PAGE 7
PAGE 7
Kuka sosai hajiya takeyi wai umar yazaba ko ita ko husna ,,,har kasa umar ya durkusa yana bata hakuri akan tayi hakuri ,,
Au kafito filli kacemin husna kazaba ,takuma fashewa da kuka shima umar sai yasa kuka chak hajiya ta tsaya tace nashiga uku ni rabi umar akan mace kake kuka haka lalle nayi sake ,kawai tajuya ta fita,,,
Sosai husna take kuka tace umar zan fita a rayuwarka kazauna da mahaifiyarka ,kazabeta ka barni ,,,umar yace haba husna kibarni da hajiya nasan yadda zanyi da ita kawai yabi bayanta,,,,
Daker da sidin goshi hajiya ta yarda da sharadi zaiyi aure,,yace Ya amence amma sai ya gama gini,,,
Husna dai haka ta hakura dan ita arayuwa ba abinda tafiso kamar yaranta kuma rabuwa da umar,kamar rabuwa da yaranta ne da tasa ko sun rabu ina zata da yara har hudu,,,malat ce tace momy kiyi hakuri kinji ,,murmushi tayi tace ya wuce kumuje kicin ,duk da yaran kanane tana shiga kicin dasu sbd a gidan badu isa su sakeba ,,,,
Da safe duk yaran gidan sun shirya skull ,,kafin sutafi sai sunbi sun gaida hajiya,,,sunje sun sameta tana raba sweet ,yaran hamza da ishak mazan duk anbasu bibiyu akwa khairat yar ishak itama biyu,akazo kan leema akabata day,,melat ma daya sai cewa tayi haji ya daya naga su affan biyu akabasu,,hajiya tace eh ,melat tace to mukuma day day akabamu,,,
Ran hajiya yabaci tace kunjini da yarinya zaki hada kanki dasu affan ay su mazane ,,,melat tace to khairat ma biyu kika bata,,, ce anbata ,kaji fitinanniyar yarinya nace anbata taci albarkacin yara mazan gidansu kekuwa gayamin akwai namiji a gidanku ne ,ay yara maza albarkace dasu maza bani guri, da gudu ta isa guri momynta tace momy meyasa baki hafi namiji ba hajiya kaka tace wai ,kafin ta karasa husna tace yi shuru melat karki damu da wasa hajiya take miki ,,maza je mkrt ki yi karatu kizama dr ki kaini makka,,,da gudu ta fita,,,
Dafe kai husna tayi tace wannan masifa tayi yawa wai shin me laifin ya,,ya,,mata ne
Haka dai ake tfy yau fari gobe baki,,,
Husna da umar ne suna hirarsu tace my kwana biyufa ina jin mutsi a cikina kuma naga yadan kumbura ,,,yace haba mugani ,,,daga rigar tayi ya dade yana kallon cikin,,chan yace husna anya baciki garekiba ,,,tashi tayi zaune tace haba dai,,,
Yace inaga yaushe kikayi alada tace ay tonda nafara planing banayi ,shuru yayi ,yace Allah ya kyeuta gobe maje asiviy,haka dai suka bige ta harka,
Dasafe sun shiraya tare da yara ,,don zuwa asivity ,,gabadaya suka shiga gaida hajiya,,da ker ta amsa ma husna ,takuma ce ina zaki kin wani jero yaya mata kamar samera ,,,husna murmushi tayi tace zanje asivity bana jin dadine ,,,dariya hajiya tayi tace ankuma kenan,,
A asivity anyi scan an tabbatar cikine ,,,da farko husna ranta ya baci amma kuma ana cewa namiji ne ,farin ciki ya bayyana a fiskarta ,suka rungumi juna da umar suna godewa Allah,,,
Haka suka nufi gida ciki farin ciki ,,suna tafy husna tace my yanxu kam an fasa mun kishiya nasan yau daga hajiya taji zata soni zata bari mukuma sabon gidah,,,dariya umar yayi yace my husna bazamu gayawa hajiya kina da ciki ba sai mun tabbatar,take husna ta hada rai tace ay yanxoma mun tabbatar tonda Dr ya fada ,,yace hakane duk da haka dai muyi shuru tace to ,,,
Haka husna take ta rainun cikinta bana bata boyeshiba ,,kuwa ya ganshi,,, siyayyar kayan yaro kuwa abin baa magana ,,,
Haka har Allah yakawu ranar haihuwa ikon Allah kuma aka haifi mace,,,,
*cigaban labarin*
Ko biyuni
Ummu farhana 😘
*BRILLIANT WRITERS ASS*
👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀
*YA,YA, MATAH*
(Abin Alfahari ne)
👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀👱🏼♀
*BY UMMU FARHANA*
*DEDICATE TO MY FANS*❤❤❤💋💋
*MASOYANA KU CIGABA DA HAKURI ,,NA JINA SHURU ABUBUWA NE SAI A HANKALI BA LKC SOSAI ,INA BAKU HAKURI ,RASHIN JINA KULLUM* ,,,
COMMENTS