* MUFEEDAH* *NA* ummie khady FCW ASSO.
*
MUFEEDAH*
*NA* ummie khady
FCW ASSO.
Bismillahir rahmanir raheem
Ya Allah yanda nafara lfy Allah kasa nagama lfy kasa afada kantu Kuma anisha dan tu ameen
Wannan shine book Dina nafarko In anga kuskure amun uzuri nagode🙏
Page 10
Tafiya suke a cikin mota mufeedah ba abin da take sai kalle-kalle da lek'e ta window duk abinda ta gani sai tai magana akan sa.
Haka dai su hidaya,da anisa, da najwa,da nasma suke ta yimata dariya, nasma ce ta ce " wallahi mufeedah kinfiya surutu"
Kallon ta tayi ta ce "ina ruwan ki y'ar shishshigi so kike inyi gum da bakina salon ya yi wari to wallahi ni ba haka nake ba duk abin da nagani saina tanka"
Kwashewa sukayi da dariya duk kansu
duban su tayi ta ce " in dariyar ku ta k'are ba wanda zan bawa tawa
Anisa ce ta ce "nan ba k'auye bane dan haka ki kama kan ki"
har ta juyo zatayi magana sai su kaji Dady na cewa kar ku takura wa yarin yata mana kunbi duk kun dame ta,
Dan ma Allah yasa bame shiru bace ya fad'a yana dariya
Momy ce ta ce " a to, dan ma bakin ta ke kwatar ta ai yarinyar tawa bata daukan wargi"
haka dai su kai ta hira har suka k'araso gida horn sukayi me gadi yazo ya bude musu yana yi musu barka da zuwa,
Tunda mufeedah ta fito daga mota take ta kallon gidan ta na d'aga kai sama ta na kallon dogon benan dake gidan,
Mahmud ne ya ce " hidaya wannan kallo haka? wannan ai sai dan kwalin ki ya fado"
ya fad'a ya na mata dariya
Duban shi tayi ta ce
"barni na kashe kwar kwatar idona"
Anisa ce ta ce ke komai aka d'a saikin mayar?"
"To bai war Allah so kike in dunga shiru ko? To nayi"
Dady dai kallan su yayi domin shi yana mamakin mufeedah domin she karun ta sunyi kad'an a ce tana zaro zance kamar haka she kara goma take Amma duk abinda a ka ce zata baka amsa dai-dai da taka.
cikin gida suka shiga masu aiki kuma suka dinga shigo musu da kayan su sha shan su, kowa da ya shiga bangaran sa d'akin sa ya nufa don duk sun gaji,
Hidaya jan hannun mufeedah tayi su kayi d'akin ta
dama ita dakin ta daban ne najwa da nasma suma d'akin su daban ne amma falon su guda d'aya ne falo ne dama da two bedroom aciki nan ne b'an garan su,
Hidaya ce suna shiga ta shige toilet tayi wanka, bayan ta fito ta dubi
mufeedah ta ce" y'ar uwa tashi kema ki shiga kiyi wanka"
Mufeedah dake k'arewa d'akin kallo tunda suka shigo ta ce nayi a k'auye kafin mutaho"
Hidaya ce ta ce to ai yanzu ta fiya mukayi kuma mungaji Momy ce ta koya mana indai munyi tafiya me nisa sosai mun gaji to miyi wanka zamuji gajiyar ta tafi"
Mufeedah ce ta ce to "nidai bazan yiba"
Nan dai suka zauna suna ta wasa har suka gaji bacci ya kwashe su
*DA YAMMA* Dady ne shida iya lansa gaba d'ayan su suna zaune akan dining area suna cin abinci,
Dady ne ya kalli mufeedah ya ce "y'ata ya naga ba kya cin abinci sosai?"
Dady na rantse gurin nan ba dadin cin abinci y'an binni dole su anan suke cin abin ci?" ta fad'a tana lan gwab'ar da kanta gefe,
Momy ce ta "ce zaki saba kema ai nanda wani dan lokaci"
Mufeed ne ya ce
"Momy wannan ai ba zata tab'a waye waba"
Momy ce ta ce "waya gaya maka? wannan y'ar tawa nan gaba zakusha mamakin ta"
Taufeeqa ce ta ce "wallahi kuwa momy yarinya haihuwar U'S rainan U'S" ta fad'a tana dariya
Mahmud ne ya ce Dady da gaske mufeedah a U'S aka haifeta?"
Kafin ya rufe baki mufeedah ta ce "me ne ne U'Z?"
Ta fad'a ta na shan kunu,
Dariya duk sukayi amma banda mufeed danshi duk dagowar da zaiyi ya kalle ta sai ya banka mata harara dan shi kwata kwata hau shinta yake ji dan shi da za'abi ta tashi ma da an maida ita Inda ta fito,
Dady ne ya ce" eh
Kaddara Kuma ta maida ita k'auye"
Duban mufeed ta yi ta ce hidaya wannan wanna ku haka yake da fuska kamar ta shanu baya dariya shi?"
Haisam ne ya ce "yana yi mana yaya mufeed kaimata dariya tasan kanayi mana"
Uffan be ce ba
Dady ne ya katsa musu hirar da cewa babban yaya gobe Monday ka dau mufeedah kuje maka rantar su hidaya tunda dama yanzu ne lokacin daukar, sababin d'a lubai ka kai ta ayimata duk abinda ya dace domin ta fara zuwa da wuri"
Taufeeq ne ya ce "to Dady"
Momy ce tace yauwa Masha Allah murna su najwa suka farayi saboda za a sata makarantar su
"Idan lesson techar dinsu yazo zan dunga tura ta yana mata nata daban in Allah ya te maka tana ja sosai sai ayi mata jumping "
Momy ta fad'a
Mufeed ne ya ce "Momy wallahi yarin yar nan kanta ba ja ya ke ba dan Allah kubar ta karta wahalar da shi,
gurin wasa ne kawai kanta yake ja amma banda karatu "
Dady ne ya ce "kai bana san Shashancin banza ba y'ar uwar ka ba ce kar na k'ara jin wannan maganar abakin ka kowa ai ba a haife shi da iya wa ba"
ya fad'a cikin daure fuka
Mufeed ne ya sosa keyar sa yana fad'in "sorry Dady"
Haka dai su kai ta Hira har magaruba sannan koya ya Mike domin zuwa ayi sallah,
*WASHE GARI*
Wajan karfe tara taufeeq ya d'au ki mufeedah suka tafi makaran tar da za a sata tunda suka je mufeedah taga taufeeq suna turanci shida malaman ta ce tab yanzu kalli mufito da bawan Allah nan lafiya amma kalli daga zuwa nan sun zuyar mai da hankali ya fara wani gwaran ci tab wallahi bazan koyi wannan yaran ba wannan ai cutata zasuyi su koyan mugun abu,
Bayan Taufeeq ya gama komai Sai suka karb'eta sukace ta zauna ta fara karatu tun da dama lokacin daukan ne yanzu nan da kwana uku za abata uniform,
Nan idonta ya ciko da k'walla ta ce yaya dan Allah kar ka tafi ka barni wallah wannan gwaran cin nasu zasu ko yamin nikuma wallahi bazan koya ba"sai ta rushe da kuka.......
Love all my fan's
Share fisabilillah 🙏

COMMENTS