SHAKUWAR YARINTA 28

  HAKUWAR YARINTA                 continue lll.  CIGABAN LABARI

 


HAKUWAR YARINTA

                continue lll. 


CIGABAN LABARI

 

Labeeb yana gama hutawar shi ya fito dan yaje gidan mahaifinshi yana zuwa y tarar da hjy maria a gidan wato mummy tana ta faman rarrashi jamilu akan yayi hakuri yazo su koma can daya gidan bayan y shaida mata bazai kara zuwa ba nan ta bashi hakuri, mummy na ganin labeeb tace meya kawoka yace munyi waya da daddy ai yace nazo nan na same shi" tace to yi maza ka koma can kan ya fito y ganka gamu nan tahowa gidan ai" yace mata to kawai y tashi y fita ya koma chan gidan su, tun daga nesa yake hango wata yarinya wacce   yasan ya girmeta kawai saiya karasa wajan dan ya gaji da zaman cikin gida mutum ne shi mesan haya niya da jamaa tana zaune a kofar dakin su tana hada shayi a butar su yazo y tsaya a wajan yace mata kina jin hausa tace masa eh ina wuni bai amsataba yasamu waje y zauna a wajan yace mata me kikeyi tace ruwan buzu nake hadawa yace mata nima zansha tace zakasha kaima tana zaro ido" yace eh ko bazaki banba kafin ta bashi amsa saiga yaba ya fito a dakin jin magana a waje yace sannu yaro yace sannu baba yace zaka iya sha kuwa naji kana abaka yace eh inasha a awajan buzu iro in mukazo hutu , kun sanshi ,yaba yace kwarai kuwa yaro ai shiya kawomu nan aiki dani da yata da matata labeeb yace au tare kuke da sabuwar nany di jabeer yaba yace masa eh" Lili data zuba mishi ruwan buzu a dan karamin kofin su ya sha yace mata ya sunan ki tace masa suna na Lili yace nikuma labeeb nanya saki  baki yana sha suna yar hirar su da baba suna nan zaune saiga daddy da mummy sun shigo yace ga babana nan bari naje ya tashi da sauri ya nufi parking lot hjy maria ta wuce cikin part disu  da tunda tadawo bata shiga ba , nan labeeb y rugume daddy shi yana mai fashin cikin yace me kake a waje yace yanzu nashigo naje can gida mummy tace na dawo yanzu zaku taho "kawai ya tabe baki baice komai ba labeeb yace daddy kazo muje wajan su baba da Lili kasha irin shayin nan na iro jamilu na kallon wajan da yake nuna masa yace waye baba kuma yace gasu can tare suke da sabuwar nany di jabeer jamilu na kallon su ya gane su  ya gansu da matar nan da inya ganta yake tuna mahaifiyar labeeb da suke masifar kama yace to muje nasha dama mura nake nan labeeb ya jashi suka je yana zuwa yaba ya miki yana gayda shi yace zauna baba nima shayin nazo sha labeeb yace kun iya dafawa nan yaba ya zubamai yana daria yace ranka ya dade da kanka aida kace akawo ma yace aa nima anan zansha ya ansa ya farasha, yana sha yana dan jefawa yaba tambaya dan yasan daga inda suke yaba kuma da abun nema yasamu ga abokin hira har gida basaj yaje wajan iro ba ,nan ya rinka bashi labarin har zuwan su da auran shi da Jamila da rashin haihuwar da basa samu da yanda yake son Lili ta samu ilimi na zamani suna ta hira Lili da labeeb ma sai ta tsuniya take bashi kaman sun shekara da sanin juna labeeb nata daria , nan yace Lili ta karamai shayi bata ankara ba ta zubamai kadan a hannu bazafi dai dan ya fara hucewa nan labeeb da neman magana yace saiya rama Lili ta tashi a guje tayi hanyar filin polo shima tashi yayi ya  bita da gudu yaba nata kiran shi labeeb kazo to a sama magani ina yabi Lili da  gudu can sukayi tana gudu yana binta a baya abinka damai ciki duk kibar Lili ya fita ,tana juya wa taga y daina binta ya tsaya yanata ninshi tace bakasan na fika gudu ba tayi masa  gwalo nan ya juya yace zan kama kine itama tana ta biyoshi a baya nan a kasan filin taga ya zauna ta karaso nisa dashi tace kaga na fika gudu bullluuuu 🤪🤪ta masa gwalo tace dan luluti yace ai kema yar lukuta ce tace ni ai da safe muna motsa jiki da yaba anan yace mata nima inaso ina motsa jiki mummy ce ke hadani tace haka nafi kyau kaka ( mesanda) kuma yayi ta bani wahala yace saina rame ni kuma na kasa ramewa nan y fashe da kuka , Lili sai duk jikin ta yayi sanyi tazo kusa dashi tace kanaso ka rame ya kalle ta kawai tace zan koyama irin yanda ake mana a makarantar mu a yamen yace mata ni ai ba iya motsa jiki ne matsala taba harda cin abinci yana turo baki tace to saika nacin kadan yace bazan iyaba tace zaka iya kullun zan na baka irin shayin mu kazo ka ansa yace mata promise tace yes i promise labeeb ya bude baki yace a ina kika iya turan ci tace ina zuwa makaran ta a yameen yace mata yanzu fa tace nadaina yace kinaso nasa daddyna ya kaiki tace masa saina tambayi yaba nan ta miki ya mika mata hannu yace tayani in tashi suna daria ta tayashi y mike suka koma wajan iyayen su har a lokacin jamilu  suna hira da baba labeeb na zuwa yaba ya dauko magani zai saka masa a wajan da ruwa y zuba sai labeeb yace ai ba zafi baiji ciwo ba nan jamilu ya mike yanawa baba godiya suka wuce ciki labeeb na dagawa Lili hannu direct bangaran su labeeb suka wuce suna shiga suka tarar da inna a falo jabeer nata masifa wai ta cika musu falo da wari ta fita ta barshi baya bukatar taimakon ta jamulu yace lfy nany ruky ta fadi abun da jabeer ya fadawa inna nan jamilu ya kwashe shi da mari yace kuma bazaa sake chanja masa me aiki ba tunda haka halinsa yake jabeer ya wuce ya fita direct wajan mahaifiyar shi yayi ,nan jamilu ya bawa inna hakuri yace mata kuma duk sanda jabeer yayi wani abu ta fadasa nan yace wa labeeb y wuce daki shikuma ya fita dan zuwa part disu a bakin koma yace karo da maria tana shirin fitowa ,tace haba jamilu yazaka na bawa yaranka kunya gaban masu aiki salan su raina shi "yace ohhh so kike ya tashi da irin bakin halin ku kenan ta bata rai tace mesa ya kakemin hakane jamilu komai  ba nayi ba daidai ba ni maria sbd kuskuran da nayi a baya yace mata har yanzu ma shi kike kuma ina nan ina tara ki bai jira ta sake magana ba fuuu ya fice ya barta anan... Bayan sallah isha mesanda ya shigo gidan bayan fitar da yayi da yamma nan ya hango labeeb ya fito da niyar zuwa wajan su Lili dan shifa yanzu ya samu wajan zuwa indai zaina shan shayin nan nasu ,har zai wuce yazo wajan parking lot ya gaida mesanda da suke kiran shin grandfa ," labeeb yace grandfa welcom mesanda dake shirin fitowa a mota yana karasowa ya daga sandar shi y kwadawa labeeb yace me halin ubansan a tsaye zaka gaida ni jibi yanda kayi kiba kaida babanka kun  samu na banza ko zanyi maganin kane ya sake kwadamai a kafada nan yaji zafi sosai ya gudu yana sosa wajan mesanda ya rinka kiran shi kazo ban gama da kaiba kazo nace ma" ina labeeb ko juyowa baiba ya wuce dakin shi ya saka key ya kulle mesanda har part disu ya biyo shi , sai jabeer ya samu a falo suka wuce dakin labeeb sunata kiran shi yaki bude kofar mesanda yace zaka hadu dani ne gobe nan ya bar wajan ya koma part dishi jabeer na biye dashi ya sanan mai marin da mahaifin shi yamai dazu , yace na fuskan ci jamilu taurin kaine dashi ya rantse bazai baku farin ciki ba  kaida mahaifiyar ka sbd small mistake da akayi masa zanyi maganin shi jabeer da mamaki yace grandfa me mama tayiwa daddy mesanda na dorara sandar shi ya girgiza kai yace kai yaro ne kome zan fada maka bazaka gane ba sai nan gaba jabeer y taba baki zai juya yace good night grandfa yace masa night kawai ,nan ya wuce part disu ,inna kuwa tunda aka mari jabeer data dawo bangaran su bata sake komawa ba nan ta bawa yaba labarin duk abin daya faru ta kuma ce masa ita batasan aikin nan gaskia, gidan ma bai kwanta mata ba kawai ya sanan d iro yasamo musu wani gida ,yaba ya amsa mata ne kawai amma a ranshi baiga lefin gidan ba jabeer ne matsalan inna kuma tunda baba rakia ta bata kaya dasu turare ba shikenan ba sai tana kwalliya"..washe gari da safe  maria ta tafi Germany dan ganawa da wasu business partner na mahaifinta tana fita jamilu ma ya fita dan zuwa wajan babe dishi daya kamawa hotel akan zai sallameta ta tafi ," bayan fitar sa labeeb y fito dan zuwa wajan su Lili yaga wani securitin gidan yazo y dauke shi akai kaman wani barawo yanata chilla kafa yana cewa take me down ina zaka kaini ka kyaleni bai dire shiba sai a bayan gidan a gaba mesanda , cak y tsaya yake kallon sa yasan tunda aka kawoshi nan wani abu zaiyi mishi kaman yanda ya saba a baya , Lili tunda taga an dauki labeeb aka yana ihu tabi bayan su da dabara a hankali har taga inda aka ajiye shi aganban mutumin nan da suka ganin yazo ran nan, ita dai ta samu waje ta buya a bayan wata bishiya wace duk ciyayi ne da bishiyu kaman kaje daji bazaka taba cewa a gidan bane , mesanda yace ni kayiwa rashin kunya jiya ko yaran banza yayi kalan kuka😩 yace grandfa kayi hakuri bai karasaba ya kwadamai sanda tareda cewa niba kakan ka bane labeeb y fara kuka kaman ranshi zai fita, yacewa wani a wajan dorashi akan hayin can ya nuna mai wani gidan tururruwa da cinnaka a wajan sunfi dubu 🐝🦟🦗 yace daurashi in yayi mutsi saina fasa kanshi da bindiga cak aka dauki labeeb aka daurashi kaman yanda mesanda ya fada yana  tsaye da sandarshi a wajan shikuma labeeb duk ant 🐜 dinan sun gama shiga jikin shi yana tsaye kaman soja yana kuka yana cewa grandfa dan allah kayi hakuri na tuba bazan sake ba kayi hakuri mesanda yace kamin shiru sakaran yaro kun zame mana masifa kaida ubanka marasa amfani kawai shidai labeeb kuka kawai yake yayi kusan 30m ahaka san nan mesanda yace a sauko dashi, duk abin nan da akeyi Lili na labe tana gani mesanda yayi tafiyar shi yace subarshi nan ya koma da kafar shi , labeeb na wajan a kwance yana kuka abinka da fari fat duk jikin shi yayi jajur kuka kawai yake , Lili sai da taga duk sun bar wajan sunyi nisa sanan ta taho wajan labeeb da gudu ta dagashi tace masa me kayi musu labeeb ya kasa ko magana kuka kawia yakeyi ganin bashida niyar magana ta taimaka mishi ya tashi tana dafe dashi har suka bar wajan direct part disu tayi dashi dan mahaifinta ya saka mishi maganin kasan cewar tasan ya iya hada maganin kuma baya rabo dashi kala kala suna zuwa suka shige cikin baba da inna na zaune suna shan shayinsu , tuni suka tashi suka anshi labeeb suka kwantar dashi akan shimfidar su inna na salati yaba yace meya same shi nan Lili ta sanan dashi komai duk abinda daganin labeeb ko magana bayayi kawai jan rai yakeyi da soshe soshe , nan danan yaba ya dauko wani maganin ya hada mishi y shafa mishi kan kace me labeeb ya daina susa harya samu bacci anan dakin nasu ,yaba da inna sai mamaki sukeyi wan nan wani irin abu ne anya kuwa lafiya ,dama jiya a zaman da sukayi da jamilu ya dan bawa yaba wani labari kadan acikin gidan.. bayan kusan 2hr labeeb y farka a bacci bakowa a dakin sai Lili dake saka tana  kyalle da sunan ta jiki, "kasan cewar ta iya sana'ar inna ce a yamen " sai kallon ta yake sai can yace mata nagode da sauri Lili ta dago tayo kanshi tana cemai ka tashi bari na kira yaba kawai taga ya fashe da kuka Lili ta dawo take tambayar shi menene ko har yanzu yamai kyarkayi "yace mata Aa kawai ina jin tausayin kaina ne bansan meyasa ba kaka baya sona yafison jabeer, ni kowa baya sona daga daddy sai uncle Ahamad kawai suke sona nan ya sake rushe wada kuka Lili kallon shi kawai take da damuwa tama rasa me zata ce masa , labeeb ya sake magana yace kaka yace jabeer ne kawai zai koma school banda ni ,ni anan zan zauna zaa chanja min school ita dai Lili sai kallon shi take yana ta magana" nan labeeb ya fara bawa Lili labarin irin ta kuran da tsangwamar daya tashi besan wata soyyarya ba bayan ta baba rakira da mahaifin shi , daddy shi bai taba koda nuna mishi hoton mahaifiyar shiba koya kaishi wajan dangin ta gudun kar a bashi labarin abin daya faru a shekarun baya yafi sai lokacin daya dace zai fada mashi dan su dau fansa," Lili nata kuka tana tausayawa labeeb dake ta bata labari " yaba yana waje wajan aikin shi saiga Alhj  jamilu nan  ya dawo yana ganin yaba da fara'ar sa yace baba sannu da aiki yace yauwa barka da dawowa yallabai , nan jamilu ya shige part di su labeer, jabeer kawai yagani yana breakfast a dining jabeer y taso ya gaida shi yace mai ina labeer jabeer na sosa kyeya yace ban ganshiba nima daddy, saiga inna ta fito daga kitchen dan kwashe kayan da jabeer yaci a dining yau kan inna tayi kwalliya kaman ba itaba ta saka kayan da baba rakia ta bata ta saka jan hijabi har kasa da yayi masifar mata kyau abinka da fara , data fito jamilu bai gane taba saida ta gaidashi ,tana ganin shi tace ina kwana yallabai har kasa ta zukunna jamilu kasa amsawa yayi sbd mamakin kamarta da matar shi daya sake fitowa yanzu kawai saidai matarshi bata kaita tsayi ba , inna bata jira amsar shiba ta wuce dinning nan ta hada kayan tayi haryan kitchen har zata shiga jabeer yace ki sake kawomin tea tace to ta wuce kawai, jamilu na zaune a wajan tadawo da tea di jabeer a hannu ta mika masa jamilu yace , ko labeeb na wajan ku tace eh yana can yace yaje shan shayi kenan ,inna tayi kasa da kanta tace aa yallabai Lili ta kawo shi jikin shi duk ciwo kasan megida na yana hada magani shine ta kawoshi aka saka mai bata kai ga karasawa ba jamilu ya mike yace ciwo kuma wani irin ciwo inna bata bashi amsaba zata wuce jabeer ya watsa mata tea di wai ba dadi kaman tasamai gishiri a ciki yana masifa yace haka ake hada tea baki iya bane  tace yanda nayi dazu yanzuma haka nayi inna jiki na rawa tana yarfe jikin ta jabeer zai sake magana yaji an dauke shi da mari an sake dauke shi da wani marin sai da jamilu ya mashi kusan uku zai sake na hudu jabeer y daga kafa zai feta a guje yaji ubansa ya rikeshi ya jiyo dashi a gigice yace tarbiyar da aka baka kenan to daga yau sai yau inna sake ganin ka kayiwa ko wani kallon banza ne don suna kasa daku ko wane wllh saina karya ma kafafuwa kana jina ,inna kuwa tunda taga haka tabar wajan tayi part disu da sauri, tana shiga ta tarar da yaba yana kara shafawa labeeb magani yana kuka yana ta yarrashin shin inna bata ko kalle suba ballan tana suga wani abu nan ta cire hijab dita ta saka wani san nan tayi wajan su ta zauna kusa da yaba ta lacuci man da yake shafawa  labeeb da dabara tashafa a wajan daya dan taba ta dan karya tashi, " alhj jamilu nafitowa direct wajan su inna yayi yana shiga yaga labeeb fuskar shi duk ta kunbura tayi jajir sbd kuka , jikin shi kuwa duk reactions sun fitomai abinka da fari a haka ma maganin da yaba ya saka mai sun ragu , labeeb na ganin shi ya sake fashe wada kuka yace daddy yayi sauri y karaso wajan shi yace meya faru dakai labeeb nan labeeb na kuka da taimakon Lili labeeb ya bashi labarin duk abin daya faru," alhj jamilu bai tsaya jin sauran labarin ba ya miki ya fita direct part di mesanda yaje a zuciye ,yana shiga ya tarar dashi a study room dishi jamilu ya buga table di da karfi yana nuna shi da yatsa ,yace Aliyu mesanda kake ko waye ,saida mesanda ya dan yazana da yanayin na jamilu yace hakuri na ya fara karewa akanku wllh wllh ka sake taba min dana sai naga bayanka ni zaiyi exposing dika ta inda bakayi tunani ba kasandai nasan komai naka yanzu da abokan business dika kaika san bawani wuya zaimin ba akwai abinda nake jirane shiisa har yanzu nake tare dakai amma wllh saina maka fiya da abin da kamin a shekarun baya" mesanda yayi wata kasai taccan murmushi yace baka isa kaga bayana ba sbd nina raineka ,kuma karka manta har yanzu tsohowar ka tana nan darai da kanin ka harda iyalinshi ma ,ka kurkura kayi wani abu zaa maimaita labarin baya , so get out in my office stupid " jamilu yayi daria me isarshi yace shiisa nacema akwai abun da nake jira kafin naga bayan ku duka , wan nan y zama na karshe da zaka taba labeeb sashi da kukayi y tashi a maraici be ishe kuba anbicin kuwa baka isa ka hanashi ciba dan har yanzu beci na diyar uwarshi da kuka kashe maiba ,jamilu ya juya a fusace ya fita mesanda kawai ya girgiza kai only God knows what is in his mind (😭 what will happen again ?)

Jamilu ya dawo part di su inna yazo y dauki labeeb yayiwa su yaba da inna godiya harsun fita yaba yace ga sauran maganin a kara shafa mai anjima in sha allah kan gobe sun gama fita jamilu da har sunyi gaba yace Lili ta biyomu dashi , nan yaba y bawa Lili tabi bayan su da maganin suna shiga ba kowa a falon jamilu y kwallawa baba rakia kira tazo , jamilu yayi dakin labeeb da shi Lili na bayan su ya kwantar da labeeb baba rakia tazo tana ganin labeeb ta fashe da kuka tace meyasa mi dan nan ni rakia ,jamilu ya bata labari lili dai na gefe baba rakia ta sake fashewa da kuka tace allah allah ka sawaka marayan nan ka kawo karshin abin nan" labeeb yace nany ruky zansha tea nan ta tashi da sauri taje ta hado mai Lili ta ajiye zata fita labeeb yace aisai ta zauna anan .......

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: SHAKUWAR YARINTA 28
SHAKUWAR YARINTA 28
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjDC1vCpOjap5bt02qg30y8b3wHX7MdG-pWbTxahcooujFo24yoWBUCmPaFn08M7BBe9WLVS1GD-CEPYnGXQtbtxCKQJMEi10rs71NAG8sQIFb-oNWnuJ-wzE8s4-htyv2gBHeuk3hg4vTTvPpIWhpruixrxhQ29M-R7apD26cFtAYYahbsRh5YG9ivJidO/s320/img_1696062560803.webp
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjDC1vCpOjap5bt02qg30y8b3wHX7MdG-pWbTxahcooujFo24yoWBUCmPaFn08M7BBe9WLVS1GD-CEPYnGXQtbtxCKQJMEi10rs71NAG8sQIFb-oNWnuJ-wzE8s4-htyv2gBHeuk3hg4vTTvPpIWhpruixrxhQ29M-R7apD26cFtAYYahbsRh5YG9ivJidO/s72-c/img_1696062560803.webp
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/shakuwar-yarinta-28.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/shakuwar-yarinta-28.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content