*MUFEEDAH* *NA* ummiey khady
*MUFEEDAH*
*NA* ummiey khady
*FCW ASSO*.
Bismillahir rahmanir raheem
Ya Allah yanda na fara lfy Allah kasa nagama lfy kasa afada Kan tu kuma anisha dan tu ameen
Wannan shine book Dina nafarko in anga kuskure mun uzuri na gode🙏
Page 12
Ya sha wahala sosai domin kuwa su momy sai wajan la asar sannan suka dawo gida suka barshi, a asibiti,
Mahmud ne yake gurin shi,
Momy ce naji tana fad'a wa yaya taufeeqa ce wa mufeed ko ya a kayi mufeed har ya samu karaya har biyu a hannu d'aya ga gocewar
k'ashi daya samu a k'afar shi,
Yaya taufeeqa ce ta zaro ido ta ce "innalallahi wa'inna ilaihir raju'un? Momy garin ya ya"
Momy ce ta ce "ina na sa ni, nima abin mamaki yabani Allah dai ya kyau ta amma dai ya sha wahala"
taufeeqa ce ta ce "Allah ya bashi lafiya bari in tashi in shirya direba ya kai ni na dubo shi"
Momy ce ta ce "to"
ni kuwa zuciya ta fal farin ciki mugu yana can ba lafiya wani nisha di na ji yana shiga ta,sosai
muna zaune muna wasa auta haisam yazo ya same mu ya ce "kun san me?"
kallon shi muka yi muka ce "a a menene?"
Idon shi fal k'walla ya ce " yaya mufeed ne bashi da lafiya mun kaishi asibiti ni da MOMY da Dady bashi da lafiya a can ma muka barshi"
Kallon shi nayi na ce
"shine kuma abin da muwa har kana asarar hawayan ka?
hmm uhmm ai wallahi gwanda ma da kuka barshi a can har na ji Dadi"
Najwa ce ta dube ni ta ce
"yaya bashi da lafiya shine zaki ce kinji da di? ni kuwa ban ji dadi ba, Allah yasa ya dawo gida"
kallon ta nayi na ce "tashi ki bishi kema ki zauna a can sai kifi jin dadi"
na harare ta ina barin wajan fita nayi daga d'akin wasa na tafi d'akin mu ina ta murna, rawa nai tayi ina juyi ina fad'in Allah ya k'ara mugu na can yana shan allura,
Yaya taufeeqa ce ta kira ni, da gudu naje, ina zuwa ta ce "mufeedah maza jeki canza kaya kuzo direba ya kaimu mu dubo mufeed a asibiti"
ina jin haka na dur k'ushe agurin hannu na akan ciki na ina fad'in wayyo Allah ciki na, ciwo ya ke min, yaya taufeeqa ce ta ce
"daga maganar zuwa asibiti sai ki dur k'ushe kina ihun cikin ki? da gudu mafa kika taho nan da na kira ki"
ta fad'a ta na kallo na k'ara rike cin nayi ina fad'in
"wayyo yaya taufeeqa ki tafi cikin zai cire ciwo ya ke min"
Taufeeqa ido kawai ta zuba min cike da mamaki,
Anisa ce ta ce ai kawai ku tafi tare da ita sai a duba ta tunda asibiti zaku kallon Anisa nayi na ce
" wallahi ba zani ba allura za ayi min"
Anise ce ta ce ''ai kuwa sai kinje"
ihu na k'ara saki ina
"yaya Anisa ashe ba kya kauna ta? gunda za a hala kani kike son inje? to wallahi ba zan je ba, yaya mufeed ya ci ubana ki ke so ko ?to wallahi ba zani ba"
yaya taufeeq ne yazo wuce wa yaji ihuna ya shigo yana tambayar lafiya, kuma ya ganni nayi sharkaf da hawaye da gumi
nan a ka hau bashi labari suna yi suna dariya nikuwa ganin ya zo yasa, sai na k'ara b'are ba kina,
"to dole ne sai kin je da ita yarin ya ta ce ba zata ba sai ki ta kura mata ita kad'ai ce yarin ya a gidan nan?"
yafad'i haka ne saboda yasan bana san zuwa saboda bama shiri da mufeed
wai saboda a ta bak'an ta min shine ta kwashe yaran gidan kaf ta tafi dasu wai dan naji ba dadi tun da nak'i zuwa ni kuwa ko a jiki na d'akin mu ma, na shige nai kwan ciya ta ina kallo har barci ya yi awan gaba dani har suka je suka dawo ban ta shi ba,
dama Momy kuma itama tana d'akin ta dan duk wannan haniyar ma batasa
n anayi ba tana d'a kin ta,
hayani yar su ce ta ta she ni ina bud'e idona naga Arif,
Arif ne ya ce "mufeedah sannu har kin ta shi?"
ya fad'a yana kallo na,
kallon shi nayi na ce " I na tashi"
"ya jiki munje asibiti nida baffan mu sai ka ce ke baki da lafiya shine na ce wa baffa zan zo in duba ki anjima direba sai ya mai da ni gida"
ya fad'a ya na mun murmushi, domin kuwa jinina da Arif ya had'u muna shiri sosai,
kallon shi nayi na ce " wane mak'ar ya cin ne ya ce maka bani da lafiya? to ni lafiya ta k'alau"
hidaya ce ta ce "au dama rashin lafayar k'arya ki kayi?"
hararar ta nayi na ce " I ina ruwan ki"
haka dai muka kasan ce da Arif a gida har dare ya yi direba da zai kai shi mukace sai mun rakashi har gida haka kuwa akayi, muka kai shi muka dawo, muna sai mun had'u a makaran ta,
*BAYAN KWANA BIYU*
gida ya yi min dadi ba abin da ke damu na in lokacin makaranta ya yi mushirya mu tafi in munwo naci abinci nashiga wasa na da sab gogi na, ba abin da ke damu na,
su bakin mugu kuma yana can a kwan ce da b'allallan hannu,
duk zuwa dubiyar da ake bana ce wa zani duk da san yawo irin nawa,
duk wasana yanzu bana wasa da karatu saboda kullum in naje karanta muryar bak'in mugu nake ji ta na amsa kuwa a kunne na
yan da yake yawan ce wa, ni jaka ce shi yasa nake bada himma yanzu a makaran ta har anyi gaba da ni, ina nufin an k'ara min aji,
saboda sunga yanda nake bada himma an mai dani primary 3 saboda na iya rubuta sunan na da sauran wasu abubuwan,
shima uncle din mu me zuwar mana lesson yana mutu k'ar kokari akai na, da yaga ina mai da hankali yanzu sosai,
*BAYAN SATI D'AYA*
kwatsam na tashi da safe na sauko k'asa domin yunwa na ke ji sosai na kwanta banci abin cin dare ba,
ba kowa a falon
ina zuwa dining na nufa na hau bud'e kulolin abin cin chips na gani da kunin gyad'a sai farfesun kayan ciki,
nan nahau ci kamar Allah ya ai koni kamar daga sama na ji an ja wani mugun tsaki, mtswwwww ina d'a gowa a tsora ce dan nasan nidai da na sauko ban ga kowa ba ido hudu mukayi da yaya mufeed yana ji fana da wani mugu war harara bud'ar bakin shi sai naji ya ce "banza mayya wallahi zakici uban ki, ya fad'a ya na jan k'wafa take naji tsoro da fargaba sun dirar min naji duk yunwar da nake ji ta tafi sama ko k'a sa,tashi nayi da sauri nayi sama ban d'aki na fad'a ina gudawa nida ban wani ci abin cin kirki ba amma na b'ige da gudawa, haka nayi ta tsii kamar ruwa tsabar tsoro, dan nasan indai yaya mufeed ya kama ni to sai dai gawa ta dan wannan kallon tsanar da yake min ba kad'an ba yafi na kullum,
nasha alwashi wallahi bazan ta b'a yadda in k'ara haduwa da shi ba yan zuma ban san zan gan shi ba, da ko yunwa zata kashe ni bazan sauka ba,
to ya a kayi ma ya dawo gida yaushe kuma ya dawo fad'a a zuciya ta
*BAYAN SATI BIYU*
family d'in mu ana ta shirye shiyen bikin yaya taufeeqa sai murna muke musaman ma ni da aka ce Inna ta zata zo kuma naji Dady na ce wa inta zo bazata koma ba,
yau sauran wata d'aya cif bikin gidan mu an mana dinki kala kala kullum gidan ciken yake da baki y'an uwan Momy da y'an uwan Dady wato y'an uwan mu,
yaya Salim ne ya zo wanda shi zai auri yaya taufeeqa kafin ta fito nazo wuce wa ta sitting room gani na ya yi, sai ya kira wo ni, "mufeedah zo nan ina zaki "
ya fad'a yana min murmushi
nima murmushin na sakar masa na ce
"lambu zani na hau lilo"
"lilo kuma da sassafen nan ? bazaki bari Sai yamma ba?"
dariya nayi na ce "yaya salima yanzu fa goma tayi ba sassafe bane,
kuma da yamma uncle din mu zai zo ya koya mana karatu shiya sa zan yi yanzu"
haka dai mukai ta hira har yaya taufeeqa ta fito ta ce
"au nan ki ka zo kina ta masa surutu?"
kallon ta ya yi, ya ce "hira muke yi ba suru ta take min ba" tashi nayi zan tafi ya mik'o min alawoyi kala kala ya ce
''to gashi in anje ana lilo adin ga sha"
karb'a nayi nai masa godiya na tafi lambu ina murna,
Ina zuwa lambu kasan ce wata mesan wasan ruwa famfo na nufa na wanke fiskata na war watsa ruwan a jiki na,
na hau lilo ke nan ina shillawa na dauko alawata zan sa a baki ke nan naji an fizgoni ana jana kiiiiii kamar wata a kuya jana yake ina tirjewa kawai sai ya dauke ni yaje ya bud'e d'akin kare ya wurgani ciki kai na ya bigi bango wata k'ara na saki amma ko tausayi na wanda ya wurgani bai jiba kawai naji anja kofar kejin karan an rufe d'ago kai na da ke min wani a zababben ciwo nayi idona ya sau ka akan mufeed ..........
LOVE U ALL MY FAN'S
COMMENT AND SHARE FISABILILLAH🙏

COMMENTS