*MUFEEDAH* *NA* ummie khady FCW ASSO. Bismillahir rahmanir raheem
*MUFEEDAH*
*NA* ummie khady
FCW ASSO.
Bismillahir rahmanir raheem
Ya Allah yanda nafara lfy kasa nagama lfy kasa afada kantu Kuma anisha dan tu ameen
Wannan shine book Dina nafarko In anga kuskure amun uzuri nagode🙏
Page 9
K'arasawa gaban Inna ta yi ta ce
"Inna ga aiken ki nan"
Ta tsallake ta da gudu ta yi d'aki
Kafin Inna tai magana wata k'atuwar mata shirgegiya ta shigo da k'atan ice a hannun ta tana huci.........
Tana ce wa "wallahi yau In na kama ki Sai dai iya yan ki su haifi wata"
Taufeeq ne ya ce "bai war Allah lafiya? Me ya faru?"
Kallan shi tayi da ja ja yan Idanun ta. ta ce " Kai yaro lafiyar ce zaka ganni a haka na shi go muku gida?"
Ta fad'a cikin gurb'ataciya hausar ta domin kuwa ba, ba haushiya ba ce, inyamura ce.
Dady ne ya ce "ki yi hak'uri ki fad'a mana meya faru"
Kallon dady ta yi ta ce "ai yau in ban sumar da yarinyar nan ba hankalina ba zai ta b'a kwanciya ba"
Inna dai kasa magana tayi, ta yi shiru kawai ta zu bawa sarautar Allah ido,
Dady ne ya ce "subhanallah ba za'ayi haka ba kiyi hak'uri kifada ma na me ya faru"
Ya ran su na in yamuranci ta fara yi ta na hargagi ta na fad'a ta na sharce gumi.
Mufeed ne ya tashi da fura a jikin sa ya ce "dady matar nan kawai huce hau shinta guda daya ne kawai a bata mufeedah ta yi mata duk abin da za ta yi mata shi ne kad'ai abinda zai kwantar da han kalin baiwar Allah nan"
ta shi ya yi, ya nufi k'ofar d'akin da mufeedah ta ke ciki.
Inna ce ta tare shi ta na fad'in "sannu mugu mai bak'ar zuciya, sarkin marasa hankali, ni ai ban san rashin han kalin na Ka ya kai har haka ba kai yanzu dan ba kada hankali Sai ka dauko mufeedah ka mik'awa wannan basa mudiyar? Dan ka wai an mata laifi?"
Inna ta fad'a ta na ban kawa mufeed wata uwar harara.
Mufeed ne ya ce "haba inna daga fad'ar gaskiya"
"Wa ce gaskiya kawai dai kafito min a mutum ka ce ka tsani mufeedah a fito da ita a bawa basa mudiyar matar nan ita ta kashe ta, dan wannan ta kama mufeedah ai sai wata ba ita ba"
Mufeed ne ya ce " to miye a ciki da waya kai ta?"
Inna ce ta ce "gya tumun kane ya kai ta"
Ta fada ta na wa mufeed da k'uwa
Mufeed ne ya yi k'wafa ya ce "me laifi daban wanda ake sauke wa kwan dan fad'a da ban dan kawai ka fad'i gaskiya"
Dady ne cikin fad'a ya ce "babana ungo maza karbi wuce ka ta fi masau kin mu kafin mu k'raso"
Kasan cewar dady yana da gida agarin inyazo anan ya ke sauka shida iyalan sa,
Inna ce ta ce "ai da kabar shi ya zauna yaci gaba da hargi tsa zance dan cin k'wa ka wai"
Ta fad'a binshi da harara shi dai mufeed ko takan ta be k'ara biba ya karb'i key ya yi wuce warsa.
Momy ce ta tashi ta k'ara sa kusa da matar ta dafa ta ce baiwar Allah, dan Allah ki yi hak'uri ki share hawayan ki ki fada ma na meya faru yanzu zamu da mataki"
Matar ce ta dube ta ta ce " ina da garken awakai a k'ofar gida na, daga gefe guda Kuma Ina Sana a ta ta soya k'osai da wainar shin kata kullum da safe inayi ne dan in rufawa kai na asiri mijina ya gudu ya barni da yara guda goma nina ke cida su.
Kawai yarin yar nan ta zo wuce wa ta lek'a garken nan taga a kuyoyin nan sun cinye abincin su. Shine naji tana cewa Allah sarki haka aka barku ba abinci to ku fito ku je ku nemi abinci yunwa bata da dad'i,
Kafin in farga ta korosu kan kayan sana'a ta, tana maza ku je ku yi kiwo ku dawo yinwa bata da dad'i
Haka ta koro su duk suka yomin kai na suka barar min da kullun wai nata dana wake na da man gyad'a kwalba goma da na ke sayar wa da wainar da na soya da miyar da kosan dana soya duk gasu can cikin k'asa. Wallahi ta cuce ni kuma bazan yadda ba"
Ta k'ara she maga nar tana d'aga hannun ta sama alamar ran tsuwa,
Dady ne ya ce "tabbas ba a k'yau ta miki ba, zamu dau mummunan mataki akan ta kiyi hak'uri yanzu kud'in naki nawa ne?"Kallon shi ta yi ta ce " kudina da yawa malam"
Kallon ta yayi ya ce "ba komai kifada"
Nan ta hau yi masa lissafi murmushi ya yi ya ce "ba komai" nan ya sa hannu a cikin aljihun sa ya fito da rafar y'an dubu-dubu ya mik'a mata,
Kar b'a tayi ta zube a gaban sa ta na godiya,
Inna ce ta ce "to ba sa mudiya me waina a ta shi a k'ara gaba dama bara ce ta kawo ki dan kunga ya zo, ni wallahi ban yadda mufeedah ta yi wannan aika-aikar ba sharri ne ka wai ake mata"
Taufeeq ne ya kalli Inna ya ce "Inna ki yi shiru mana komai ya wuce"
Kallon shi ta yi ta ce "kai ba zanyi shirun ba a shigo har gida a sambad'a k'arya hadi da damfara Amma ka ce na yi shiru to ba zanyi shirun ba"
Taufeeq ne ya ce "to ai Sai kiyi ta yi"
Ya sa kansa ya fi ce
Dady ne ya ce wa matar nan "ta shi ba komai Allah ya kiyaye gaba"
Ta shi ta yi ta karkad'e jikin ta ta fi ce da kud'in ta a hannu,
Ko kallon in da Inna ta ke batayi ba,
Dady ne ya k'ara k'u dira a ranshi a Kan dole ma Sai ya tafi da mufeedah,
Inna ce ta keta kumfar baki ta na fad'a Dady dai Allah k'yau ta kawai ya ke ta fad'a,
Inna ce ta nufi d'a kin da mufeedah ta shi ga ciki ta na "bari ku ji gaskiya daga bakin mufeedah yan zu za ku ji gaskiyar abin da ya faru don mufeedah bata k'arya"
Dady ne ya yi murmushin ta kai ci dan shi ya dad'e da sanin Inna ce ke d'aure wa mufeedah gindi ta na ta asar da taga dama a wannan gari,
Ta tura k'ofar d'akin ta na "mufeedah ya rinyar kirki fito ki fad'a wa baban ku abin da ya faru"
Inna ce ta yi turus ganin mufeedah na gado ta ja bargo ta na barci,
Inna ce ta ce " Allahu akbar bai war Allah, Allah sarki baiwar Allah baccin wahala ma ta ke yi, an baki wahala, Allah ya saka miki"
Dady ya ce "Inna za mu je masau kin mu anjima zan dawo"
"To babana ku yi hak'uri fa daga zuwan ku an d'aga muku hankali sha anin muta nan garin namu ne sai addu'a"
Inna ta fad'a ta na duban su,
Nan suka ce mata ai ba komai zasu dawo anjima in suka huta,*Da yamma*
Da yamma bayan Dady da yaran sa sun dawo gidan Inna suka k'ara gaisawa.
Mufeedah na gefe kamar mutuniyar kirki
Dady ne ya ce "Inna ta Ina ne man wata alfarma a wajan, ki"
Inna ce ta ce "fadi kan ka tsaye babana"
Dady ne ya ce "Inna dan Allah dan annabi ba dan ni ba ki bani mufeedah in tafi da ita wajena zan sata amakaran tar sun hidaya Inna dan Allah karki ce a'a"
Inna ce ta ce "ai kuwa dole na ce a'a wato babana shi yasa ka kasa fad'ar magana ka tsaya kana ke wa ye to wallahi sai dai ka yi hak'uri amma mufeedah nan gani nan bari, ubanta ma ya hak'ura ya barta bare kai"
Momy ce ta ce "Inna kiyi hak'uri ki bamu ita insha Allahu zaki mamakin mufeedah kin ga anan ansa ta agaba a binda ma bata yi ba cewa ake tayi"
Inna ce ta ce "to suyi ta fad'a mana mufeedah dai ta sha tabara ta sha yasin nan gani nan bari"
Dady ne ya ce "to Inna ki shirya mana kema mu tafi tare"
Inna ce ta ce "wa? ni? babu Inda zani"
Mufeed ne ya ce " ai dady kawai kabar mata ka yan ta su k'arata"
Mufeedah najin haka ta k'wallara k'ara ta ce wallahi Inna sai naje kano kullum Ina ce miki ina san zuwa kano sai kice in yi hak'uri za ki kai ni kuma kin k'i ki kai ni yanzu dady zai ta fi dani amma zaki hana wallahi to sai na je, ko ki barshi ya tafi dani ko in bisu a k'afa"
Inna ce ta rike hab'a ta ce yanzu mufeedah so kike ki tafi kibar ni" sai idon Inna ya ciko da k'walla
Mufeedah ce ta ce "Inna saratu ma fa ta tab'a zuwa birni amma ni ban ta b'a zuwa ba kullum in suka je birni ita da goggon ta in ta dawo sai ta bani labari amma ni baki tab'a kai ni ba?
Inna ce ta wulla mata da k'uwa ta na ce wa saratu k'an war uwar ki ce da zaki ce duk In da taje sai kunje
In za abi sal sala ke in da Ki ka je saratu ta isa ta je can sha sha sha kawai"
Mufeedah ce ta k'ara rushewa da kuka ta na fa d'in sai ta je,
Mufeed ne yay tsaki ya ce "ka ji butulu ana san ta, ta na gudu"
Mufeedah ce ta ce " i din ina ruwan ka dan shishshigi"
Wata uwar harara ya watsa mata ya na kissima abin da zai mata in har tabisu,
Nan dai akai ta dan bar wa da Inna da mufeedahn ta da kyar dai Inna ta yar da a tafi da mufeedah tunda ta dage amma da sharadin sati zatayi ta dawo.
nan dai dady ya hau murna dan dama wuyar ta, ta yadda mufeedah ta bisu
Washe gari mufeedah tun asuba ta tashi ta yi wanka, ta ranga gad'a kwalliya tana jiran dady.
Inna ce ta ce "yanzu mufeedah murna ki ke zaki ta fi ki bar ni"
Mufeedah ce ta ce "i wallahi inna" ta fad'a ta na dariya
Inna ce ta ce "ai kuwa zaki fad'awa aya zakin ta ta mu na nan Zaki dawo da k'afa funki"
Nan dai sukai ta dan barwa,
*Da yamma 4:30pm*
Lokacin Dady sun shiryo zasu ta fi
Saratu ce ta ce "mufeedah yanzu in Ki ka tafi yau she zaki dawo"
Mufeedah ce ta ce barana bare wata dan sai birni ta ishe ne har nayi gya tsa sannan zan dawo"
Inna ce ta fara share hawaye ta na "mufeedah karki tafi ki barni"
Mufeedah ta na ce wa "inna kiyi hak'uri aradu yau sai na kwana abirni"
Hidaya ce ta kamo hannun mufeedah suka shiga mota,
nan mufeedah ta dinga d'aga wa inna hannu, ta na wa saratu gwalo akan ta tafi birni ta bar ta yara ne suka bi motar da gudu suna
Yeeh mufeedah ta ta fi birni yeeh mufeedah ta tafi birni,
nan Audi ya gansu suna ta ihu suna bin motar da gudu ana ya tam baye su lafiya nan wani yaro daga cikin su ya ce
"mufeedahn Inna binta ce aka dauke ta, ta ta koma birni da zama Inna binta Kuma gata can ta na kuka Audi ne ya ce alhamdullihi shi kenan "mun yarda dan yan mun gwaro mun huta da kuda, Allah raka taki gona mun rabu da annoba...........
Love u all
My fan's
Share fisabilillah 🙏

COMMENTS