*MUFEEDAH*
*MUFEEDAH*
*NA UMMIEY KHADY*
*FCW ASSO*
Bismillahir rahmanir raheem
Ya Allah yanda nafara lfy Allah kasa nagama lfy kasa afada kantu Kuma anisha dan tu ameen
Wannan shine book Dina nafarko In anga kuskure amun uzuri nagode 🙏
*Page* 20
jina yi an buɗe murfin ɓarin da nake ciki an ce barka da isowa my princess kallan me maganar nayi ganin ban sanshi ba yasa ban tanka shi ba na ɗau jakata da wayata da ke caji a mota nayi ganin lamar zan fito yasa shi matsawa daga jikin motar har nagama kulle motar be sake cemin komai ba nima kuma ban kalle Inda yake ba,da suri na nufi a jin mu saboda bana san wani abin ya wuce ni,
shi kuwa mutumin daga ɓangaran shi daya ga har ta gama abinda take yi a motar ta fito bata ce masa komai ba har ta wuce kawai sai ya juya shima ya shiga tashi motar ya nufi get
bayan mun gama lecture Cafterria muka nufa nida Hidaya da friends din mu sa'adah da nusy ƙawayan mu biyu ne duk faɗin b u k saboda Momy ta yi mana faɗa sosai akan tara friends,
bayan mun je kowa ya zabi abinda yake so nikuwa dama wanar fulawa da drink nace akawo min bayan munga ma muka ta shi kowa ya yi gida kasan cewar bamu da wata lecture ɗin da za muyi, tafiya muke a mota muna hira da Jamal a waya boy friend ɗin Hidaya, ne shi wayar ta sa a hands free roƙona ya ke akan in shawo masa kan ta yana san ya fito amma taƙi sam wai ita ba yanzu za, ta yi aure ba in ma za tayi to sai dai a haɗasu ita da ni,
drive na ke yi ina ta tin tsirewa da dariya saboda yan da naga hidaya na ta harar wayar shi kuma yana ta marairai ce min can na tsagai ta da dariyar na ce "haba saurayin mu har sai ka tsaya ka biye ta ai da kabi ta hannu na da tuni an wuce gurin" nafaɗa ina mata gwalo
ita kuma sai ta zare ido alamar abin ya bata mamaki
da sauri ya ce " ah haba dai?"
na ce "au baka yadda ba?"
ya ce "ba haka bane kawai dai ban kawo hakan ba ne sam"
nayi murmushi dai dai san da nake karya kan motar zuwa layin mu na ce
"kai in ban da abin ka, ka yadda ta jira macen da bata da saurayi? taɓ kai ma a gaishe ka"
dariya ya yi ya ce "hhhh sister in kika ce haka dariya kike ban Nasir har yanzu yana kan bakan sa akan ki amma kin ƙi saurar shi in yakira waya tun kina ɗauka kina masa wula ƙanci har kin dai na ko wane kafa da kika san kuma zai same ki duk kin yi blocking din shi why? kuma kinsan har cuta ya yi?"
"oh my lord, jamal kasan me?"
nafaɗa cikin murya mai rau ni,
kafin yaban amsa na ce
"wallahi ba laifina bane laifin abokin ka ne na gaya mishi haryan zu fa ni yarin ya ce....." kafin na rufe bakina gaba ɗaya suka kwashe da dariya daga Hidaya harshi da ke cikin wayar kallan ta na yi na ce
"almura da kinyi tsit kamar bake a motar nan"
Jamal ne ya ce "duk da ba saurarar shi kike ba amma kulashin da kike ya na samun relief ai"
murmushi nayi na ce "to miye amfanin na bata masa time?" haka dai mukai ta hirar abokin sa wanda ya ke bala'in sonanikuma ban shiryawa soyayya yanzu ba
muna ta hira Inda Hidaya tai shiru kamar bata wajan,
har muka zo bakin gate,
tunkan mu ƙara so bakin gate din duk securitys ɗin da muka zo wuce wa sai sun ɗago mana hannu alamar gaisa wa muma kuma sai mu ɗaga musu hannu,
har muka k'araso gida gate keeper yazo ya wanga lemana kofa sannan muka shiga ciki nan nayi parking sannan na ce "to jamal mun ƙaraso gida zan faɗawa Momy da Dady maganar mu"
ya ce "yawwa sisto"
HIdaya ta ce "taɓɗi jan wallahi da kin taro march"
ɗage girata nayi guda ɗaya na ce "and so what?"
sanin halina yasa ta ce "dear dan Allah kabar maganar nan kaɗan bani lokaci nida kai na zan ma maganar kaɗan bani lokaci ba da yawa ba dan Allah kace kar ta faɗa" ta fad'a idon ta na ciko da k'walla
dariya na saki jin ya ce "ok dear i love u nd am proud of u" na ce su dear da dear manya shiga
falo mukayi Momy muka tarar ita da Aminiyar ta Hajia mairo sai ɗan ta abeed abokin mr mugu ne dake ge fanta yana dan na waya gaishe su mukayi muka haraura sama gado nafaɗa saboda gajiya"
da yamma muna zau ne muna hira maama ta kira ni wai yaushe zanzo ido na zari na ce "maama ai ban daɗe da dawo wa daga gidan ki ba fa"
"i na sani biki zaki rakani dangin baban su nina ranar fridaya"
gyaɗa kai nayi nace "to Maama bari tunda saura four days jibi zanzo"
"Ok" ta ce sannan muka yi sallama
wayar na a jiye a zuciya ta na ce " Maama ke nan batasan zuwan mr mugune yake sani zuwa ba amma wannan zuwan nashi gidan Abba zani"
ban je gidan Maama ba sai ran juma'a da sassafe, da yamma ta yi muka shirya muka tafi biki, ana gama event din daga gurin bikin nace zan ta tafi gida,
nan ta kalle ni baki a sake ta ce "gida kuma? a wannan lokacin?" shiru nayi maya ban bata amsa ba ta cigaba da fadin "to baza ki ba sai ran lahadi zamu tare"
gyada mata kai na yi na ce "to Maama Allah ya kaimu"
dariya tayi ta ce "amin my daughter ko ke fa"
Ranar lahadi muka yo gida nidai Maama da yaran ta
muna shiga gidan na ga motoci alamar gidan a cike yake da muta ne baki na sake ina bin compound din da kallo kafin nayi magana Nina ta ce "Maama yau gidan Dady a cike"
"I taro za ayi akan bikin yayar ku sanda"
a jiyar zuciya na saki saboda da har gabana ya fad'i
can kuma sai na tuna sanin cewa dama in dai za'a yi biki a family din mu to an saba irin wannan taron kafin zuwan bikin domin ba a barin baban amarya yayi kayan daki shi kad'ai
sauka mukayi daga mota part d'in mu na nufa saboda nasan yan matan family din mu duk an taru a falo ana shan shafta
shaga nayi da sauri Nina ma ta biyo ni muna shiga aka sa ihu ana fad'in ga yar halak nan yanzu muke maganar ki nan aka sake baje hira kowa na ta nuna cin buri akan bin da kuma nuna shirin da ya ke akai
nan na kalli hidaya na ce "sisto yaushe zamu kai ankon mu ne gurin dinki?"
dariya ta saki "ta ce yaushe dai ke Zaki kai, ai ni tunsan Kika ta fi aranar da daddare na kira sa'idu tailor yazo ya kabi nawa sannin halin ki yasa banbashi na ki ba"
kallan ta nayi na ce "kin kyau ta"
ana ta hira ana kwasar dariya can muka ji jiniya na tashi a unguwar can kuma sai muka jita a compound nasma ce ta ce "wow ga yaya Mufeed nan ya kara so lallai bikin nan zamu shoshale"
dariya duka suka saki suna ihu ni kuwa ambatar sunan yaya Mufeed da akayi sai da gabana ya badi saboda tun sanda na tafi boarding ban sake ganin sa ba harya tafi makaran ta yasamu aiki nikuma nagama makaran ta duk sanda zaizo in naji bana zama a gidan harsai yazo ya tafi sannan nake dawo wa yauma dana san zan kanshi to da ban ma zo gidan ba da cewa Maamaa nayi bana jin Dadi,
zunbur na mike tunawa da nayi Momy na part din ta kuma nasan dole sai ya shigo dan gaida ta, kofa na nufa batare da yan uwana sun kula da niba dan suna can suna gaiyar surutu da suri na fita dan bana ma so ya shigo falon ina nan sauri nake sosai wayata ce ta yi ringing da kamar ba zan duba ba can kuma sai da d'ago wayar na kalla dauka nayi nakai kunne na kaiwa sai naji na yi karo da mutum baya nayi zan fad'i sai kuma naji an cafko hannu na waya ta ce ta subuce daga hannu na naga itama an cafke ta cikin kware wa batare da an bari ta kai kasa ido na d'ago ido na zaro gabana ya bada wani rass.......
Comment and share
COMMENTS