*MUFEEDAH*
*MUFEEDAH*
*NA* *UMMIEY KHADY*
*FCW ASSO*
Bismillahir rahmanir raheem
Ya Allah yanda nafara lfy Allah kasa nagama lfy kasa afada kantu Kuma anisha dan tu ameen
Wannan shine book Dina nafarko In anga kuskure amun uzuri nagode 🙏
*Page 19*
Juyo da wayar ya yi sai tin fiska ta ya ce "yawwa yaya Mufeed ga sister Mofy nan zata yi ma ya hanya"
gaba na, naji ya faɗi rintse ida nuna nayi domin abin ya zo min bazata ban taɓa tunani Haisam waya ya ke ba ko da yake a ji yeta ya yi yana cin abinci yana video call
Ido na, na rintse ilahirin jikina ya fara rawa zuciya ta ta fara bugawa da sauri da sauri, da sauri na miƙe ba tare da na buɗe idon nawa ba nayi hanyar hawa sama
Haisam ne ya bita da kallo ya ce
"sister ba kƴa jin daɗi ne?"
ko kallon sa banyi ba na haura sama cikin sassarfa,
tura ƙofar ɗakin mu nayi wanda ya kasan ce mallakin mu ne ni da Hidaya,
shiga nayi na tadda ta tana waya da saura yin ta mai suna jamal zama nayi kan kujera na rufe idona ina jin yanda zuciya ta ke hawa da sauka, ɓan garan Haisam kuma juyo wa ya yi, ya kalli yayan nashi ya ce "yaya M sister mofy bata jin daɗi"
daga can ɓangaran ya gƴaɗa kai batare da ya ce komai ba nan suka cikaga ba da hirar su, Hidaya ce ta sauke wayar daga kunnan ta, ta, ta ɓata ta ce "kee malama bacci ki ke ne"
firgigit nayi na buɗe ido na ce " ya fara ɗauka na ne''
kallo na ta yi ta ce " uhm naga alama"
sai ta kai na nashiga yi saboda da kar wani banzan abu can ya da meni
mema ya da meni da wani mr mugu tunda ra bona da shi she karu aru-aru yanzun ma ban kalle shi ta cikin wayar ba taɓe baki na nayi na ai yana azuciya ta yanzu na wuce ajin mugun tar sa tunowa da soja ne ya sa na ɗan zare ido can kuma nace yo idan zai zo ma ai bazama nake ba balle ya min wani abin, duk maganar da nake a cikin zuciya ta nake yi,
Hidaya ce ta dube ni ta ce " ALLAH ya shirye ki"
" Amin" na ce nan muka shiga hira tana bani labarin jamal
Anisa ce ta shigo ta ce "ashe kuna nan?"
amsa wa muka kayi da "i"
kallan ta na yi na ce "yaya Anisa wannan kayan fa?"
"i naku ne ankon yaya sajda ne gashi nan naku ne, Momy ta ce in kawo muku keda Hidaya da su Nasma"
haɗa baki muka yi gurin faɗin "wow amma fa ya yi kyau"
Anisa ta ce "ya yi kyau kam sai aka ɗinki da wuri dan wallahi Momy ta ce in gaya muku barin ma ke Mofy ke ce mai ruwan ido gurin zaɓar style biki remains four weeks"
Hidaya ce ta fashe da dariya tace "hhhh a she Momy ma ta gano ki kullun in aka ce kina da ruwan ido akan abu sai ki ce ba haka ba ga Momy ma ta ga noki hhhh"
tashi nayi na cire hijab din jiki na na ɗau less da atamfa da material ɗin nayi gaban mudubi ina kara su a jiki na na ce " wannan karan zan baku mamaki"
haka dai mukai ta hira har magaruba tayi mukayi ƙasa muka tadda Momy nan muka yi sallah sannn muka zau na muka baje a falo muna cin abinci muna hira gaba ɗaya ƴan gidan maza da mata har yaya taufiq yaya taufiqa ma tazo gidan ita da yaran ta mr mugu ne kawai baya nan
cikin haraha anayi anata tsokanar juna can dai aka soko yaya muhmud a gaba muna ta tsokanar sa saboda wata mai aikin gidan Abba da ke sanshi in ta ganshi harcan za tafiya take shi kuma ya tsane ta nan kuma aka faɗa maganar bikin yaya sajda
washe gari da safe muka shirya tsaf muka yi break fast sanna muka fita muka hau mota mukayi B U K nida Hidaya ta
muna isa makaran ta nayi parking kenan ina ƙo ƙarin ɗaukar ja kata wanda Hidaya tai saurin fitowa daga motar ganin an fara lecture
jina yi an bude murfin ɓarin da nake ciki an ce barka da iso wa my princess.......
COMMENT AND SHARE 🙏

COMMENTS