shin kana da bukatan mallakan email address? Ko kasan cikin kasa da minti biyar za ka iya bude google account Kwantar da hankalin ka kabi w...
shin kana da bukatan mallakan email address?
Ko kasan cikin kasa da minti biyar za ka iya bude google account
Kwantar da hankalin ka kabi wannan bayanin dake kasa don bude akwatin sakon ka cikin kankanin lokaci.
Karanta wannan: Hanyoyi 3 da zaka gane inda wayarka take bayan ta bata ko an sace
A matsayin kana mai amfani da waya a wannan zamanin dake cike da fasaha akwai bukatan ka mallaki email naka don a turo maka ko kai ka tura sakon ruburu, hoto, sauti ko bidiyo.
Ko a makarantun da aka ci gaba malami yakan iya ba da assignment ko project sai yace a tura masa ta email, kenan yana da kyau ka mallaki na ka kuma ka iya sarrafa shi.
Karanta wannan: Yadda zaka maida sunanka na facebook ya koma guda daya
Kirkiran email address Abu ne mai sauki a yanzu matukar kana rike da waya kirar android ba sai ka je ka biya kudi an bude maka ba ko farkon budewa ne ko kuma karawa za kayi.
Bude email address ba Abu mai wahala bane cikin Dan kankanin lokaci zaka bude kuma ka fara aiki dashi, ga abubuwan da ake bukata kayi a kasa lokacin kirkiran adireshin email.
Karanta wannan: Yadda zaka kir-kiri facebook account cikin sauki
MENENE AMFANIN EMAIL ADDRESS?
Email address yana da matukar amfani don yanzu a wannan zamanin anci gaba sosai za ka iya tura sakonni daban-daban ta email ga kowa a fadin duniya. Daga cikin amfanin email akwai wadannan;
* Tura hoto; ana amfani da email don tura hotuna ga Wanda ake bukatan turawa, za Ku iya cinkin gida, television, radio da sauran su, Wanda zai saya kila yana nesa, za a iya daukan hoton abun ta waya ko computer sai a turawa mai sayan don ya gani, Idan ya masa za Ku iya cinki ko da ta email din ne.
Karanta wannan: Yadda ake whatsapp biyu a waya daya
* Tura hoto mai motsi (Video); ba a tura hoto kadai amfanin email ya tsaya ba har video ana iya turawa tun daga kan fina-finai, comedy da sauran su, kuma abunda zai fi burge ka da lamarin shine ba kamar Bluetooth, zender ko share it yake ba Wanda sai kuna kusa da Wanda zaka turawa kafin ya turu. Ko mutum yana wani gari ne zaka iya tura mishi duk lokacin da ya bude data sakon zai shigo kamar dai WhatsApp ko Facebook.
* Tura sakon rubutu; Haka kuma ta email zaka iya tura sakonnin rubutu zalla, za ka iya hada hoto da rubutu ko kuma ka hada video da rubutu ka turawa Wanda kake bukatan turawa.
* Yin aikin makaranta; a wasu makarantun musamman Inda aka ci gaba malami yana iya bada assignment sai yace a tura masa ta email, bayan an tura masa sakon zai isa gare shi ya maka kuma ya turawa kowa makin daya samu.
Da zaran ka dauko hoto, video ko kayi Rubuta ka tura nan take yake tafiya sai dai Wanda aka turawa bazai gani ba sai ya bude datan shi, yana budewa Idan akwai network mai karfi sakon zai shiga ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai abu daya baza ka iya tura sako ta email ba sai kana da email address, haka baza ka iya turawa Wanda baida email address sako ba. Kenan dole ne sai dukan Ku kun bude email kuma kun San email din juna kafin Ku iya turawa junan Ku ko wane irin sako ta email.
Kafin bude email address akwai abubuwa wadanda ya kamata ka sani ko ka mallaka, daga cikin su akwai;
* waya misali kamar android da sauran wayoyi masu kama dasu
* Dole sai da data a layin wayar
* shekarun haihuwa
* lamban waya
* Sunan da zaka sawa email, Da sauran su.
Wadannan abubuwa Dana lissafa ana amfani dasu wajen bude email kenan ya zama dole ka mallake su kafin ka fara budewa.
Sai dai ba lallai bane ka samu daman budewa da Sunan da kake so domin ba a iya bude email daya da suna biyu, Idan ka saka sunan email da kake so idan wani ya Riga ya bude dashi zasu fada maka kuma zasu nuna maka sunaye masu kama dashi sai ka zabi daya ko kuma ka sake gwada wani sunan ko ka saka wasu lambobi a gaban sunan.
Karanta wannan: Kowa zai iya zama blogger
Bude Google account cikin sauki
(Don sanin Yadda ake tura sako ta email, yadda ake dorawa da goge email akan wayar android, ka ziyarci Wannan shafin www.Lambunsadarwa.com.ng)
Ga bayanin yadda ake bude email address;
- Da farko za ka shiga nan Bude email address kyauta don bude wa.
- Zai bude maka wani guri inda za ka sa sunayen ka
- Zaka rubuta sunan email address din naka a inda kaga an sa @gmail.com.
Misali idan sunan da kake so shine Asan ne, sai ka rubuta asan@gmail.com
Idan akwai mai amfani da irin Wannan sunan za su fada maka sai ka chanja sunan sai ka saka @gmail.com a gaban sunan
- Sai ka saka password na email na ka, ka samu password mai wahala kuma kar kowa yasan password na ka, Sai ka danna next.
- Za su bukaci lamban wayar ka sai ka rubuta musu.
- abu na gaba shine rubuta ranar haihuwa da bambance kai na miji ne ko Mace, sai ka danna next.
- Sai ka karanta dokoki da ka'idojin su idan ka amince sai ka taba I agree, ka yadda da duk abubuwan da suka fada kenan.
Idan baka yadda ba bazai yiwu ka iya bude wa ba kenan idan kana bukata dole sai ka amince da bayanan su.
Wannan shine yadda za a bude email address da zaran ka danna I agree zasu kai ka zuwa kai sai ka saita duk abubuwan daya kamata ka saita.
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHASAPP
Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
COMMENTS