Furar Danko 70

  𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲   🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣0️⃣.......Zaune take a falo dafe da kanta dake matuƙar sara mata saboda ɓacin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta ɗauke da tunanin sake kiran Daddy ɗin kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya ɗagawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya ƙwace mata. Ƙaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “My Daughter yau babu gaisuwa ne?”.

        Nan ma shiru ta kasa magana. Tofa yasan an kai ƙololuwar ɓacin rai kenan, dan haka ya sake tausasa harshe cikin komawa serious ya ce, “Mawaddat miya faru? Ko baki da lafiya ne?”.

             Hawayen da take riƙewa ne tun ɗazun suka kufce mata, da rawar murya irin ta mai kuka ta ce, “Papa bazan iya ba, bana son damuwa gida zan dawo. Wannan ba rayuwan da zan iya yi bane...”

     “Kwantar da hankalinki sanarmin mike faruwa?” ya faɗa like bai san komai akai ba. Da ƙyar ta iya masa bayanin abinda ya farun kamar yanda Daddy ya sanar masa. Anan ɗin ma murmushi ya sake yi ɓoyayye. Kafin ya ce, “Mawaddat rayuwar aure haka take, a komai ita mace ƙarƙashin ikon mijinta ta ke, wajib ne kuma yimasa biyayya in har shima bai keta dokar UBANGIJI ba ko jagorantar ta saɓa masa. Anan kam ba'a yarda ta masa biyayya ba sam, dan ba'ama wani biyayya ko tarayya wajen saɓama ALLAH......”

         “Bazai yiwu ba Uncle You, domin ni da kai da shi duk mun san matsayin wannan zaman ba sunansa aure ba, Please Uncle kace masa ya sakeni idan ma bazai yi haka a yau ba zan dawo gida idan kwanakin da akai yarjejeniyar sun cika ya sakenin, zan iya ɗaukar komai amma banda kan aiki na, domin shine rayuwata, shine farin ciki na, shine mafarkina, shine babban burina tun kafin nasan kaina, shi waye da rana tsaka zai datse hakan da tunanin nuna gadara ko ƙarfin ikon abinda bashi da ikon!”.

       “Mawaddat aure kona kwana ɗaya ne sunansa aure, da auren nan baida kimar da za'a kirasa ko kwallonsa da wannan martabar da muhimman mutane basu taru cikin shigar kamala domin ɗaurashi ba. Da wasu mutane basu ajiye muhimman ayyukansu ba domin halartarsa. Ki kwantar da hankalinki komai ya tafi cikin tsarin da muke fatansa, Aliyu kuma zanyi magana da shi duk da nasan shima ba son hanaki aikinki yake gaba ɗaya ba tunda ya sanar miki next week zakiyu resuming be a good girl mana sweetheart, maybe ma yana tsokanarki ne dan yaga yaya zakiyi. Dan haka ina son ki zama jaruma mana kamar yanda ya sanki.....”

        “Amma Uncle fitan yanada muhimmanci fa yau. Kasan inada case ɗin yarinya da ke aibiti, tun juya kuma ya kamata naje na shigar da case ɗin court”.

      “Kar ki damu indai wannan ne yanzu zan fita ni zanje da maman yarinyar mu shigar da ƙaran, ke kuma sai ki cigaba da shirinki matsayinki na lawyer ɗin nata hakan yay miki ko?”.

            A hankali ta ce, “Eh”.

       “Yauwa ɗiyar albarka na. Ki daure kinji, kar Aliyu ya samu na tsokanarki, bamma so ki bari yaga hawayen nan, maza ki sharesu ki zauna kurum kamar ba'ai komai ba Kinga kinyi winning”.  

    Ta gamsu da zancen nasa ɗari bisa ɗari, dan dolene itama ta mannama velleger ɗin can haukan da sai ya gagara barci a yau. Da ga haka ta miƙe bayan sunyi sallama da Uncle Yousuf da ke dariya daga can ta nufi bedroom. Fuskarta taje ta wanko da canja kayanta zuwa wando da riga marasa nauyi na zaman gida, ta sake dawowa falon ɗauke da laptop ɗinta. Dai-dai nan ya fito shima, alamunsa sun nuna yay wanka dan sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsarsa sai ƙamshinsa mai sanyi da ke tashi. Zaune ya kai idonsa a kanta sai dai fuskarsa babu walwala, duk da taji motsin nasa ko sau ɗaya bata nuna alamar hakan ba balle ta ɗago, lap-top ɗinta kawai take ƙoƙarin kunnawa. Shi kuma sai ya tsira mata idanun nan nasa na macizai da take kira, ƙin ɗagowar tata bai hanata jin kaifin idanun nasa a kanta ba, amma ta dake ta cigaba da abinda take yi. 

        “Break fast fa?”.

     Ya faɗa a dake still dai idanun nasa a kanta. idan kujerar da ya ke zaune ta motsa to itama ta motsa. Cije lips ɗinsa yay yana wani sake ƙanƙance idanunsa a kanta. Kusan minti ɗaya yana kallon nata kafin ya miƙe tsam zuwa inda ta ke, lap-top ɗin ya ɗauke da ga jikinta ya ajiye gefe, karon farko ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka kaɗa saboda kukan da tayi, fuskarta na nuna matuƙa ranta a ɓace. Nunawa yay kamar baiga kallon da take masan ba, kafin ta furta abinda ke bakin nata ya kwasheta gaba ɗayanta a cikin hannunsa yayi sama da ita kamar wata ƴar baby, (🤣dama abu ba abu ba sai masifa). 

         “Bana son wulaƙanci malam miye haka? Dalla sauke ni”. Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai tana kai masa ƙananun duka a ƙirji, amma ko gezau kansa tsaye ya nufi hanyar kitchen da ita, saman cabinet ya direta, ya juya ya sakama ƙofar key. Dai-dai ita kuma tana dirowa da ga inda ya ɗauratan ta iso ga ƙofar. Wani shegen kallo ta watsa masa da faɗin, “Matsa min”.

    “Idan kinyi abinda nace kenan”.

Ya faɗa cikin halin ko'in kula yana saka key ɗin cikin aljihun wandonsa da jingina da ƙofar yana mai harɗe ƙafafunsa waje guda. Ƙarshen ɓacin rai Lulu ta gama kaiwa, dan haka cikin kaushin murya ta ce, “Kasan na iya fiye da abinda kake tunanin ka'iya na rashin mutunci ko. Aliyu! Ka buɗe ƙofar nan ka bani hanya na wuce kafin na saka dana sanin sani na”.

          Jikin ƙofar ya bari da ɗan taɓe baki batare da yace komai ba ya nufi frizzier ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe, sai da ya ƙarema kayan ciki kallo sannan ya rufe ya nufi store. Daga sama har ƙasa yake bin store ɗin da aka tsatstsage da kayan abinci kala da iri da kallo shima, har da su doya da airish da ruwa da kayan miya da akaima ajiya irin wadda bazasuyi saurin lalacewa ba. Shi sai abin ma ya so bashi mamaki da dariya, to su da suka jibge waɗan nan kayan matar gidan ta iya abinci ne?....

      Shigowar Lulu a fusace ya saka tunaninsa yankewa, ya juyo gaba ɗayansa yana dubanta, huci take sosai idanunta sun juye gaba ɗaya har wani tara ƙwallan masifa sukeyi. Gashi yanda yaga sun ɗan kumburo tun ɗazun ya fahimci kuka tayi, yaji ba daɗi a ransa, dan sam baya son ganin wani ya shiga damuwa a dalilinsa, sai dai dolene yay abinda yayin dan ya fahimtar da ita da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu komai sai da izini... Da sauri ya dubeta jin tana ƙoƙarin saka hannu a aljihunsa alamar son zaro key. Hannun nata ya riƙe yana ɗan waro idanu waje, duk yanda taso fisgewa bai sakar mata ba sai da ya zare key ɗin da ga aljihun nasa, sai kawai ya maƙalashi jikin belt ɗinsa ta inda yasan bazata ce zata ɗauka ɗin ba yana sakin wani shegen murmushin mugunta. Da sauri ta ɗauke kanta da ga dubansa gaba ɗaya tana jin kamar ta fasa ihu, a zuciyarta kuwa tace (ɗan iska). 

        “Yanzu mi zaki dafa mana? Dan yunwa nake ji nikam ga shi nace su Ammah kar su ƙara aiko abinci injiki.”

     Harara ta watsa masa cikin gatsali ta ce,  “Ashe zaka mutu da yunwa kuwa a gidan nan”.

             “Zadai mu mutu, dan kema dai duk tsiya dole ki nema ai. A yanzu ma haka idan kina son fita da ga kitchen ɗin nan ki nema mana abinci, inba hakaba ALLAH anan zamu yini”. Ya ƙare maganar yana fitowa da ga store ɗin. Ɗaya da ga cikin kujeru huɗun da aka sakama table a tsakkiya yaja ya zauna. Hankalinsa kwance ya jawo wayar ya fara buga game ɗin ball, ya kuma ƙure ƙarar yanda ta cika kitchen ɗin da hayaniya. Lulu data gagara fitowa a store kanta ta dafe, sai faman haɗiyar rai take zuciyarta na ƙuna. Ta rasa yaushe ne guy ɗin nan yay mata irin wannan rainin har haka, bata taɓa haɗuwa da mutumin da ke latsata a yanda yake so da gadararsa irinsa ba, ya bala'i bala'in shigar mata hanci da yawa. Gadararsa da son nuna shi ɗin wani ne da iya taurin kai na cimata zuciya. Fitowa tai a bisa shawarar da zuciyarta ta bata, ta cije lips ɗinta tana jin kamar idan ta ƙarasa garesa ta shaƙesa kawai, amma sai ta ture tunanin gefe. Kujerar dake kallon wadda yake zaune ta dafa cikin ɗan sassauta zafinta dan ta fahimci ihun da take masan kamar tunzurashi yake da jin daɗin latsata. “Aliyu kafa san aiki nakeyi ka ɗakkoni ka kawo nan, kai miyasa baka bambance lokacin shiririta dana serious?”. 

        Batare da ya ɗago ya kalleta ba hankalinsa ma akan game ɗin sa ya ce, “Yima mijinki girki ne ba serious ba?”.

     “Kai kasan mijin ma, Ka bani key na wuce, idan abincin kake so ai kasan gidan abinci, dan in har abinda zan girka zakaci ka siyama kanka wahala dan ban iya ba ma sai kabi wani sarkin”.

       “Hummm ashe kuwa in dai ba zakiyi abinda nake so ba kuma ya dace ga matar aure to aikin ma zai gagareki yi ne, duk da a farko banda wannan niyyar. Dan haka kina da zaɓi kenan, yin yanda nake so kuma na tsara a gidana, ki samu yanda kike so kema. Ko ƙin yi, kema ki ƙi samu. Abinci kuma duk yanda kika iya kiyi zanci a hakan ko baiyi ba”.

            Luuuu tai da idanunta kamar zata lumshe su sai kuma ta buɗe, komai ma ya gundireta, tama rasa yaya zatai da mutumin nan mai shegen taurin kai da gadara. Wai miyasa ma ta amince ne da wannan tsarin da shi? Miyasa bata bada damar a nema wani ba?. Tsaki taja mai ƙarfi da kai hannu ta dafe kanta, sai kuma ta janye tana mai watsa masa hararar zaka banbance tsakanin aya da tsakkuwa ta bar wajen. Da kallo ya ɗan bita ganin ta nufi hanyar store, tana shiga yay mata gwalo da sakin murmushi nan nasa da take kira na mugunta yana kashe ido ɗaya a hankali ya ce, “2-0 Madam”........✍️

     _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

COMMENTS

Name

ADSENSE,4,Airtel,1,ANDROID,9,AQIDARMU Book 1 Complete Hausa Novel,1,AQIDARMU Book 2 Complete Hausa Novel,1,Arbitrade,4,Arbitrage,1,AUREN MU Complete Hausa Novel,1,Babban Yaya Hausa Novel Complete,1,Babu So Complete Hausa Novel,1,Bakar Inuwa Complete Hausa Novel,27,Billyn Abdul Novels,7,BLOGGING,13,Business online,10,Crypto currency,17,Dare Daya Hausa Novel Complete,1,Daudar Gora Book 1 Complete Hausa Novel,48,Daudar Gora Book 2 Complete Hausa Novel,95,DOWNLOAD,2,Duk Karfin Izzata Book 2 Complete Hausa Novel,34,Education,3,Email,1,Facebook,4,Finance,1,Furar Danko Book 2 Complete,9,Furar Danko Complete Hausa Novel,31,fyade hausa novel by maman teddy,1,fyade hausa novel Complete,1,Gidan Haya Hausa Novel Complete,6,Gidan Haya Complete Hausa Novel,4,Gidan Haya Hausa Novel,1,Gidan Kwarata Complete Hausa Novel,1,Glo,1,Google,1,GURBIN IDO Complete Hausa Novel,1,Hamshakiya Hausa Novel Complete,25,JARABABBEN NAMIJI Complete Hausa Novel,1,Jikar Maguzawa Complete Hausa Novel,23,Job,7,KASUWANCI NA Complete Hausa Novel,1,Layikan waya,2,Loan,8,MA'AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel,1,Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel,70,Mufeedah Complete Hausa Novel,25,Namijin Zuma Complete Hausa Novel,26,nihaad complete,62,Nihaad Complete Hausa Novel,62,nihaad hausa novel,62,Npower,13,Pc Tools,2,Qamshi Hausa Novel Complete,14,Raina Kama Complete Hausa Novel,29,Sakayyah Book 2 Hausa Novel Complete,30,Sakayyah Hausa Novel Complete,60,SHAKUWAR YARINTA COMPLETE HAUSA NOVEL,20,Support,26,Tabarmar Kashi book 2,7,Teach and guide,8,TUMFAFIYA Complete Hausa Novel,1,TUMFAFIYA Hausa Novel,50,TUMFAFIYA Hausa Novel Complete,19,UNCLE DATTI Hausa Novel Complete,1,Watsapp,3,Waye Mijina Hausa Novel Complete,5,WEB LANGUAGE,1,WEB TUTORIAL,2,Yar Aikin Karuwai Book 1 Complete,1,Yar Aikin Karuwai Book 2,1,Yar Aikin Karuwai Hausa Novel,1,Yaya Mata Complete Hausa Novel,22,Zafafa Biyar Novels,7,
ltr
item
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||: Furar Danko 70
Furar Danko 70
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEizJW5XsvjyBQuQvHgZMToahTwMKekaTGa4yQ0TVduuAktjSLdqCHisobr7UX5-6Z_J1yrq4osfp5eJCDPDdHfyOdgV_IiIxFSf8K-EmnOE0yZknSMoHsksEaaXe8mPcw-f6RFEg2VTEHUBpHXLPs8qkuFiWLMIH9gO8hR4gXMeW3xcMi494dc82oUeK486/s320/img_1696029890866.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEizJW5XsvjyBQuQvHgZMToahTwMKekaTGa4yQ0TVduuAktjSLdqCHisobr7UX5-6Z_J1yrq4osfp5eJCDPDdHfyOdgV_IiIxFSf8K-EmnOE0yZknSMoHsksEaaXe8mPcw-f6RFEg2VTEHUBpHXLPs8qkuFiWLMIH9gO8hR4gXMeW3xcMi494dc82oUeK486/s72-c/img_1696029890866.jpg
NAGARTA24 || job || npower || crypto currency || arbitrade || loan || teach and guide || support ||
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-70.html
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/
https://www.nagarta24.com.ng/2023/10/furar-danko-70.html
true
1779421581242976301
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content