula wata ba,daga auren zan Fara kula Mata,ki kwantar da hankalinki ke kadai nake da ita,tace to ni ko mene kazo wajena ko me kaji kana so ka dawo gida Zan baka, Affan ya samu salon wayon da zaina Mata dama tana damunsa da kukan zafi da kyar take yarda da shi, tunda hakane shi yaga hanya,Murmushi yayi Yana Jin dadi yace ke nake bukata Ina cin abinci,tace ka Bari Mana sai 10pm ni wlh zafi,yace okay so kike na fara yin Yan Mata...Raudah da sauri tace ba damuwa muje ko Mene Zan maka Kawai ka fada zanyi,yace Kuma har 10pm din Zan sake round 2 tace to da sauri, Wai ita Kar yayi budurwa,idan zai fita da kuka suke rabuwa ita bazai fita ba sai dai su zauna tare a gida.AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️ AUREN MUπŸ›’️

           86-90


Official

By
AsmaBaffaPage naki ne
AIDA MAMAN TASNIM


     
      Nusaiba tana cika Iddarta ta shirya a boye sai gidan Aslam tana zuwa taga gidan ya sake haduwa komai an canja Masa new design,a bakin  gate ta tsaya ta kasa shiga gida tasan ba halin shiga idan ta tuna abinda ta aikata gate din take shafawa da hannayenta tana zubar da hawaye ta Dade a haka har ta gaji ta juya gida inda ta fito,washe gari gidan Sufyan ta shirya taje gidan ta zaci gwauro ne bata san Yana sakinta da wata daya ya koma ya nemi gafarar Iyayensa ya auri tsohuwar budurwarsa Zahrau sun rabu tana sonsa Yarinyar kirki Yar tarbiyya ai Kuwa Yana aurota bai Dade ba ya samu Offer a land and housing sai dai albashinsa ba Kamar na Aslam ba amma ba laifi,yanzu iyayensa da Yan Uwa duka komai Yana musu,Zahrau har Kara takura Masa takeyi akan dole yayi musu abubuwa,Nusaiba tana Shiga gidan taga Zahrau tana gyarawa Sufyan kwalar rigarsa suna dariya cike da so ai kasa karasawa tayi tasan yayi aure ta juyo da sauri ba tare da sun ganta ba,ta dawo gida sai kuka Wanda ba shiri Mama ta shirya ta tafi gidan da Mum take ta manta irin wulakancin data Yi Mata lokacin da Mum tazo a gyara.

    Mama gidan da Mum take ta shiga tana ta kwada Sallama Hajiya Zainab ta tafi gidan biki sai Mum,Mama tana ta sallama ba ji ba gani Mum ta fito sai taga Mama Fuska ta daure cike da bala'i Mum tace Wai wace ne ta damemu da Sallama taki ci taki cinyewa,Mama ta marairaice tare da langabar da kai tace surukata...ohhhhh da baki san ni surukarki bace sai yanzu dan Allah malama Fadi me ya kawoki sauri nake yi Ina da aikin yi,Mama tace zuwa nayi Dan Allah Surukata ki taimaka kisa danki ya maida Nusaiba dakinta dan Allah kuyi Hakuri komai ya wuce zamu gyara Inshaallah dan Allah ki taimaka Mana,Mum wani kallo ta Mata up an down sannan ba tare data furta komai ba ta tofar mata da yawu tuf ta juya tare da komawa ciki ta bar Mum a tsaye kikam,gajiya tayi da tsaiwa ta juya ta koma gida dabarunta sun Kare dama duk Shirin da tace shine kawai zata yi,Nusaiba ana gida zaman gida Wasa farin girki, bayan wasu Yan lokuta Shehu baya dagawa mama da Nusaiba kafa baya sakar musu fuska da Mama da Nusaiba wahala suke Sha sauran yaransa yake yiwa abinda suke so kawai,suna haka katsam sai ga Aslam,Shehu Yana gida yace a'a dana yau Kaine a gidan? Aslam yace ae Abba ya zauna kusa da Shehu a tabarma ya gaisar da shi ko kallon Mama da Nusaiba baiyi ba Wanda gasu nan a tsaye sun taho da sauri sun tsaya musu a kai suna magana kasa kasa da ita da Nusaiba,Shehu yace ashe haka arzikinka dama yana nan ya dawo naji labari Ina ta so ma nazo har gidanka Allah mun gode maka,Aslam yace Abba Kai na daban ne nasan me kaunata ne Kuma babban mutum ne Kai idan ba damuwa bana Inshaallah zamu tafi aikin Hajji tare da Kai,Shehu yace wayyo Allah dadi kashe ni Aslam ya dinga dariya,Nusaiba da Mama harda murna tunanunsu bikon Nusaiba zaiyi shi yasa ya Fara kashe musu kudi irin da,Aslam yace Kawu ba iya Makkah zaka tsaya ba Paris da Dubai zaka je inda Nusaiba take mafarkin zuwa yanzu gashi Shehu Babanta shi zai je Kuma Aslam Yana sani yayi hakan Sabo da farkon aurensu haka tace sai an kaita honey moon Paris ko Dubai,yace sannan duk Sanda kaji kana son hutawa Abba karka damu ka hada kayanka kazo gidana ka huta,ko me kake bukata Kawai ka kirani a waya,Shehu Kamar yayi suman dadi haka yake ji gani yake Kamar a mafarki,yace Kuma tare da abokinka zaku je Baban Siyama Kawu da Aunty,Shehu yace Alhmdllh na gode na gode ya dinga godiya Yana murna,Aslam yace Maganar shirye shiryen visa Zan kiraka a waya ya mike ya zaro Yan dubu dubu ya mikawa Shehu yace gashi kayi amfani da wannan,Mama ta dafe kirji,Nusaiba Hawaye ya Fara antayo Mata a kumatu,Mama tace surukina dan Allah kayi hakuri abinda Muka maka,Nusaiba tace dan Allah ka yafe min ka dawo muyi aure,Aslam yayi hanyar barin gidan ya juyo yayiwa Nusaiba da Mama kallon banza yace mugaye kawai yaja Tsaki ya juya shi da Shehu Suka fice,har mota Shehu ya rakashi ya tafi sannan ya dawo Yana taku dai dai Yana doro,Shehu yace Alhmdllh Yana takama a gidan ya zama Dan gayen dattijo aka bar Mama da Nusaiba da bakin ciki.

    Aisha tuni an maida Aurenta da Farooq suna zamansu lafiya yanzu duk Karya da fadan da sukeyi sun daina sai mutunta juna kowa baya so wani Abu yazo ya shiga tsakaninsu,soyayya suke me tsafta abinsu su,Nabeela kuwa tana yin Idda ta samu miji wani babban mutum ne me Mata ta hakura da Affan tasan babu aure a tsakaninsu ma tunda Dan Uwansa Yana raye amma ta take gaskiya yanzu Kam ta hakura ta auri me Mata Kuma tayi zamanta babu Neman rigima,Sabeer ma yayi aure ya auri zankadediyar  matarsa Habiba.

    Raudah da Affan suna soyayyarsu sosai matsalar Raudah kishin tsiya,yau tana zaune a gida Affan ya fita sai ga Wayar Landlady ta shigo tana ta kiranta dagawa tayi tun kafin tayi magana Landlady tace Raudah maza maza fito ga mijinki Affan da wata sun shiga shopping zo ki gani da idonki,Raudah tace what? Na fada Miki maza basu da amana mijina haka ce ta rabamu da shi na aminta da shi Ashe maci amana ne,gani Ina ShopRite maza kizo kafin ya bar wajen, Landlady tayi gaskiya domin Affan ne da wata zasu shiga ciki ita Kawai dan ta ganshi da mace shine tace budurwarsa ce bata San cewar Amaryar liman bace ogan Affan Kuma Liman dinne yasa Affan ya kaita wajen wata Mata  suna business tare da matar Liman,matar daga kasar waje tazo shine Affan ya kaita.

   Raudah hijab ta zurma ta fito da uban gudu tare da bude motarta ta shige ta Mata key motar taki tashi tayi tayi motar taki ta fito da sauri daga gidan sai ga yaron Affan da machine yazo gidan zai karbi takardu,da sauri tace dan Allah kaini ShopRite sauri,ya zaci ma wata masifa ce ta faru ya juya machine ta hau da sauri tana cewa kayi gudu Yi sauri Salahu dan Allah Yana tambaya lafiya Hajiya? Kayi sauri please duk ta gigita me machine suna ta fyalla gudu a titi tana kayi sauri ka Kara wuta Yana tsinka gudun gaske a rude yaje ya daki mota Suka watse a gefen kwalta Raudah ko motsi bata Yi kanta ya fashe daga gefe Yana jini,me machine din Kuwa Suma yayi Yana farfadowa yasan inda yake sai raunuka da yaji,mutane sun taru akansu aka kwashi Raudah da Salahu yaron Affan zuwa asibiti,lokacin Affan ma ya koma Office Kawai yaji Kira Yana dagawa ya mike Zumbur a gigice Yana tambaya a wanne asibitin ya tafi da sauri figi motarsa sai asibitin,matarsa Kawai yake cewa dakin da Raudah take aka kaishi Yana Shiga ya iske ta farfado amma ta karye baras a kafa sai kanta an nade daga gefen da bandage,tana ta kuka a kwance Affan bai ma tambayi me ta fito Yi ba Kawai ta lafiyarta yake Yi,ganin tana ta kuka ya Fara lallashinta,a gefenta ya zauna tare da maida kanta jikinsa Yana lallashinta tana hawaye yace Inshaallah Zaki warke kinji,anjima kadan za ayi aiki a dora min ke,ya Isa haka kukan Affan ko aiki sai mataimakinsa yayiwa magana ya kula da komai ya tafi jinyar matarsa sai ta warke zai dawo ya sanarwa liman gaba Daya family Suka Zo dubiya har Liman,a ranar aka dora Raudah ana ta zuwa dubiya har Yusuf da matarsa sunzo,shi kuwa yaron Affan tuni ma an sallame shi sai da Raudah ta kwashe sati biyu a asibiti Affan shike jinyarta shike Mata komai bai bari ma yan uwan Raudah sun zauna ba tunda suka zo dubiya,mamanta ce ma ta dage sai da tayi sati guda a asibitin sannan ta koma.

    Wheelchair aka bawa Rauda da sandunan koya tafiya lokacin da aka sallameta,Raudah tana tuna dalilin fitarta daga gida sai hawaye da kukan takaicin halinta tana nadama da Dana sani,gashi Affan din yand a yasan bata tambaye shi ba ta fito amma ko zancen bai Mata ba ta lafiyarta yake Yi ya daina zuwa aiki sai jinyarta shike Mata komai ita Kuwa me zata ce da wannan bawan Allah tayi dacen miji da wani ne sai dai a kaita gidansu in ta warke a dawo da ita, motar Affan ce ta shigo gidansa ya fito ya Bude dayan bangaren sannan ya bude booth ya dakko wheelchair ya dakko Raudah tare da dora ta a Kai tare da rufe motar ya turata a hankali zuwa ciki,Raudah tana ta zagin kanta a zuciyarta abinda ta aikata,Affan gwani ne wajen gyara da tsafta sai da ya gyara gidan nan tsaf sannan ya yiwa Raudah wanka shima yayi ya dorata saman kujerarta suka fito,ya shiryata cikin gown gajera marar nauyi,abinci yayi order aka kawo musu har gida suka ci sannan ya fita masallaci ita Kuma tayi sallah a zaune saman kujerarta.

    Washe gari tana Palo tare da Affan suna kallo Landlady ta shigo bayan sun gaisa Affan ya koma bedroom ya basu waje,Rauda ta kalli Landlady tana hawaye tace kin cuceni ke ba matar kwarai bace Kuma ba abokiyar zama bace,sam bakya Dora mutum a hanyar gaskiya gashi nan abinda Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala,Ina zamana da mijina lafiya ke kin kasa aure kinzo kina zugani bakya taba yabon maza sai dai ki Fadi sharrinsu shi yasa da yawa wasu matan idan Suka taru basu da aiki sai fadan sharrin maza basu fadan alkhairinsu a haka wasu Wanda suke zaune lafiya da mazajensu shike nan an gurbata musu zuciya sai su Fara zargin nasu in ba a yi sa'a ba rashin zaman lafiya ya Fara kenan,Mata in Suka taru basu da aiki sai zagin maza da halayensu ki sani wata idan bata dauka ba wata dauka zata Yi karshe auren ya mutu ma,ba kowa ce take auren miji me kule kulen mata ba Kamar mijinki da Kika taba aure Bmbai yuwuwa kiwa maza kudin goro,na Zama sakarai da ilimina da hankalina na zauna Ina daukan shawararki landlady kiji tsoron Allah kije kiyi aure ki daina lalata Mana namu,kuma Indai zugace zata kawoki gidana karki sake zuwa inda nake bani ba bake har abada,kin girmeni babbar mace ce ke amma baki da tunani, Landlady tasan itama bata kyauta ba tace kiyi hakuri Raudah wlh aurena dana Yi na fuskanci halin mijina kenan sai nake tunanin kowa ma haka yake wannan yasa na kasa kara yin aure amma Inshaallah nima na gane gaskiya,Raudah tace oho Miki ni dai in bada alheri Zaki Zo ba karki sake zuwa gidana yanzu ma ki tashi ki tafi, Landlady ta mike jiki ba kwari ta tafi,Raudah tana hawaye Affan ya fito yace Wai me yasa kullum sai kinyi kuka ne kina Jin sauki fa kin kusa fara tafiya da kafafunki Inshaallah.

   Raudah tana kujerarta ta miko hannu tare da rike hannun Affan tana hawayenta tace dan Allah ka yafe min na tuba bazan sake ba,ta bashi labarin komai zugata da Landlady keyi tace karshe gashi ta kaini ta baro na karye ta fashe da kuka,Affan yace ai Raudah tunda naji kinyi hatsari nasan kishi ne ya fito dake shi yasa ma ban tambayeki ba nasan baki da wata matsala face kishi,abinda yasa Kuma bana damuwa so ne a kaina akeyi Kar wata ta kwace ni to ni ai na Zama dan gata gashi kin jawa kanki kin karye Allah ya takaita ma,haba wifey babu izinina Kika fito haba Raudah kishi fa idan yayi yawa zargi yake kawowa,da sauri tace wlh bana zarginka Kawai in ta zugani ne sai naga kamar haka ka yafe min kayi hakuri bazan sake ba babu ruwana yanzu gashi na karye a banza,Affan ya kyalkyale da dariya tana hawaye ta duke shi a kafada,yace ai Ni Kika jawa aikin,ki sani bazan taba cin Amanarki ba na Sha fada miki,to yanzu idan ta kasance Zan Kara kishiya yaya kenan Raudah? tace ai ma Inshaallah baza ta faru b,to idan ta faru fa? Mutuwa zanyi Kawai,yace kin gani wannan halin naki sai ke Kika ce kin tuba kuma? Baki ta turo tace ae na tuba bazanyi fada ba bazan ce komai ba Kuma bazan bibiyeka ba sai dai Kawai aga na mutu,Affan yayi dariya sosai tace ai kana da kyau ko wacce sonka zata dinga yi ni Kuma bana sooooo....ta karasa da kuka,To yanzu Raudah nifa ba ni nayi kaina ba Nima tashi nayi na ganni haka,Raudah tace ka kakalo shi Mana tunda kana ta gyara jikinka kana daukan wanka kullum kayi ta matso kyawunka kana fita gashi nan sai kafi 1h a toilet kana wanka duk ka goge fatarka kullum fari kake sake Yi kullum gashi nan bature kake Zama,Affan dariya Kamar me yace to na daina wankan sai na zauna miki a kazami gobe kice Nima Ina warin hammata,yanzu sai kince kin tuba kin daina ko? Raudah tace Zan dinga yiwa kaina Addua kaima ka tayani,Affan ya sake sakin dariya tace wannan ba abin dariya bane kaje kullum kayi ta gyara Suma ba ji ba gani ko wacce Yar iskar budurwa tana zare Ido gashi nan gaf ake da yaye dalibai daga Yan secondary zasuyi candy gashi Yan University sun kusa gamawa naji a labarai ance final exam zasu zana Kuma Yan Service sun gama miji suke jira wallahi ta Allah ba tasu ba, Affan har wani dadi yake ji ana kishinsa yace to ya Isa me Miji,Raudah tace kayi hakuri na tuba Allah kishi irin na baya da nayi bazan sake ba amma zan dinga dan yin kadan kadan shi yasa nake baka hakuri kayi hakuri dani Dan Allah har Allah ya yaye min,Affan yace to an gama Raudah,no your love zaka ce ta gyara masa Yace Okay My love,My one and only, My Heart,My soul my life Kuma Queen dita,Raudah Murmushi tayi tana Jin dadi tace ga mijina me jinyata me so na wata tazo itama Watarana ayi jinyarta haka dole naji haushi,kwana nawa baka Yi komai dani ba lafiya iceko? Affan yace Baby rigima baki da lafiya a karyen zanyi wani xxx dake,Raudah tace a'a in kana so kayi Zan maka komai Zan daure ai na Fara Jin sauki kafar basai a lallabata a gefe daya ba,Wai wayo take wa Affan Kar ma yaji Yana so ya Karo aure tunda bata da lafiya ko yayi sha'awar wata ita bata da lafiya baza ta iya Masa komai ba akan haka gwara ta daure tunda tana gani idan Yana Mata wanka Yana shiga yanayin bukatar mace daurewa Kawai yake yi shi yasa gwara ta tari abin.
   Affan da wuri ya amshi tayin Raudah yana murna yau zai gagije,ai Kuwa da dare haka kafa aka sata a gefe Suka jiyar da juna dadi.

    Washe gari Raudah tana kallon labarai a tashar hausa suna zaune da Affan taji ance gomnati ta dage jarabawar waec da dalibai zasu zana Yan secondary school an Kara wata uku nan gaba,Raudah tace Alhmdllh Yan banzan Yara aci gaba da shiga aji,Me labarai tace kungiyar Asu jibi Monday zasu Kara tafiya yajin aiki na Sai baba ta gani,Raudah ta kyalkyale da dariya tace maga karyar gama degree dan ubanku,Affan Yana jinta waya yake dannawa amma sai da ya tsaya kallon Raudah tana bashi dariya matuka.

  Bayan kwanaki ya Fara koyawa Raudah tafiya har ta iya ta Fara takawa da kanta har ta dawo tana tafiya normal Kamar bata taba karyewa ba,likita yace ta dinga Dan zaga unguwa tana tafiya a kafa me dan nisa,tare da Affan Suka fito sunyi gayu sosai Affan sanye da 3qrt da t-shirt komai fari,ita Kuwa Abaya ta sa silver color me shegen kyau tayi rolling suna tafiya a layin suna zancen soyayya suna nishadi kamar saurayi da budurwa ka gansu gwanin birgewa,Suna ta nishadi yana tsokanarta,wata Yar budurwa ce tazo wucewa Raudah da sauri ta koma ta bayansa tare da rufe Masa idanu da tafukan hannayenta dariya sukeyi  musamman Affan, sai wurin magriba Suka dawo gida.

    Siyama kwance suke da Aslam a makeken bed dinsu sun gama soyewa suna hutawa ta juya tare da hugging din Aslam tace My Sugar dan Allah ka biya min makaranta na koma Nima nayi karatu,marairaicewa tayi da shagwaba please ko ba degree ba ko NCE ne dan Allah kaji, Aslam yace ni bana son fitarki aje a gurbata min Mata Muna zaman mu lafiya,Siyama tace Ina da hankali fa Inshaallah babu abinda zai faru wace ma ta Isa ta zuga ni na yarda ilimi Yana da dadi kaga Zan sake wayewa sex dinnan ma Sai kaga albarkacin makaranta da gogewa nazo Ina maka style har na tintsira gudi gudi,dariya Affan yayi ba shiri yace ba wayon da Zaki min Yar nan,Siyama ta sake cewa to yaran mu fa ko Dan yaranmu da zamu haifa zai musu Rana,Yan dagwai dagwai dinmu jikokin Mum, Yan fararen yaranmu masu Yan kunnuwa Affan yace naji amma sai kin samu ciki Zaki fara yarona tun a ciki ya dinga Jin turanci,Siyama tace Indai ciki ne Ina da shi fa,watanmu biyar da aure Ina da ciki,Aslam yace haka ake cikin,da gaske fa nake idan baka yarda ba muje asibiti gobe,ta ya Kika sani? tace Sanda na dinga zazzabi rannan na siyo wannan tsinken na pt na gwada Allah ya nuna Ina da ciki,shine baki fada min ba? gobe Zan kaiki asibiti ai,gari na wayewa Suka shirya sai asibiti bayan an Mata gwaji nagartacce aka tabbatar tana da ciki na wata uku dai dai,Aslam sai Murna harda kissing dinta a kumatu Suka dawo gida murna taki karewa,Siyama tace ai mu irin jinin haihuwa ne ana taba mu muke samun ciki,dariya yayi sai Murna yake zubawa daga nan ya Fara musu Shirin barin kasar.

    Su kawu,Aunty da Shehu sai Wanda Affan yasa zai rakasu ko Ina suna filin jirgi,Landlady ma tazo zata tafi Umrah tana filin jirgi a nan Suka hadu da su Shehu,Shehu yaga dai dai shi yaji Landlady ta masa harda cewa sannu,tace yawwa sannunku,sai ga Shehu ya zage Yana yiwa Landlady tambayoyi kema Makkah Zaki? tace ae Umrah zanyi yace ke Kuwa ki karasa ladanki Mana kiyi aikin hajjin gaba daya amma kiyi Umrah Kawai ki dawo sabo da rashin rabo,Landlady tayi Murmushi bai san me kudi bace,Shehu ya zake suna ta hira da Landlady,Shehu harda cewa daga nan mu Paris zamu wuce sai Dubai, Landlady ta zaro Ido ta zaci wani shegen me kudi ne Shehu ta saki jiki harda bawa Shehu labarinta kaf amma bata nuna Masa me kudi bace, tun a nan Suka kulla soyayyarsu in sun dawo zasu Yi aure, Landlady a ranta tace gwara ko talaka ne Indai na samu me so na Nima nayi auren nan na huta kullum sai dai na rungumi pillow na gaji,Shehu Yana ta murna ya samu matar aure shi kam.

   AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

 
           91-95Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne
Bk


       Affan yau zai koma aikinsa cikin shiri ya fito tare da Raudah tana shagwaba ta rakashi har mota tana kumburo baki irin na Yan Shagwabar nan da sangarta,Affan ya zaro kudi Yan dubu dubu na dubu goma ya Mika Mata ta karba tana cewa na mene? yace baki nayi ki kashe,duk da tana da kudi bata da wata matsala sai da taji dadi yace sabo da wasu mazan tunaninsu Kawai ci da Sha zasu bawa mace basu iya bawa mace dan kudi ko Yaya ne gwargwadon samunsa Watarana haka sabo da ba iya abinci da sutura bane matsalarta,in ka bata kudi maybe a danginta akwai Wanda take so ta yiwa kyauta ko ta kyautatawa kawaye ko Yan Uwa bare uwa uba iyayenta kuma,zata kyautata muamularta da Yan Uwa da abokan arziki amma mazan da yawa basa ganewa, Raudah tana shagwaba tace to ai Ina da kudi Kuma ma Ni ka dawo da wuri yafi min muhimmanci,nasan kina da su ai amma kudinki daban nawa daban wannan naki ne kiyi abinda Kika ga dama da abinki, tace to na gode Allah ya Kara budi yasa kafi haka,karfe nawa zaka dawo? 5pm ya furta Yana kallonta,dire diren kafafu ta fara tana kukan tabara yayi nisa gaskiya ni ka rage, kina aiki fa My life kin San Kuma ka'ida kiyi hakuri tare fa muke bacci kin San da Ina gida ba aiki dole Ina gida, Alright ta furta Allah ya tsare a nemo mana halali Banda haram, Inshaallah ya furta Yana cewa am gonna miss you,me too yace come here..dan kanta ta shigar cikin motar yayi kissing dinta tace ko na zo nayi driving naka? Kina amaryar Zan bar matata ta fita, dariya Suka Yi tare da dagawa juna Hannu ta Masa bye sannan ya tashi motarsa tare da barin gidan,bayan yaje Office ya kirata yafi sau biyar, sai Yamma ta sake gyara gidan tasan bai son kazanta ko ya take, girki ta shirya Masa lafiyayye ta cakare tana zumudin ganin angonta.

     Siyama Kamar bata da ciki ana gobe Mum zata tafi tazo gidan Aslam,Siyama tana sama taji door bell da sauri ta fito,sanye take cikin wasu Pakistan masu kyau Riga da wando da mayafinsu farare tas sunji adon golden,Wandon me Kama da skert ne idan baka sani ba zaka rantse skert ne,dankwalin daurawa tayi a kanta amma Jin muryar Mum sai ta Yafa mayafin sannan tazo tare da bude kofar, fara'arta ta fadada tace Sannu da zuwa Mum tana Jin kunya kunya Mum ta shigo ta zauna kujera ta zuba lace me tsada, Siyama a kasa ta durkusa tare gaida Mum cike da girgimawa ko itace ta haife ta sai haka,ta mike ta cikawa Mum gabanta da kayan ci da Sha, Mum sai Murna da farin ciki danta yayi dace tace oh bakya gajiya Yar nan da hidima Allah dai yayi muku Albarka,Siyama ta amsa da Ameen tana zubawa Mum lemon a cup ta Mika Mata sannan tace bari na Masa magana ta haura sama da sauri,Mum tana ta washe baki Sabo da farin ciki,Siyama tana Shiga ta Samu Aslam yana aiki a system daga shi sai boxers,bayansa ta zaga ta duka tare da rungume shi ta baya hannayenta ta sarkafo ta wuyansa ta Masa rada a kunne Mum tana nan fa tazo tana Palo ka tashi ko nace ta shigo Nan? Ko kince ta shigo ai baza ta shugo turakata ba,to tashi tana jira fa dan Allah,yace wannan rawar kafa da kike Yi haka ko Ni bakya min haka ni ya kamata ma na Fara kishi da Mum kinfi sonta da ni,Mikewa tayi tace to ita ta haifa min Kai ai da bata haifa ba na Samu,Jallabiya ta dakko Masa ya saka sannan yace muje,tace kaje Kai kunya nake ji ta ganmu tare,bana son gulma sau nawa Muka je wajenta tare,Ni dai kaje tace,baki ya tabe ya fice ya samu Mum tana eban gara,Mum baki ta bude ta kasa rufewa tace me Zan gani haka Aslam wato sumarka da kake tarawa me shegen yawa bata Isa ba shine kaje aka zana maka kitso a kanka kalli kitso Kamar Kan mace,Aslam yace Surukarki ce tayi min tace tafi son kitso nafi Mata kyau,Mum duka ta durma Masa a gadon baya ya saki kara Yana shafa wajen yace da zafifa Mum,lallai a tsefe kitson nan yau yau,dama dazu tayi shi da safe idan Zan fita pcap nake sawa,Mum tace ya muku kyau,yaushe zaku tafi ne ku? Yace sai next week akwai abinda Zan karasa,tace to shike nan Allah ya nuna mana,tace Ina Siyaman ne? Yace Wai kunya take ji,kirata Mana mene abin kunya yarinya taki sakewa dani,a waya ya kira Siyama tana dagawa yace kizo inji Mum,Fitowa tayi Aslam Yana kokarin jawo hannunta tayi maza ta matsa bangaren Mum tare da Zama a kasa Mum tana sama,Mum tace ki zauna a kujerar Mana Siyama ai an Zama daya ki daina wani kunya Nima na Zama mamanki ai tashi ki zauna kema,Siyama sai lokacin ta samu kujerarta daban ta zauna,Aslam sai kashe Mata Ido daya yake ta dauke kallonta daga garesa,Suna ta hira da Mum kadan kadan take saka musu baki,Mum bata dade ba tace tafiya zata yi driver da ya kawota shine ya maida Mum,Yana dawowa daga rakiyar Mum ya Mika hannu zai Kama Siyama sabo da ta Harare shi dazu,zillewa tayi tana dariya,wayo ya Mata kamar ya fasa kamata yace kawo min lemo,taje ta kawo Yana kwance a 3seater tana Miko Masa ya hada da hannunta ya rike,Lemon ya ajiye a gefe ya jawota jikinsa,tana shagwaba tace dan Allah ban dade da yin wanka ba yau tunda ka yini a gida sai wanka kake sani wankana sau uku kenan,tana zamewa zata gudu ya Mata rikon tsauri ya Kama bakinta Yana tsotsa sosai tare da murzata bata Sanda ma ta biye Masa ba ta shiga tayashi daga nan Suka lula duniyar ma'aurata cike da so da kauna.

     Nusaiba ce zaune a gida ta zuba tagumi gabanta tuwon masara ne miyar kuka da rana tsaka domin kudin abincin da Shehu ya bawa Mama na cefane ta kwashe ta kashe wasu Kuma tayi zubin adashi sai wahala yaransa suke sha,Mama ce ta kalli Nusaiba ta tabe baki tace idan Zaki ci ma kici wa ya hanaki duk inda Kika Yi aure ki bari ki haihu ai da yanzu kina da yaro da Aslam ko Sufyan a ciki dole Wanda Kika Haihu da shi ya dinga kawo Miki kudi na ciyar da dansa amma Kika ki yarda da shawarata ke baza ki haihu ba sabo da idan wannan ya talauce ki kashe aure ki auri wani ke baza ki tsufa ba Kika dinga Shan kwayoyin hana daukan ciki babu Wanda kika samu ciki da shi gashi nan ai kin koma marar amfani baki da wani amfani.
   Nusaiba ta kalli Mama tace yanzu Mama nice na koma marar amfani sabo da bani da kudi bana samo Miki kudi yanzu nice marar amfani sabo da kin gama cinye kudin Mazajen Dana aura? Mama tace ae baki da wani amfani an fada dan ubanki kuma idan ke Kika haifeni naji labari,amma wlh Mama Zaki gani Inshaallah Abba sai ya Miki kishiya Kuma Inshaallah sai an sake ki kema kiji in da dadi, ruwan mari Nusaiba taji ta ko Ina a fuskarta Mama tace dan ubanki sa'arki ce ni oh sabo da Ina Zama inyi zance dake shine Kika rainani,Nusaiba tace ae din na fada tana kuka tace wallahi Kuma ko Zaki kashe ni sai na fada Inshaallah sai an sakeki kema Kamar inda Kika kashe min aure Kika dorani a hanyar banza,Baki min tarbiyya ba baki ma cancanta ki Zama uwa ba ma,Mama ta mike ta rufe Nusaiba da duka ta ko Ina amma Nusaiba bata fasa fadar abinda taga dama ba.

    Affan kuwa Yana Office ya fara tunanen matarsa irin farin cikin da yake kwasa a wajenta tun kafin 5pm ya tattara sai gida,shi da yace sai 5pm Raudah tana kitchen sai ganinsa tayi ya shigo bayan ya Mata sallama ta amsa ya Rungume abarsa a jikinsa,Allah yasa ta gama kwai Kawai take dafawa shima ya dahu tana jira ne ta sauke ya shigo,Gas din ya kashe tare da Daukanta cak Kamar jaririya sai bedroom dinsa,burin Raudah ya cika ya dawo da wuri tace kasan me na tuna? Yace sai kin fada Yana ajiyeta saman gadonsa tana dariya kasa kasa tace fadan mu da kullum bamu da aiki sai fada Murmushi yayi yace sabo da yawan appointment dina ne,dariya Suka yi yace ai kin rainani da yawa ne,tace ai kuwa Watarana da na maka Tsaki ka mareni gaskiya na maru sai da na kwana kumatuna suna zafi tun daga ranar ban Kuma ba,me yasa Kika sa min Ido ne a lokacin? Maybe so ne,a'a ba wani so yanda Kika tsaneni,dariya  suke yana shafa cikinta Yana Kare Mata kallo tayi kyau sosai sanye take cikin kana nan kaya wani dan short wando da Yar rigarsa yace halina da ke iya wanka kina birgeni ga tsafta ko Ina kamshi duk wani lungu da sako kamshi yake zubawa har can head of Service clean Yana kamshi tv dinsu dake kunne a bedroom din tana ta wakoki iri iri na Nija,Raudah tace Baby ka iya rawa? Yace rawa ban taba gwadawa ba a rayuwata ba wannan ba girma rawa sai Mata ai amma Namiji me class baya rawa bata cikin swag dina, Murmushi tayi tana shafa sajensa da gemunsa tace Yan gayu, Ido ya zuba Mata itama shi take kallo cike da shauki yace Allah sarki Hussain yayi asara,dariya tayi tace ba ruwana ni da ni na fada sai ka Fara Jin haushi kace Ina zancen tsohon mijina,yace ki daina cewa  Hussain mutanen kirki su ake kira da Hussain amma shi Usaini yake su Usaini anyi asara,Raudah ta Masa Shuru sabo da tana magana zai ce tana Masa maganar wani,tashi ki kawo min milk before na fara servicing dinki,tace alright ta mike tana cewa kayi timbidi da yawa,dariya yayi yace dan Allah karki sa na tuno timbidin Yara me karni na kasa Shan madarar,Ni timbidin mazan aure nake nufi,lips dinsa ya lashe tace Allah ya shiryeka suna dariya yace ameen taje ta kawo Masa madarar tare suka shanye tace ka Dade kayi karko duk nasan ba rago bane,kissing dinta ya Fara Yana sarrafata Kamar zai cinye ta danya itama haka har Suka lula duniyar su ta Dadi.

     Aslam tunda Siyama ta samu ciki kullum Kansa Yana saman cikin tun cikin ma bai fito ba,ya dinga Tambayarta me take son ci,in Banda gyada me gishiri ba abinda take ci kullum sai abinci Wanda ya Zama dole tana ci ta koshi ga gyadarta a kusa,bayan Mum ta tafi da sati daya Aslam da Siyama Suka tattara Suka tafi yawon shakatawarsu kasashen duniya,Nusaiba sai labari ta ji,ta zauna tana ta faman bala'i ita Daya a tsakar gida tace Siyama baza ta taba ganin dai dai a rayuwarta ba,tsawa kwarantsa sai ta fado Mata a kai ta mutu kowa ya huta,shima Aslam sai ya talauce ya tsiyace da izinin Allah sai yayi bara a gefen kwalta sai yazo wajena ya nemi taimakon Naira hamsim,Mama tace Ameen Inshaallah basu babu ganin dai dai Siyama sai ta dawo tallan goro,Siyama tace Kuma baza ta taba haihuwa ba, Inshaallah cewar Mama bari zata dinga yi jini ya barkewa shegiya sai ta shekara tana zubar da jini mijin bai samu damar saduwa da ita ba suna ta fama su kadai.

    Kawu da Shehu watansu kusan biyu a kasar waje ana kaisu yawan bude Ido Suka koma Saudiya a karshe Suka sauke farali can suka hadu da Aslam da Siyama, daga nan gida Suka dawo Suka bar su Aslam a can,Shehu yayi bulbul yayi kyan gani gashi suna ta waya da  Landlady ita ta Dade da dawowa Nigeria sun gama shirya aurensu ,sai daga baya yaji ma ashe tana da kudi
   Shehu bayan sun huta da sati biyu ya samu Mama cikin dare suna kwance ya tashe ta yace tashi zamuyi wata magana,Mama ta mike tana Jan tsaki wacce magana ce wannan sai cikin dare mutum yana baccinsa Fadi ni naji mene? yace dama fada Miki zanyi Zan Kara aure wani watan idan Allah ya kaimu  za a daura min aure,ban gane ba wanne aure? Wanda Kika sani dai shi Zan Kara ma'ana Zan Kara Mata ku Zama ku biyu,banyi dan naci zarafinki ba,ahayye eheheheeeeee heeeeeeyy  Mama tayi shewa tace dama ka dade kana cin amanata ban sani ba kwarto a wanne dakin zaka sakata daki uku ne daki daya namu daki daya na Mata daki daya na maza to Ina waje? Shehu yace Aslam ne zai min auren nan fa kwandala bazan kashe ba shine zai min komai yace, yace idan so nake ma zai bani gida na saka Amarya,nace a'a gwara na hada Kan Yara na gida na Zan kawo ta tunda gidan zaiyi part guda yace zai gina min part daban a cikin gidan nan a wancen part din dana katange ban gina ba,Mama ta fashe da kuka da ihu cikin dare tace amma Allah ya tsinewa Aslam Albarka bazai ga annabi ba,Su Nusaiba sunji ihun Mama Suka firfito,Mama cikin tsakar daren ta fito tsakiyar unguwa tana zunduma ihu da kuruwa sai da makwafta suka fito Shehu yace kowa ya koma gidansa akan Zan Kara aure take wannan haukan,aka dinga tir da halin Mama,da kyar su Nusaiba Suka lallabo ta ta dawo gida tace wallahi yau bazan kwana a daki ba a tsakar gida Zan kwana tun suna lallashi har Suka gaji Suka koma daki ita Kuma Mama a tsaye gari ya waye Mata tana faman zunduma ihu,Shehu bakin ciki Kamar ya kashe shi ta gama tozarta shi,Kamar Wasa da safe sai ga motar yashi tana ta saukewa a kofar gidan Shehu aikin Aslam ne,Mama tace Nusaiba ku fita ku barbaje yashin nan a kasa duk ku tirje shi,sauran yaran Suka ki zuwa Nusaiba ce take taya uwarta kishi ta fito Kamar sabon kamu tana eban yashin tana watsarwa a cikin kwata,Allah ya kawo Shehu ya kamata ya nada Mata shegen duka Kamar zata mutu,Shehu Yana shiga gida Mama taci kwalar Shehu tace idan kayi min kishiya shegiya nake algungumi azzalumi Allah ya isa shine ka samo me kudi zaka auro bazan yafe ba sabo da mu talakawa ne wallahi sai ka sake ni ka sakeni,a gaban yaranta tayiwa Shehu haka Shehu hannunta ya cire daga jikinsa ta karfi yace ki tafi gidan ubanki na sake ki saki daya,Mama Hannu ta daura a Kai tana ihu shine ka sakeni Allah ya Isa kuka take ta tattara nata ya nata cikin fushi ta tasa keyar Nusaiba kadai Suka tafi Kauye garin su Mama su biyu,shi kuwa Shehu yace Allah raka taki gona aka ci gaba da gini.

    Aslam tsabar muguntarsa ya samu part din Amarya aka kera shi Kamar gidan wani hamshakin me kudi 3room and Palo aka Mata sai kitchen dinta da komai,babu inda za ayi gate wani makwafcin Shehu zai tashi daga unguwar yayi sabon gida Aslam ya siyawa Shehu gidan aka bajeshi tare da hade shi a bangaren Amarya aka mata gate me cin mota biyu abinta ko Ina yasha tiles da Interlock kyau Kam ba a magana gidan ya keru,ita Kuwa bangaren Mama Yana nan sai paint aka mata Kawai shi ma me paint ne yaji kansu ya musu komai siminti ne,Mama Kuwa da Nusaiba tunda Suka koma Kauye garau garau ma da kyar suke samu ga kazanta,daga dankali sai kunu sai tuwo,dambu,danwake shima kadan ake basu,Basu taba sanin da a Rahma suke ba sai da Suka zo Kauye ashe a gidan Shehu ba karamin dadi suke ji ba,sun rame sunyi baki,tsakanin Nusaiba da Mama sai fada suke Yi babu mutunci a tsakaninsu

    Yau suna zaune a wani dakin kasa Wanda shine makwancinsu sai tabarma wata yarinya ce ta shigo ta ajiye musu kunu a wani dan karamin kofi Wai shine abincin ranansu ai Nusaiba tace wallahi duk da bani da kudin mota gida zan koma wajen mahaifina,Mama ashariya ta dannawa Nusaiba tace sai kin dawo marar mutunci marar biyayya ga uwarta,tace ae naji tafiya zanyi wallahi yau bazan kwana a garin nan ba,Fitowa tayi ta shiga dakin wata tsohuwa a gidan me siyar da daddawar miya,Nusaiba tasan inda matar ke Adana kudinta sai ta dinga Jan Me daddawa da surutu suna ta hira har lokacin Sallah yayi tsohuwar ta mike ta fice zata Yi Alwala tana shiga bandaki Nusaiba ta bude wajen ajiyar ta kwashe dubu uku tasan zai isheta kudin mota har da rara,ranar kuma an daura auren Shehu da Amaryarsa Landlady

    kayan daki na gayu da tsada Landlady ta zuba a gidan kana gani kasan ba karya,a ranar da yamma Kuma ta tare ba kowa a gidan sai Raudah Wanda ma har Affan yazo Daukanta zasu tafi gida sai ga Nusaiba da Kaya niki niki a Ghana must go ta dawo.
  Affan ya dau wankan sugar yana tsaye a jikin mota yana jiran Raudansa Nusaiba sai kallonsa takeyi har da goge Fuska ko zai kyasa yace Yana sonta,Jakarta ta rike a hannu a Dan gayence Wai Kar ta kwafsa,zata wuce ta gaban Affan tace sannu lokacin Rauda ta fito taji Nusaiba tana cewa bawan Allah wani gidan kake nema ne? Affan ya kalleta sama da kasa yace ke lafiya Ina ruwanki dani karki jawo min matata yau ta hanani bacci mijin tace ne ni nan da kika ganni bani da amfani wajen Yan matan waje gwara kija tsummar ratuwarki ki Kara gaba gwandala ta baza kici ba,Nusaiba dariya tayi irin ta samu Hanya tace hmm amma matar taka ta birgeni haka ake son mace,Affan yace ae ai ta Isa ne kin san wasu ai basu Kai su mallaki miji ba sabo da Basu iya allonsu ba basu da hali na gari shi yasa ake yawan sakin Mata basu iya Zama da miji ba,Nusaiba sai taji Kamar da ita yake,yace Amaryar Shehu Muka kawo ai Shehu yayi dacen mace yanzu zai samu kwanciyar hankali ance uwar gidansa ballagaza ce ita da yarta Basu San me suke ba ance ma ko a unguwa an tsane su,Nusaiba Kamar ta fashe da kuka bawan Allah ya tsaya sai caba Mata magana yake,ita bata San ma Affan bai San ko Shehun ba sai dazu ya ganshi Suka gaisa labari Suka ji a layin ana fada, Raudah ce ta karaso tana hararar Nusaiba ko kunya Raudah babu akan kishi ganin layin ba kowa sai iya su harda shafa gemun Affan ana Masa shagwaba tace muje ta juyo ta kalli Nusaiba tana Mata up and down,Affan yace baiwar Allah ko Zaki Mana wanke wanke da shara a dauke ki aiki kin tsaya kin zuba Mana Ido, Raudah tace ai wallahi gwara aiki ya kashe Ni idan ba namiji zaka dauka ba Indai macece bana so zanyi komai da kaina,Nusaiba juyawa tayi tana tuna rayuwarta a gidan Aslam,da kyawun Aslam da yanda yake nuna Mata so da kauna,kuka ta saki tana tafiya kasa shiga gidansu tayi ta zauna a kofar gida bakin kofar su tana ta kuka,tausayi ta bawa Raudah taje wajenta tace baiwar Allah kuyi hakuri wlh bamu fada dan mu wulakantaki ba mun San darajar dan Adam kune bakwa kau da kai ga mazajen wasu kiyi hakuri idan abinda mijina yace ya Miki zafi,Nusaiba tace ba wannan ne ya dameni ba,nadama nayi a rayuwata na tafka kuskure,to Allah ya Mana me kyau cewar Raudah tana juyawa motocin Aslam biyu Suka Yi parking daya motar securities ne daya kuma shine a bayan motar tare da Siyama,Fitowa yayi a hankali wanka iya wanka ga kyau,zagawa yayi tare da budewa Siyama mota ya riko hannunta ta fito da dan karamin cikinta a gaba ya Fara Fitowa ta Sha Abaya ta zuba kyau Kamar ba Yar kasar nan ba,sunyi kiba da kyau sun Kara wani fresh,da gani kasan sun dan huta a kasar waje, Nusaiba ta bisu da kallo kawai,Aslam Yana ganin Affan ya koma gaban Siyama ya kareta Wai Kar ya ganta tsohuwar budurwarsa Kar so ya dawo sabo,Affan dariya abin ya bashi,ke Kuma Raudah da kin ga mace sai boye Miji a tsiri nunawa lallai ita fa matarsa ce,Aslam zai wuce tsabar kishi harda nunawa bai San Affan ba,Affan ya Mika Masa Hannu da kyar ya karba Suka gaisa Siyama ta dawo gaba tace Affan kaine a unguwar tamu,yace Amarya Muka kawowa Alhaji Shehu kawar matata ce,Siyama ta kalli Raudah tace Sannu Ina yini,Aslam harda Jin haushi dan me zata gaisar da Raudah ai Raudah ce ta kamata ta gaida Siyama,Raudah ta amsa da fara'a Suka gaisa ta gaida Aslam ya amsa,Affan yace Nasha Kaye a wajenka mene abin bata rai,tunda ka lashe zabe Kai fa kace ba gaba,Murmushi Aslam yayi ba shiri ya dai tsaya sun gaisa sosai harda bawa Affan katinsa yace gashi idan kana so Watarana mu gaisa,Affan ma ya zaro katinsa yace ga nawa Wai ya nunawa Aslam shima fa babban yaro ne da aikin yinsa,Raudah sai kallon cikin Siyama takeyi dama itama ta samu nata da Affan,gidan su Siyama zasu shiga Wanda dole sai ka wuce ta kofar gidan su Nusaiba,Nusaiba tana tsaye tana ta faman kallon Aslam Kamar mayya,Aslam ya gane itace harda shafa cikin Siyama suna tafiya,Siyama tayi dariya tace dan Allah ka kyale babyn nan haka kullum hannunka na kai,Siyama tace Nusaiba kece dama ko magana haba Nusaiba,Nusaiba an sakko tace Charity sannunki tana tabe baki ,Hannun charity ya rike Suka Shiga gida me kyau Nusaiba bata gane gidan su Siyama bane yanda Kawu ya gyara gidan yayi kyau ya canja sosai,haka ta Shige gidansu ta iske kannenta duk basa nan sun tafi sashen amarya,Shehu Yana dakinsa yaji sallamarta,Fitowa yayi yaga Nusaiba a gabansa ta zube gudun Kar ya koreta ta fashe da kuka ta rike kafar Shehu tana dan Allah Abba ka yafe min na tuba wlh bazan sake biyewa Mama ba,Shehu yace Nusaiba ki ma biye Mata ni ba ruwana kece a wahale,Ka yafe min Abba yace dama ni bana Fushi dake na yafe Miki, Yar da na Haifa ai kullum Addua Zan Miki Allah ya shiryeki ,Nusaiba taji Dadi sai ta share waje ta samu wajen Zama duk da haka bata leka wajen Amarya ba abinci taci duk Yan uwan Shehu sun tafi itace ta gyara gidan tsaf tare da kannenta tayi wanka,Shehu Kuwa ana yin Sallar Isha ya wuce bangaren Amarya landlady anci gayu ta hade cikin rigar baccinta pink ta Sha kyau na musamman,Shehu duk an gigice anga sabon jini,kajin da ya siya Mata sai da ya siyawa yaransa ya basu nasu na Amarya Kuma daban,Nusaiba yaushe rabon da taga nama tana Kauye sai yanzu,kannenta su Ameer sai dariya suke kyalkyala mata.

    Landlady wayayya ce wacce tasan ta Kan maza ga iya shagwaba da kisisina Shehu tun a wajen kwanciyar aure yasan sai yanzu yayi aure da haukarsa Kawai yake yi,washe gari kasa Fitowa yayi ko kafar gida Yana ta soyayya, Landlady girkinta tayi Nusaiba itace tayi nasu girkin ita da kannenta,da yamma Kuwa sai ga Shehu a kitchen ya ajiye hula a gefe Yana taya amarya wanke wanke,Yana gamawa yazo Yana yanka Mata Alayyahu,yau ma Shehu kwanan farin ciki yayi sun gurji juna shi da Landlady gaba daya Shehu ya susuce ya samu mace Yar gyara wacce tasan kanta,Satin Landlady daya ta Fara girki da su Nusaiba duk da haka Nusaiba bata taba shiga gidan ba sai da ta gaji taga kannenta sai shatara ta arziki Aunty Amarya take musu amma banda ita,haka da Yamma tayi wanka ta shirya ta Shiga bangaren Amarya a ranta tace gaskiya  Aslam bashi da mutunci mutumin nan ba karamin makiri bane shine yayiwa Amarya wannan mu Kuma ko oho Nusaiba harda goge kwalla ta shiga Palo ac da kamshi Kawai ke tashi,Abbansu taji a kitchen suna ta Wasa da dariya da Amarya suna girki a hankali tayi Sanda Kamar barauniya ta leka kitchen din ta hango Landlady akan cinyar Shehu suna kissing,da sauri ta dawo baya tana rufe Ido ta zauna tana mamaki tace oh duniya ashe Abba dan duniya ne haka,Amarya ce tace naji Kamar yarmu na sallama ta mike ta fito tasan Nusaiba a hoto,Nusaiba tana ganin Amarya shegu kudi ba karya sai ta Mata kwarjini har kasa ta rusuna tace Ina yini Aunty,Aunty ta amsa da fara'a tace sai yau Zaki zo min kema kishi kike taya mamanki ko banga laifinki ba,Nusaiba mayyar masu kudi tace ba haka bane tana sadda Kai Kamar ba Nusaiba ba ,Shehu ne ya fito,Nusaiba tace Sannu Abba tana Zama a kujera ya amsa da fara'a sai rawar kafa yake sabo da anzo gaida Amaryarsa,bedroom ya shige Landlady tace Nusaiba jeki kular min da abincin can bari naje,Nusaiba ta Shige kitchen Itakuma Amarya ta wuce ciki tare da Shehu suna soyewarsu aka bar Nusaiba da aiki,Wasa Wasa sai gashi Amarya bata aikin kirki a gidan nan gaba Daya kusan Nusaiba ce ta Zama Yar boyi boyi ita take Kai kanta tayi ta dirzar aiki  ba tare da an sakata ba sabo da Landlady tana da kudi.


AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

            96-98


Official

By
AsmaBaffa
Page naki ne

FUTURE RM          Nusaiba gajiya tayi da rashin mahaifiyarsu ta tattara kannenta suka koma gaban Abbansu tare da durkusawa,Shehu yace Yaya aka Yi ne? Nusaiba tace zuwa Muka Yi mu roke ka dan Allah Abba ka dawo da Mama gida badan halinta ba ko don mu,Amarya Landlady tana ji,Shehu yace babu ruwanku Kar na sake ji Kun min maganarta Indai maganarta Zaku kawo min to karku zo inda nake,ku tashi ku bani waje ya musu tsawa suka mike sum sum Suka bar wajen,Nusaiba babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa gaskiya halin Nusaiba da uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi.

    Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata.

   Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah, Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye.

    Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi.
   Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki ta bature Sorry Sorry.
  Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty.

    Washe gari da Yamma Sunday Aslam Yana gida Yana zaune a center carpet Yana shan lemo Yana aiki a system Siyama kwance take a cinyarsa tayi dai dai da dan cikinta tana ta Wasa da botin din rigarsa Suka ji door bell sai da dan cikin Siyama ya motsa sakamakon karar da yaji ba zato,Siyama tace wash dan cikina zai fasa min ciki ni bana son karar nan tsoratani take yi yace Zan cireta to tunda baki so amma idan muna sama fa taya za muji knocking? ai idan na haihu sai a maida yace to ba damuwa,tashi ki bude kofa Siyama direct tace bazan iya ba wlh na gaji kayi hakuri,dariya yayi yace wannan ciki Ina ganin ta kaina da shi,tashi to na bude Siyama tace bazan iya ba dan Allah karka tashi naji dadin kwanciyar nan Allah kace su shigo mana,Aslam yace yau baza kiji kunyar ba kenan? Tace ko Kawu ne sai dai yayi hakuri bazan tashi ba,da Kansa yace ku shigo Aunty ta bude kofa tare da shigowa bayanta Mama ce sanye da Hijab,Aslam Yana ganin Mama ya daure Fuska tam ba mutunci,Siyama kuwa bata tashin ba kamar yanda ta fada,Aunty ce ta harareta ba shiri ta mike zaune a gajiye ba dankwali ma a kanta doguwar rigace a jikinta Yar kanti tace Aunty Sannu da zuwa,ta gaishe da Aunty ta gaisar da Mama ta amsa tana washe baki harda cewa Siyama Allah ya raba lafiya,Kitchen ta shiga ta kawo musu lemo da snacks ta zauna kusa da Aunty ko minti daya bata Yi ba ta kwanta a cinyar Aunty,Aunty tace ke dagani a kanki aka Fara ciki da kinzo waje ki kwantawa mutum a jiki,Siyama kin tashi tayi har Aslam ya gaida Aunty Kawai ko kallon Mama baiyi ba ya mike zai haura sama Aunty tace Aslam wajenka nazo fa,dawowa yayi ya zauna yace Aunty gani,Aunty tace wata Alfarma nazo nema wajenka dan Allah Aslam abinda Mama da Nusaiba Suka maka ka yafe musu kayi hakuri Allah ma Yana yafe Mana bare dan Adam ka yafe Mata,Mama ta karbe harda durkusawa a kasa dan Allah Aslam ka yafe min nasan munyi maka laifi ka yafe min dan Allah,Aslam ya kalleta shekeke bai ce kala ba,bazai yafe ba,Aunty tace kayi hakuri Aslam Allah Yana son bawa me hakuri da yafiya,ganin Aunty ce take ta rokonsa Kawai yace to amma fa bai ce ya yafe ba,Aunty taci gaba tace dama Shehu ne tunda ya saketa yau wajen watanta hudu yaki ya dawo da ita babu irin hakurin da bata bashi ba yaki yarda kowa a dangi da Yan Uwa har abokai sunje wajensa akan Maganar yaki amincewa,Kuma wlh ta tuba ta gane gaskiya a matsayinta na Yar uwa musulma akace yau Allah ya shiryata ai abin farin ciki ne ga mu musulmai to dan Allah ka sa baki kayiwa Shehu magana ya maidata Kaine kadai zaka fada Masa yaji dan Allah,Aslam ya gama Jin Aunty yace ni Aunty mene hadina da iyalin Abba Shehu,Ina yaro me zai kaini shiga zancen manya in yaga dama ya dawo da ita idan bai ga da ba ta hakura ta koma Kauye inda tafi wayo ni ba ruwana da ai bata san dan Adam me daraja bane bata taba zaton ma Zan Mata rana ba a rayuwa,Aunty tace bana son taurin Kai Aslam ya Ina rokar ka kana botsewa,yace Aunty shike nan taci darajarki albarkacinki Zan Masa magana amma bata da matsayin da Zan taka har can wajensa Zan dai kirashi a waya kawai in ya yarda tayi murna idan bai yarda ba ruwanta mutum dai abinda ya shuka shi zai girba Kuma Alhmdllh ko yanzu tun a duniya ba ayi nisa ba sun Fara girban nasu hukuncin,bazai yuwu ka shuka gero kace zaka girbi shinkafa ba bazai yuwu ba kowa yayi yanda yake so to bazai ga yanda yake so ba, idan Kuwa kayi abinda baka so to kuwa zaka ga abinda kake so haka rayuwa take,basai Yar taki ta auri me kudin ba jarinku kuci gaba da cin duniya gashi nan talaka ma ta rasa yanzu sai ku nema Mata hatimin annabi Yusuf ta sha ko ta samu ko talaka ne abinda bakwa so din dai...Aunty ce tace ya Isa haka Aslam idan baza kayi ba ka Mana Shuru ni ban ma San haka kake da mugun riko ba,Aunty baki San me aka Masa bane har uwarsa sun zageta babu wulakancin da basuyi Masa ba cewar Siyama,Aunty tace bana so Siyama gyara nazo bana son tone tone ke me Miji Zaki zake ki tare masa Maman Nusaiba ai uwarki ce kema,Mama tace Siyama kiyi hakuri ki yafe min,Siyama tace ni baki min komai ba zagina nane da tsine min da kuka yi Kuma kanku ta koma to haushin me zanji,Aslam yace ko ma dai mene dan kanku Kuma ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba Zan Masa magana,Aunty tace yawwa ko Kai fa Basu dade ba Mama tana Jin tsoro ta damu sai an tafi Aslam tsoro yake bata,ai Kuwa Suka tafi Suna tafiya Aslam yace lallai Aunty ai Kawai lallaba su nayi ba inda zanje ko waya bazan Masa ba ta shekara dari bata koma gidan Miji ba,Siyama tace a'a fa ka riga ka fadawa Aunty yanzu jiranka zata yi kayi hakuri dai kayi Masa waya sabo da Aunty idan baka yi ba ka raina min Iyayena fa Kuma ni nasan mijina ba haka yake ba Wanda na aura me yafiya ne da hakuri yace naji Mrs Aslam zanyi ku kyaleni na Sha ruwa please,Jikinsa ta koma ta kwanta.

    Yaran Mama Kuwa tunda Suka ji tana gidan Kawu kullum suna gidan Wajen uwarsu Yara da mahaifiyarsu akwai shakuwa ta musamman sabo da yaran Aunty da Kawu Suka dage Shehu yayi hakuri ya maida Mama sai Nusaiba itama duk da Shehu Yana Mata fada haka take bashi hakuri bata gajiya amma Shehu ya kafe yaki abinka da me hakuri bai iya Fushi ba, Landlady ce ta siyowa su Nusaiba kayan sawa harda takalma da kudinta ganin Basu da suturar arziki Musamman Nusaiba da Sufyan ya kwace Mata sutura gaba daya ya hanata shi yasa bata da kayan sawa,Aunty har Raudah ta bugawa waya tace dan Allah ta hado Mata kayan da zata bayar kwance ta Aiko Mata zata bawa Yar mijinta bata da kayan sawa,haka Raudah ta ciko Leda da Kaya masu kyau kusan ma sababbi ne Landlady ta bawa Nusaiba kala bakwai a ciki  sai Ihsan da take Yar budurwa itama aka bata wasu a ciki kala hudu, har takalma kala hudu Raudah ta bada da mayafai duk aka bawa Nusaiba,Nusaiba tana murna sosai wani bangaren Kuma idan ta tuna tsiyar data shuka da daular da ta shiga ita da sutura ma Sai dai ta bawa wani yau ta dawo gidan jiya ita ake bawa kwance a rayuwarta ta baya talla ne Kawai bata dauka ba,Watarana cikin dare sai kuka take tilka ta koshi.

     Tunda Aslam yace zaiyi ma Shehu magana ya manta ma da batunsu har an wuce Sati biyu Mama tana jira a gidan Kawu,Kawu ma yaji Shuru Shuru waya ya bugawa Aslam da Kansa yace bayan sun gaisa yace Aslam kaci gidanku Ina batun Maganar da kace zaka yiwa Shehu akan matarsa,Aslam sai yanzu ya tuna ma da batun Yana Office ma yace Kuyi hakuri wlh na manta,ka manta ma kace cewar Kawu,Aslam yace Bari na kirashi yanzu yanda Muka Yi zan sanar da ku,Aslam Shehu ya Kira bayan sun gaisa yace Kawu dama magana zamuyi,yace Ina jinka Aslam,yace Alfarma nake nema a wajenka Abba,Shehu da sauri yace Fadi Aslam ko Mene shi Inshaallah zanyi maka,yace akan Mama ne dan Allah kayi hakuri Allah ma muna Masa laifi Kuma Yana yafe mana bare dan Adam musamman ma Wanda yasan yayi laifi ya tuba ya gane kuskurensa,ko dan yaranta ma kayi hakuri yaran zaka duba,Shehu ko musu bai iya yiwa Aslam sai yace dama Ina sonta ai iskancinta ne yayi yawa bata da mutunci ko kadan amma zata dawo Inshaallah tunda kayi magana Inshaallah Zan dawo da ita amma ka kyaleta ta Kara Shan wahalar rayuwa tukun nima sai na gama amarci na sannan ta dawo yanzu Kam kace ta koma Kauye zan Mata magana,Aslam Yana dariyar Shehu Wai sai ya gama Amarcinsa a fili yace to Abba za a fada Mata na gode,Aslam nan take ya Kira Kawu ya fada Masa yanda sukayi da Shehu,Kawu yace Alhmdllh kaga kaima ai ka samu lada yanzu bari na sanar mata.

    Kawu Mama ya samu yace ki godewa Allah Aslam yayi Miki rana Wanda duk duniya babu me miki irinta ya sa Shehu zai maida ke dakinki amma yace ki koma Kauye zai Miki magana da Kansa,Mama ta fashe da kukan farin ciki tace dan Allah ku barni a nan ku taimakeni Kauye wahala inda kasan Ina cikin wuta,Kawu yace ai yace Indai a nan kika zauna bazai dawo Dake ba ai da sauri Mama ta Fara tattara kayanta zata tafi kauyen nasu haka,Kawu yaji tausayinta amma gwara ta Sha wahala sosai yanda ko ance ta sake yin wani abin baza tayi ba,Haka ta koma Kauye taci gaba da Shan bakar wahala a gidansu tunda ba iyaye ne da ita ba a gidan Yan Uwa ne Kuma Yan uwansu kaf basu da mutunci kowa dan iskan Kansa ne kudi Kawai shine mutuncinka a idon su,Gashi idan tana so ma a San Mata abincin sai taje anyi aiki da ita a gidan surfe da daka sai tayi dole,hannun Mama yayi kanta yayi kaushi sabo da wahala,gashi Shehu Shuru har ta sake yin wata guda a kauyen su Nusaiba sai rokonsa suke Yi har kuka sai da Suka yiwa Shehu sabo da Ameer yaje yaga halin da mahaifiyarsu take ciki,Shehu sai lokacin ya nemi yan uwan Mama maza Suka Yi magana za a sake maida aure sabo da ta gama Idda tuni,bata sani bama sai Yan uwanta ne Suka sanar Mata an maida Aurenta da Shehu,Zabura Mama tayi gwanin tausayi tace yazo ne? Yace ae yazo ya koma ma yace idan kin shirya ko yaushe zaki iya tarewa a dakinki,Mama tace yau Zan koma ai tsofaffin gidan Mata Suka ce ai Kya tsaya dai ki gyara jikinki,Suka hana Mama Sai lokacin suke bata abinci ishashe sabo da sunji taci gaba zata koma birni lokacin abinci sai ta ture,har kyautar Sabulai da su Omo suke bata Kuma ta daina taya su aiki amma abinci sai ta ture,kowacce sai ta bata kyautar magungunan Mata na gyara jiki,Mama sabo da an Mata kishiya ta dage da Sha tana ta gyara kanta bata aiki kaushin Hannu duk ya gudu babu tayi Yar kibarta da haske,sai da tayi gyaran sosai sannan ta shirya wasu dattijai su biyu Suka rakota gidan mijinta,Yaranta sai rungumeta da murna Kamar me,Su dai dattijai suna kawota Suka koma Kauye abinsu,Yaran Mama sun zagayeta suna ta murna yau sun rasa inda zasu saka kansu,Nusaiba ce ta kawo Mata abinci a plate da cokali harda siyo Mata lemo, Mama ta bude abincin ta ga shinkafa da Miya da nama harda salat,Mama yaushe rabo tace haka kuka ci gaba a rayuwa? Nusaiba tayi dariya tace Mama ai yanzu Abba abinda muke so muke dafawa,haka yake cewa mu zabi abinda muke so,Ameer yace kinga shagon Abba da kasuwancinsa ya bunkasa sosai, Mashaallah cewar Mama ta Fara antaya loma sai da taga bayan abincin nan tas,Nusaiba tace a Karo miki? tace na koshi Alhmdllh,duk da haka Nusaiba sai da ta tsamo Mata nama a tukunya kusan guda goma tace Mama cinye nasan yanzu kina yiwa mutum baki ko tsinuwa zata Kama mutum sabo da rashin cin nama akwai dafi me zafi yanzu a yawunki,Mama tayi dariya tace sai ku kuka da kanku amma ai kullum Albarka nake saka muku ko laifi kuka min naji haushi a bayan idon ku sai nace na yafe muku Allah ya muku albarka,Nusaiba tace badan Aslam ba shike nan Mama baza ki dawo ba,Mama tace ke dai bari Naga rayuwa yanzu fatana ki samu miji ko talaka ne, ameen cewar Nusaiba zanje Nima na nemi gafarar Aslam da Sufyan.

    Shehu dai a ranar ma Mama bata ganshi ba haka ta kwana ita kadai,washe gari da Yamma Nusaiba ta shirya ita da Ihsan kanwarta ta rakata Suka Fara zuwa gidan Sufyan sun ci sa'a Yana gida dake weekend ne,shima matarsa tana da ciki,matar bata San su waye ba ta sauke su cikin mutuntuwa Nusaiba sai kallon gidan takeyi komai an zuba sabo,Sufyan ne ya fito ya ga Nusaiba abinka da so,Sufyan gangariyar so yayiwa Nusaiba tsakani da Allah bai wani bata Fuska ba tunda yasan shima Yana da laifi tana da aure ya dinga soyayya da ita,gaisawa Suka yi tace zuwa nayi na baka hakuri ka yafe min abinda nayi maka,Yace oh ba damuwa na yafe Miki Nima ki yafe min munyi kuskure Allah ya yafe mana,tace na gode ta mike zasu tafi ya bata 5k taki karba sai Ihsan ya bawa ita Kuwa ta karbe Suka wuce gidan Aslam

    Tunda tazo bakin gate ta Fara hawaye ta tuna haukar da tayi da wannan gidanta ne ta cuci kanta,Ihsan tace Aunty kiyi hakuri haka kin Riga kin cuci kanki Siyama ta Shige gidan kunyi change kawa da kawa Kun auri miji daya haka Allah ya rubuta sai kin Fara Shiga gidan itama gashi tazo ta Shige ta fiki wayo da Imani Aurenku Aunty kawaye ko wacce ta dandani zumar Mijin Daya shike nan 50-50,Nusaiba tace yau na shiga Uku ubanki Ihsan wato har kinyi girman da Kika San mene zumar maza zanci Ubanki wallahi sai na fadawa Abba yaci ubanki wato Yar iska kike so ki dawo,Nima fa Aunty na Isa auren nan wlh 18yrs fa komai na hada wlh ina samun miji aure zanyi ni dai,gashi nan a novel nake Jin soyayya idan Muna karantawa a makaranta a Wayar wasu friends, writers da basa tsaftace alkalaminsu wani ka rantse Bf kake kallo,Nusaiba tace ai wasu na daya daga cikin Wanda suke gurbatawa Yara tarbiyya komai fada akeyi gatsal batsa tun farko har karshen novel yawanci ma yaran Mata sunfi manyan matan karatun novels,Allah ya shirya yasa su gane su gyara alkalaminsu wajen rubutu sabo da tarbiyyar yaranmu masu tasowa gaba,Ihsan tace to Aunty da dadi auren? Baki Nusaiba ta bude tace ke in kina da saurayi ki fito da shi gwara a Miki auren nan, Ihsan tace Ina da abina,dariya ta bawa Nusaiba suna rike da hannun juna tace waye? tace Mahmoud wani yayan kawata ne manager ne a bank baki ganshi ba Aunty ya hadu mugun sona yake kin San na fiki haske duk gidanmu nice ziza haka yake ce min Zizata,Nusaiba tace ba karya Ihsan na yarda to kice ya dinga zuwa zance,tace dama ce Masa nayi Kar yazo Abba zai dukeni,kice yazo kina yin candy sai a daura mu Sha biki,Murna Ihsan take yi writers sun ruda yarinya da soyayya.

   Suna compound na gidan Aslam sai ga motar Aslam ta shigo ya dawo, door bell Nusaiba ta danna amma Siyama tasa an hanata yin kara,knocking tayi Allah yasa tana kitchen ta fito tace Baby tare da bude kofa ai Kuwa Ihsan ta washe baki tace irin Yan Novels,dariya ta basu Siyama tace kune a gidan ku shigo suka shiga kamshi da sanyi Yana dukan su,Siyama tace yau an tuna da kawancen kenan? Nusaiba tace uhm zuwa nayi mijinki ya yafe min ko na samu hakkinsa ya daina bibiyata na samu mijin aure,Siyama tace Inshaallah ma ya yafe Miki Nusaiba,Duniya kenan Wai Nusaiba ce yau ke neman Yafiyar wani,bana son Iskanci tunda kin aure shi da shegen munafuncinki da kutungwila ai sai ki kyaleni,Dariya Siyama tayi tace kece Kika yiwa kanki fa Nusaiba babu laifina,Nusaiba tana dariya tace da laifinki Mana tunda kece kike kula da shi idan ba shishigi ba Ina ruwan Yar aiki da kula da mijin matar gida,to ita matar wa yace tayi wasarere da mijinta,Kinga mu ki kawo mana kayan dadi muci karki dame mu cewar Nusaiba,Siyama ta kawo musu abubuwan ci da sha sai lokacin Aslam ya turo kofa tare da shigowa,Siyama ta mike taje tana Masa oyoyo oyoyo harda Masa kirari ga hantsi leka gidajen kowa,me karya icen dawa sai giwa,hadarin sama zo da jido ko tsawa,angon Siyama Oga yazo, Kaine da gidan Kaine da dakin, bakaki me karya gada,ko su bi ko suki sai dai su bari, abi oga a zauna lafiya,Oga karya kafafun arna,aje gari ya jima sai kwarya,sunyi bakar tafiya ka kayar,Dan asali kuji babban suna,sai an Kai su tasha ko sunki,dariya yakeyi shi mamaki ma Aslam yake sai kace wata Yar tauri yanda ta iya kirari kamar me Waka kullum da Kalar da take Masa ba irin na baya ba Indai tana nishadi to zai Sha kirari sai dai ya tsaya Yana kallonta Kuma wani Dadi yake ji sai yaji Kansa yayi wani gingiringim, rungumeta yayi tana dariya itama hannunsa ta rike ta kaishi ya zauna ta kalli Nusaiba da Ihsan Wanda Suka zuba musu Ido suna Shan kallo Siyama tace ga Sadauki ku gaida shi,Sadauki Aslam shi Kuma an murtuke Fuska ba raini,Nusaiba tace Ina yini wani kallon banza ya Mata da kyar yace lfy,Ihsan Kuwa tana gaida shi ya amsa da fara'a yace ya school tace Alhmdllh,Siyama tace wannan ba karatu take ba na Santa har gidan kawarta take tafiya karatun Novel soyayya ta sani Kawai,Ihsan tayi dariya Nusaiba tace ta ya Kika sani? tace ni da tayi a gabana naje gidan kawata ce yayar kawar Ihsan basu San Ina wajen ba in Banda zancen aure ba abinda sukeyi wallahi ku aurar da ita da wuri Ihsan Nema take ta lalace,Ihsan Fuska ta boye tana Jin kunya a hankali tace ai Ina da saurayina,Aslam yace ae lallai da gaske ne,Siyama tace kaji ko Baby na fada muku,bakya so kiyi karatu me zurfi? Aslam ya tambaya,tace ai yace zai biya min a gidansa sai nayi a can dakin mijina,dariya ta Kama Aslam Wai dakin mijjnta,Yace to Masha Allah,Nusaiba ce ta katse hirar tace Siyama tana mintsinawa Siyama Ido Wai ta yiwa Aslam magana,Siyama tace Sadaukina Nusaiba fa zuwa tayi ka yafe mata abinda tayi maka shi Kawai take bukata,ke dan Allah saurara karki min wannan zancen bana so ya mike ya haura sama abinsa ya barsu,Siyama tace tab akwai aiki,yanzu abinda za ayi Zan ta rokar Miki shi Inshaallah zai hakura,Nusaiba jikinta yayi sanyi tace dan Allah ki taimaka Kawata,Siyama tace karki damu,Nusaiba tace Bari mu tafi Kar Mama tayi Mana fada kin San yanzu Mama an San annabi ya faku,dariya Suka yi Siyama tace Ina zuwa ta haura sama da sauri ta shiga bedroom ta samu Aslam ya tube zai shiga wanka yaga ta bude akwati tana eban turaruka da kayan make up ya kalleta yace Ina Zaki Kai su? tace Nusaiba Zan bawa,yace bada abinda na siya ba zube yaje ya kwace kayan ya maida akwati ya kulle abinsa,Siyama ta Bata rai tace to ka bani kudi na basu kudin mota,yace badai kudina ba Indai Nusaiba ce baza ta sake cin kwandala ta ba har abada,Wai mene Haka Baby ai ni zaka bawa na basu ba wai Kai ka basu ba,bazan bayar ba bana son musu,tace fine ai na tuna Ina da abubuwan da Aunty ta kawo min tsaraba ban saka ba ai wannan Nawa ne ba naka ba,ta dakko Abaya masu kyan gaske blue da black kala biyu ta zuba a Leda da turaren da aka bata tsaraba sai sabulai,Aslam yace wannan kayan da nace Zaki saka min su sunyi kyau su Zaki bayar baki Isa ba kokawa Suka Fara tace ciki ne dani maza ka zubar da cikin,yace zanyi fushi,Siyama tace ka Dade baka yi fushi ba kayi,to shikenan tunda ban Isa dake ba sai na kunyata ki,zai fito wajen su Nusaiba ya disgata tasa key ta baya ta kulleshi a dakin ta fito abinta ta basu suna ta godiya,Nusaiba tace mu dai zuba Mana snacks din nan a Leda mu tafi ya min Dadi,Siyama ta juye musu a wata ledar da lemuka sun Kai biyar suka tafi da Kaya niki niki  sai da ta rakasu sannan ta dawo ta bude kofar Aslam yayi Fushi sosai bai san har snacks da lemukansa an basu ba,itama Siyama bata kulashi ba tace kuma ga kayan lefenka nan tunda dama ba ni ka mallakawa ba halak malak mene amfaninsu ban Isa nayi iko da kayana ba.

    Yana shafa lotion bai kulata ba Wai fushi yake,ya fito ba snacks din da tayi a kitchen gaba daya Yana so zaici babu,ta dawo Palo tana kwashe kwanika yace ke Ina snacks din? tace na hada musu da shi,yace flour tawa da na siyo da kudina,Siyama tace harda lemuka sunfi biyar idan kaga dama ka fashe sabo da fushi,kwafa yaja ya mike zai bar gidan tace wlh kana cin abinci a waje sai anyita dani zaka ga makirci idan baka sani ba ka sani makira ce ni ta karshe,dariya ta bashi yace to shike nan ki nuna min makircin naki na gani ya juya zai fita ta Sha gabansa tace hmm muje bedroom idan ka min service sai ka wuce dan tani ka cinye ma harda kujerun restaurant din,yace ai ke ba kunya ce dake ba dama can,tace ae naji a haka aka gani aka ce ana so,ke har kina da bakin magana matar data dinga kuka a kaina idan ba a baki ni ba sai kin haukace, Kai ba a sirri da Kai Siyama ta furta tayi mukus,bakya Jin magana Siyama kin rainani koshi ya Miki yawa in Kika sake sai na Miki ta Abba Shehu da Mama na hanaki abinci,Dariya Suka Yi tace ai nasan baza ka iya ba, wash ka tuna min da dadinka muje ta riga shi yin sama harda Yi Masa dan Kira sai kace karuwa dole sai da ta sashi dariyar dole ya bita ba shiri,abinci ta kawo Masa    yaci ya koshi sannan Suka fara shagali.

    Raudah yau ta koma aikinta ta riga Affan dawowa gidan ta gyara a gurguje tayi wanka ta cakare sannan tana girkinta tasan gaf yake da dawowa, Landlady ta dakko Shehu a dankareriyar motarta Suka zo gidan Rauda Shehu an faso gari an auri me kudi motocin Landlady ma har ya koya shi Kansa driving yake ya fita inda yaga dama da motar, Mama Kuwa sati biyu kenan Shehu ko dakinta bai kalla ba tunda ta dawo,abin Yana Mata ciwo tana gidan amma bai taba lekota ba sai da ta shafe sati biyu,tana dai ta Shan gyaran jikinta,gashi ta dawo birni tayi kiba tayi haske ta murje,sai gayu take yi.
   Har landlady tazo da mijinta Suka Sha hira Affan bai dawo ba gashi wayarsa bata shiga,hankalin Raudah ya tashi,bayan sunyi Sallar magriba Suka tafi ba tare da Affan ya dawo ba,Rauda tayi Sallar Isha ta zuba tagumi taji karar motarsa,da sauri ta mike ta fito taga shine ya fito ras da shi, dama yasan shi take jira hankalinta sai ya tashi,kankame shi tayi tana murna tace Allah na gode maka daka dawo min da mijina gida lafiya,Murmushi yayi yace kiyi hakuri aikine ban gama ba munyi baki gashi wayata haka kawai naga ta dauke ta mutu duf,tace okay shi yasa naji shuru ya rike hannunta Suka Shiga ciki,wanka ya shiga ta bude toilet din ta Shiga ta dakko ribbon dinta zata fito yace zo nan My Sugar, tana zuwa ya jawota ciki ya cire Mata Kaya Suka yi wankan tare,Towel din ya daura ya jawota ya bude ya sata itama a cikin towel din nasa guda daya tal Suka daura su biyu sai rike towel din yayi bazai dauru ba tana manne a jikinsa suka fito suna tafiya Kamar masu ciwon kafafu suna dariya  bayan sun shirya tace yau Ina da wani labari me dadi amma muje Dining Suka fito yaga abinci na musamman kala kala an Masa yace na mene haka  tace nasan baza ka iya guessing ba,wata takarda ta Mika masa tana Murmushi tace read,karantawa yayi bakinsa yaki rufewa ya wani saki dariya ta farin ciki ya duka a wajen yayi sujjudulshukur ya mike yace My Sugar You are pregnant for 3mnths oh my God dana Yana cikin mahaifarki,tace kasan kwana biyu Ina zazzabi da tashin zuciya shine na biya asibiti daga wajen aiki aka min test gashi Ina da ciki,ka kusa Zama Daddy rungumeta yayi yace dole muyi celebration yau, kissing dinta ya shiga Yi kamar me sannan ya zauna a kujera itama taja ta zauna ya sake rungumota jikinsa Yana cewa Zan iya Kuwa cin abincin nan yanzu murna zata barni Kuwa,ai yau Zan fadawa Yaya Yusuf,Raudah tana ta kallon yanda yake murna itama haka,tun daga ranar Affan kullum kafin ya fita sai ya Dora bakinsa a cikin ya kwararawa dansa Addua sannan yace Baby Daddy zai fita a Mana addua idan ya dawo ma haka sai yayi Masa addua yace Daddy ya dawo,Raudah Kuwa yanda take ji da cikin nan nata Kamar kwai.

   Aisha ma da cikinta Farook murna ba a magana,haka Sabeer matarsa har ta samu ciki sai amai take fama,Nabeela ma tana fama da nata.
    Yau Shehu ya sanarwa Landlady zai raba musu kwana ya gamsu da shiryuwar matarsa ya Kira Mama ya kira Landlady ya musu nasiha sosai da yaransa ma ya tarasu sun Sha nasiha sannan yau ya Fara kwana a dakin Mama yaji ta zam zam Kamar ba ita ba to ta Sha gyara,Kuma Mama haka suke gaisawa da Landlady ba gaba sai dai dan kishi na Mata Wanda baza a rasa ba dole.AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: πŸ›’️AUREN MUπŸ›’️

         99-100


Official

By
AsmaBaffaPage naku ne

Hafsa Abdullahi
Fateema Farouk
       Nusaiba tana zaune yau Mama ta aiketa kasuwa zata Yi Mata cefane ta shiga Napep sai me Napep yace Zan Sha Mai Hajiya tace to,gidan man da Affan yake nan ya shiga,Yaron Affan Salahu Wanda Suka Yi hatsari da Raudah akan machine dinsa Yana gidan man Affan ya sashi aiki da machine dinsa a gefe yaga Nusaiba a Napep sai kallonta yake Yi sai ta Masa Kama da matarsa data mutu da ciki wajen Nakuda,Kawai ganin tana Kama da matarsa yaji Yana sonta,Yana ta faman kallonta Kamar maye,wajen Napep din ya karasa yace Yan Mata sannu,Nusaiba rabon da wani Namiji ya kulata a duniya har ta manta sai yau,farin ciki ya kamata amma ta danne tace yawwa,yace dan Allah ya sunanki? tace Nusaiba yaji sunan matarsa data mutu mamaki ya kamashi yace ikon Allah dan Allah Dan yi dariya na gani,dariya ya bawa Nusaiba ta murmusa yace har dariyar iri daya wlh sannu baiwar Allah wallahi birgeni Kika yi haka Kawai naji Ina sonki  Sunana Salahu,Nusaiba a ranta tace ji wani suna dan Allah sai ace Nusaiban Salahu ko dadi,kallonsa tayi sama da kasa Salahu matashi ne Kamar su Affan wankan tarwada ba laifi baida makusa kuma Yana gayunsa da tsafta Dan birni ne, a ranta tace karfa kiwa kanki tace na gode a fili,Yace dan Allah Dan bani number dinki idan ba damuwa,Nusaiba harda Jan aji sai da ya dinga rokonta sannan ta bashi da kyar tana yanga,Salahu Kuwa haka yake son mace me yanga sai ta birge shi tuni ya Kara Jin sonta.

     A hankali waya Suka Fara da Salahu kafin wani lokaci Salahu ya siye zuciyar Nusaiba yace shi da gaske yake daga nan ya dage da zuwa zance da machine dinsa yace yafi son bazawara yanzu sunfi hankali sunga rayuwa,Yana zuwa zance an kusa turo manya aka samu munafukan layi Suka fadawa Salahu tsiyar da Nusaiba ta shuka aka sake ta,shi yasa ake so ka shuka Alkhairi duk tsiyar me hassada bazai samu abin fada akanka ba,gashi Nusaiba ta kamu da mugun son Salahu Kawai taga ya daina zuwa Kuma ya daina kiranta a waya idan ta kirashi sai yace zai Kira bazai kirata ba,Addua taci gaba da Yi ba dare ba rana tayi ta kuka a boye ba tare da wani ya sani ba,Soyayya ta sa Nusaiba kuka sai yanzu tasan mene so akan Salahu,sabo da sauran Wanda ta aura kudi Kawai ta hango Basu samu damar zuba soyayya da ita ba sai Salahu talaka me rufin asiri.

    Tun Mama bata fahimci haka ba har ta gane bata tambaya ba ta rabu da ita,Shehu ne ya Kama Nusaiba tana wanke wanke tana kuka bata San ya shigo ba,Kujera Fara ya ja ya zauna ya dakko lemonsa na roba ya balle Yana kurba Yana kallon Nusaiba ya harde kafafu,Mama ce ta fito tace yau me Zan gani Nusaiba me ya faru,Ka gani Abban Ameer, Shehu dariya ya dinga Yi Yana kora lemo abin Yana Masa dadi yace sai kin tambaya akan mene yarki soyayya ta fada talakan da kuke gudu a kansa take wannan an zuga shi ya daina zuciya dama bata San so bane shi yasa da kudi ne a zuciyarta ba soyayya ba yanzu Kuma da damarta ta gudu ba me kudi talakan ma Neman sa akeyi Ido rufe to an same shi da kyar Kuma ya subuce ga sonsa take sosai,Mama taji tausayin yarta Jin Nusaiba ta sake rushewa da sabon kuka tace yarka ce dai wallahi ba daidai bane,Shehu Yana kora lemo Yana tuntsira dariya Nusaiba da Mama an shiga wani hali Yana kallonsu Mama tana lallashin yarta.
   bangaren Salahu yana mugun son Nusaiba amma abinda aka fada Masa shi ya hanashi ci gaba da nemanta amma zuciyarsa ta kasa hakura da ita.

     Siyama cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe,washe gari Monday Aslam Yana da meeting ya fita da sassafe ko bacci bata tashi ba nakuda ce ta tasheta, Jin ciwon na musamman ne Kawai bata nemi Aslam ba sabo da tasan meeting ne da shi akan wani contract zai iya rasa wa sai ta Kira Aunty,Aunty da sauri tazo tare da Yayarta Suka Kai Siyama asibiti,Kamar jira ake ana basu daki Siyama ta haifo danta Kato Namiji kyakyawan gaske,Kuma ta haihu lafiya Kamar ba ita ba, nan da nan aka Mata duk abinda ya kamata zuwa 2pm aka sallame su duk Aslam bai San me akeyi ba,Aunty gidanta ta wuce da Siyama a can tayi Mata wanka da towel ta koya Mata sannan tayi na sabulu da kanta,Aunty ce ta wanke jariri tsaf aka sa Masa sabon kaya farare masu tsada da kyau aka sashi a showel fari Yana kamshi,Siyama ma shiryawa tayi  cikin doguwar rigar atamfa sabuwa a gidanta Aunty ta dakko mata ta shafa turaruka ta zauna taci abinci ta koshi,Jariri sai cin hannunsa yake Yana Jin yunwa,tana gamawa Aunty tace a bashi nono,Siyama ta dauki jaririnta tana washe baki ta tsura Masa Ido tace yanzu Aunty dana ne wannan? Hararta Aunty tayi tace nono akace ki bashi,Siyama ta saka hijab Wai baza a gani ba,Nusaiba ce ta shigo ganin yaro taga me jego an lulluba da hijab,tace malama ki fito da nono ki ba yaro,Siyama tace Aunty na rasa bakin yaron fa,Ina Zaki ganshi kin lulluba,Da kyar ta samo bakin yaron tace Bismillah dan yaro kayiwa ubanka kaka gida,Aunty ce ta maketa a kafada tace ke dai anyi marar kunya wlh,Siyama tace Aunty ai gaskiya ne shike nan ubansa yau sunyi handing Over,Nusaiba ta fisge hijab din data rufe kanta,Siyama ta Fara masifa wai mene haka Zaki ga sirrina ta jawo ta sake rufawa kanta da jariri,Nusaiba tace ga yaron irin ubansa, Sai da ta gama bashi nono ko koshi baiyi ba tace ya isheka haka karka yi katon ciki, ta mikawa Nusaiba yaron tace gashi kalli danki Kamar zai ce min Mummy, Nusaiba ta karbi dansu tana gani tace wannan yaron wayo zaiyi,Siyama tace bakya ganin idonsa Kar Kamar zai Kira sunana,kalli girarsa cewar Siyama,Nusaiba tace irin ta ubansa ce ya fiki karfin jini,Aunty ce ta tashi Jin rashin kunyar da suke yi

   Siyama a hankali tace ba dole ba ya fini karfin jini ai ansha aiki ayi fama anyi gumurzu,Nusaiba tace ai aikin maza kenan ni kaina yanzu da kyar nake bacci Sabo da ba harka yo na Saba da wanga lamari,dariya sukayi sai tafawa suke suna iya shege wani abin Aunty tana jinsu,Kawu ne ya shigo Suka Yi mukus,ya dauki jariri yace Siyama ashe asibiti aka kaiki? tace wallahi Kuwa kawu na haihu,Kawu yace to rasa kunya ai na gani,Shuru tayi,Makwafta da Yan uwa ana ta zuwa barka,Aslam ya Kira yaji ya matarsa tana dagawa yajita da murna tace Ina gidanmu fa kazo sai ka daukeni mu koma gida,yace lafiya? Kuma shine baki fada min ba ai na gama meeting dinma Ina hanyar gida tace gidanmu zaka taho bani da lafiya,da sauri ya juya Kan motarsa sai gidan su Siyama Yana zuwa yaga Nusaiba ta fito daga gidan ta Shige gidansu wasu matan suna ta shiga wasu na Fitowa harda Maman Nusaiba,Fitowa yayi zai shiga gidan Yar uwar Aunty harda ce Masa an samu karuwa Allah ya raya,Aslam yace ta haihu ne? Au baka sani ba ai tun safe Muka kaita asibiti tana nan lafiya kalau da jariri,Aslam ai ko gama ji baiyi ba ya kutsa Kai cikin gidan,Yana shiga Yan barka duk sun Gama sun fita Kawu ya shigar da shi tsohon dakin Siyama Wanda yanzu ya Sha kujeru da tiles,Zama yayi sannan Aunty taje Suka gaisa,Siyama ta mike da yaronta har da pillow din da take zama a kai,ta Shiga inda Aslam yake,Murmushi ya sakar Mata itama haka jaririn ya karba Yana kallonta yace Kamar bake ba Anya ma kin Sha wahala Kuwa

   Na ganki Kamar wannan ba daga cikinki ya fito ba,dariya tayi tace Allah ne ya amsa Adduar da kake min kullum Allah ya sauki matarka lafiya to Allah ya amsa Nafeelar da kake yi akan cikin nan Allah ya amsa, yace ah naga zahiri yace baki ji yanda hankali na yake kanki ba akan haihuwar nan sai gashi ko waya sai dawowa nayi Naga jariri,Siyama tace ai kana fita daga gida ko Office baka Kai ba na Fara ciwo Kai nakuda masifa ce na zaci wucewa zanyi har nace da Aunty a Kira min kai,Aslam harda abin tausayi wai Allah sarki Sannu, kai haka ake nakudar dama bazan sake haihuwa da wuri ba,Aslam yayi dariya yace baki Isa Yara nake so,Siyama kamar zata Yi kuka Kamar yace yanzu zai Mata wani cikin tace dan Allah kayi hakuri kayi min rai wallahi nasha wahala daurewa Kawai nayi amma mutuwa ce Kawai banyi ba harda hawaye,Aslam ta bashi dariya yace to Mene na kukan Kuma kin manta da dadin da ake ji kafin ayi cikin,dadin banza mene amfaninsa kaci Dadi ko kaci wahala,dariya ta Kama Aslam,yace kece fa Watarana kike cewa ayi Miki, to yanzu na gane gaskiya bani ba wannan lamari, tace kazanta haihuwa Ina haihuwa sai amai na dinga amai,haba ya ake cewa abarnan mabiya ta taho da komatsai da tarkace tayo shara Suka shirkito kasa daga cikina na zaci kayan cikina ne duka ai sai amai wayyo kazanta daga yau sai na tsinewa me girman Kai ya taho a cikin wannan kazantar za ayiwa mutane iyayi,Aslam ya dinga dariyar labarin Siyama an Haihu harda cewa daina fada min kazantar nan Kar na kasa cin abinci dake,tace dama ni yanzu na Isa na maka girki kaci ai nayi kazanta da yawa bai ma dace ba wlh Me danyen jego da girki haba kana da gaskiya karka kaci abincina Allah wannan kazanta haka.

    Yaronsa yayiwa Addua a kunne sosai Yana ta kallonsa idonsa tar yace wannan idon naki ne ba nawa bane,Siyama tace kalli da kyau idonka ne gashi nan a soye,Siyama ta Mika Hannaye tace bani shi ya gaji uwarsa yake so,yace eh lallai shike nan daga na dauke shi ko minti Sha biyar baiyi ba Wai na baki danki ya gaji a Ina Kika gane ya gaji,Siyama tace to shikenan rike shi magana ta kare,Aslam wayarsa ya zaro ya Kira Mum ya fada Mata ya hadata da Siyama ta Mata barka Mum ana ta murna anyi jika,Aunty ce ta roki arziki ya bar Siyama tayi sati biyu a gida sai ta koma ba a sonsa ba da kyar dai ya yarda yaje ya kawo Mata kayanta na sawa da Dan yawa sai na jariri da Suka siyo daga kasar waje komai dai ya kawo,ya jibge Mata kayan shayi da su maltina,juice,ruwan roba,sai kullum Kuma Yana Hanya da su Fruits da nama da sauransu.
   Nusaiba kullum sai tazo ganin jariri safe da Yamma kamar danta,har zuwa take ta goya shi,Yau ma tun rana tazo ta goya jariri tana gidan har Yamma,Siyama tace Nusaiba bari nayi wanka sai na karbe shi ki huta,tace to Aunty tace wanka ma za ai masa shima Siyama ta shiga wanka Aunty tayiwa jariri wanka ta shiryashi a kayansa wasu milk color yaron ya Kara wayo,Nusaiba ta dauke shi tana zaune yana hannunta Aslam yayi sallama tare da shigowa,Aunty ya gaisar Nusaiba ta gaida shi da kyar ma ya dan iya motsa bakinsa ya amsa shima albarkacin Yaronsa ne da kullum take daukanshi iyaye da dansu,Yana dakin da aka bawa Siyama kwance akan katifarta katuwa dakin ya Sha gyara Yana ta kamshi, shigowa tayi daure da zani a kirji tayi wanka,ya kalleta jikinta duk ruwa zanin ma ya jike a jikinta ya manne Mata a jiki surarta ta bayyana sosai,duk inda ta motsa sai ko Ina na jikinta ya motsa,Aslam yasan ba samu zaiyi ba yace Wai ni idan an Haihu kyau akeyi ne? Kinga kyau fa Kika Kara kin ganki Kuwa kullum nazo sai Naga kinfi jiya kyau har bana so na daina kallonki, Murmushi Siyama tayi tana tsaye tana goge kunnenta da cotton,tace ae ance tana sawa har zuwa arba'in wasu haka take sasu kyau in suka Haihu zuwa 40 days zaka ga mutum ya dawo dai dai,yace yanzu naji zance kinje saloon din? tace ae mana naje jiya na kusa da gidan nan gashi nan an gyara gashin sosai yace okay, yace karbo min dana daga hannun waccen sauri nake yi bacci nake so naje gida nayi,tace to saurin mene Kuma kayi baccin a nan Mana

    Murmushi yayi yace yan barka fa,Siyama tace Kai rabu dasu sai na koma palon Aunty,Yanzu Zaki suna? ta mike tana cewa Kawu yace babu me zuwa ya bata Masa paint din gida,yace yayi daidai ai, fita tayi ta karbo Jaririn a hannun Nusaiba,jaririn ta bata ta wuce gida abinta.

  Ranar Suna yaro yaci suna Muhammad raguna manyan gaske uku ya yanka Mata,albarkacin Landlady sai ga Raudah tazo barka da cikinta tsoho itama harda cewa Allah ya bamu ita ku Nima aga nawa haka Siyama tace Allah yasa.
  Satin Siyama uku a wajen Aunty,me aiki ce ke gyara gidan Aslam kafin ta koma ma sai da aka Masa gyara na musamman,Aslam ya canja furniture na gidan,da Kansa ya dakko matarsa da jaririnsa Muhammad,Allah yasa me aikin nasu babbar macece ita taci gaba da kula da Siyama da jaririn nata tana daukan darasi,tun kafin arba'in jini ya dauke taki fadawa Aslam sai tayi Sallah a boye,Aslam ya gaji yace ban yarda dake ba Baby har arba'in ta wuce ace har yanzu bai dauke ba,Siyama tace bai dauke ba harda mazewa,yace wallahi sai na duba na gani da kaina ya jawota tana tirjewa karka gani kazanta baza ka iya cin abinci ba babu kyan gani,suna ta kokawa yayi dariya yace baki Isa ba sai na tabbatar ba komai,ya dauketa cak ya hau cire Mata kaya yaganta ras ba komai yace au abin haka ne Baby? yaji haushi sosai yace haka Allah yace? Ya tsareta da Ido tace kayi hakuri ka yafe min ni tsoron ciki nake yi dan Allah na siyo maganin planning na dinga Sha ka yarda I promise Ina yaye Muhammad sai na daina sha,yace to naji karki sake min haka bana so kin San irin hakurin da nakeyi,to ai nace kayi hakuri ta furta tare da rungume shi ta baya,shanmatarsa tayi ta tura shi saman bed ya fada,tace baka da karfi dama na fada sai na kayar da Kai watarana,dariya yayi ya dauketa ya jefa ta saman bed da karfi sai da kashinta yayi kara ta saki kara,yace sorry ya Kika ji to? tace da dana da komai ka dinga jefar da me Da harfa Da ne dani,Muhammad yana Dan bed dinsa a gefe ya saki kuka ta dauke shi tana cewa Kai kaci Uwaka Nusaiba,Aslam yace Allah kiyaye ta Zama uwarsa wannan muguwar, Naga kayanki a jikinta da na hanaki ki bata shine Kika bata ai gashi ta min kyau,Siyama tayi dariya tace baza ka bani haushi ba Mallam ta zauna tana bawa danta Nono,Aslam so yayi taji haushi tunda ta bada kyautar kayan nan abun yana ransa, ya dawo ya zauna a kusa da ita,tana bashi kadan tace ka koshi,yace mene haka wannan ai rowa ce,katon ciki zaiyi haka Kawai,Aslam yace nono ne yake sa katon ciki ke baki Isa ba dama muguntar da kike Masa kenan ki ba yaro abu ya koshi harda bata rai ba shiri ta bashi ya koshi,Yana Sha harda yo aman nono a jikinta,Aslam yace kazama sai karni dole na fara tunanin kishiya,Siyama sai ta Fara kuka tace shi yasa nace maka bana son haihuwar nan ka nace yanzu ga irinta nan kana ce min kazama,yi hakuri to ni da yau ma zanbi sahun jaririn ki bani nima na kora,ba wani nan cewar Siyama,ta tashi ta cire kayan ta zuba a washing machine ta wanke sannan tayi wanka ta fito,yaron ta kaiwa Nanny ta gyara shi,tana dawowa Aslam ya sunkuceta sai saman bed daga Nan suka Fara soyewa.

    Bayan wata biyu Nusaiba sabo da tunanin rashin miji duk ta rame gashi Ihsan har an kawo kudin aurenta za ayi bikinta ita Kam shuru,Mama haka take aikin lallashin Nusaiba tana cewa ta ci gaba da addua,Nusaiba har gidan Siyama take zuwa sabo da Jaririn nan burinta taje ta goya shi,kaunarsa take yi har ranta,yau Aslam yana gida sai ga Nusaiba ta shigo da sallama,Siyama ta amsa tace ba wajenki nazo ba wajen Dana nazo na kwana biyu ban ganshi ba,Ina yini Aslam,yace lafiya da kyar Yana hade rai,Siyama ta kalleshi bata ji dadi ba mutum me kaunar danka, Siyama ta Mika mata shi tace bari na kawo Miki Pampers a saka Masa yanzu na Masa wanka,kayan shafe shafen jaririn ta kawowa Nusaiba,ta Fara Shafa Masa mai yayi Mata Kashi a jiki,Siyama tace ki cire shi a jikinki da sauri,Nusaiba ko a jikinta tace kyaleshi ya gama na wanke sai da ya Gama ta Shige toilet dake wani bedroom a palon ta sake wanke yaron tas Siyama ta karbo shi ta maza ta shirya shi da kanta,Nusaiba ta tube kayanta ta wanke tayi wanka,Charity ta bata wata Atamfa riga da skert kusan sabuwa ce ma tace ta barwa Nusaiba,Nusaiba ta shanya kayanta ta dawo Palo ta dauki Muhammad yayi bulbul dashi yayi wayo fari tas da shi, dalilin haka Aslam yace na yafe miki duk abinda Kika min kinci darajar Dana Muhammad,Nusaiba tace na gode taji sanyi a ranta bata son irin bata ran da yake mata.

    Sai Yamma likis ta koma gida, Siyama kuwa ganin Nusaiba ta tafi tace dan Allah wannan abinda kakewa Nusaiba ka daina Sweetheart,ba dadi tana son danka ka dinga Mata haka Indai tazo kana nan bata sakewa, kin San fa me ta min Yarinyar nan bai kamata ma ki dinga kulata ba tunda wani abin a gabanki akayi,ya Ilahi ta gane kurenta ta nemi yafiya me yayi saura gaskiya ni ka daina Mata haka ba dadi,to nan fada kike min ko umarni kike bani ko kuwa shawara? tunda kina sonta haka sai aje a maida aure ta dawo ku Zama kishiyoyi sai kuci gaba da zumunci,Siyama ta bude baki tare da furta haka nace maka? Kawai kace sonta kakeyi har yanzu zaka dawo da ita shine magana kawai,dansa ta Mika Masa ungo danka ko na fatalar da shi,ya karbi abinsa ya haura sama Yana dariya a ransa,tace ka dawo muyi magana akwai wani abu kasa a ranka wannan Maganar bata mutu ba,bai kulata ba tun daga ranar Siyama bata sake zancen Nusaiba ba, bakinta kanin kafarta har Bata so ma Nusaiba tazo su hadu da Aslam.

Tana zuwa kofar gidansu taga Machine din Salahu masoyinta Wanda ya fece,ko kallonsa bata Yi ba zata wuce ya dakatar da ita yace Nusaiba dan Allah kiyi Hakuri ki yafe min nayi kuskure,Kiyi hakuri dan Allah,tunawa tayi yanda itama tayiwa wasu laifi Kuma aka yafe mata tace ba komai na yafe maka,Yace dan Allah ki bani dama na dawo da Maganar auren mu,dama gwadaki nayi na gani da gaske kina sona tsakani da Allah Kuma na tabbatar naji labari,Nusaiba tace waye ya baka labarin? Yace Aslam tsohon mijinku shi yace kin canja yanzu Kar na dauki zugar mutane idan Ina sonki tsakani da Allah na dawo na aureki ya fada min kinyi nadama ke yanzu sabuwar Nusaiba ce,Nusaiba Murmushi tayi jin Wai Aslam da Kansa yasa baki a aureta shi da ya tsane su,juyowa tayi tace in ka shirya ka turo manya bani bukatar yin sabuwar hirar soyayya da kai ka azabtar da zuciyata,Salahu yace kiyi hakuri na gode Kuma Inshaallah Jibi za a turo ki fadawa Abba,Nusaiba Kamar bata murna ta fada gidansu sai Murna tana cewa Mama Allah ya amsa ta bawa Mama Labari,Mama tace Kai duniya shi yasa akace ka taka a sannu.

    Bayan wata daya aka Sha bikin Nusaiba da angonta,Ihsan da nata itama ma'aikacin banki,Mijin Nusaiba gida ne Wanda iyayensa Suka mutu suka bar Masa gado ya gyara shi sosai ya maida shi na zamani yayi kyau dan madaidaici harda gate dinsa ko Ina tiles tsakar gida broken tiles ne dagwas, Landlady ita tayi kayan kitchen na Nusaiba da Ihsan sauran Kuma Shehu ne yayi Kamar yanda uba ke yiwa yarsa,Affan ne da Raudah Suka hada lefe Akwatu hudu kasancewar Angon yaron Affan ne na hannun dama,machine din ma Lifan Affan ne ya siya Masa,Siyama ce ta tasa Aslam a gaba da kuka sai ya bata kudi tayi gudunmuwa dan Dansa da Nusaiba ke so yace me za ayiwa Nusaiba me ya dace, Siyama tana share hawaye tace a bata jari tunda mijinta baida hali sosai sai rufin asiri idan aka bata sai ta dinga sana'a a gidanta ko irin dan siyar da su Maggi,omo etc,Nawa za a bata? dubu dari ? Yace to Zan Miki transfer ki tura Mata kice gudunmuwarki ba ruwana a ciki,Siyama tace hakan ma yayi na gode,haka ta turawa Nusaiba Suka Yi shawarar kayan da zata dinga siyarwa nan gaba,Ango Kuma yace in sun Gama amarci zai maida ta makaranta itama tayi ilimi,Nusaiba sai godewa Allah akeyi ana murna.
  Siyama kuwa Private University Aslam ya sata taci gaba da karatunta tana kula da danta Wanda yayi wayo sosai.
   Aisha ta Haifi yarta mace katuwa,Nabeela ma mace ta Haifa,sai matar Sabeer da ta Haifi Yan biyu duka maza manya,su Aslam sune na hannun dama a nan.

   Raudah ce bata Haihu ba har sai da cikinta ya shiga wata goma,Affan yace idan ba dama Kawai suje asibiti ayi aiki a cire dan,Raudah tace bazai yuwu ka kassara min rayuwa ba in samu matsala Ina lalacewa wata zaka aura haihuwa ta Allah ce a barni Allah zaiyi ikonsa haka Kawai ayi min aiki nazo na samu akasi matsala ta afku shike nan sai naji gudar Amarya a gidana bada ni ba,Affan yayi dariya yace wannan zafin kishi Ina za a kaishi Raudah ni nace zanyi kishiya Ina nake da wannan kwarin gwiwar ni waye ni,who be me? bayan kin gama dani sai abinda Kika ce,Suna haka Kamar Wasa Raudah ta fara Nakuda,damtsen Affan ta rike tace bala'iiii ah'ah Affan....wayyo ta kwala ihu ta rike Mara tace Subhannallahi...mutuwa zanyi..Affan yace idan Wasa kike ma ki daina,tunda yaji Raudah ta hayayyako Masa da masifa da bala'i Kamar zata cinye shi karka isheni karka dameni,Malam ka saurara min bana son wulakanci...yace to da gaske ne nakuda ce muje asibiti tana masifa taya Zan iya tashi ta balla Masa harara,bata ita yake ba ya dauketa da kyar ya sata a mota,tace kayan haihuwar ko da yatsunka za a yanke cibin? Affan yace ki dinga bina a hankali Baby, tace Kar na sake Jin kalmar nan a bakinka,Affan ya koma da gudu ya dakko takarkacen data shirya,ya figi mota tana ta faman wash wash Allah na har suka je asibiti aka dauketa cikin gaggawa,Affan hankalinsa a tashe sunfi kafin 1hr sannan aka ce Masa ta haihu,Uwar gidan Liman ce a wajen Raudah itama Namiji ta santalo katon gaske da gani ya dade a ciki,Raudah ta Sha wahala ba a sallameta ba sai washe gari da Yamma sannan,Matar Yusuf har tazo,Haka Maman Raudah da kanwar mamanta sunzo Suka ce tafiya zasuyi da ita,Affan yace bai yarda ba ya dauke jariri ya Hana kowa

    Da kyar ya hakura yace iya sati biyu daga Haka karta Kara ko kwana daya,suka tafi kuwa har kudin rago Affan sai da ya tura raguna guda biyu sai dai suyi waya da Rauda ko video call yaga jaririnsa,Ranar Suna yaro yaci Abdallah,su Raudah acan sun Sha shagalin suna,tana cika sati biyu Affan yaje airport ta sauka da jaririnta ya dakko matarsa Suka dawo gida,sai lokacin suka nemi yar aiki Nanny dattijuwa me Kamala,Siyama har barka taje mata itama.
   Nusaiba Kuwa an Kama sana'ar Omo da su Maggi etc Hannu bibiyu har yasa ta zana waec da Neco tana Fitowa bata samu direct degree ba sai NCE ya sama mata ta Fara zuwa,Siyama kuwa anyi nisa a school,Su Nusaiba an farfado kullum Mama cewa take ta kula da mijinta ta rike shi Hannu bibiyu Kar tayi Wasa da aurenta.
    Bayan wata biyar Landlady ciki ta samu dama bata taba haihuwa ba yanzu ta samu a gidan Shehu,Ihsan itama sai ciki har ta samu ciki kullum laulayi da amai,Nusaiba kuwa nata cikin ko abinci ba komai take iya ci ba sai abinda taji zuciyarta ta raya mata Haka suke fama 

    Siyama danta har ya fara rarrafe gwanin sha'awa gashi ta tara masa suma an daure Masa ita kamar yaron turawa kowa ya kalle shi yasan ba karya dan gidan Yan gayu ne,shi kuwa Affan Abdallansa kaishi yake ana Masa shegen aski style style har sumar tayi yawan gaske Yana zama,Babu style din da ba'a Masa yaron nan,kayansa ma in aka saka Masa kasan babansa dan wanka ne yanda ake kwalkwale yaron nan,idan Yana gida har goya shi yake yasa zani ya daure abinsa a baya Kamar mace haka Affan ke yi, yau ma Yana gida ya goya Abdallah a bayansa ya daure shi da zani harda jijjiga shi Raudah tana Masa dariya.

   Bayan wasu watanni Nusaiba ta Haifi yarta mace Siyama sune na jikin gado,ranar Suna aka sa mata Jawahir, Nusaiba ana zaune cikin rufin asiri ba rashin ci ba rashin sutura Yar unguwarta idan zata je ya dauki matarsa a machine dinsu abinsu shar, Nusaiba da shegen Iyayi harda koyon machine Lifan ta iya sosai sai ta saka riga da wando ta sa Abaya da mayafi taci glass ta tuka machine taje inda taga dama,Landlady ta haifi Namiji itama. Muhammad din Siyama yayi wayo ya Fara Kiran Daddy da Mummy Yana tafiyarsa ko Ina dagwai dagwai Amma ba sosai ba, idan Aslam bazai dade a Office da shi yake tafiya yaron suje su dawo
  
  Yau Aslam yana zaune a dakinsa a kasan dan karamin carpet dake jikin bed dinsu Yana cin abinci, Siyama tana zaune a saman bed tana bawa Muhammad Nono da yan hakoransa ya gartsa Mata cizo,bata san Sanda ta duke shi ba ji kake dim dim a bayan yaro,dariya yake yana kallonta ya dage kafa daya ya riketa da hannunsa dadi ya gama kaiwa yaro,ya zaci Wasa take Masa sai ya sake cizonta,Siyama ta fisge nononta ta cillo shi kasa aka wani dangwarar da yaro da karfi yaji zafi ya fashe da kuka tace idan ka sake cizona sai na mareka yaro marar kunya ,Aslam Fuska ya daure takaici ya kamashi yace mene haka Wai ke aljanu ne dake ne? wannan yaron me ya sani sabo da Allah dan ya cijeki baza kiyi hakuri ba,Siyama tace kaji zafin Kuwa Ina magana Yana min dariya na yaye shi daga yau yayiwa Kansa bazai sake Shan nono ba,yace ai lokaci bai Kai ba baki Isa kin yaye min yaro ba,ai Kai sai ka bashi naka nonon ya sha,dansa ya dauka da yake zaune yana kuka ya lallaba shi yace kyale Mummy taje da nononta ga abinci yaci gaba da bashi abincin Yana ci,a banza kuma ta huce tazo  zata dauke shi Aslam yace kyale min yarona baza ki dinga dukansa a banza ba,Dariya tayi tace Indai shine gashi nan rigimarsa ma ta isheka,an Masa wanka? Siyama tace ae an masa,yaci gaba da lallaba shi Kamar zaiyi bacci sai yaki yi gashi Aslam ana so a Sha soyayya da Siyama yaro yaki bacci,Light ya kashe ko zaiyi bacci amma yaki yi,saman gadon ya kwanta da shi,Siyama zata Yi magana yace shiiiit Shuru Shuru...ana ta lallaba yaro har ya fara bacci Aslam ya lallaba zai tashi yaro ya fashe da kuka,Siyama ta dinga dariya tace matsa ka gani ta kwanta tare da yaron ta sa Masa nono a baki Yana Sha sai bacci Aslam yace wow tana bawa jariri nono yana cire Mata Kaya,aka dauke yaro aka maida shi bed dinsa, sai da suka kwantar dashi yayi bacci,bargonsa Dan karami aka lulluba Masa kansa a waje,tace Yana tashi wajen Nanny Zan kaishi,Aslam yace ban yarda ba babu Nannyn da Zan Bari ta dinga kwanar mim da yaro komai dattijantakarta a zamanin nan da duniya ta lalace sai an kula sosai da yara,gashi nan kyuya ta matanmu tasa suna ta jefa yaransu ga halaka ko a lalata maka rayuwa danka musamman ya mace sai an kula sosai nawa Zaki ji yaron gida yayiwa Yar wani fyade,Yar aiki ta lalata yarka tana lesbian da ita,akwai na kirki a Yan aiki Kinga ko wannan Yar aikin na yarda da ita ta dade a gidan nan I think farko ma a nan kuka taba ganinta,tun Mum tana kasar nan take Mana aiki amma komai yarda ya kamata a kiyaye,Siyama bargo ta ja musu tace to Allah ya Kare mu da yaranmu yace ameen shi yasa baza ki aiki ba karatu dai zan bari kiyi Amma kina gamawa shike nan

   Tace to ka tuna min gobe Ina da test ko karatu banyi ba ta mike zata dakko littafi yace ai sai dai kici Kan jaki amma yau babu karatu sai na aure, yaron ne ya farka kadan ya kwala Kira Daddy,Aslam yace baya nan,Jin muryar Aslam sai kuka Siyama tace wannan yaron da babba ne yau sai yaci dukan tsiya,Aslam yace je ki dauki danki ni na gama bangarena bazan sake daukansa ba na gaji,ya isheni da kuka ya hanani bacci karki haifo wani da wuri wannan kadai ya ishemu nan gaba idan Muka huta da yawa sai a Karo haba Yara su dami mutum,Siyama ta tuntsire da dariya tace Kai da kace ayi sauri a Karo yace na janye magana ta yau,kaiwa Nanny shi,Siyama tana ta dariya tace kace danka bazai kwana can ba,yace Kai Mata Allah ya kiyaye kaishi,juyawa tayi zata fita yace Madam da kayan baccin Zaki fita ai tana dakin dake palon kasa,ta fita ta Kai Mata Muhammad,ta karbe shi suka kwanta sai yayi shuru ya koma baccinsa,ta dawo tace har ya koma bacci,yace dumin uwarsa yake son ji ai Kuwa bai Isa ba sai in ba da dare ba,ya jawota Suka Shige bargo
   Haka rayuwar ta kasance musu cikin farin ciki da kaunar juna sai jarabawar rayuwa da Allah baya barin bawa ba jarabawa.
            ALHMDLLH

Masu Sharhi Ina Matukar godiya wacce ba adadi, gaba Daya yan group din BABU KAUNA musamman masu bibiyar littafin nan Ina Matukar gode muku

Sai Watarana kuma idan da rai da lafiya cikin yardar Allah na sake muku sabon Novel Amma fa Zan dade banyi sabo ba sai an huta an huta an gaji sannan.

Copy by Zainab Butalawa


AsmaBaffa


COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: AUREN MU Complete Hausa Novel
AUREN MU Complete Hausa Novel
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg4geJ_4T9dcPJINDkp9PX47RLDlIpTzcyBiY_cKaaY1mlYa8NW20ZzDTkYGelnQuiRShpJooCQRBJ3WgcLK04r-VNAWalm2_3bzQCZjN6vFKAPM1sVYu2pbtF21BxqMA3b3KxPMZzHmy9fsjO9U6nt6aiiS4rTMRynCrKNwQH_fXvKOV7FkPa2PKEd0CxL/s320/img_1696842014213.webp
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg4geJ_4T9dcPJINDkp9PX47RLDlIpTzcyBiY_cKaaY1mlYa8NW20ZzDTkYGelnQuiRShpJooCQRBJ3WgcLK04r-VNAWalm2_3bzQCZjN6vFKAPM1sVYu2pbtF21BxqMA3b3KxPMZzHmy9fsjO9U6nt6aiiS4rTMRynCrKNwQH_fXvKOV7FkPa2PKEd0CxL/s72-c/img_1696842014213.webp
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/auren-mu-complete-hausa-novel.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/auren-mu-complete-hausa-novel.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content