Duk Karfin Izzata Book 2 Page 2

      💖Story And Written💖

     💖Story And Written💖


                     ⬇️

               *Star lady*Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai


Book 2


*Episode 2*......sosai Aunty amarya take kuka kamar ran ta zai fita sai rarrashin ta Ammi da Ummi suke chikin nitsuwa Abba ya fara magana "ku tashi muyi musamu mu kai Aiman ma kon chinsa, ku kuma Aisha ku tashi ku tafi kowa tayi part nata, kukan ya isa yanzu ba abun da Aiman ke bukata  face Addu'a, kuma ina son sanar daku chewa ban yar ku sanar dasu farida yanzu ba ku bari sai bayan kwana biyu domin idan kuka sanar dasu yanzu tofa dole Aryan da Ahmad zasu samu lbr kuma kunsan me zai biyo baya idan suka sani a yanzu, yana kai karshen maganar ya miƙe ya fiche daga ɗakin miƙewa su Ammi ma sukayi gaba ɗaya suka fice sai kuka Aunty amarya take kamar ranta zai fita.After 8 days da rasuwar Aiman, gaba ɗaya family sun haɗu a palo Abba, harda su Aunty mardiya Su Aunty farida gaba ɗaya family Abba sun haɗu A nitse Abba ya fara magana 


"Duk kan ku ina mai baku hakuri da rashin da mu kayi san nan ina rokon Allah da ya baku hakuri da juria rashin ɗan uwan ku, a tare suka haɗa baki wajen chewa Amin, sun kuyan da kai kasa Aryan yayi sai furzar da iska mai zafi yake daga bakinsa chigaba da magana Abba yayi 


"Safras Khalid Fahad Yusuf Aryan duk da chewa kai Aryan  matar taka bata nan Amma In Sha Allah zamu gano ta, to ga amanar ƴaƴana nan na baku ku kulamin dasu idan ni bana ganin ku to kusani Allah na ganin ku musamma Safras Aryan Yusuf Fahad kusani marayu kuka Aura idan kuka chutar dasu wlh Allah ba zai kyale kuba.


Chikin rashin fahimtar Aunty amarya tace ranka ya dade ban gane me kake son kace ba wai wasu ya'yan naka kake maga kuma amanar wasu ƴaƴan ka basu? Dawo da kallon Abba yayi kansu ya chigaba da magana


"Kamar yadda kuka ji na faɗa hakane gaba ɗaya yaran nan na musu Aure nan dai Abba ya basu labarin yadda ya haɗa Auren nasu da kowa da matar sa, chike da tashin hankali da ruɗu hiyana ta ɓoye fuskantar a chikin chinyoyin ta saboda wani kukan bakinchiki da yazo mata shike nan na shiga uku na yaya prince ne mijina wayyo Allah ni nasan rayuwata tazo karshe kenan.


Chikin ɓachin rai Aunty amarya ta fara magana "wlh ban yar da ba tayaya za'ayi a haɗa ɗana da wanchan kazamar yar kauyen, dawo da kallon ta tayi kan Aryan dake zaune ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuchi dan tun lokacin da ya samu labarin rasuwar Aiman kullun chikin kukan zuchi yake ya koma shiru baya magana bayama fitowa waje kullun yana kwanche a ɗaki


"Kai Aryan idan har na isa da kai to ka saki yarinyar nan yanzu dan ni bazan haɗa zuri'a da masu kiwon shanu ba, chikin jin haushi Aunty Maryam tace "haba Aunty amarya dan Allah ki kyale yaya Aryan yaji da abun da yake ji mana" "zaki min shiru ne ko sai na zabga miki mari wlh yau idan kunga Aryan bai saki diyana ba tofa mutuwa nayi tana magana tana huchi kamar wata zakanya


"Ba yau ba yanzu zan rubuta wasiya idan kika kuskura koda mutuwa nayi ki ka sanya Aryan ya rabu da matar sa  tofa sai kin fuskanchi hukunchi mai tsanani gaske" chewar Abba 

Chike da izza Aunty amarya tace "wlh babu wan da ya isa yasa na bar ɗana ya zauna da wan chan kazamar yarinyar, rai a matukar ɓache Bgs ya miƙe tare da miƙar da Aryan ya riko kafaɗar sa  suka nufi waje  tun lokachin da Aryan yasan Aiman ya rasu kullun yake chikin rashin lfy bai da wani kuzari sai yawan tunani


Miƙewa Aunty farida tayi tare da faɗin "ku tashi mutafi tayi magana tana kallon su hiyana, a tare suka miƙe gaba ɗayan su har da su Aunty Maryam suka nufi waje.


Palon ya rage daga Abba Ammi Ummi sai Aunty Amarya, shiru sukayi suna jin yadda Aunty amarya ke surfa ruwan bala'i dole sai Aryan ya saki diyana,Abba batare da yayi Magana ba yasa hannu a aljihun sa ya chiro wayar sa, ya shiga contact ya fara kiran wata number wadda akayi saving da My Brother.


Kira ɗaya a ka ɗaga sanya wayan a hand-free Abba yayi chikin girmamawa ya fara magana "Assalamu alaikum, daga ɗayan ɓangaren aka amsa da wa'alaikumus salam jin muryan wadda ya amsa Sallamar yasa Aunty amarya tayi sauri kwache wayar a hannun Abba ta katse kiran tana faɗin "dan girman Allah kayi hakuri karka sanar wa yaya wlh in dai Aryan ne na barshi yaje ya chigaba da zama da matar sa har abada Allah ya basu zaman lfy Allah yasa a gane ta" tana kai karshen maganar ta miƙe tare da ajiyewa Abba wayar sa a gefen sa ta nufi waje da sauri tana faɗin Allah na tuba kayafi min, duk bachin rai da raɗaɗin rasuwar Aiman dake damun Abba hakan bai hanashi yin ɗan murmushi ba dawo da kallon sa yayi kan Ammi da Ummi ya fara magana


"Aisha kije ki sanar wa farida nache ta shirya hiyana ta mata duk abun da ya dache ta kai ta part ɗin mijinta, ita kuma salma ta shirya Zahra itama ta kai ta part na mijinta, ke kuma hauwa'u ki sanar da mardiya akan ta shirya lamrat da amrat suma ta kai su part na mazajen su, suyi sauri yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom nashi.


Kallon Ummi Ammi tayi chikin fargaba da tsoro abun da zai biyo baya tace "ki tashi muje mu isar da sakon ko? "To kawai Ummi tache a tare suka miƙe suka bar palonAfter some hours


Aunty farida da Hiyana ne zaune a bakin gadon a ɗakin su hiyana Aunty farida ta tsara mata make up sosai 


hiyana tayi kyau sosai kamar ka sache ta ka gudu da ita, sanye take chikin wata danƙareriyar lace pink colour ta yafa mayafi fari a kanta, chikin nitsuwa Aunty farida ta fata magana


"My Hiyana na san baki son Yaya prince Amma kiyi hakuri wan nan itache kaddarar ki kuma kisani hakan kamar jarabawa che Allah ya jarab cheki to kiyi kokari ki chinye jarabawar ki, kuma awan nan karon mu zaki tai makawa kinji ko? ina mai rokonki da ki daure nasan kina da hakuri sosai kuma nasan zaki iya to ki kara hakuri nasan zaki sha wahala zama da yaya prince amma ki daure In Sha Allah zamuyi nasara a kanshi kinji ko? kuma In Sha Allah kema zaki fara son shi yanzu zan faɗa miki ta yadda zamu fara yakar sa

            abu na farko duk da nasan baya san ganin mace a kusa da shi amma ya zama dole kirin ƙa kasanche kusa dashi koda kuwa baya so 


Abu na biyu ki dai na saka hijabin da kike sawa ki koma saka kananan kaya idan kin san yana gida, na uku zan roki maki alfarma a wajensa ko da yake ma koban roke saba nasan Abba zai che ke zaki rinƙa kai masa abinchi, kinga a nan ma zamu iya yin nasara, san nan idan ya dawo daga wajen aiki kiyi kokari ki saba masa da chire masa takalmi da socks da kan ki, nasan zaki sha wahalan hakan Kuma nasan zai iya chewa baya so to amma ko yache hakan karki dai na kirin ka yimasa kinji koh?


Kuka Hiyana take sosai kamar ranta zai fita rungumota Aunty farida tayi sosai tana bubbuga bayan ta tana bata hakuri awan nan yanayi Ammi ta shigo ta samesu "feeda Abban ku fa yace kiyi sauri ki kai Hiyana part na mijinta  tun ɗazun fa su salma  suka kai su Zahra" "to kawai Aunty farida tace tare da miƙewa ta kamo hannun Hiyana suka sufi wajen


Wani hawayen farinchiki Ammi taji ya zo mata burinta ya chika hiyana ta zama matar ɗan ta,  sai dai awani ɓangare na zuchiyar ta kuma tana tausayawa hiyana sosai dan tasan Hiyana ba karamin wahala zata sha a wajen Bgs ba amma ta ɗauki kudirin taya hiyana yaki ta kowani haliMaiduguri


ɗankareriyar mota kirar  marcedes Benz che ta shararo a guje gudu mai motar yake sosai kamar zai tashi sama,ji kake kiiiiiii mai motar ya kwashe wata mahaukaciyar yarinya da ta zo tsallaka titi, wata mahaukachiyar birki yaja chikin sauri ya buɗe kofar motar ya fito kyakkyawa ne sosai fari tas dashi, chike da tashin hankali ya nufi inda yarinyar ke kwanche a saman titi ko motsi batayi kamar ta mutu ga jikin ta duk jini kanta ya fashe sosai, wani dogon salati yayi kafin ya karisa in da take juyawa yayi gabas da yamma babu kowa a kan hanyar, dawo da kallon sa yayi kan yarinyar, zuba mata manya manyan fararen idon sa yayi yana kallonta, gani yayi hannunta ya ɗan motsa alamar bata mutuba chikin sauri ya duka ya ɗauke ta ya nufi mota da ita gidan baya ya buɗe ya kwantar da  ita ya rufe kofar ya buɗe gidan gaba ya shiga da sauri ya kunna motar  yaja ta da gudu ya nufi asibiti da ita


Yana yin parking a chikin asibitin ya fito ya ɗauke ta chak ya nufi chikin asibitin da ita, kai tsaye office na Babban Dr ya nufa, batare da yayi Sallama ba dan tsabar ruɗewa shiga office ɗin yayi kai tsaye, Dr na zaune yaga an shigo masa office chikin sauri ya miƙe yana faɗin "Ahzan lfy!?  subhanallah wan nan fa!? Yayi maganar yana nuna yarinyar da Ahzan ɗin ke ɗauke da ita chike da tashin hankali Ahzan yace " Dr walid ka taimake ni wlh yanzu shigowata garin nan ke nan ina sauri na karisa gida na buge yarinyar nan


Hannu Dr walid yasa yana masa nuni da gadon dake chikin office ɗin yana faɗin "ka kwantar da ita tun da Allah yasa kai ma babban police ne yanzu zamu fara dubata, Ahzan bai jira Dr walid ya karisa maganar ba ya nufi gadon da sauri ya kwantar da yarinyar, chikin sauri Dr walid ya fara shirya kayan aiki 


Fitowa waje Ahzan yayi ya zauna saman wata kujera tare da chiro wayar sa daga aljihu kira ya danna tare da manna wayar a kunnen sa, kira ɗaya akayi picking, chikin rawar murya Ahzan ya fara magana "eh dady na shigo amma fa akoi matsala" chikin tsorata dady yace "wani matsala kuma Ahzan? "Accident na samu na buge wata mahaukachiyar yarinya che yanzu haka muna asibiti" "subhanallah ka turomin address ɗin Asibitin da kuke ganin nan zuwa" to kawai Ahzan yace tare da katse kiran ya shiga massage turawa dady address din asibitin yayi san nan ya mai da wayar aljihun sa ya dafe kan sa da hannu biyu....Dan girman Allah kumin afuwa jiya nache zanmuku page 2 to ina baku hakuri da rashin chika alkawari da nayi wlh ban samu charji bane sai wuraren 4 shiyasa amma In Sha Allah zuwa gobe zakuga sako masu zafi amin afuwaNEW TEAM💖

💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖


*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*

     👇👇👇👇


*1,DUK ƘARFIN IZZATA*

       by(Star Lady)


*2,GIDAN AUNTY*

       by(mss lee)


*3,SARKI SAMEER*

      by(xeemat....love)


*4, JINI DAYA*

      by(mrs bbk)


*💫STAR LADY💫*3


💖The Talent Troupe Writer's 💖*DUK ƘARFIN IZZATA*


    💖Story And Written💖

                     ⬇️

               *Star lady*

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: Duk Karfin Izzata Book 2 Page 2
Duk Karfin Izzata Book 2 Page 2
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgDpC_Uo8kqQCq6YJex1RtNrTerEjQWCUSq42XOgLbMh-ph2T0SBi18zQJ7Z8QV6QkL5_DelcF_9D880EzskXdHmvhWrsgV7xnQFoSJ9TuqFlGufcKRwe5Z4xYHCH5ExgYWqt2mF2TNwl8UYDZRCHuXvWs1PLrEQr1Vu6hQhxrCO24GI-_2so0a5nndURZc/s320/img_1696447418929.webp
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgDpC_Uo8kqQCq6YJex1RtNrTerEjQWCUSq42XOgLbMh-ph2T0SBi18zQJ7Z8QV6QkL5_DelcF_9D880EzskXdHmvhWrsgV7xnQFoSJ9TuqFlGufcKRwe5Z4xYHCH5ExgYWqt2mF2TNwl8UYDZRCHuXvWs1PLrEQr1Vu6hQhxrCO24GI-_2so0a5nndURZc/s72-c/img_1696447418929.webp
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/duk-karfin-izzata-book-2-page-2.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/duk-karfin-izzata-book-2-page-2.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content