[whatsapp business] Yadda ake kasuwanci ta whatsapp cikin sauki

Assalamualaikum, barkanmu da sake haduwa daku a cikin wannan shafi mai albarka, wannan shafin, shafine da yake kara wayar da kan al'umma...

Assalamualaikum, barkanmu da sake haduwa daku a cikin wannan shafi mai albarka, wannan shafin, shafine da yake kara wayar da kan al'umma wajen kimiyya da fasahar zamani, A yaune insha Allahu zamuyi muku bayanin yanda ake yin kasuwanci ta whatsapp, a baya munyi muku darasi akan yadda zakayi kasuwanci ta facebook, da kuma yanda yakamata ka bunkasa kasuwancinka, to a yau kuma zamuyi maku yanda zakayi kasuwancinka ta whatsapp cikin sauki, Da farko dai idan kanaso ka fara kasuwanci ta whatsapp, to zaku dauko wani application ne mai suna "Whatsapp business" shidai wannan application din mai suna "whatsapp business" kamfanin whatsapp ne suka kir-kire shi, saboda ganin yanda mutane suka koma yin kasuwanci a yanar gizo-gizo, wannan ne yasa wannan application din yayi wa masu manyan kasuwanci da kananun kasuwanci, domin ya saukake masu wajen tafiyar da kasuwancinsu, saboda su samu saukin kasuwanci da whatsapp, akwai hanyoyi da dama da wannan application din yake da amfani, saboda wannan application din na  "business whatsapp" yanada abubuwa na ban mamaki, wanda insha Allahu yanzu zamuyi bayani akansu

Ban-banci tsakanin whatsapp business da kuma whatsapp

E akwai ban-banci tsakanin whatsapp business da kuma whatsapp din da muka saba yin amfani dashi, sai dai kuma ban-bancinsu kadan ne,

Karanta wannan: Koyi html, css, java acript da programming cikin sauki a offline w3shool
Yadda zaka kirkiri account a Bulk Sms domin yin kasuwanci
Ma'anar kalmar Protocol a computer
Yadda zakasa password wa applications dake kan wayar ka
Yadda ake format din computer
Hanyoyi guda 8 da zaka bi domin koyon engineering
Abubuwa 3 da zakayi kafin kayi apply na Google adsense



Ta yaya zan bude account a din whatsapp business?

Shidai yanda ake bude account a whatsapp business duk kusan iri dayane da whatsapp din da muka sani, sai dai kuma wanda baza'a rasa ba, da farko dai idan kanason bude account na whatsapp business, sai kaje google ko playstore kayi search na "whatsapp business, kai tsaye zakaga ya nuna maka application din, sai kayi downloading dinshi, bayan ka gama downloading dinshi sai kayi install na application din, bayan ya gama install din, sai ka shiga cikin application din zakaga kamar dai yadda ake bude asalin whatsapp, kamar dai yanda kuka gani a wannan hoton na kasa
bayan ya nuna maku wannan shafin sai ka danna "AGREE AND CONTINUE" bayan ka danna gurin zakaga ya kawo ka wani shafi, inda zaka sanyar lambar wayarka, amma ka da kasa "0" na farkon lambar wayar naka, bayan ka gama, sai ka danna "Next" , bayan ka danna zakaga ya nuna maka haka

Anan yana tambayarkane dai-dai ka sa lambar wayar naka? Idan ba dai dai bane, sai ka danna edit, domin gyarawa, idan kuma dai-dai ne sai ka danna ok, zakaga yakawoka wani shafi inda zaka sanya wasu code, zakaga an turo maka message ta wayarka, to sai kaduba kayi copy na code din da suka turo maka, da zaran ka sanyasu zakaga wayar naka takama yin verify, sai ka dan jirata na dan wani lokaci, bayan ta gama verifying din, zakaga ta nuna maka wani shafi , sai ka danna "Continue" bayan ka danna, zakaga ya kawo ka wani shafi tare da wasu rubutu sai ka danna "Allow" bayan ka danna zakaga ya kara nuna maka wani shafin tare da wasu rubutu, shima sai ka danna "Allow" Bayan kagama budewa zakaga ya kawo ka wani shafi tare da gurin da zaka cike:
Na farko shine gurin da zaka sanya sunan ka , to anan gurin ne zaka sanya sunan kasuwancinka, sannan kuma a kiyaye saboda idan ka sanya sunan kasuwancin naka to babu yanda zakayi ka canza, saboda haka ka sanya suna wanda ka tabbatar cewa shine sunan kasuwancin naka,
Sannan kuma idan ka duba kasan gurin zakaga inda zaka zabi "category"  idan kashiga anan ne zaka zaba sunan wani kalan abubuwa ne zakayi kasuwanci akan shi, to sai ka zabi bangaren naka kasuwancin
Misali: bangaren kayane, ko bangaren mutane, ko bangaren labarai ne, ko kuma bangaren ilimi ne, duk zaka gansu sai ka zabi naka bangaren.
Sannan kuma acikin shafin idan ka duba sama zakaga waje sanya hoto, to anan ne zaka sanya hotonka, amma a lura wajen sanya hoton, saboda ba kowani irin hotone ake sanyawa s ciki ba, a'a shi wannan hoton abin da zakayi kasuwancin ka ne a ciki zaka sanya, Misali: idan ina sayar da takalma ne, to hoton takalmar zan sanya , ko kuma idan ina sayar da riguna ne to hoton riguna zan sanya a ciki, to duk bayan ka kammala wadannan sai ka danna "Next", bayan ka danna zakaga yakawoka wani shafi kamar haka
Zakaga yanuna maka iri daya da asalin whastapp dinka, zakaga komai-da-komai irin na asalin whatsapp dinka ne, amma wajen ban-bancin wuri daya ne, saboda idan ka duba hoton da kyau zaka wani guri inda aka rubuta "Describe your business" to sai ka danna gurin, bayan ka danna zakaga ya nuna maka wani shafi kamar haka 

Yawwa kunga a nan shine profile dina na whatsapp business, amma zakuga ni ban saka hoton kasuwanci na ba, amma akowani lokaci zan iya sawa, sannan sai na biyu zakuga ya nuna sunan kasuwancina, sai kuma na uku, wato number whatsapp business dina kenan, sai kuma na hudu wato "Business adress" shikuma anan ne zaka sanya "business address" dinka, misali : kaduna, zaria da sauransu
Sannan kuma sai ka dan kara yin kasa kadan zakaga ya nuno maka kamar yanda kukaga hoton sama, wato akwai location

Location
Wato wajen location anan ne zaka zabi location dinka, na wurin da kake
Kaga duk lokacin da mutum ya shigo , "profile" dinka kai tsaye zai san inda kake ba tare da yasha wani wahala ba, kaga da zaran ya duba "profile" dinka bazai sha wahalar yin bincike ba , kai tsaye zai iya zuwa shagon ka, ko kuma wurin da kake yin kasuwanci, idan ka danna "Set location on map" zai kaika "google map" ne, sai ka zabi gurin da kake, bayan ka zaba, sannan sai ka danyi kasa kadan, zakaga inda aka rubuta "Description"

Description
Shikuma description ananne zakayi dan rubutu game da abinda ya shafi kasuwancinka , (wani business ne kakeyi, menene kake sayarwa da dai sauransu )
Misali: zaka iya cewa "muna sayar da wayoyi kala-kala, sannan kuma duk wanda ya sayi waya a hannun mu to zamu kawo mashi har gida"
Atakaice dai ina nufin ka sanya bayanai game da kasuwancinka, bayan ka gama sai ka duba kasan , zakaga gurin da aka rubuta "Business hours"


Karanta wannan: Yadda za kasa password wa applications dake kan wayar ka
How computer is working?
Yadda ake kirkiran android application na Gallery da wayar android
Yadda zaka bude Email address a 2020 (Google account)
Website guda 11 wadanda zaka samu hotuna kyauta don dorawa a blog site


Business hours
Shikuma business hours anan ne zaka saita ranaku da kuma lokutan da za'a dinga samun ka, idan ka shiga ciki, zakaga inda aka rubuta "Schedule" to bayan ka danna gurin zakaga ya nuna maka kamar yanda yake a wannan hoton

Abu na farko shine "open for selected hours"
Misali daga karfe 12:00pm na rana zuwa karfe 06:00pm kake yin aiki, sannan kuma zata iya yiwuwa ba kowace rana kake yin aikin ba, to idan ka shiga "Open for selected Hours" anan ne zaka zabi ranaku da customer dinka zasu iya samunka , misali: idan kowani lokacine sai kayi selected dinsu duka, idan kuma ba kowani lokaci bane sai kayi selected din ranakun tare da lokaci, sannan bayan ka gama wannan zakayi "back" bayan kayi back zakaga ya nuna maka ranakun aikin ka da kayi selected dinsu, kamar haka

Email
Shikuma email, ananne zaka sanya "email" dinka, yanda mutum zai tura maka sako kai tsaye ta email dinka.
Website
Shikuma website, anan ne zaka sanya website dinka, idan kana dashi,
Bayan ka kammala, to sai ka danna "Save", duka zai yi maka saving na duka bayanan daka sanya , sannan zakaga ya dawo da kai whatsapp dinka, kamar haka
Bayan ya dawo da kai whatsapp dinka, kamar dai yanda kuka gani a hoton da yake sama, idan ka lura zakaga wata sarqa a sama bangaren dama, sai ka taba gurin, bayan ka taba gurin zai nuna maka kamar haka
Bayan ya nuna maka haka, zakaga gurin da aka rubuta labels, sai ka danna gurin, bayan ka danna zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka
Sai ka danna gurin da aka rubuta business setting
Bayan ka danna gurin, shima zakaga yakawoka wani shafi kamar haka
To shikuma wannan ananne zaka saita bangaren message da sauransu, sai ka danyi kasa kadan
Kamar dai yan kuka gani a wannan hoton, gasu kamar haka

Business profile
Idan ka shiga business profile to ananne zakaga profile dinka,

Statistics
Shikuma statistics idan kashiga ananne zakaga message din da ka tura, da kuma wanda aka turo maka, da kuma message din da aka karanta.

Short link
Shikuma short link shine link din da zai taimaka wa mutane wajen basu link address dinka, a mai-makon ka dinga rubuta lambar wayar ka, kana bawa mutane, kawai zaka sanya link dinka ne, tanan zasu biyoka kai tsaye,

Default message
Shikuma default message, anan ne zaka rubuta wani sako, yanda duk wanda ya shigo wannan link din naka zai gani, sannan bayan ka sanyashi, sai ka dawo baya, a kasan gurin zakaga bangaren message



Karanta wannan: Yadda ake samun kudi ta facebook cikin sauki
Kowa zai iya zama blogger?
Idan na chanja template adsense dina zai samu matsala?
Yadda zaka kirkiri android application na Wall paper da wayarka


Away message
Shi away message,  zaka iya shiga ka kunna shi, idan ka danna open to duk wanda ya shiga ya turo maka sako, to idan baka a kusa, to wannan sakon daka rubutu shine zai gani, Misali: zaka iya rubuta "Yi haku a halin yanzu bamu a kusa, amma da zaran mungani zamu sanar da kai, ko kuma zamu baka amsarka" sai kayi saving dinshi

Greeting message:
Shikuma greeting message shine message na godiya, sannan idan wannan bai maka ba sai ka duba kasan gurin

Quick message
Shima quick message, zaka rubutunshi da turanci akayi, amma zaka iya canzawa zuwa harshen hausa.

Duk bayan ka gama sai kayi saving dinshi, to sai ka dawo baya, shikenan ka gama saita profile dinka, daga yanzu duk wanda ya shiga profile dinka a maimakon ya ga lambar wayya sai yaga wadannan abubuwan da ka sanya a profile din naka.


Bayan kayi duk abubuwan da na fada sai ka dawo whatsapp dinka kamar haka

Bayan ka dawo whatsapp dinka kamar yanda kuka gani a hoton dake sama, to zakuga wani alamar sarqa ta bangaren dama, sai ku sake dannashi bayan ka danna, zakaga ya nuna maka kamar haka

Bayan ya nuna maku kamar yanda kuka gani a hoton da yake sama, zakuga gurin da aka rubuta labels, sai ku dannashi, bayan ka danna, zakaga ya nuna maka Labels kala-kala,
1. New costomer
2. New order
3. Pending payment
4. Paid
5. Order complete

To sukuma waddannan gurine wanda zasu riqa tan-tance maka , sannan kuma idan wadannan labels din basuyi maka ba zaka iya kir-kiran label dinka, kuma zaka iya sanya "Siyayya" da dai sauransu, abindai da ake nufi da wadannan sune zasu tan-tancemaka : misali akwai wanda ya biyaka kudi amma baka bashi kayanshi ba, to sai ka sanyashi a inda ya dace.

Karanta wannan: Yadda ake whatsapp guda biyu a waya daya

Wannan shine hanyar da zskabi domin yin kasuwancika ta whatsapp, da fatan kuna jim dadin kasancewa da wannan shafi mai albarka, idan baka gane wani abu ba game da wannan darasin sai kayi mana comment a kasan wannan posting din, mungode


Facebook: Yi like a shafinmu na facebook

Whatsapp: Zaka iya biyomu ta whatsapp


Twitter: Yi following dinmu ta witter

Instagram: Yi following dinmu ta instagram

Call & message: 09036117711

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: [whatsapp business] Yadda ake kasuwanci ta whatsapp cikin sauki
[whatsapp business] Yadda ake kasuwanci ta whatsapp cikin sauki
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjiQHy7SafrPxGgfV1Hj0xyRbnw7CrjLmz-IyNgdPAFjk9KDN8XYk7_jWrzahTwpHhkun5ayddU4h6-2MUl2ZSn4mYbWg_klTZREISZgJNdardPiNsKil53OaLXrKid4XHR8Zpo8nJV-nw/s320/whatsapp+b.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjiQHy7SafrPxGgfV1Hj0xyRbnw7CrjLmz-IyNgdPAFjk9KDN8XYk7_jWrzahTwpHhkun5ayddU4h6-2MUl2ZSn4mYbWg_klTZREISZgJNdardPiNsKil53OaLXrKid4XHR8Zpo8nJV-nw/s72-c/whatsapp+b.jpg
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2020/01/whatsapp-business-yadda-ake-kasuwanci.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2020/01/whatsapp-business-yadda-ake-kasuwanci.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content