Assalamualaikum, barkanmu da warhaka, barkanmu da sake haduwa daku a cikin wannan shafi mai albarka. Wannan shafine da yake kara wayar da ka...
Assalamualaikum, barkanmu da warhaka, barkanmu da sake haduwa daku a cikin wannan shafi mai albarka.
Wannan shafine da yake kara wayar da kan al'umma akan abubuwan da suka shafi fasahar zamani da sauransu.
A yaune zanyi maku bayani akan yanda zakayi whatsapp guda biyu a waya daya, ko kuma ince yanda zakayi whatsapp da lambobi guda biyu a waya daya.
Karanta wannan: Manyan abubuwa 5 da ya kamata ka sani kafin fara blogging
Nasan mutane zasuyi man tambaya akan cewa tayaya zaka iya yin whatsapp guda biyu kuma a waya dayya?
Kowa yasan cewa indai ka bude whatsapp to babu yanda zakayi ka kara wata lambar wayar ka aciki, sai dai idan zaka canza lambar wayar gaba dayanta, to ayanzu nazo maku da hanyar da zakayi whatsapp dinka guda biyu kuma a waya daya tal, sannan kuma kowanne daga cikinsu za'a iya turo maka saqo, ba tare da wani matsala ba.
To da farko dai idan kanason yin haka sai kaje playstore ko matambayi baya bata, wato "google" kenan, sai kayi serching din wani application mai suna "Business whatsapp", da zaran kayi searching dinshi a playstore zakaga ya nuna maka application din, sai kayi "install" dinshi, bayan kayi install na application din, sai ka bude ciki, zakaga ya nuna maka shafi kamar haka
Kamar dai yanda ake bude whatsapp din da kasani, idan ka lura ma zakaga duk kusan iri dayane, koda za'a samu ban-banci to kadan ne,
Sai ka danna "AGREE AND CONTINUE" bayan ka danna, zaka sun nuna maka gurin da zaka sanya lambar wayarka, to sai ka sanya sabuwar lambar wayar ka, amma idan zaka sanya lambar wayar naka, ka cire "0" na farkon lambar wayar naka, misali "9036117711" haka zaka sanya lambar wayar naka, matuka ka zabi country code na kasarka,
Misali na Nigeria shine "+234"
Bayan kayi haka, sai ka danna "Next", bayan ka danna zakaga sun nuna maka gurin da zaka sanya "code" to idan ka jiracesu zakaji sun turo maka code din ta lambar wayar da ka sanya, sai kayi copy dinsu ka sanya a ciki,, dazaran ka sanya su a ciki zakaga wayar naka tana "verify" sai ka dan jira ta gama, da zaran ta gama zaka ta nuna maka wani shafi, sai ka danna "ok", bayan ka danna zakaga ta nuno maka wasu rubutu, sai ka danna "Allow" zakaga ta kara nuno maka wasu rubutu, shima sai ka danna "Allow" da zaran kayi haka, shikenan ka gama bude whatsapp dinka, saura kuma abinda ya rage iyakan ka sanya sunanka, da hoto da sauransu,
Bayan ka gama, to yanzu zaka iya hawa whatsapp dinka na farko, haka zalika zaka iya hawa whatsapp dinka, wanda ka bude yanzu.
Karanta wannan: yadda ake kasuwanci ta whatsapp cikin sauki
Shin zan samu matsala da dayan whatsapp dina bayan na bude wannan
A'a bazaka taba samun matsala ba, dukkansu babu wani matsala, bugu da kari duk lokacin da aka tura maka da sako duka zaka gansu a wayarka
Sannankuma nasan zakuyi man tambaya akan cewa menene amfani yin hakan?
Duk kusan amfaninsu daya ne, sai kuma shi "whatsapp business" kamfanin whatsapp sunyi shine domin yin kasuwanci da makamantansu,
Da fatan kuna jin dadin kasancewa da wannan shafin namu mai albarka, sanna kuma duk wani abu da baka gane ba ko kana da tambaya akai, game da rubutun wannan shafin sai kayi mana comment a kasan wannan shafin,
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
COMMENTS