Furar Danko Book 2 Page 9

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣
.........“Wlhy wlhy wlhy Mawaddat ban aikata komai ba wa Sultana, sannan ban san yanda akai muka rasa kuɗin nan ba a cikin Company, iya bincike kuma nayi amma ban gane komai ba har zuwa yau. Yanda kike kallon al'amarin ba haka yake ba. Kinƙi bani damar na warware miki ne tun farko shiyyasa amma yau zan sanar miki komai. Sai dai dan ALLAH ina son ki fahimceni, sannan kiyi bincike dan ki tabbatar da gaskiya ta. Ina zaune a gida tare da iyalina Sulaiman yay kirana hankali tashe yana kuka. Cikin sauri na shirya na nufi Garko house da yace min yana can a zatona ma wani abu ne ya faru da Baba wlhy, kasancewata ba baƙo ba a gidan yasa kai tsaye aka buɗen gate na shiga, hakan ya ƙara sakani sake shiga ruɗani, bayan nai parking nayi kiran Sulaiman ya sanar min na zagayo ta baya sashen masu aikin gidan yana acan. Na ɗan ji mamaki, amma sai bance komai ba nace masa ina zuwa. Wannan ne karo na farko danai ta wajen, da kwantace na shiga sashen dan alokacin duk masu aikin na can cikin gida suna aikinsu. Na samu Sulaiman zaune yana kuka ga yarinya gefensa kwance ya rufa mata bargo. A lokacin bansan matsayin Sultana a gidan ba, zamma iya cewa ranar ne nai mata ganin farko dan har sannan ba wani shiga gidan nake ba Sosai ai. Cikin tashin hankali da ruɗewar da nake a ciki nima na shiga jera masa tambayoyi. Da ƙyar ya iya sanar min fyaɗe yayma yarinyar. Kuma wlhy shi bada manufar hakan ba a zuciyarsa. Yazo ne wajen yarinyar mai aikinku dan sun saba kasancewa a tare kawai sai ya samu Sultana a ɗakin, kasancewar baya cikin hayyacinsa saboda abinda wai wani abokinsa ya yaudaresa ya basa da kayan maye a ciki kawai ya afka mata dan tana masa gizo ne like yarinyar da yake zuwa wajen nata sai daga baya ya fahimci abinda ya tafka ɗin. Kuka yake riris da roƙon na taimakesa, wlhy idan wani yasan wannan al'amarin to gaba ɗaya farin cikin family ɗin ku zai ruguje. Kai iyayenku ma zasu iya rasa ransu musamman ma Baba. Dan ya ɗauki son duniya ya aza akan Sultana kamar kowa na gidan gashi bata da isashiyar lafiya. Bani na aikata al'amarin ba amma wlhy na shiga matuƙar gigitaccen ruɗani a lokacin jin yarinyar ƙanwarku ce, dan wlhy bamma san sanda hawaye nima suka fara zubomin ba. Shine ya kawo shawaran yana son na taimaka masa mu kaita can waje ta yanda in mu ajiyeta kamar wani ne yay mata za'a fi saurin fahimta a kaita asibiti, muma kuma hakan zai fi bamu damar kaita asibiti da wuri karta rasa ranta. A ɗan gajeren tunanina a lokacin sai na fahimci hakan shine dai-dai saboda a ruɗe nake ni kaina bana iya gane komai dan tashin hankali, inba hakaba kafin a farga anan tabbas za'a iya rasata. Sannan su masu aikin zai zame musu tashin hankali. Ace a sashensu abun ya faru da ƴar masu gida dolene ace su nemo wanda ya aikata. Na biyu tashin hankalin daya tabbatar min Baba da Dada zasu iya shiga koma su rasa ransu. Wannan shine ya ƙarfafani muka ɗakko Sultana cikin duhun magriba muka saka a motata muka kawota ƙarƙashin bishiyar da aka ɗakkota. Bakuma mubar anguwar ba har sai da aka ɗauketa zuwa asibiti. Ban fahimci nayi kuskure babba a bama Sulaiman gudunmawa ba sai da na dawo gida nake bama Kareema labari kamar akan wani abun ya faru. Kalamanta ne sukai matuƙar rikitamin lissafi da zama nayi nazari nima. Matuƙar damuwa na shiga, har na yanke shawarar tunkarar Sulaiman da batun akan magana ta gaskiya mu fito kawai mu sanar da iyayensa gaskiya, musamman ganin yanda aka kama maigadinsu da wasu masu aikin gidan aka rufe kuma da taimakonsa ne koma nace shine ya saka akai hakan. Sai dai mi koda nai masa zancen sai ya shiga roƙona da kalaman da suka sake rikitamin lissafi, ina tsaka da neman mafita ke kuma kikazo da naki kalar salon..”

       Kuka suka sake haɗe kai sunayi, sai da sukai mai isarsu sannan ta ɗakko masa camara ɗin ta bashi, hankalinsa ya tashi da ganin komai, dan tabbas duk wanda zai gani inba yasan gaskiya ba zai ce harda shi aka aikata, sai dai idan kai nazari a yanayin shi akwai sutura jikinsa saɓanin Sulaiman zaka iya fahimtar gaskiya. Laifinsa dai biyewa da yay aka fitar da Sultana a gidan. Roƙo sosai Mawaddat tai masa akan karya bar Sulaiman yasha ruwa a rayuwarsa akan wannan kuskuren har sai ya fito ya tonama kansa asiri, sannan maganar kuɗin Company ya binciki yayan nata sun salwanta ne da haɗin kansa, kuma kuɗin na hannunsa, dan taji suna tattaunawa da yaronsa Malami akan batun, sai dai ba komai taji ba da ƙyau gaba ɗaya. Wannan shine abinda take so ya mata koda bayan ranta. Ya tabbatar mata zaiyi amfani da shawaranta, dan yana son ya samu salama shima a ransa, hakan kuma bazata faru ba har sai ya fidda wannan ɓoyayyen sirrin da neman gafarar su Baba garko. Maganar kuɗi kuwa da tace ya bincika itama tai matuƙar girgiza masa zuciya, har ya fara shiga waswasi akan al'amura da dama game da abotarsa da Alh. Sulaiman ta rana tsaka. Kwana biyu da yin haka naƙuda ta tasarma Mawaddat, a lokacin daya samu Mommy na bata abu harga ALLAH a ruɗe yake, sannan ko Mawaddat ɗin ce tai mata haka a irin yanayin itama zai iya kawo hakan a ransa dan ya fahimci Mommy nada zafin kishi na masifa, shi da yake fuskantar ƙalubalen daga gareta shi yasan wannan saboda a zahiri da wahala ka gane tanada kishi a ƙanƙanin zama da ita. Dan ga wanda bai santa ba bazaice akwai ba, duk da yasan sun cuta mata, sannan tabbas tanada ƙyawawan halaye kishinne mai zafi kawai matsalarta, amma shi laifinta da yake gani shine kasa fahimtarsa da tayi tun farko. Lokacin daya ɗauki hanyar asibiti da Mawaddat cikin kuka dana azaba ta kamo hanunsa ɗaya ta ɗora a kan cikinta da faɗin, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, ka sake roƙamin matarka ta yafemin, ga amanar abinda ke cikina nan na baku, soyayya ta gaskiya daban samu daga gareka ba ina roƙonka dan ALLAH abinda zan haifa in har ya rayu shi ya samu. Kada ka bama kowa daga cikin ahalina abinda zan haifa ka riƙesa a wajenka ciki harda Dada. Idan da hali ma ka nisanta shi da su dan duk sanda Sulaiman yasan gaskiyar lamari kowane irin mataki zai iya ɗauka, kaima ka nisanta kanka daga al'amarin sa, inba hakaba wataran sai kayi dana sani, dan ƙarya yakeyi babu wani abokinsa daya bashi kayan maye da kansa yasha har cocaine yana sha dama, sannan ya jima yana lalata rayuwar masu aikin gidanmu, na taɓa tarar Dada da zancen amma bata yarda ba, sai ma balbaleni datai da faɗa akan idan taji batun a bakin wani saita ɓata min raina. Wannan dalilin yasa kaga na shige masa kamar munfi kowa shiri, amma ba haka bane ba, ina binciken abubuwa ne a kansa dan na jima ina zargin yana safarar miyagun kwayoyi a ƙasashe daban-daban musamman ƙasar Mexico, sannan yanabin hanyoyi daban-daban wajen ɗibar kuɗin baba. Na yi shirin idan na kammala bincikena na bama Baba bayanan ta hanyar gani da ido da zai tabbatar. Dan haka akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a cikin camara ɗin nan da suka shafesa sai kayi takatsantsan dan dama saboda shi na mallaketa...”

       Wannan magana ta Mawaddat ta saka rayuwar Daddy sosai a wani hali bayan rasuwarta, shine dalilinsa na hana ahalinta jaririya daya maidama suna Mawaddat, tare da nuna mata soyayyar data roƙa garesa kuma yay mata alƙawari, wadda harga ALLAH bayan rasuwar tata kuma sai yake jin soyayya mai nauyi a kanta. Sai tausayin yarinyar da ya ringa ɗibarsa kuma shima. Dalilinsa na hana Mommy Mawaddat shawarar da yaji dangin mahaifiyarta na bata ne, hankalinsa ya tashi da jin abinda suka faɗa mata akan marainiyar ALLAH da batama san minene duniyar ba, sai dai ita Mommy bata san yaji ba. Yaso yay mata uziri amma jin itama ta karɓama ƴan uwan nata da cewar ai duk abinda Mawaddat tai mata saita ramashi akan Lulu ya saka zuciyarsa a razani lokacin. Dan baiyi tunanin kishin Mommy zaisa idonta rufewaba ta karɓi shawarar ƴan uwan nata. Wannan dalilan yasa ya sake tsayawa akan al'amarin Lulu ya hana kowa jingina da ita. Sai kuma ga abinda yafi na Mommy ya ɓullo masa, bai san yanda akayi Alh. Sulaiman yasan da camara ɗin hannunsa da Mawaddat ta bashi ba, kawai a wata rana ya samesa da batun a rikice, yace ya bashi camara ɗin Please. Amma sai shi Daddy kansa tsaye yace bazai bada ba har sai Alh. Sulaiman ya sanar masa gaskiyar al'amari game da harkar shigo da kayan shaye-shaye daya tsunduma shi, sannan ya faɗa masa gaskiya akan ya akai kuɗaɗen nan suka salwanta da kuma haikema Sultana a sashen masu aiki bayan kowa ya shaida bata zuwa can ɗin sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Wani banzan kallo Alh. Sulaiman yay masa tare da masa nuni da baida hankali. A kausashe ya ce, “Isma'il kai wanene da zaka titsiyeni? Yaushe ma ka kai inda kake tunanin ka kai ɗin? Kana almajirin gidanmu dan na jawoka kaci arziƙi har kake ganin idonka yay tsaurin sanin abinda ni kaɗai ya shafa. To daga yau ka kama kanka. Camara kuma idan baka bayar ta arziƙi ba zaka bada ta tsiya. Sannan ita wannan yarinyar ka shirya dan dolene na hukunta rayuwarta da laifin mahaifiyarta, dan ni bana yafiya bana kuma barin bashin gaba. Sannan sabo da kaza a wajena baya hanani yankata. Ba ita data zama ɗiyar ƙanwata ba, ko ita ƙanwar tawa da tana raye saina ɗan ɗana mata azabar sanin ainahin Sulaiman, amma duk da haka wannan ƴar tata zata fansheta ne”.

      A lokacin tsawa Daddy ya daka masa, sai dai kafin yace komai Alh. Sulaiman ya bar wajen.

      Wannan ne sanadin komai da zama mafarin ɗauke Lulu daga Nigeria Daddy ya maidata Garmany ya nema mata Nanny da tunanin ya kuɓutar da ita daga sharrin Alh. Sulaiman, shine kuma mafarin duk wani rikicin dake a tsakaninsu, dan har yanzu dai camara na a hannun Daddy duk barazanar da Alh. Sulaiman ke masa yaƙi bashi ita. Ya kuma kasa gayama kowa ciki harda Uncle Yousuf da Mommy dama Baba Garko....


     Wannan kenan. 

         


        *_★CANADA★_*


    Zuwa yanzu wata irin nutsuwa ce ke saukarma Lulu maiban mamaki, yayinda girman da cikinta keyi ya fara ɗaukar hankalinta. Da farko ta ɗauka tunbi ta fara tarawa, hankalinta ya tashi ta fara tunanin ko kunun gyaɗar da take shane ya kawo mata haka. Ta yanke hukuncin fara fita motsa jiki kawai da alƙawarin daina shan kumun gyaɗa duk da tasan hakan bamai yiwuwa bane. Sai dai bata san yaya zatai hakan ba dan yanzu hatta security ɗin gidan na ƙofa Alh. Sulaiman ya canja shi, idan zata fita dole saita kira Dada ita kuma ta kirashi sai yasa a buɗe. Gefe guda ga cid ko bodyguard zata kirasu ma ita bata sani ba yasa suna bibiyar al'amarin ta. Ta fahimci hakanne a randa sukai fita yin wani shopping ita da Ummita. Hankalinta ya ƙara tashi, dan zuciyarta zuwa yanzu ta fara ayyana mata abubuwa da dama. Cikin harda tunanin anya kakar tata da kawunta basu da wata manufa a kanta. Wannan shine mafarin data fara natsar da zuciyarta waje guda da hankalinta domin fahimtar abubuwa a matsayinta na lawyer. Abu na biyu shine randa ta amshi wayar Ummita da nufin kiran Daddy a karo na farko. Dan ita nata wayoyin ma ta mantosu a Nigeria tun sanda ta taho, tanata ma Dada naci akan a kawo mata sai taita cewa ta manta. Koda Lulu ta saka number Daddy ta kira sai taji Alh. Sulaiman ya ɗaga. Hakan ya ɗaure mata kai akan miya kawo wayar Daddy hannun Uncle ɗin nata, amma sai ta tsinkayi Alh. Sulaiman ɗin na ƴar dariya da faɗin,........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: Furar Danko Book 2 Page 9
Furar Danko Book 2 Page 9
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgyg9oiWvC0y4hb-4ivXj0iF3AZHkFsAZZnkXLy89lgu9Gb_Nlqrs93gu6YwrxRwWS1iysM-pRD3lExuwsMK3mxOSTuEdtXCCMUmBbgcuvrwGElBLl68hThYeAhVmg-OWWSO-KLskLowRiML7VYTRTfZY6uuP7kEdQpSahzuovD3hFZe0r864mRHM8azJ4K/s1600/img_1696515891961.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgyg9oiWvC0y4hb-4ivXj0iF3AZHkFsAZZnkXLy89lgu9Gb_Nlqrs93gu6YwrxRwWS1iysM-pRD3lExuwsMK3mxOSTuEdtXCCMUmBbgcuvrwGElBLl68hThYeAhVmg-OWWSO-KLskLowRiML7VYTRTfZY6uuP7kEdQpSahzuovD3hFZe0r864mRHM8azJ4K/s72-c/img_1696515891961.jpg
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-book-2-page-9.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-book-2-page-9.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content