Assalamualaikum , barkanmu da warhaka, dafatan kowa yana lafiya, Darasin mu na yau shine zamuyi darasin ne akan abubuwan da yakamata kayi b...
Assalamualaikum , barkanmu da warhaka, dafatan kowa yana lafiya, Darasin mu na yau shine zamuyi darasin ne akan abubuwan da yakamata kayi bayan ka mallaki website naka na kanka, akwai abubuwa masu matuƙar muhimmanci da yakamata duk wani wanda ya mallaki website ya fara kula dasu kafin ya fara aiwatar da wani abu acikin sa, saboda waɗannan abubuwa yana da matukar amfani ka sansa, saboda indai har mutum ya tsayar da tunanin shi waje guda sannan kuma yayi nazari, to lallai ya kamata yayi nazari akan su, to matuƙar yayi haka, to agaskiya zai matuƙar wahala kaga wannan website ɗin nashi bai fice a idon duniya ba.
Saboda rashin maida hankali wajen kulawa da waɗannan abubuwa sune suke sawa kaga website yaƙi yin wani tasiri.
Ga abubuwan da yakamata kayi kamar haka:
1. Menene dalilin da yasa na mallaki website?
2. Wani abune zaka riƙa sanyawa a cikin website ɗinka?
Matuƙar ka tsaya ka natsu ka karanta waɗannan abubuwa guda biyu da zamuyi bayanin su, to insha Allahu ba tare da wata matsala ba zaka iya ƙir-ƙiran website ɗinka, kuma ka samu riba dashi.
1. Menene dalilin da yasa na mallaki website?
Wannan dai tambayace mai matuƙar muhimmanci, da yakamata ka fara sani a matsayinka na wanda ka mallaki website, domin indai har zaka iya samar da amsar da ta dace game da wannan tambayar, to gaskiya zai yi wuya kaga mutum bai cimma nasara akan website ɗinshi ba.
Dalilin wannan tambayar saboda akwai wasu mutane sai kaga sun buÉ—e website nasu na kansu, sai kaga bayan sun buÉ—e, sai kaga sun fara yin tunanin cewa to menene zan sanya acikin website É—in?
Kai! a taƙaicema idan mutum ya rasa gane abubuwan da zai sanya, sai kaga mutum ya kama wallafa rubutun siyasa ko na free Browsing ko kuma rubutun labaran ƙwallo da dai sauransu, to matukar ka kama irin waɗannan rubutun, to daga karshe ma zaka rasa abubuwan da zakayi aciki, kuma a dalilin hakane duk wasu masu shiguwa shafinka to zasu daina shiguwa, kai kuma zakaga to meye amfanin shima, kawai daga karshe dai zaka rabu dashine kawai gaba daya.
Read more: Abubuwa uku da zakayi kafin ka nemi apply na adsense
Yadda zaka bude email adress cikin sauki
Read more: Abubuwa uku da zakayi kafin ka nemi apply na adsense
Yadda zaka bude email adress cikin sauki
2. Wani abune zaka rika sanyawa a cikin website dinka?
Lallai shima wannan tunani ne mai matukar muhimmanci, wanda ace yakamata kayi wannan tinani kafin ka bude website, domin kuwa bazai yiwu ace ka bude website amma baka san abubuwan da zaka rika sanyawa a ciki ba, sannan kuma ba zai yiwu ka bude website ka riƙa sanya abubuwa daban-daban a cikinsa ba, yakamata kayi nazari akan abubuwan da mutane zasu riƙa sha'awar shi, Sannan kuma ya kasance abubuwan da kake yi acikin shi zaiyi masu amfani, Sannan kuma ka tabbata duk wani abu da zaka wallafa shi a website dinka, ka tabbata kayi nazari akansa, ka tabbata kana da cikakkiyar masaniya akan shi, saboda ba zai taba yiwuwa ba wanda yake kallon kwallo yace zai bude website na yanda za'a riƙa samun kudi aciki ba, bugu da kari ya zamana duk lokacin da zakayi rubutu akan abu kanada masaniya sosai-sosai, kuma kayiwa mutane bayani dalla-dalla ta yanda indai sun karanta, to zasuyi na'am da wannan abun daka rubuta.
Matukar ka kiyaye wadannan abubuwa da kaga na lissafo to babu matsala zaka iya kir-kiran website dinka, ba tare da wani matsala ba, kuma zaka dinga samun traffic lokaci-lokaci, sannan kuma zakaga shafinka yayi farin jini a idon duniya.
Da fatan za'a kiyaye waÉ—annan bayanai kafin mallakan website.
Don neman karin bayani sai kayi mana a comment. Mungode
Facebook: Yi Like a shafinmu na facebook
Whatsapp: Zaka iya biyomu ta whatsapp
Twitter: YI FOLLOWING DINMU TA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU TA INSTAGRAM
Call & message: +2349036117711
Facebook: Yi Like a shafinmu na facebook
Whatsapp: Zaka iya biyomu ta whatsapp
Twitter: YI FOLLOWING DINMU TA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU TA INSTAGRAM
Call & message: +2349036117711
COMMENTS