Yadda ake samun kudi ta internet ba tare da ka kir-kiri website ba

Assalamu alaikum, barkan mu da warhaka, da fatan kuna lafiya. Duba da ahalin yanzu mutum babu wata hanya da zai iya samun kudi ta internet, ...

Assalamu alaikum, barkan mu da warhaka, da fatan kuna lafiya.
Duba da ahalin yanzu mutum babu wata hanya da zai iya samun kudi ta internet, dole sai yana da website daya kir-kira da kanshi, to ayau nazo maku da wasu hanyoyi guda uku wanda zaka samu kudinka ta internet masu tarin yawa kuma ba tare da website ba, mallam ina mai baka shawari da kada ka tsaya a shafukan sada zumunta kana bata lokacinka wajen yin chatting ko karanta labaran kwallo da dai sauransu, wadannan sune abinda yake shagaltar da mutanen mu, Kai har ma yasanya basu kula da wasu manyan damammaki ba da zasu iya amfani dasu domin samawa kansu wasu ƴan kudade, wani abin mamaki ma wani sai yaje yayi aiki ya wahala sannan yake samun kudin da zai sayi datan da zai shiga shafukan yanar gizo, amma kuma bai taba sanin ta yaya zai samu kudi a internet ba.
To ka kwantar da hankalinka a yau insha Allahu a cikin wannan darasin zamu kawo maku wasu hanyoyi guda hudu da zakayi amfani dasu domin samun kudinka ta cikin internet, mutane ma da dama suna tunanin cewa babu yanda za'ayi ka iya samun kudi sai kanada website, to agaskiya wannan batu ba haka yake ba, ga bayanin yanda zaka samu kudi ba tare da website ba dalla-dalla.
1. Advertisement
2. Affiliate marketing
3. Referral
4. Freelance

Yanzu zamuyi bayaninsu dalla-dalla

1. Advertisement:- 
Advertisement a Hausa ana kiranshi da "Talla", Duk wani wanda ya shahara da shiga facebook zaka dinga ganin wani labarin yanda zakaga wasu mutane sukan leƙa daga wannan zaure zuwa wancan zaurw, To ba komai bane ke kaisu ba sai dai kawai suyi comment da wani link, zakaji sunce ka shiga nan domin sanin wani abun ko kuma samun wani abu, to ka sani duk mutanen da kaga sunayin irin waɗannan abubuwa, to ba komai suke yi ba face sunayin ma wasu kamfanoni talla ne, saboda haka da zaran ka danna wannan link din da suka baka to zakaga ka shiga kamfanin website din da suke yin ma talla, Sukuma za'a basu wasu ƴan kudi ta sanadiyyar danna musu da kayi, Duk da dai wadannan mutane masu irin wannan tallan ba kowani lokaci mutane suka cika kulasu ba, amma idan kanaso zaka iya yinta ta hanyar daya kamata.
Misali: zaka iya sanar da abokanka da kukeyin chatting da su, to zakaga indai kayi haka zakaga ana shiga cikin link dinka akai-akai, kaga anan zaka samu kudi fiye da yanda kake tunani, saboda duk wanda ya shiga ta link dinka, sannan kuma yayi register, to wallahi zaka samu kudi sosai, akwai kamfanoni da yawa da suke irin wannan, kamar irinsu online shopping da kamfanonin layin waya, akwai ma wasu sauran kamfanoni da suke neman wadanda zasu dinga yin masu talla ido rufe, wanda insha Allahu indai kuna shiguwa wannan shafin zamu riƙa kawo muku ko kuma ka biyoni ta facebook, kaga anan kwata-kwata bai dace ka tsaya kana bata wa kanka lokaci wajen yin chatting da dai sauransu
Shin ba zaka amfana da wannan damar ba?

2. Affiliate Marketting:-
Shikuma wannan yana nufin "Tallata kayan kamfani ko kuma website" akwai kamfanoni ko website da yawa wadanda zakayi register dasu
Misali kamar Kanoweb.net, Qservers, Jumia, Konga, Entireweb, dukkansu idan kayi register da wadannan kamfanoni to zasu baka adireshin da zaka riƙa baiwa mutane domin jawo hankalinsu zuwa website din wannan kamfanin.

Wasu kamfanoni a lokacin da wani ya shiga link dinka yaje ya sayi abinda zai saya, to ba tare da bata lokaci ba zasu biyaka kudinka, wasu ma koda kuwa basuyi siyayya ba zasu baka wani abu ta dalilin bin link dinka da ya bi, kaga mallam a mai-makon ka tsaya wajen bata lokacinka wajen yin chatting a whatsapp da facebook, mai zai hana ka tsaya ka dinga yin register da irin wadannan kamfanoni ka samu kudinka ba tare da kasha wani wahala ba3. Referral:-
shikuma "Referral" wanda a hausa ana kiranshi da "Jogora", shikuma Referral wata hanyace da ake samin kudi da ita ta hanyar jawo wani yazo shima yayi register da wannan website din, bayan kaima kayi register din.

Yawanci sababbin website ne da suke bukatar su dinga samun traffic to sukan bullo da wannan hanyar, baya ga haka kuma akwai wasu kamfanoni da suke da bukatar ayi masu talla, to sukan baiwa mutum yayi register, bayan kayi register to zasu baka adireshin da zaka gayyato masu mutane ta wannan link din da suka baka, bayan ka gayyato wani shima yayi register to zasu baka wasu ƴan kudade , daga cikin kamfanonin da suke yin irin wannan akwai konga.com, da dai sauransu.


4. Freelance:-
Shikuma wannan yana nufin "ƙwadago" wato a hausance kenan, shikuma wani sabon tsarine da kafar sadarwa ta yanar gizo-gizo ta dauka shine yadda zaka iya yin aiki, sannan kuma bayan ka gama aikin sai a biyaka, sannan kuma duka a internet ne ake yin aikin haka ma ta internet ne za'a biyaka kudinka, sai dai kuma wannan sabon abune wanda bakowa ne yasan yadda ake yin sa ba. Kuma mutane suna samun kuɗi sosai ta wannan hanyar,
Kusan duk wata ƙwarewa ko iyawa da ka sani kana da ita to akwai masu bukatar irin wannan, idan kana da buƙatar yin irin waɗannan ayyuka to ka riƙa yawan shiga google kana yin bincike na "Types Jobs" matuƙar kana yin haka to abubuwan da zaka riƙa samu suna da matuƙar yawa sosai, daga ciki akwai koyarwa, wato "teaching" a turance
Zaka riƙa yi ma wasu assignment na makaranta da sauransu
Kaga anan ɗan uwa ko kuma ƴar uwa bai kamata ka riƙa ɓatawa kanka loƙaci ba.
Da fatan an amfana da wannan darasin namu kuma ana ƙaruwa sosai a ciki, duk mai tambaya ko neman ƙarin bayani sai ka aje mana comment a ƙasaa, mungode


Facebook: Yi like a shafinmu na facebook

Whatsapp: Zaku iya biyomu ta whatsapp

Twitter: Yi following dinmu ta twitter

Instagram: Yi following dinmu ta instagram

Call & Message : +2349036117711

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: Yadda ake samun kudi ta internet ba tare da ka kir-kiri website ba
Yadda ake samun kudi ta internet ba tare da ka kir-kiri website ba
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhS5c-aZO2JpUODy0HfM2EBqeEJK-809WsjZkDukltMGGNVuGDJmwaXPB_sYeER7XanDM8LrZ56wVWPiB0V0hlzNGeOae0TR-3XevlHTxzX2N4js2S3aHNzPo6kiVNnzjNUapd05oc22hg/s1600/interne.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhS5c-aZO2JpUODy0HfM2EBqeEJK-809WsjZkDukltMGGNVuGDJmwaXPB_sYeER7XanDM8LrZ56wVWPiB0V0hlzNGeOae0TR-3XevlHTxzX2N4js2S3aHNzPo6kiVNnzjNUapd05oc22hg/s72-c/interne.jpg
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2020/01/yadda-ake-samun-kudi-ta-internet-ba.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2020/01/yadda-ake-samun-kudi-ta-internet-ba.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content